Showing 48001 words to 51000 words out of 181864 words
zaman Almamoon a cikin gidan nan ko? Wallahi idan wani abu ya same shi. Sai na kashe wancan Mahaukacin"
Dukar da aka kai mishi a baya yasa shi sake Malik.
"Kyale shi Fahad, ba laifin shi bane yana da iko da Almamoon."
.wayar shi ya ciro tare da kiran dan Ba'are ya tambaye shi suna ina ga kakan Almamoon tazo ganin shi. Yana gaya mishi asibitin ya gayawa Ansar.
Shima yayi amfani da kalmar kaka ce saboda yasan idan suka ji haka zasu bar shi ganin Almamoon. Yana gaya mishi sunan asibitin ya shiga motar shi da sauri, ya bar gidan kamar zararre, dama kuma ai zararren ne (🙄🤸😁🤣)
Koda ya iso asibitin, dakyar ya sami dakin da aka kwantar da Almamoon bayan ya gama shan bakar wahala, yana shiga ya kura mishi ido, yana mai da numfashin sa, tare da goge gumin goshin sa, kafin ya kalli dan Ba'are, kasa mishi tijara yayi domin irin karfaffan mazan nan ne, da shi da Mohan fadi kawai Mohan zai nuna mishi da cikar halittar jiki irinta mazan da suke daukar karfe. Idan Mohan ya saka mata matukar ta kama shi idan zai d'aga hannun, toh rigar zata iya darewa, sabida tarin kwanjin shi.
Takowa yayi tare da kai hannun shi zai dauki Almamoon, yaji an rike hannun. Tare da mai dashi baya, sake kai hannu yayi zai dauki Almamoon, ran Dan Ba'are ya b'aci dunkule hannun yayi zai sauke mishi naushi Nurse ta shigo.
"Nazo duba mara lafiyar ne zamu mishi allura"
Sauke hannun shi yayi yana kallon Almamoon, Nurse tana gama abinda zata yi ta fita, wani azazzaben dambe ya kaure a tsakanin su, karan buge buge ya farkar dani.
Kallon su nake kafin na tashi dakyar. Na nufe su tare da riko malam Ansar. Bakina yayi nauyi ina son nayi magana amma na kasa, dakyar na koma bayan shi na rungume shi. Tare da zaga hannuna kirjin shi.
"Ya isa Hammah ANSAR" na fada a hankali, kamar ba zan iya magana ba, cak ya tsaya kamar an zare mishi duk wata kusarin shi. Ji yaƙe kamar tunda yake ba a tab'a kiran shi da suna Yaya ba, baki daya gwiwar shi tayi sanyi sama da kullum. Yau shi Almamoon ya kira Hammah ko mafarki yake ne?
Anya ba mafarki yake ba? Indai da gaske ne shi Hammah ANSAR ne, toh tabbas Almamoon yana rungume dashi kenan. Wani bahagon naushi Dan Ba'are ya kai mishi. A fuskar shi sai da ya kufa a kasa, tare muka fadi.
"Almamoon rabu da munafuki" inji Dan Ba'are,
"Hammah Khalil! Ka daina dukar shi, bana jin dadin haka." Na shiga tsakanin su. Muna kallon juna. Tafiya nayi luuuu zan fadi suka tare ni dukkan su biyu, ɗauka ta suka yi tare da mai dani gadon, suna kallon fuskana. Lumshe idanun nake ina kuma buɗe shi.
"Ya Hammah Mohan yake?" Na tambaye su a gajiye, gyara kwanciya na suka yi sannan Dan Ba'are yace min.
"Ana ta lafiyar ka waye yake ta Mohan?"
Sam ban ji dadin abinda ya faɗa ba, dan haka na tashi zaune.
"Zanje naga halin da yake ciki"
"Baka isa ba, wallahi sai na falla maka mari, kuma mun zo da Baba Mari ne"
Komawa nayi na kwanta, haka ya fita can sai gasu tare sun shigo d'akin, suna shigowa dan Ba'are yana fita.
"Sannun kaji, Allah ya baka lafiya ashe baka da lafiya ne"
Gyada mata kai nayi ina jin kwalla na cika min idanuna, shafa kaina tayi tare da cewa.
"Zan zauna da kai kaji"
Gyada mata kai nayi, muna cikin haka Malik ya shigo tare da kallona.
Murmushi ya sakar min, na maida mishi nima.
"Ya jikin naka?"
"Da sauki"
"Allah ya baka lafiya"
"Amin Ya Allah, ina ka baro Hammah Mohan? Kasan bai da lafiya kake barin shi babu wani a kusa dashi? Kasan yadda rayuwar shi take cikin hatsari ka bar shi shi daya a gidan? Ku mai dani gidan kawai nayi jinyar a can"
"Ba zaka kuma komawa gidan ba, domin ina kaunar ka" juyawa nayi na kalli Malam Ansar.
"Ba zaka tab'a samun yadda kake so ba,dan haka babu ruwanka dani."
"Kayi hakuri dama nazo duba halin da kake ciki ne, kuma Alhamdulillahi, zan koma domin na bar Fahad a jikin shi."
Gyada mishi kai nayi, tare murmushi.
Haka ya tafi ba tare da na yarda mun kuma magana ba, sabida bana son yadda yake kallona.
Hankalin su Baba Mari da Hammah ANSAR ne ya dawo kai na.
"Baba Kinga shi taurin kan bala'i ce dashi dan haka ki saka baki mu koma gida dashi."
"Hmm" na fada ban kuma magana ba sai ga Dan Ba'are da manyan ledojin shi guda uku, ya ajiye min.
"Sannun bawan Allah Ubangiji ya saka da Alkhairi, Sannun da tallafan rayuwar shi mun gode"
Cikin wani irin murmushi yake kallon mu, irin yayi katon bajinta. Dariya ya bani irin wanda ake yin shi a cikin rai haka, na kalle shi nayi murmushi. Zuba hannu Yayi a cikin aljuhun wandon shi yana kallona. Janye idanuna nayi daga kanshi ina kallon Malam Ansar da ya cika ya batse.
"Hammah Khalil ka tafi ka duba halin da Hammah Mohan yake ciki kaji"
"Toh babu damuwa, duk yadda kace haka zamu yi, Baba sai an jima. Kai kuma be careful" ya saka kai ya fice daga d'akin.
"Baba kin gani ko? Hidima suke mishi waye ya sani ko wani abu ne yake shiga..."
Fisge ruwan hannu na, nayi tare da sauka a gadon na shiga tura shi har kofar dakin, ina kai shi gurin na ce mishi.
"Kar na kuma ganin ka a nan idan ba haka ba hmm"
Na nuna mishi hanya tare da banke kofar..
"Mamoon,.kayi hakuri nasan babu dad'i."
"Baba kina ji yana zargina shi din waye shi? Meye na tsare mishi da yake zargina? Ina dalili zai saka Ni a gaba"
"Kayi hakuri" haka tayi ta rarrashinsa, dakyar yayi hakuri, sannan ya shiga ban daki yayi alola da wanka ya fito, tare da gabatar da sallah.
Yana idarwa ya zauna yana kallon kayan da Dan Ba'are ya kawo shi. Flast da ruwan zafi. Sai kayan ciye ciye.
Haka na zauna na ci kadan sauran na turawa baba. Tana ci tana kallona.
"Me yasa meka?"
Kasa magana nayi tare da kasa kallonta.
"Ina tambayar ka? Kasan jikinka ba karfi ne dashi ba, kai asalima baka da nau'in karfin maza, don Allah ka daina saka kanka cikin kasada kaji, ka daina cilla rayuwar ka cikin damuwa, malam Ansar yana da laifi gurin sakawa lallai sai kayi abu dole amma ka tab'a bibiyar me yasa yake maka haka? Sabida yana kaunarka gani yake baka cancanci zama a inda za a tab'a lafiyar ka ba. Don Allah karka tab'a min zuciya, wanda aka yi na shekaru sha ma bai warke ba, idan wani abu ya same ka ba zan tab'a yafewa kai na ba.[7/15, 4:04 PM] RamlatArManga: https://www.wattpad.com/1099611906?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=B2xbg56NQ%2Bj7itiadIMLq5S6mXv9S%2FsKyYdkh0H8PJKgwqgLqD%2Fo961ZM5LierkVHLwx3qEwMnG%2BOkvdE6rc9D1tbKk2fSwjLb0oWove1cVKshUkIo7LVOxrft0MhTCk
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
_*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
Domin samun labarin masu kayatarwa na Hausa danna Link din nan a sha sauraro lafiya....
BABI NA SHA BAKWAI.
Kwalla ne suka cika min idanuna, na kalli Baba cikin kuka nace mata.
"Amma ko ma yayya ne dole yayi min uzuri, tunda nima mutum ne me rayuwa, taya zai dinga jifana da abinda ya fito bakin shi? Shin wannan adalci ne ko son Zuciya? Baki daya na kasa gane mishi bai da aiki sai gaya min maganar da ta fito bakin shi wallahi ki gaya mishi ya daina ko na kafta mishi rashin mutinci."
Na fada ina share kwallar da sune zubo min,
"Kayi hakuri"
Baki daya malam Ansar yaci uwar rena min hankali, dan yaga bana mishi magana ne wannan karon ya isa haka. Kuma zai ga yadda ake rashin mutunci, sai dai bai gaya min magana ba sai na rama.
Haka na share kwalla na, na cigaba da sauraron Baba, har dare yayi.
Shigowar Mohan da su Dan Ba'are ya sani mik'ewa zaune ina kallon shi, fuskar shi a sake. Kallona yake kamar me cikakken lafiya.
Murmushi nayi mishi tare da nuna mishi gurin zama. Kallona yake kamar yana son gano wani abu a tare dani, amma bai ce min kome ba, tunda ba magana ce yake ba. Sauka nayi tare da nufar shi na kawo shi bakin gadon ya zauna, zama nayi a kusa dashi ina me kallon kayan ciye ciyen da yake dakin na shiga mika mishi ina cewa.
"Ci karka damu Ayya naga ka rame da ba nan Anya Hammah Khalil kana kula dashi kuwa?" Wani kallon banza ya watsa mishi tare da cewa.
"Ba aiki Mohan ya dauke ni ba, dan haka dan banza idan ya dagama yaci abinci idan bai gadama ba ya zauna da yunwa banza dan iska Allah ya baka lafiya kace zaka fito da halin ka cin mutuncin ka zanyi"
Kallon shi nayi cikin kankace idanu nace mishi.
"Wannan cin mutuncin da me yayi kama? Ka saka mara lafiya a gaba da wulakancin meye yayi maka"
Sake hararan shi dan Ba'are yayi yana me dauke kai tare da gyara tsayuwar shi.
Abinda ya faru kuwa ba kome bane, tun suna yara suka da wata muguwar wasa da sukewa junan su, idan mutum ya duka, dai ka sake mishi dundu a baya, shine bayan ya koma gida yana ƙoƙarin su tawo asibitin, kawai Mohan ya ganshi ya duka yana saka takalmin shi ya samu gadon bayan shi ya sakar mishi dundu sai da ya kwara amai. Kuma da ya juya ya saka fuska kamar bashi ba, shine abun yake bashi haushi yake ta zagin shi tun a mota, ya kwashe mishi albarka yakai sau dari tare da jan Allah ya isa kamar zai fasa ihu, domin dai da yaji bayan ya kame kafin ya mike tsaye kai Mohan..kwafa yayi ya kuma ce mishi.
"Dan iska mugun banxa kawai"
"Amma ba na hana ka zagin nan ba?" Kallona yayi sannan yace min.
"Mamoon dundu yayi min a baya fa" .kamar zai fashe da kuka.
Kallon Hammah Mohan nayi,
"Me yasa kayi mishi haka? Kana son ka zama mugu ne dodo me ban tsoro?" Na mishi wani iri da hannuna ina gwalallo idanuna waje. Girgiza min kai yayi tare da kwantar da kanshi yana jin babu dad'i.
"Toh karka kuma kaji" na fada mishi ina kallon Hammah Khalil ina me Cigaba da bashi hakuri.
"Kayi hakuri"
"Shi kanan nazo na zauna kusa da kai?"
Matsa mishi nayi Baba bata ce min kome ba, sai bayan da suka gama suka fita, sannan tace min.
"Karka kuma haka babu kyau"
"Toh ba zan kuma ba"
***
Washi gari sai ga shugaban marasa zuciya. Shi da abokin shi suka shigo d'akin.
"Sannun ku ya masu jikin?" Inji Abokin Hammah ANSAR,
Kallon baya nayi tare da kallon su nace.
"Da sauki" na fada a takaice,
"Ashe baka ji dadi ba"
"Eh"
Yadda nace eh din a takaice Yasaka su shan jinin jikin su, tabbas na shirya musu. Fita baba tayi zata nimo goro.
Zama Mutallab yayi tare da kallon Hammah ANSAR da yake tsaye.
"Hmm! Almamoon mun zo da wani abu me girma bamu sani ba ko zaka yarda da shi?" Ya tambaye ni bayan ya kai aya.
"Ina sauraron ku?"
Gyara zama yayi tare da fara kalkalo min iyayi, ina kallon shi. Kafin yace min.
"Ansar yayi min bayanin waye kai so ina son muyi amfani da wannan damar domin nima maka lafiya?"
Kallon bayana nayi, kafin na kalli gefena, na kuma kallon saman kai na, kafin na sauka a gadon ina leka kasar gadon kafin na ce musu.
"Toh ni dai na nime lafiyar ban gan shi ba"
Na fada ina kallon su. Kafin na zauna.
"Ya kake mai da kome da wasa ne? Wannan batun lafiyar kace da? Kuma zaka mai dashi wasa? Ai ba wasa da lafiya"
"Wai ma tukun waye ya gaya maka bani da lafiya kazo ku nima min lafiya? Ku Allah ne?"
"A'a Almamoon taimako bai zama tashin hankali ba" ya faɗa yana kallona.
"Toh zakewa da shishigi ba tashin hankali bane?"
"Almamoon karka mana rashin kunya" inji Malam Ansar,
"Sai dai na muku bindin akuya, karshen rashin kunya"
"Amma kai babu manya ne a gidan ku?" Inji Mutallab,
"A'a yara ne a gidan mu irin ku."
"Kai waye ne da zaka gaya mana bakar magana?" Inji Malam Ansar,
"Toh kayi hakuri zan gaya maka farar magana yadda zaka ci ka koshi"
"Kai"
"Dalla sauke muryan ka, ba zaka min tsawa ba ana zaune lafiya dan ban cika gane seven da seventeen ba, zaku iya cigaba bujejjunku iska kar na kuma ganin ka"
Na fadawa malam Ansar a gadarance,
"Kai kasan waye kake gayawa magana?"
" Na sani mana? Waye ban da namiji a gabana, na miji ne a gabana nake gaya mishi maganar da tafi to bakina! Ko bai kai bane na gaya mishi?"
"Ka kai ka isa idanun ka ya bude ana bin bayanka ba, dole kartin maza sun lalata maka rayuwar ka, sun koya maka mugun nufinsu. Allah ya dawo da kai kan hanya domin nasan tunda suka san kai mata maza ne shi kenan sun lalata ka"
"A'a sai dai maza mata ba mata maza ba, Sharrin da kai min kuma ya kare kalau ba zan maka baki ba Allah ya shirya ka shiryar jigida"
"Almamoon kaf garin nan baka da gata sai ni" ya faɗa a fusace,
"Ayya sabida ka fado cikin mutane ni kuma na fito kalgo, ko nace na diro daga sama, masu asali." Na gaya mishi ina kallon fuskar shi.
"Ni kake wulakantawa sabida Mahaukaci wallahi sai na hana ka sukuni gaka ga mahaukacin nan"
"A'a akan me zan wulakanta ka ni din banza, kawai gani nayi rayuwar da ka dauka bai dace bane, amma kuma kato da kai na wulakanta ka, abin dubawa ne" na fada ina kallon farcena.
A fusace ya taso min, na d'ago kai ina kallon shi. Yana zuwa ya kifa min mari. Dai-dai shigowar Dan Ba'are, kura mishi ido nayi tare da jin kwalla yana cika min ido. Cikin wani irin zafin nama ya nufi malam Ansar.
"Kyale shi!" Na fada ina shiga tsakanin su.
"Ban san me yasa kake haka ba. Amma ina son wannan ya zama na farko da na karshe, Yaron nan ba bawanka bane da zaka addabi rayuwar shi."
"Ina ruwanka? Ni na kawo muku shi. Kuma Ni nake da hurumin tafiya da shi kai har ka isa ka gaya min magana akan shi, wallahi sai na dauke shi."
Dan Ba'are zai magana na hana shi, tunda nima ba maganar zanyi ba, haka ya fita a fusace. Suna fita dan Ba'are ya ce min.
"Meye alakar shi da kai?" Ya tambaye ni yana tsare Ni da ido.
"Malamina ne kuma na zauna a gidan shi"
"Shine yake maka hauka kamar shi ya haifi ka." Shima ya tadda min nashi rigimar, kamar zai dake ni har da cewa Ni na bar Malam Ansar.
***
Washi gari.
Kai malam Ansar bai da zuciya domin da asuban fari sai gashi, duk sai ya bani tausayi. Nuna mishi kusadani nayi, domin na fahimci yana cikin kad'aici. Tunda ya zauna ya kalle ni.
"Almamoon" shiru yayi tare da tagumi.
"Me yasa kake wulakantani? Almamoon duk wanda yace yana son ka ba makiyin ka bane, Almamoon ka duba girman kaunar da nake maka wallahi jiya dakyar na rintsa."
Ya fada yana kallon fuskana.
"Malam kaga"
"Ina laifin Hammah ANSAR" ya faɗa kamar zai yi kuka.
"Amma kasan dai ni din ba mace bane?"
Sauka yayi daga gadon ya rike hannuna.
"Ina masifar kaunar ka, kuma zan iya kome domin ka sami lafiya Mamoon kawai aiki za a maka akan matsalar jinsin ka a dawo da kai jinsin mata, kaga zaka haihu zaka yi rayuwa irinta mata, zaka zama."
Dariya ya bani sannan na kalle shi. Kafin na kuma kwashewa da dariya, domin kuwa mamaki yake bani.
"Na zata hauka kake ashe turu kake bukata, Allah ya shirya ka. Idan akan jinsi ne ba zan tab'a yarda a yi min aikin ba"
Matse hannuna yayi tare da kallon cikin idanuna.
"Kayi hakuri Hammah ANSAR, kai Yaya na dauke ka ba wai soyayya ba, Hammah ANSAR soyayyar nake maka ta yan uwanta ka ce, na gaya maka ba yau ba, ni ba kamar yadda kake tsammani bane"
"Na yarda zan zauna da kai haka. Don Allah ka so ni"
Tausayi ya bani, na rike hannun shi.
" Ba zan iya wannan lamanin ba"
Na gaya mishi ina me dauke kwallar da ta cika min idanuna.
Rarrashina yake amma bai tab'a sani jin ko zan iya yarda da bukatar shi, kawai dai na dai ki amsa mishi ne, haka ya gama abinda ya ga zai yi, har ya fita bayan ya tunatar dani an kusan komawa makaranta.
*** Kwana hudu a tsakanin aka sallame ni,
Muka koma tunda daga bakin kofar nake, kallon gidan kamar ka shekara ban gidan. Yana tsaye sanye da riga da wando na Adidas, kallon fuskar shi nayi naga ya kara kyau, shima kuma ni ya kura min ido. Da murmushi na isa gaban shi ina dariya kallon shi.
"Hammah Mohan"
Wani irin kallo yake min daga kasa har sama. Tare da bina da ido, sake baki nayi kawai ina kallon shi.
"Baba ga Hammah Mohan" na fada mata a sanyayye,
"Ayya Allah ya baka lafiya" riko hannun shi nayi, shima sai bina yake da idanu. Haka na kai Baba d'akina tayi sallah tare da zama ta ga gidan, bata bar gidan ba sai da Magarib.
Lokacin da na raka ta, dake ban kawo ana