Showing 177001 words to 180000 words out of 181864 words

Chapter 60 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6278

babu ruwa a cikin shi, bakin ciki da takaici ya sani na fusata, har sai da dan cikina ya juya nayi tir da alawadarar manoman da suka bar gurin randan babu ruwa. Daga nan na dawo gida wannan shine abinda ya faru!"


Shiru Amiril Muminina yayi sannan yace musu.
"Tabbas b'acin ranki shine ya shafi yaron har yake lalata amfanin gona domin babu shafin shaidanu a tattare da shi, lokacin da ranki yab'aci akwai jinin da ta fita ta cikin zuciyarki wanda zai digq akan mahaifar yaron, shi kuma ya wuce dashi cikin jikin yaron shi yasa yake ganin abinda yake aikatawa na wani abu bane."
Dan haka Malaman tarbiyya a Musulunci, sun yi kokarin fito da wasu abubuwan da yaro yake dauka, musamman akan matsalar yaron can, wanda suka tabbatar wannan abin ya faru da shine ta hanyar jini , wanda yake had'e da mahaifar shi, da wannan suka kara da cewa.


Matukar yaro yana rashin ji ko fitina ko rigima haka kawai, ko yawan kuka da wasu abubuwan, duk Yaronki yana dauka a cikin ki, karamin misali me yasa ake cewa babu kyau sauraron waka idan kina da ciki!( Akwai wata member na grp dina, wacce take gaya mana cewa, babban D'anta sun yana da shekara goma a duniya ya sauke Alqur'ani, ta kara da cewa wallahi yaron ya kasance mai sanyin hali da kyawawan halaye, tace sabida tun ina da cikin shi ', aka bani addu'ar da Annabi Ibrahim yayi lokacin da ya kawo Hajara da D'anta ya roki Allah ya albarkaci Zuri'ar shi. Tace ayar yana cikin suratul Ibrahim, sannan tace sai daya a suratul Maryam,inda Mahaifiyar Nana Maryam tayiwa yarta da kuma bakacen da tayi,tace wallahi ban yi bakace ce ba, amma na roki Allah ya shirya shi tun daga cikina bana jin ko sautin waka, sai karatun Alqur'ani da wa'azi, ta kara da cewa Alhamdulillahi Ubangiji ya amsa min addu'a ta, domin wallahi ko cikin unguwar mu mutuntta yaron ake, ni kaina da nake uwar shi mutuntani ake, Ubangiji ya shirya min shi, dan haka yana da kyau tun daka cikin ki fara nima musu shirya da taimakon Ubangiji Allah zai tsaya miki! Wallahi sai naji matar ta burge ni ainun)


Dan haka Umma ta gaya mata gaskiya akan tarbiyya, har take gaya mata idan zata ci abu ta fara da bismillah, idan zata zauna ta zauna da bismillah (🙄😎 gaskiya ya kamata na ajiye rubutun novel haka mu koma Islamiyyan, domin dauko tarbiyya a Musulunci)


Duk dani ladubban musulunci, Umma tana daurata, duk da ta lura yarinyar ma ba tayar baya bace akan ilmin addinin Musulunci, amma itama tayi nata kokarin kuma itama Benazir tana dauka.


***
Berlin, Germany.


Goge mata jiki yake yana kallon yadda take kwance bata ko motsi, murmushi yayi sannan ya gyara mata kwanciya, yana shafa kanta, kafin ya mike tare da nufar ban daki yayi alola. Sannan yazo ya gabatar da sallah, bayan ya idar ne, ya dauko yar karamar Alqur'anin shi ya fara karantawa, idan ya gama kula da ita sai ta dauko Alqur'an ya fara karatu yana rage mishi kewa da kad'aici,.


Babu wacce yake tausayawa kamar Yar shi Widad, domin tayi karama da ɗaukar maraici, gashi baya tare da su. Ga halin da Uwarta yake ciki duk sai yaji damuwa yayi mishi yawa, yaji kamar kan shi zata buga, kome ya tsaya mishi cak. Duk sai yaji kamar babu wani amfani a rayuwar shi, tunda wacce yake dominta gata nan kwance, duk fadi tashin da yake yanayi ne sabida ita, amma baki daya. Sai yayi ya sare, tunda suka zo ake gwaje gwajen,, har yau basu ce mishi kome ba, kuma basu kuma dawowa kanta ba, sai dai kuma ana zuwa ana mata allurai da saka mata ruwa. Wannan kawai ya kara mishi kwarin gwiwar suna sane dashi, likitan da zai duba su, ba dan kasar bane kuma idan zai zo yana bin kasashen kusan biyar kafin ya iso, shi yasa suke dakon jiran shi domin duk abinda ake mata shi yake bada umarni, sannan yana daga can ake tura mishi duk wani bincike da aka yi nata, shi yasa ma yace zai zo domin zai tsallake wasu ayyuka masu muhimmanci amma haka ya tsallake su, kuma ya saka zai zo nan da wata biyar da wasu kwanaki.


Yana idarwa ya mike tare da rike hannun ta, ya saka a fuskar shi, yana kallon yadda take ko numfashin bata ja, dai na na'ura, baki daya jikin shi yayi sanyi...
#Mai_Dambu
[8/19, 1:39 PM] Yar Kasuwa👳🏻‍♀️: HAKKIN MALLAKATA
#thu-Aug-2021


BOROROJI


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


BABI NA SABA'IN DA BIYU.
---------------------------------------------
*Ina kuke matan alfarma muna da kayan ado da kawa... Musamman turaren kaya wanda zai yi awa ashirin da hudu a jikin kayan ki, muna da scentball wanda ake wurga shi a wardrob sannan muna da Oil mai dan karen kyau da dad'i! Ina uwar gidan ina Amarya, maza garzayo kar a baki labari kayan mu free order! Sannan ina uwaren gida da amare nesa tazo kusa, muna da kayan Mata ingantattun masu kyau, Muna da gumba mai kyau yar asali, muna da hadin kazar amare mai kyau yar asali sannan muna da Sha daka mai kyau na amare da uwargida! Akwai parkege na amare mace da ta yarda da kanta Hajiya taɓa Ni ta wannan Number:08130269841 sayan na gari mai da kudi gida*
Kaza
Tara bala'i-
Gumba bucket ƙarami-
Gari-
Hatsabibiyar zuma
Hatsabibin gari
Zobe-
Tsumi-,
Maina ya rikice
Zazzogau
Haɗin gigita shi
Maƙale mata


Sayan na gari mai da kudi gida..... Sai kun zo muna maraba da ku


________________________________
Shafa kanta yayi tare da goge mata hannunta. Yana jin saukar kwalla daga cikin idanun shi. Suna sauka a saman fuskar ta.


"Ki tashi haka, idan kina cigaba da kwanciya Allah kaɗai san rayuwar da da zasu kwanta, sabida ke? Don Allah ki tashi. Iya haka ma horon ya isa haka, karki cigaba da gana min azaba."


Haka yayi ta surutu, kai kusan kullum aikin shi kenan, idan yana kula da ita, baki daya ya koma bai da wani abu me muhimmancin sama da ita, kamar yadda ta badda rayuwarta domin shi haka shima ya ajiye kome, aikin shi da FBI ya ajiye baki daya. Ya zauna a jikin matar shi.


Mahaifin shi da yan uwan shi sun zo, sun duba su sai da suka Mishi sati domin baki daya bayi da nutsuwa kuma yaki wani ya zauna a jikinta sai shi kawai. Bayan tafiyar su da wata hudu likitan yazo amma bai fara duba su ba, ya fara da mutanen da suke jiran shi.


Sai da suka dauki wata biyu cur, kafin aka shiga aikin farko na bayanta, cikin niman yardan Ubangiji, ana saura sati za a shiga aikin da ita, Mohan ya tura kudi mai mugun yawa aka rabawa mabukata, tare da niman Allah ya amshi bakunar su, yasa ayi aikin cikin nasara, makarantun allo kuwa haka akayi ta kai musu sadaka.


Gidan marayu haka aka kai musu motar abinci har gidan, tare da tawwasalin Allah ya kare su ya kuma basu lafiya, musamman Maimunari.


Haka aka yi ta rabon nan har aka ya kira yace an shiga da ita aiki.


Awa goma sha daya aka dauka kafin aka fito da ita, tana kwance rub da ciki. Mikawa Mohan hannu yayi sannan yace mishi.
"Zan tafi, nan da wata uku zan dawo a duba na kanta, Allah ya bata lafiya, kai kuma ya baka hakurin jinya, amma zaka yi hakuri domin ba zata farka yanzun ba, sai anyi na kan Tukun. Shine me muhimmancin. Shi idan ana aikin ma zata fara kokarin farkawa, na fara na bayan ne dan shine Rayuwarta."


Cikin karaya yace.
"Toh Dr kana cewa zaka tafi sai bayan wata uku, ka duba ta bar yarinyar mu yar wata goma sha daya, dole yasa aka cire ta a nonon, Dr ka tab'a zuciyata ji nake kamar ba zan kai wata ukun nan ba, please ka duba al'amarin, mata ta ce. Ko zaman wata daya bamu cikin soyayyar juna ba"


Ya shiga bashi labarin halin da suka tsinci kansu, take jikin likitan yayi mugun sanyi, ya rike hannun Mohan, tare da cewa.
"Nayiwa Yarka alqawarin ba zan wuce kwana talatin ba zan dawo na mata aikin karshe ka yarda dani akwai ayyukan masu muhimmanci ne suna jirana, zan mata aiki da Yardan Allahn ku, kuma zata farka da izinin shi, ka yarda da Ubangijinku. Kuma ka nime ya bata lafiya."


Duk da ba musulmi bane amma yayi Imani da Allah kuma ya yarda shi ne mai badawa. Bayan tafiyar shi Mohan ya kira gida ya gaya musu, yadda suka yi. Sannan ya kuma ware wasu kudin yace kai gidan marayu, domin yana sauraron wani wa'azain Kabir Gombe akan marayu, dan haka ya ce.
"Abbu don Allah a kai gidan Marayu, suna da bukatar shi, a kula da su da matsalar su. Idan bai kai ba Abbu a kirani zan turo, ko ka tambayi Khalil akwai katin bankina na kasuwanci. Duk wani abu idan ana bukata a gaya min INSHA Allah zan turo."


Alhamdulillahi a cikin wata biyu Allah da ikon shi aka kuma shiga da Ita aiki na biyu, cikin nasara ana aikin ta fara motsi wannan ba karamin dad'i ya saka su ba, ana gama aikin aka fito da ita, likitan ya mikawa Mohan hannu.


"Anyi nasara! Amma zaka yi hakuri kwanciyar da tayi zai saka ta yi ta abubuwa irin na yara, kafin ta gama shan magani zata warware da Yardan Allah ku,"


Cikin gamsuwa Mohan ya mika mishi hannu, babban burin shi ya ga Maimunari a tsaye tana mishi murmushin jin dadi.


Yana tsaye aka kai ta dakin ta,sannan ya bisu.


Sai da ta share kwana biyar tana barci, kafin Allah ya nufa zata farka, tunda ta bude take kallon dakin. Ganin haka likitocin suna shigo aka shiga mata abinda ya dace. Sai da suka kai awa daya akan ta, kafin suka fita. Kallon Mohan take kamar wacce ta farka cutar makanta, takowa yayi a sanyayye ya zauna a gefen ta. Ya mika mata hannu.

Dauke kai tayi kamar bata tab'a ganin shi ba.
"Maimoon" banza tayi mishi. Duk abinda ya dace yayi mata yayi, karshe ma kara mishi ciwon kai take, musamman da suka cire mata na'urar kanta domin tayi wanka, ai kuwa sai da ya kai zuciya nesa, domin wallahi yayi hakuri wata kusan takwas, yana jinyarta, babu abinda ya fisge shi kamar kirjinta, had'iye yawun yayi makwat, tare da kallon yadda take mishi bori.


Matseta yayi da bango hannun shi yana bisa duwas ɗinta, yana matsawa yace mata.
"Ya isa haka, Hammah Mohan dinki ne"


Kallon shi tai a sanyayye kamar tasan meye ya gaya mata kafin ta tura mishi bakinta, aikuwa ya kame bakin ya shiga cinye shi, hannun shi yana yawo a jikinta, kai Mohan dan jaraba ne.(🙄 A jinyar ma ba za kyale ta ba)


Dakyar ya iya rike kanshi ya kawo ta waje, ya shirya ta cikin kayan asibitin, sannan likitocin suka kuma kwantar mishi da hankali zata dawo daidai, yayi hakuri, kafin su koma gida da lafiyarta zasu koma.


Aikuwa Yar nima tasaka shi a gaba da rikicin banza kukan banza, kuka mara tushe balle makama, amma da zai tab'a yar banza shiru take tana zare idanun kamar tsohuwar mayya, tunda ya gano ta, Malam Mohan kakar shi ta yanke saka, domin tana fara mishi hauka zai kai hannun shi mazauninta. Ko ya riko dukiyar fulaninta,,. Sai dai kuga yar banza tayi luf. Tun tana da lafiya ma Mohan yasan sirrin rigimar ta balle yanzun da take pagal.


*
Sake shi hukumar gidan yarin suka yi, daga can nesa ya hango Khalil da wasu lauyoyi, cikin isgilanci ya isa gare su..


"Ina labarin Maimunari!" Murmushi Khalil yayi mishi sannan ya shiga motar ya zauna lauyoyi ma haka.
"Mohan ya baka damar ka rayu domin kaga yadda za a buga soyayya. Ka rayu domin ka ga yadda Maimoon zata kasance da Mohan, wannan alfarma yayi maka domin yasan zaka so ka ga yadda zasu rayu"


"Karya ne wallahi sai ka kashe su dukkan su biyu."ya fada a fusace,
"Kuwa zaka mutu"
Barin shi suka yi a gurin, Khalil ya kira Mohan ya gaya mishi sun gama kome.
"Toh nagode sai dai har yau bata dawo daidai ba domin tunanin ta ya birkice wallahi ina cikin damuwa!"


"Karka damu Moha, Allah yana tare da kai, ana kam muku addu'o'in kuma nasan Allah zai amsa."


"Nagode sosai, Khalil da tsaya min da kayi da babu kai wallahi da ba zan tab'a tsayawa da kafana ba. Nagode sosai da Aminta mu"
"Karka damu nagode sosai nima"


Sannan suka yi sallama, cikin nutsuwa Khalil ya koma Niger.


***
Bayan wata ɗaya.


Alhamdulillahi domin lafiya ta samu, kuma duk wanda ya ga Maimunari ta samu lafiya, domin tunaninta ya dawo, yanzun haka suka kasar Moscow.


Inda Mohan ya tafi domin kasuwancin shi.
Ina gyara jikina ya shigo d'akin juyawa nayi tare da amsa mishi sallamar shi. Sake towel din nayi ina murmushi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da takowa gabana.


"Zaki kashe ni da shagali Matar Mohan"
"Burina kenan na raya mijina da shagalina."
Karban kayan nayi na watsa a kujeran dakin, sannan na ja hannun shi muka shiga ban daki, tare muka sake wanka, bayan na cinye shi da salona musamman, sannan muka fito daga ban ɗakin, kai Hammah Mohan.


Tunda muka fito muke manne da juna, abu daya muke tare da cinye junar mu, sai da ya shiga babban birnin lintsin kafin muka sake ihu lokaci guda, wani irin dad'i da yanayi na musamman, yasa muka haukata kan mu.


Bayan awa daya.
Ina sanye da doguwar riga, na yane kaina da farin mayafi muka fito cin abinci. Ban san wani irin yanayi na riski kaina ba, amma Tabbas ina cikin farin ciki samun mutum irin Mohan a matsayin abokin rayuwata.


Haka muka gama yawo sannan ya kai ni har dubai, wannan dakin dai shi ya kai ni, inda na rasa wani irin dad'i nake ji. Sati biyu muka yi a can.


"Wallahi ba mu koma ba, mutane su hnnai sakewa da mata na!" Ya fada yana hararan gefe da gefe,


"Hammah na ina kuma zan iya maka Ni fa babu ruwana,idan kace kar na kula su shikenan."


"Ni zaki haɗawa aiki? Na manta ban gaya miki ba, wata biyu da suka wuce Beenah ta haihu an sami mace, kuma Kinsan me? Sunanki aka saka. Suna kiranta Jewanah, wato (God gift in Urdu language) dan haka sai ki buɗe bakin aljuhun ki, domin samun takwara da wahala"


"Kai Hammah Mohan, me nake dashi sai dai kai, zaka a ra min na yi musu idan yaso na biyaka" na d'aga mishi gira.
"Gaskiya kan zaki biya dan ban koshi ba, kuma gaskiya ki biya yanzun sai a wuce gurin"


Aikuwa makale mata ya makale min sai da ya samu kanshi muka shiga wanka tare, sannan muka shirya tare da nufar kasuwa, minti sayayya sosai, sannan muka dawo masaukin mu, washi gari.


Muka dira a kasar mu ta gado, aikuwa kamar yadda ya fada, sai da muka yi sati biyu bamu ganin juna, saboda jama'a ga Mommy da tsohon ciki, dan ma ina jin wai zasu mata aiki ne, na tausaya mata domin ya hadu da girma da shekaru, kullum cin fada take. Gashi abinda na lura ta tsani ta bude ido taga Abie a kusa da ita, tayi ta kuka tana masifa duk shi ya janyo mata wannan fitinar, tass take mishi, rabonta da haihuwa shekara goma sha biyu,. Amma bawan Allah nan ya cuce ta.


Allah Sarki sai yayi ta bata hakuri, kamar zugata yake, haka zata kawo min karar shi, ni kuwa sai nayi ta kuka. Lokacin Yar Jewanah tana da wata biyar, haka muke zama muna rarrashina Mommy, idan muka matsa muyi gulmarta ni da Beenah.
"Addah Munah, Mommy gata yayi mata yawa kiga yadda Abie yake rarrashinta amma ba zai hana an jima ta saka shi a gaba da kuka ba, wallahi wancan satin da fushi na bar gidan, haba ta saka mana Uba a gaba da rigima dan bata shiga kauye ne, da ta ga abinda bata tab'a gani ba, matan da suka fita manyanta da ciki."


"Toh Magulmaciya Beenah gulmata kike da yar Uwarki?"
"A'a Mommy ba gulmarki ba muke ba."


Aikuwa ta shiga fada kamar zata dake mu, Abie na zuwa ta fashe da kuka.
"Kana jin Yaranka zagina suke wai na samu gata sai abinda na gadama nake"


"Uwata ya haka? Beenah zaki daina zuwa gidan nan da"sannan ya lallabata suka bar mu, aikuwa muka sake Dariya.


**
Na koma gidan su Hammah Mohan, nan ma sai da muka tafi har Agadaz, lokacin Widad tayi girman ban mamaki,. Daga can muka wuce Damagaram, inda na nimo abokaina Salihu Muhmuda da Amadu Bukar. Sunyi aure har da iyalin su, nasaka Hammah Mohan yayi musu alkhairi bayan ya dauke su aiki, sannan muka dawo.


Kwanan mu ashirin da biyar da dawowa aka yiwa Mommy tiyata, tare da ciro mata yaranta Biyu mace da namiji. Tun dare aka yi aikin Hammah Mohan bai gaya min ba, sai da asuba. Kuka na saka tare da kai mishi duka, yana dariya.


"Saura ke!"
Daukar matashi nayi na rufe shi da duka.


Haka muka kasance har bayan mun karya muka nufi Asibitin kamar ba a cire mata Babyn ba, sabida mun samu tana hira tas.


Zuwa nayi kan yaran ina kallon su.
"Hammah na kalli nafi yaran kyau"
"Ina za a gwada! Pure love!" Inji Mohan,
"Gaskiya kin fisu kyau,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login