Showing 6001 words to 9000 words out of 181864 words

Chapter 3 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6245

ya faɗa tare da kallon Iyar shi.
"Kiyi hakuri iyar Salihu," ta juya tana cigaba da sababinta, dariya yayi sannan yace mata.
"Zama da mutane sai ka koyi halin su"
"Almamoon ka duba girman Allah ka daina harba mutane da magana marasa Dad'i,irin wannan halin shine ya faru shekaru goma sha daya, harbin wuni da bakin magana, karka jefa rayuwata cikin ukuba mana."


"Shi kenan" ya faɗa tare da tura mata kwanon, haka bata so sai da taci yankar naman daya, sannan ya fara cin abincin. Abu biyu yaƙe dauke da Almamoon yanayin shi na Uwar shi ce da kamanin ta, bakin fatar shi na Hamma Sama'ila ne, domin har yafi Uban baki ma.


Shekarun baya bata yarda cewa yaron zai kai haka ba, domin kuwa bayan ya shekara daya yayi fama da rashin lafiya, irin su bakon dauro, tamowa, da kuma laulayi irinta yara kananu, sai da ta kai ko abincin da zasu ci gagagrar su take, a lokacin gidan da suke suka sakota a gaba sabida rashin bawa Yaron nono da kuma bata mishi wanka a gaban jama'a. Suka yi ta gulmar su da kananun magana.. haka bai saka ya tab'a ko d'aga kai tayi magana ba.


Dole Sanda ya fita niman aikin yi, domin ba zai iya rayuwa da iyalin shi babu abinda zasu taimakawa kansu ba, sabida yanayin da suke ci ko surfen an daina bata. Sun sha wahala da yaron, domin rashin nonon uwa yasa ya rasa lafiyar shi, sai da suka hada da na gargajiya, irin wanda suka sani da kansu. Suka hada mishi magani. Da yayi wayo kuwa idan basu samu wadataccen abinci ba, wanda suka samu suke hakura su bashi, su kuma su kwana haka.


Allah cikin ikon shi Sanda ya samu gadin kasuwa, abinda ya rufa musu asiri kenan, duk da haka suke biyan kudin haya, tare da abin da zasu ci, tunda likita ya gaya musu, yana bukatar kayan gina jiki, suke wannan kokarin ki basu ci nama ba zasu saya mishi, a zuba mishi akan abinci. Madara kuwa, kullum idan zai dawo da safe zai sayo mishi ta gora ya kawo mishi.


Wani irin kaunar yaron suke kamar su bada rayuwar su domin fansar nashi.


---
"Innata na gama gaya min mafarkin da kika yi?" ya tambaye ta,
" Wai na ganka ne tare da wasu manyan mutane, kuma ka zama babban mutum, sai farin ciki kake"
"Daga karshe kuma kika tashi a barci ko?" Ya katse mata labarin. Girgiza kai tayi tana cewa.
"Allah ya shirya min kai!"
Tana murmushi, domin karfafa mishi haka take.


Kiran sallah ne ya sashi mik'ewa yayi alola sannan ta dawo dakin yayi Sallah, kafin ya zauna yana kallon Innar shi.
"Inna mun gama jarabawar mu yau, Allah yasa ki biya min kudin Makarantar sakandari" ya faɗa yana tararradi yadda zata dauki maganar.
"Idan kayi min alƙawarin zaka yi karatu domin Allah da kuma tsayawa da kafarka me zai saka na ki biya maka" ta faɗa tana jan wani akwatin katako ta bude cikin shi. Kudine babu iyaka. Suka zauna aka yi lissafin su tsaf.
"Innah har zai rage ma ai kuɗin."


"So nake na cigaba da tarawa, dan ba zaka yi karatu a makarantar gwamanti da babu kulawa ba, kai ma makarantan kudi zaka tafi." Murmushi yayi sannan yace mata.
"Insha Allah"


***
Haka suka share wata biyu sannan sakamakon su ya fito, haka Aminatu ta fasa asusun aka biya mishi kusan makudan kudade na makaranta, ranar da zai fara zuwa. Suka zauna dashi aka mishi nasiha, tare da mishi gargadi.
"Karka sake kayi wasa da karatunka, kayi hakuri da mutanen da zaku hadu makarantar yaran masu kudi ne dan haka karka bari a Kama ka da laifin da zai dame mu.


Haka suka gama mishi fada, sannan zai fita Malam Sanda tace mishi.
"Kin gaya mishi gaskiya akan" kallon shi tayi tare da cewa.
"Wannan sirrin shi ne, karka manta wata rana zai fahimci dalilin haka, kai dai ka hana shi mu'amala da maza da mata,"


Kallon su yayi kafin yace musu.
"Wani sirrin kuke boye min?"
"Babu wani sirrin da a ke boye maka"
"Toh shi kenan," ya faɗa tare da barin d'akin, shi da Baban shi.
A iya yanzun haka kawai take jin kamar sun tauye mishi hakkin shi da kuma yancin shi, sai dai kamar yadda Mijinta ya faɗa haka ne, baya son tarihi ta maimaita kanta ne akan shi, shi yasa ya zab'i hakan a matsayin babban al'amari akan.


Amma kuma tana ganin kamar haka ba hujja bane, kamar tauye hakkin shi ne, kai toh idan wani abu ya same shi fa? Gwara kawai a tafi a haka. Toh gaba kuma aka dawo aka samu akasi fa? Lallai bari malam ya dawo zasu yi magana domin ba zai tab'a yiwa ba, ka sayi kura da daddare da safe ka samu kare ne, haka ba zai tab'a yiwa ba..amma shi yaron ai bai san hujjar su na maida kome haka ba.


..... Bayan malam ya dawo ne ta kalle shi kafin tace mishi.
"Malam anya bamu so kan mu ba? Taya zamu bari har zuwa lokacin da."
"Ki bar kome a hannun, idan ta fara girma zamu fahimtar dashi kome, sannan zamu sauya mishi gari domin kar a samu matsala, karki yarda wani yasan wannan sirrin. Ya zauna a tsakanin mu."


Had'iye yawun tayi sannan tace mishi.
" Sai nake ganin kamar da cutarwa, a bar shi haka ba a gaya mishi dalilin da yasa yake raye a haka ba, sannan kuma. "
"Karki karaya mana, tsoron abinda ya faru shekaru goma sha daya nake kara ada Yaron nan ba wai dan wata manufa bane, kawai ki tayani boye maganar shi nan bana son kamar yadda iyayen shi suka mishi, shima ace ya fuskanci haka.


Duk da muna namu Allah yana shine gaskiya."


"Ko a ina Sama'ila yake oho?" Ta faɗa cikin sanyin murya, me ban tausayi. A hankali yake kwalla suka zubo mata, tana kallon kasa. Ya tafi ya manta da gida, ya tafi bai kuma waiwayar baya ba, me yasa ya tafi shima? Me yasa ya gaza tsayuwa ya fuskanci rayuwar abinda ya bari, babu kome, Allah yana nan zata rike yaron ta kuma boye mishi waye shi. Domin samun goben shi.


Amma Tabbas akwai sirri me girma ga rayuwar Almamoon.


****
Asalin labarin.
Fulanin Wodaadabe Bororo.
Wato sune Fulanin da basu zama kuma basu da mazauni daya, idan suka shekara anan yau gobe zasu kara shekara a wani garin. Sannan Allah yayi musu baiwar ilimin addinin Muslunci, musamman Alkur'ani.


Zunzurutun baiwar da Allah yayi musu kasancewar su bakakken Fulani masu jajjen shanu, yasa zaka sami yaro karami an daura shi a saman saniya yana tafe yana karatun Alqur'ani, kuma ya tafi da saniyar har wata tafiya.


Yanayin shigar su ba kamar na sauran Fulanin bane, domin suna sanye da wata hafaffera, riga ce Armless, har gwiwar su rigar take, sai wandon yadi ce baka kowa wata kala, suna saka hular malafa akan su, matan su, suna tara gashi a gaban goshin su, me shegen yawa kuma suna saka bakakken kaya har kasa kamar riga da zabi ko doguwar riga.


Suna shigowa gari da matan su, tallar maganin mata ko maganin gashi, suna bin gida gida suna tallar shi, zaku gan su dogaye ne matan. Kyakyawa bakakke...


Duk da ana samun fararren su, amma bakakken sunfi yawa, suna da Albarka na dabbobi, sannan kuma suna da matukar kyakyamin abinda ya shigo musu, musamman abinda ya kasance sabon abu.


BOROROJI suna da wata muguwar dabi'a wacce take salwantar da rayukan mata da yan mata, mace kome girman mata idan har tsautsayi ya faɗa akanki shikenan.


Ismail Mohammed Wodaadabe.
Shine cikakken sunan Sama'ila, yana da kanwa daya tal a duniya Aminatu.


Dayawa abokan shi sun sha mishi barazana zasu dauke Kanwar shi, amma bai tab'a damuwa da haka ba, sabida yasan abinda ya shiryawa, wani mugun hali da yake dashi. Shine yawancin matasan bororo suna zuwa mishi yayi musu aiki, kuma idan yayi kamar yankar wuka taci.


Umar sanda shine cikakken sunan abokin shi saurayin Kanwar shi Aminatu. Zaune suke a kasar bishiya.
"Ila, shin da gaske zaka babu kanwarka dan naga baku da dangi ko daya a wannan rigar kace suna can mali"


Mik'ewa yayi bayan ya kad'e jikin shi ya rufe Alqur'anin shi. Yana faɗin.
"Duk cikin abokaina kai ne kawai kace min kana son auren Aminatu sauran kuwa cewa suke zasu yi *CIRENTA* shi yasa na amince ka nemi aurenta kai ma ai ba dangin ne da kai ba."


"Toh meye na bakar magana? Daga tambaya sai bakar magana ta biyo baya." Kallon shi yayi da wutsiyar ido, yace mishi.
"Ba bakar magana ba ce farar magana ce."
"Ai kaji ka mutumin banza kawai"
"Idan ni mutumin banza ne toh Sannun na Allah" ya faɗa yana kad'a kan shanun shi.
"Ban da ina girmama Aminatu da ba zan tab'a yarda na bi ka ba"
"Idan baka bini ba sai na fadi na mutu dan ka ki bina"


"Wai kan Ila bakinka baya mutuwa ne?"
"Sai ranar da kasa ta rufe min ido" ya faɗa abin shi haka bai dame shi ba, sai ma kara hada kan dabbobin shi yake suka bar gurin kiwon, ba tare da ya gayawa Sanda ba, ranar juma'a, Sanda ya shiga gari juma'a aka daura auren Aminatu,
[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: I'm on Instagram as @s.square_fashion_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=gorfmwut2x22&utm_content=cgl6gfx
```Zaku iya samun kayan mu daga turaren zamani na wuta, shu'umar humra, dambun nama na mata, tsumin. Da sauran su kayan mu ba irin nasu bane sai an gwada akan san na kwarai..... Akwai haɗin kayan amare da na uwargida...🗣️🗣️Friday Promo!!! Buy 13pcs @15k only : Turaren wuta 5pcs, humra 3pcs, Turaren tsugunno, shu'umar humra, mopping and toilet perfume, curtains and carpet parfume &kasko💃🏻💃🏻```


🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Littafi na D'aya...


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris


_🙄 Daga farawa naga yadda kuke sakawa Dan baki namu ido fa😛🤭 Wallahi ko hmm_


BABI NA UKU.
Wata tafiyar.


Sake baki Salihu Muhmuda yayi tare da Amadu.
"Amma zamu haɗu" suka fada mishi,.mik'ewa yayi cikin rashin tsoro yace musu.
"Idan muka hadu abinda kuka bani ku hanani" ya faɗa yana fita daga kujeran,
"Mara mutunci"
"Lokacin da aka zo rabon shi bana nan"
"Mugu"
"Eh gadon shi nayi"
"Dan iska kawai"
"A'a sai dai guguwa"
Ya fada tare da barin tabirin su, kamar zasu fasa jarabawar, karshe haka suka mike zasu kai, sai a lokacin Amadu ya kai idanun shi kasar tabirin su ya lura da rubutun da Almamoon yayi ya ajiye musu. Da sauri suka dauka. Murna kuwa baki yaki rufuwa.


Koda suka gama, fitowa suka yi. Tare da samun shi a kasar bishiya ya zauna yana ta rubutu, idan ka ga hancin shi har baki, daga gefen fuskar shi kuwa saje ce ya kwanta gwanin ban sha'awa.
"Kai mara mutunci" banza yayi musu.
"Mun gode"
" Da aka yi me?"
"Da bamu amsar da kayi"
Kallon su yayi sannan yace musu.
"Ai ina mamakin yadda Uwayen ku suke kashewa jakuna kudin makaranta." Ya fada tare da mik'ewa.
"Wawa kawai dan baki duna"
"Eh toh ta yiwu ni bakin ne, amma kuma ina takaicin haduwa da katon jaki" ya faɗa tare da nufar hanyar ajin su.
"Almamoon dan me gadi"
Cak ya tsaya tare da juyawa ya sake murmushi, kafin tace mishi.
"Eh toh dukda haka yafi cirani" da Yaron ya ji abinda ya gaya mishi fasa ihu yayi tare da burgima, an zage mishi uba an can dan cirani.


Haka yayi ta kuka har Malamin su ya shigo tare da tambayar su meye ya haɗa su.
"Zagina yayi na bashi hakuri" inji Almamoon,
" Karya yake cewa yayi Ubana dan cirani"
Tsaki malamin yayi sannan yayi musu fada.
... Bayan sun gama jarabawar suna nufi hanyar gida, yau ya shirya musu tsiya shi yasa bai kula su ba.
"Yau idan muka je gida zan samu anyi mana abinci me dad'i?" Suna son yayi magana amma dake yayi shiru basu kuma takalo shi ba.

Haduwa da wasu yan samarin unguwar su, suka tsaya tare da make su, amma ban da Almamoon, wuce su yayi. Sai da suka bar gurin.
"Mamoon kai wani irin mugun mutum ne ka ga sun tsare mu ba tsaya ba."
"Me ya faru daku?" Ya tambaye su, kamar bai ga abinda ya faru ba.
"A'a babu"
"Nima naga alama" ya ga musu tare da wuce su, matasan nan ba kome yasa suka make su Amadu Bukar da Salihu Muhmuda ba, sai dan tsokanar su da suka yi, kuma akan idanun shi suka tsokane su. Shi kuma baya tab'a bin bayan karya.


Haka suka isa gida idan suka gaya mishi maganar banza ya gaya musu wacce tafi tasu muni.
"Dan banza munafuki wanda baya yarda yayi wanka a gaban mutane." Wannan maganar tayi mishi zafi, da gaske ne baya tab'a wanka a gaban mutane, kuka kamar yadda babba zai shiga ban daki yayi wanka, haka shima yake. Rasa amsar basu yayi har suka isa cikin gidan, zasu nufi dakunan iyayen su yacewa Salihu..
"Ka tambayi Iyakar me yasa bata wanka a waje"
Ya gaya mishi sannan ya shiga dakin su. Samun Innar shi yayi tana ta daman cura fura da aka kawo mata aikin shi take.
"Sannun Innata"
"Sannun D'an albarka, dauki abincin ka yau Allah ya taimaka malam ya samu dan albashi ya sayo maka shinkafa aka dafa, duba ka gani har da nama."


Kallonta yayi sannan yace mata.
"Innah hala ko cin namar baki yi ba daga ke har Baba." Ya fada idanun shi na cika da kwalla.
"Mun ci mana"
Ta faɗa tare da maida hankalinta kan aikinta, bude kwanon yayi ya ga Bama kusan ya lullube abincin, sai ganye da aka zuba a saman namar, ture abincin yayi tare da cewa.
"Ba zan ci ba"
"Yi hakuri Bawan Allah, sanyin idaniyar Innar, Dan da aka haifa tsiya na barci, Kasan yadda nake kokarin kyautata maka, toh maza ci sai ba baka labarin wani mafarkin da na jima ina yi akanka"
"Wallahi ba zan ci ba sai dai muce tare"
Shafa kanshi yayi tare da cire mishi hular kanshi, gashin kanshi irinta Bororoji yana nan daga tsakiyar kanshi anyi Mishi wata irin kitso me hawa biyu, doka sai wasu kanana da aka saka musu wuri wato braid, gashin nan baki suddin har gadon bayan shi, wuyar shi a daure yake da guru da azurfa, murmushi yayi sannan yace mata.
"Gobe za a fara shadi a rugar Baima, zamu je don Allah Innah ki bar ni naje" kura mishi ido tayi cike da tsoro.
"A'a ba zaka je ba"
"Don Allah nace Innata..."
"Iyar Mamoon! Wallahi nakawo miki dokaciya, kiyiwa Mamoon fada da irin maganar da yake zarowa nan."
"Toh Allah yayi min baƙi bari nayi shiru kar kayi Magana"
Rufe mishi baki Innar shi tayi.
"Kiyi hakuri Iyar Salihu."
"Ina dalili yaro sai kace mace gurin zaro magana, na kara jin yacewa Salihu me yasa bana wanka a gaban su."
"Toh ai dalilin da nasa nima bana wanka a gaban jama'a kenan" ya faɗa tare da kallon Innar shi, kamar zai yi kuka.
"Iyar Mamoon"
"Toh kiyi hakuri" ya faɗa tare da kallon Iyar shi.
"Kiyi hakuri iyar Salihu," ta juya tana cigaba da sababinta, dariya yayi sannan yace mata.
"Zama da mutane sai ka koyi halin su"
"Almamoon ka duba girman Allah ka daina harba mutane da magana marasa Dad'i,irin wannan halin shine ya faru shekaru goma sha daya, harbin wuni da bakin magana, karka jefa rayuwata cikin ukuba mana."


"Shi kenan" ya faɗa tare da tura mata kwanon, haka bata so sai da taci yankar naman daya, sannan ya fara cin abincin. Abu biyu yaƙe dauke da Almamoon yanayin shi na Uwar shi ce da kamanin ta, bakin fatar shi na Hamma Sama'ila ne, domin har yafi Uban baki ma.


Shekarun baya bata yarda cewa yaron zai kai haka ba, domin kuwa bayan ya shekara daya yayi fama da rashin lafiya, irin su bakon dauro, tamowa, da kuma laulayi irinta yara kananu, sai da ta kai ko abincin da zasu ci gagagrar su take, a lokacin gidan da suke suka sakota a gaba sabida rashin bawa Yaron nono da kuma bata mishi wanka a gaban jama'a. Suka yi ta gulmar su da kananun magana.. haka bai saka ya tab'a ko d'aga kai tayi magana ba.


Dole Sanda ya fita niman aikin yi, domin ba zai iya rayuwa da iyalin shi babu abinda zasu taimakawa kansu ba, sabida yanayin da suke ci ko surfen an daina bata. Sun sha wahala da yaron, domin rashin nonon uwa yasa ya rasa lafiyar shi, sai da suka hada da na gargajiya, irin wanda suka sani da kansu. Suka hada mishi magani. Da yayi wayo kuwa idan basu samu wadataccen abinci ba, wanda suka samu suke hakura su bashi, su kuma su kwana haka.


Allah cikin ikon shi Sanda ya samu gadin kasuwa, abinda ya rufa musu asiri kenan, duk da haka suke biyan kudin haya, tare da abin da zasu ci, tunda likita ya gaya musu, yana bukatar kayan gina jiki, suke wannan kokarin ki basu ci nama ba zasu saya mishi, a zuba mishi akan abinci. Madara kuwa, kullum idan zai dawo da safe zai sayo mishi ta gora ya kawo mishi.


Wani irin kaunar yaron suke kamar su bada rayuwar su domin fansar nashi.


---
"Innata na gama gaya min mafarkin da kika yi?" ya tambaye ta,
" Wai na ganka ne tare da wasu manyan mutane, kuma ka zama babban mutum, sai farin ciki kake"
"Daga karshe kuma kika tashi a barci ko?" Ya katse mata labarin. Girgiza kai tayi tana cewa.
"Allah ya shirya min kai!"
Tana murmushi, domin karfafa mishi haka take.


Kiran sallah ne ya sashi mik'ewa yayi alola sannan ta dawo dakin yayi Sallah, kafin ya zauna yana kallon Innar shi.
"Inna mun gama jarabawar mu yau, Allah yasa ki biya min kudin Makarantar sakandari" ya faɗa yana tararradi yadda zata dauki maganar.
"Idan kayi min alƙawarin zaka yi karatu domin Allah da kuma tsayawa da kafarka me zai saka na ki biya maka" ta faɗa tana jan wani akwatin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login