Showing 174001 words to 177000 words out of 181864 words
ko matata? Karka yarda ka ce zaka min iyayi akan mata ta, wallahi ranka zai mugun b'aci, dalla matsa ka bani guri."
Kura mishi ido suka yi baki daya ya fita hayacin shi, gani yake kamar cutar shi zasu yi, dan haka Abie da kan shi ya rike hannun shi tare da cewa.
"Karka zama mutumin da bai amsar ƙaddara mana, ka yarda dani babu abinda zai faru da Matar ka Insha Allah." Jikin shine ya shiga rawa tare da karkarwa, ya ce.
"Abie da gaske?" Ya tambaya hawaye na zuba mishi, share mishi kwalla yayi tare da cewa.
"Insha Allah!"
"Don Allah Abie kar wani abu ya faru da ita!"
"Da izinin Ubangiji babu abinda ya gaggare shi. Ka yarda dani."
Haka suka yi ta rarrashin sa, kwalla na zuba mishi,suka nufi airport aka gama kome, sannan suka dawo, a daren suka bar kasar,.sannan suka bar su Mommy da Innah da Beenah da suka shiga tattara kayansu zasu koma Nijar, inda zasu sauka a Niamey, gidan Abie.
Kallonta Innah tayi tare da amsar kayan hannunta tana ce mata.
"Sannun Zainabu! Dama baki da lafiya ne?"
"Uhmm" tace bayan ta ajiye kayan hannunta da sauri ta nufi ban daki,ta shiga kwara amai.
"Subhanallahi ikon Allah, Sannun amma ai baki ci kome ba naga yau tun farar safe, ban da ruwan zafi babu kome a cikinki."
Wasu kwallar wahala ne suka zubo mata, wato idan ta fahimta, Abie jika mata aiki yayi, wayyo Allah wannan abin kunyar da me yayi kama? Ina zata shiga ne? Maimunari na haihuwa ga Benazir da tsohon ciki, itama haka zata jera da su, abin kunyar yayi ƙamari.
"Sannun Mommy, tashi na wanke gurin" inji Benazir,
"A'a barshi na wanke ai kema ba dadin kike ji ba, taimaka mata ki kaita dakin ta."
"A'a ba sai ta kaini d'akina ba, takai ni dakin shi, nafi son kamshin turaren shi." Ta fada a wahale,
"Ai haka ne? Toh Allah ya raba lafiya, rabo ajali." Ta fada tare da gyara ban dakin, murmushi Beenah take tana kallon Mommyn su. Tana kaita dakin ta riko rigar shi ta daura akan hancinta, wani irin yanayi me dad'i yana ratsa ta.
"Mommy ko na duba miki turaren shi ne, tunda kina son kamshin, idan yaso sai kina fesawa."
"A'a nafi son na jikin rigar shi" ta faɗa tare da kwanciya, idanunta a lumshe, fita Beenah tai ta barta a dakin suka ci-gaba da tattara gidan,
Barci me nauyi ne ya dauke ta, haka tayi barcin da rigar shi a saman fuskarta.
**
Wajen karfe biyar na yammacin washi gari.
Abie ya kira Mommy, bayan sun gaisa take tambayar shi.
"Ya jikinta dai?"
"Toh da sauki zamu ce, amma zamu dawo ni da Khalil, shi zai zauna da ita, idan yaso kafin ayi aikin zamu yi ta kokarin ganin mun zo dubata"
"Toh amma kashe kudin ba zai yi yawa ba, kawai ku dawo din idan za a mata aiki sai ku je baki daya amma ayi ta sintiri a hanya akwai matsala"
"Toh shikenan, amma ya naji muryan ki kamar baki da lafiya?"
"Mura yake damuna"
"Allah ya baki lafiya"
"Amin Ya Allah Nagode"
"Ki kula da akanki da yaran Insha Allah jibi zamu shigo"
"Allah ya yarda" ta faɗa tare da zuba yawun a jikin wani abu.
Sako kafarta tayi kasa, sannan ta mike a hankali,ta nufi hanyar ban daki tayi wanka sannan ta fito daure da towel, zama tayi sannan ta kira Yumnah, shigo tayi da sallama.
"Mommy gani"
"Yumnah, kice Beenah ta dauko min kayana zan yi sallah ne"
"Toh Mommy"
Ta juya da sauri,. Kwanciya tayi sai da yarinyar ta kawo mata kayan, sannan ta saka tace mata.
"Kicewa Beenah tazo dakin nan ta had'a kayan Abien ku."
"Toh"
Ta fita da sauri, haka Beenah ta shigo ta had'a kayan tana sallah, tana idarwa tace mata.
"Benazir don Allah ki nima min abinda zanci yunwa nake ji"
"Toh Mommy me zaki ci?"
"Beenah duk abinda kika bani zanci."
"Toh" fita tayi dake suna da garin kunun tsamiya, haka ta dama mata da Fanke ta kawo mata, haka tayi taci hannu baka hannu ƙwarya. Tana gamawa ta mike tare da yawo a dakin domin zata iya amai, wayarta ta dauka tare da kiran wani shagon magani ta gaya musu abinda take bukata ko awa daya baayi ba, sai ga shi an kawo mata maganin. Dake ta biya baki daya, sa hannu Beenah tai sannan ta kawo mata maganin.
Bata sha ba gudun karta yi ama, sai da taji yunwa tasha. Da kunun.
Baki daya kamar an mata iyaka da falo, suna ta had'a kayan tana kwance, kuma zasu yi waya da Abie amma bata gaya mishi ba, kuma ta hana a gaya mishi, kuma irin cikin nan ne mai shegen saka fitina domin ya sakata mugun jaraba, ga laulayi ga fitin. Shi yasa bata son Fitina,.
Ranar da zasu dawo haka ta daure ta gyara jikinta, sannan ta kwanta a dakin, basu suka iso ba sai dare, a gajiye suka shigo gidan, shi kan Khalil daukar matar shi yayi suka tafi masaukin shi,
Abie kuwa bayan yayi wanka ya fito ya ci abincin dan ya ganta a dakin da yace zai shiga da abinci dakin ta shiga mishi masifa, shine ya fito yaci a waje, yana kallon Kanwar shi da Yumnah.
"Wai meke damun ta?" Ya nuna musu kofar dakin shi,
"Abie bata da lafiya ne, kuma bata cin abincin sai kunu"
Mikewa Innah tayi ta nufi inda Mijinta yake, tana dariya.
"Allah ya bamu irin naku ai da mun ware!"
Shi da Yumnah suka ci-gaba da hira, bayan ya gama ta kwashe kayan takai kitchen a daren ta wanke sannan tazo ta zauna a kusa dashi.
"Abie ya jikin Addah Munah?"
"Da sauki karki manta idan kinyi sallah ki sakata a cikin Addu'arki."
"Insha Allah, Abiena" rungume ta yayi sannan ya sumbaci goshinta, ya rakata dakin sai da ta shiga ban daki tayi alola da kama ruwa , yana tsaye ta kwanta yayi mata addu'o'in, yana cikin yi tayi ta hamma sannan ya tofa mata, kafin ya fita. Tare da kashe mata wutar dakin,
Dakin shi ya nufa a dan tsorace, bayan ya shiga ya same ta tana amai.
"Subhanallahi! Sannun" haka tay taimaka mata, ta fito ya wanke ko ina sannan ya shiga jera mata Sannun cikin jin haushi tace mishi.
"Zaka kyale ni da Sannun ka ko sai na fita a d'akin"
"A'a, Allah ya baki hakuri yi zaman ki, yan mata" ya fada tare da shiga ban dakin yayi wanka, ya a fitowa ya samu ta kashe wutar ɗakin, hango shi da tayi babu kaya ba karamin gigita mata lissafi yayi ba, dan Abie irin mazan nan ne masu kira mai kyau babu ko tumbin, kasancewar yana da tsawo, kuma zamani an Cigaba yana ƙoƙarin kula da lafiyar shi, ta hanyar motsa jiki, dirowa tayi a gadon ta fara rigima, shagwaɓa rikici. Kamar Baby Yumnah, dan ma Innah ta tafi da Widad tana gurinta, domin Yarinyar ta makale mata, itama kuma yadda take son Uwar Yarinyar haka take kaunar Yarinyar.
"Hammah don Allah!" Wani irin rikice mishi tayi, a sanin shi tunda aka daura auren, idan ya nime ta bata tab'a yarda tazo. Sai yara sun yi barci, musamman da suka dawo sam taki yarda ko hiran soyayya suna yi a gaban yara, kunyar Maimunari yasa basu sakewa, idan ma ta shigo dakin shi kamar daukar wuta ko mara gaskiya zai ga jikinta har rawa yake, dan haka ya zuba idanu yana kallonta.
"Zainah me kike bukata? Jikinki akwai zafi ko zamu je asibiti ne"
Yayi kokarin b'oye bukatar shi, cikin kuka me dauke da bukatar shi tace mishi.
"A'a kai nake so"
"Toh gani a gaban ki" fisge towel din tayi, lumshe idanun shi yayi..yana mamakin sauyin ta, matar da idan ya shiga d'akinta kamar yazo mata da alfasha, tayi ta kuka tana cewa ya rabata da abin kunya, dan haka tallafeta yayi tare da mata matsuguni a saman kirjin shi.
"Yau da kanki"
Gyada mishi kai tayi sannan, kwantar da ita yayi tare da mata rumfa da faffadar kirjin shi.
(😂inji Ubaid yace dan Iya wannan sai dai yar iya)
Ajiye kome yayi a gefe ya gurje soyayyar shi, domin ita ta kawo kanta, ya kuma tara mata gajiya sannan ya tashi ya had'a mata ruwan zafi, bayan ya taimaka mata ta shiga wanka.
Ya gyara d'akin, bayan ta fito ta samu yana gyara gadon, zama tayi shima yayi nashi ta fito, tana kwance, kayan barci ya saka sannan ya rab'a gefenta, tare da shafa gashin kanta, juyowa tayi tana kallon shi. Janyota yayi jikin shi ina shafa bayanta, ta kuwa narke Mishi, ya gaji sosai dake ya dawo daga tafiya ne amma matar nan haka ta hana shi hutawa. Kallonta yayi idanunta babu barci.
"Me kike so?" Ya tambaye ta a gajiye,
"Kai"
"Toh Zainah" haka bawan Allah nan ya raba dare akan matan nan, sai da suka dauki lokaci kafin ta samu nutsuwa, wanka yayi da ruwan zafi ya zo ya kwanta, karfe shida ya tashi yayi sallah asuba, sannan yayi nafilla da yake kafin sallah asuba. Yana idarwa ya tashe ta, bude idanunta tayi sannan ta zuro kafarta kasa, tare da ɗaukar towel dinta ta shiga wanka. Bayan ta idar ta fito ta gabatar da sallah asuba, sannan ta kwanta a gefen shi.
"Hammah barci kake ji?"
"Ke kuma rigima kike ji?"
"A'a kawai kai nake so"
"A'a kayana dai kike so"
"Kai Hammah meye haka" ta faɗa a shagwaɓe,
"Zainah na gaji wallahi, kuma ina son ma huta koda na awa biyar ne gaya min meye kika sha ne?" Ai kamar ya zage ta, ta fashe da kuka tana faɗa cewa.
"Idan ba lalura ba me zai saka na zama haka, ka hada ni da ciki me jaraba kace min ina rigima"
Tashi yayi zaune bakin shi dauke da sunan Allah, ya d'agota yana fadin.
"Alhamdulillahi! Kanin su Yumnah ne a jikin ki?"
Murmushi yayi tare da rufe fuskarta.
"A'a ai dole ayi ban ruwa, wannan kyakyawan dashen, Tabbas yana bukatar ruwa domin yayi yabanya"
Ai kuwa bawan Allah nan ya dage tare da aikin Alkhairi da aikin lada.
....
Khalil ya gaji sosai, dan haka matar shi ta taimaka mishi yayi wanka sannan ta dauko kular da ta kawo mishi na abinci, sai da yaci ya koshi sannan ya zauna suna hira sama sama, ganin zata fara barci ya sashi dole ya taimaka
_Zaku yi hakuri a madadin three pages zai zauna a biyu, domin zan cigaba da typing ɗin FREE Pages din kishi._
#Mai_Dambu
[8/18, 8:23 PM] Yar Kasuwa👳🏻♀️: HAKKIN MALLAKATA
#wed-Aug-2021
BOROROJI
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA SAB'ANI DA ƊAYA.
-----------------------------------------------
Ina kuke matan alfarma muna da kayan ado da kawa... Musamman turaren kaya wanda zai yi awa ashirin da hudu a jikin kayan ki, muna da scentball wanda ake wurga shi a wardrob sannan muna da Oil mai dan karen kyau da dad'i! Ina uwar gidan ina Amarya, maza garzayo kar a baki labari kayan mu free order! Sannan ina uwaren gida da amare nesa tazo kusa, muna da kayan Mata ingantattun masu kyau, Muna da gumba mai kyau yar asali, muna da hadin kazar amare mai kyau yar asali sannan muna da Sha daka mai kyau na amare da uwargida! Akwai parkege na amare mace da ta yarda da kanta Hajiya taɓa Ni ta wannan Number:08130269841 sayan na gari mai da kudi gida*
Kaza
Tara bala'i-
Gumba bucket ƙarami-
Gari-
Hatsabibiyar zuma
Hatsabibin gari
Zobe-
Tsumi-,
Maina ya rikice
Zazzogau
Haɗin gigita shi
Maƙale mata
Sayan na gari mai da kudi gida..... Sai kun zo muna maraba da ku
_______________________________
Cikin kaunar da soyayya mai karfi Beenah ta kula da al'amarin mijinta, shi kuma ya nuna mata yayi kewar ta, anan take shafa mishi Mommy na da ciki.
Dariya yayi ta mata, yana cewa.
"Eyye kice zamu yi wasu kanen!"
Gyara kwanciya tayi a jikin shi tana cewa.
"Eh mana, Allah yasa ta haifa mana yara maza dukka."
"Kuma kyakyawan irin ku!"
"Kwarai Abie ne ko Mommy kasan shi yafita kyau domin shi baki ne ita kuma fara ce, shi yasa Addah Munah tafi mu kyau.
Kaga Baby Widad mana yadda Allah yayi mata kyau ba Uba ba Uwa ba, kamar na boye kayan ta."
Sumbatar wuyarta tare da rungumo ta, ta baya yana shinshina gashin kanta, har barci ya dauke su.
Da asuba bayan sun yi sallah suka kuma komawa, barci.
***
Bayan kwana uku, suka tattara sai Nijar, inda suka yadda zango a Niamey, Khalil ya wuce da matar shi. Mommy kan ita dangana ta akayi da asibiti. Domin laulayi take sosai.
Yumnah da Innah suka dawo gida, tare da Baby Widad, abin tausayi yarinya da iyayen ta amma ta zama marainiya, dan ma bata damu da nonon uwar ba, ga Innah tana tattalinta haka sata take ganin Innah kamar uwarta.
... Umma Khalil sun je har asibiti suna gaishe da Mommy, sannan suka nemi a basu Widad. Abie bai hana su ba, sai dai yarinyar taki fir musamman da Hajiya Latifah ta nace dai ta dauke ta, nan yarinyar tayi ta kuka. Haka yasa Abbu yace mata,
"Kina son Yarinyar kika shegenta ta tun bata bata taka doron kasa ba, ai ban zata da kanki zaki ce a baki ita ba, na fi daukar cewa k'iyayyar uwarta ne zai damammali yarinyar ashe ba haka bane "
Wani irin kunya ce ta kama ta, karshe haka ta sunkuyar da kai, bata iya mika hannunta ba.
"Hammah Mamman, kayi hakuri ta dauki gudar jinin Mohan, haka zai kara mata imani da tsoron Allah, kuma tayi tuba irin wanda ake son musulmin kwarai yayi."
"A'a ai babu amfanin bata, yau Maimunari tana fuskarta rayuwa ce sabida ita, da yau bata rabata da mijinta ba, taya har wani zai samu damar cutar da ita?" Ya tambaye su ranshi a b'ace,
"Amma kuma ƙaddara karban shi ma ibada ce" inji Innah.
"A'a ban da irin wannan,.domin Kuwa son kai ya shigo cikin al'amarin na yarda da ƙaddara amma ban yarda akan cewa kaddara ce tasa Lateefah kashe musu aure ba a daren idan aka yiwa Nairah ko Radiyah ya zata ji?"
"Kayi hakuri duk abinda ya faru ya faru, sai dai a tari gaba. Allah ma muna mishi laifi ya yafe mana balle dan Adam! Dan haka itama Maimunari nasan da tana nan zata yafe mata, ai ba wani abu bane jarabta ce" Abie ya fada tare da sake murmushi, yana kara bawa Abbu hakuri, ita kam Widad tana jin muryan Abie ta shiga mika mishi hannu, daukarta yayi yana cillata.
"Ni dai karka karya min kishi ace nice na ƙaryata da gayya!" Inji Umman Dan Ba'are,
"Ai da narasa matar so! Wannan fararren idanun kamar na larabawan Libya!"
"Abie amma ai tafi Matarka kyau, kuma tafi Ammyn kyau"
Inji Benazir da shigowar su kenan.
"Nifa dama ina kulata ne sabida tana kama da Mohan, amma ban da haka, akan me zan damu kaina da ɗaukar mummunar mace" rufe baki Benazir tai tare da cewa.
"Abie! Da bakinka kake fadar haka? Kaga yar fara balarabiyar Libya da nijar, bafulatanar Mali da Burkina faso. My Bororoji baby"
Amsar yarinyar tayi tare da rungumo ta, sannan ta sake sautin kuka me ban tausayi, tana kara rungumar yarinyar a jikinta, tana jin wani irin kaunarta yana cika mata zuciyarta.
"Allah ya bawa Mahaifiyarki lafiya yasa ta tashi da kafarta."
"Amin Ya Allah, Allahummah Amin." Inji Hajiya Latifah da tayi laushi gwanin ban tausayi, haka suka yi ta amsawa da Amin.
**
Bayan kwanaki ƙalilan aka sallami Mommy zuwa gida ya Cigaba da jinyarta, kullum su Benazir suna hanya sai da Mommy tayi mata tas tace bata son ta kuma zuwa mata, taji da kanta itama.
Haka ta hakura domin da Khalil ne yayi magana toh sai ya hadu da rigima sosai zata yi ta kuka, tayi ta fushi tare da kin cin abincin, sai idan dan cikin ta ya isheta da juyi nan ne zata shiga niman abinci kamar mahaukaciya,.sai ta gama ci zata zauna tayi ya bakin rai kamar zata fashe. Sai da ya zauna ya gaya mata duk abinda take yaron cikin ta yana dauka.
Shine ta rage wasu abubuwan, dan ma tana shiga gurin Umma, kuma itama tana yawan gaya mata tayi ya rage wasu abubuwan na rikici, da saurin fushi domin yaro yana dauka domin har ta kawo mata wata kirsa wanda ya faru lokacin khalifancin sayyidana Umar, Allah ya kara yarda dashi. Yace akwai wata rana yayi tafiyar rangadi izuwa wata shashi na yankin da yake shugabanci, yace sai ya hango wani yaro ya shiga gonar mutane, yana ta musu barna,kuma abin da aka noma bai kai a cire ba, sai ya daka mishi tsawa bai saka yaron ya razana, suka kad'a suka raya yaron nan yaki gonar, sai Amiril Muminina ya tambaya suwaye iyaye nan aka gaya mishi ai iyayen yaron mutanen kirki ne, mahaifiyar shi tana aikin jinya mahaifin shi kuma babban mai koyarwa addinin Musulunci ne.
Dan haka yace yana son ganin iyayen yaron, dan haka baka raka shi ya tafi yaga iyayen yaron, nan ya tambaye su Meye yasa dan su ya kasance haka, iyayen suka ce basu yi kome ba, saima bautar Allah da kuma kyakyawan mu'amalar su da mutane, sai ya Amiril Muminina ya dubi uwar Yaron yace mata.
"Wannan yaron ba haka kawai yake wannan rashin jin ba akwai wani abu, ko lokacin kina dauke da cikin shi wani abu bai faru dake ba?"
Sai tayi shiru, na wani lokaci kafin tace.
"Eh wata rana na fito aikin jahadi da nake yi na jinyar mutane da kuma amsar haihuwa, lokacin ina da tsohon ciki, sai na ratsa ta wani gona, anan na hango Randa cikin farin ciki na karo kuzarina dan na isa ga Randa, gashi ana zafin rana sosai.
Koda na iso sai na iske randan nan