Showing 159001 words to 162000 words out of 181864 words

Chapter 54 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6293

da Ita" ta faɗa tana shafa kanshi, d'ago kai yayi yana kallonta.
"Ka hakura da ita bata dace da kai ba! Bata damu da kai ba, asalima matar da ta kai iyayen ta kotu meye zata haifa maka tsiya da bala'i, ba matar zama bane."


"Amma da baki tozarta ta ba, ai ba zata kai iyayen ta kotu ba, me yasa kike manta laifinki hmm Ammyn Kenan, wallahi abinda aikata shi yake kore min manema na, zan koma gurin Haddir, domin idan na cigaba da zama bakin cikin ki ne zai kashe ni, gashi nan ana zaman lafiya yarinyar da Hammah Khalil zai aura tace ta fasa sabida rashin adalci irin naki, sai ki Cigaba Ni sai ba zan cigaba da zama da wannan abin ba."


Ta fada tana kuka, sabida tausayin Yan uwan ta, tana kallon abinda mahaifiyar su, amma babu halin magana, babu wanda ya isa ya dakatar da ita..


Haka ta tasha kuka sosai domin tana son Safwan amma mahaiyarta,, tayi mata sanadin rashin sa, har abada domin ta samu labarin ya kusan aure, shi kan shi ma ya turo mata hotunan amaryan shi, kuma ya gaya mata yana sonta har kwanan gobe, kawai Mahaifiyarshi yake son yayi mata Biyayya, yana son ta rabu da Mahaifiyar shi lafiya, yana son idan zata sauko karta sauko...
Wannan Pagen yana magana ne fa akan biyayya ga Uwa.... Alhamdulillahi Ubangiji ya jikan Iyayen da suka rigamu gidan gaskiya, wallahi biyayya ga Iyaye shine babban kalubalen wannan zaman kuyi kokarin rabuwa dasu lafiya! Don Allah Karki yarda karka yarda rayuwar ta tashi babu ka tashi zero! Iyaye ba abin wasa bane, iyaye ba abin yarwa bane, karka yarda aci kasuwa a watse iyayen ka basu ribanci kasuwancinka ba, Karfin nasarata Addu'o'in iyayena, karfin Cigaba na Fatan Iyayena, bani da shekaru masu yawa. Amma Alhamdulillahi na rabu da mahaifana lafiya Yar uwa, ki gwada rabuwa da iyaye lafiya sai ki wayi gari ki rasa me kika yi Allah yake rufa miki asiri..... Addu'ar Iyaye ce.... Alhamdulillahi.....
_Kuyi hakuri babu lokaci yau din nan ne, yau addu'ar arba'in makociyata. So dakyar na samu damar typing ɗin su, kuma idan nace sai dare wallahi zan manta daki domin aiki zan shiga_
#Mai_Dambu
[8/15, 4:59 PM] Joindah: https://www.wattpad.com/1115798063?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=H4PLUmmQMtRivq0LpRHlS38%2Fr1hLcjzt2XEZ3yHCmyzI3xoWStQC02%2FROcdRbxcPubxgSNp7F%2BbsI7AVD0kyhHL5jlei18XLmYIFmbPXjnlRmUgtZXxtCYJkkmcIRyXT
#sun-Aug-2021
HAKKIN MALLAKATA
BOROROJI


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


BABI NA HAMSIN DA UKU.


Yana son duk abinda zai yi da amincewar mahaifiyar shi, yana son ita da kanta tace mishi ya je ya auro Radiyah, yana bin duk wani sharadin ta, dan a zauna lafiya.


Shi yasa baki daya yaƙi d'aga hanaklin shi, shi yasa yaki damuwa da irin hukuncin da ya yanke, baki daya ya ki mai da hankali kan Radiyah. Burin shi Mahaifiyar shi, ta ji dadin biyayyar da yayi mata, wannan dalilin da yanayin ya saka shi dauke kai akan Radiyah, kuma ita kanta tana mamakin yadda tunda tace bata son ganin su, har yau bai kuma mata magana ba, bai kuma kallon ta da batun ba.


Dan koda tace ya nime auren Yar kawarta amincewa yayi jikin shi har da rawa, haka da yayi ne yasa ta jin lallai zata barshi ya auri Radiyah, amma sai ta nunawa mahaukaciyar uwar su basu da hankali zata amince mishi.
*
Gefe Mohan ya motsa sosai kuma ya maida hankali, duk da yaki zuwa gurin Jalilah da sunan zance haka bai hana a fasa kome ba, Maimunari ce dai yasan ya rasata kenan. Shi yasa ya rungume auren Jalilah bawai dan yana da bukatar haka ba, kuma yau da gobe yana bukatar kulawar mace, idan ya dubi shekarun shi kara hawa suke, matar da yake so baya tare da ita.


Dan haka ya watsar da damuwar shi, domin yayi imani da Allah. Tunda mahaifiyar shi taki Maimunari ba zata tab'a kaunarta ba, ya kan zauna yayi dogon nazari akan me yasa kome yazo mishi a jagule! Me yasa kome yake bukata sai ya rasa? Shin ko dan bai kyautatawa mahaifiyar shi ce? Ya rasa gane abinda yake faruwa da al'amarin shi.


Da sallama ya shigo falon mahaifin shi, sanan ya nemi guri ya zauna, kafin yace mishi.
"Abbu kana jin labarin Maimunari kuwa?" Yayi tambayar a sanyayye.


"Baka tambaye ni, me yasa naki auren Yar Sarkin maradi ba?" Sunkuyar da kai yayi yana wasa da capter din falon.


"Abbu kayi hakuri, nasan tun wata biyu da suka wuce ya dace a ce anyi bikin kuma Allah bai nufa ba, ban san me ya faru ba. Kuma bana son na tambaye ka kar na shiga abinda bai dame ni ba. Ba wai damuwarka bata dame Ni bane sai dai bana son na cika bincike ne!" Ya fada mishi.


"Eh toh da farko yarinyar ta amince amma daga baya taki, wai na mata tsofa, na zata ko wani abu nayi ashe iya kawai girman da nayi ne, shine nace mata toh babu damuwa, kuma Allah yasa haka shine mafi alkhairi." Ya fada yana kallon Mohan da ya sunkuyar da kanshi.
"Mohan Maimunari ta kusan haihuwa, domin cikin ta ya girma. Sai dai kuma tana cikin damuwa ne, domin ko kwana biyu da suka wuce naji labarin bata da lafiya jininta ya haura." Da sauri ya D'ago kan shi yana kallon mahaifin shi.
"Abbu don Allah, ka hada ni dasu, dan girman Allah ka taimaka min, ina son sanin halin da Mata ta, take ciki ne idan ma cire abin cikin za ayi a cire. Ta huta wahalar tayi yawa"


"A'a yanzun take da wata takwas, idan aka cire karfi da yaji, abin cikin ba zai rayu ba..Insha Allah sunce nan da sati Uku zasu mata aikin shi." Kamar Ya fashe da kuka,yana faɗin.
"Abbu don Allah" ya zube gwiwar shi a kasa, idanun shi jajjur.
"Kayi hakuri! Insha Allah akwai lokuta da zaka ganta."


"Abbu kafin nan na kuma rasata kenan, na rasa ta har abada, ina kara hango nisan da take min, Abbu kayi wani abu, sabida ni Khalil ya hakura da Benazir, an tace ba zata aure shi ba dan zan auri Jalilah, don Allah Abbu kayi wani abu, don Allah ka taimaka min kar ya rasa yarinyar da take so, na yarda zan dauki kome amma ban da na zama sanadin rasa masoyin shi."


"Insha Allah ba zai rasa ta ba, ba zai rasa ta ba."


Sam iyayen su basu san abinda yake faruwa ba, sai da Mohan yayi bayani, kuma koda Hajiya Nuratu taji labarin bata ji zafin Benazir ba, sai ma burge ta da tayi tana son taga mutum na kishin dan uwan shi, uwa uba son kai ƙarara da aka nuna musu,idan wasu ne zasu ga kamar dama haka shiryayyen al'amari ne.
Dan haka ita da kanta ta sami Abban Khalil tayi mishi magana shima ya gaya mata ai ya samu labarin, dan haka suka kira Abie tare da tuntubar shi. Dariya yayi musu sannan yace musu.
"Ai shi ya biye mata ne har da d'aga hankalin shi? A'a kar ya damu tana taya yar uwarta kishi ne, shi yasa take ganin idan tayi haka shima zai ji zafi, itama tana can a dame balle shi, dan haka ku kwantar da hankalinku. Insha Allah Benazir matar Khalil ce."


"ALHAMDULILLAHI, mun gode sosai da wannan Alfarmar da kayi mana."


Haka suka tattauna abin su, sannan suka yi sallama, wani abu da mutane ya dace su fahimta, duk wata tushen matsala daga mace yake, mazajen da suka san ciwon kansu, zai yi wuya su zama tushen matsala, sai dai su zama ƙarshen matsala. Dan haka bayan sun gama tattaunawa ne Abbu da Abba suka kara tattaunawa akan matsalar matan su, shi Abba ya isa da gidan shi kuma ya san matar shi bata da matsala akan wannan maganar,


Dan haka bayan sun rabu kowannen su ya koma gida, koda Abba yasa mi Umma da maganar dariya abin ya bata, tace mishi.
"Ai tayi mishi da kauna shi yasa naga kamar bai da lafiya, ashe inda matsalar yaƙe kenan! Ai karka nuna mishi kunyi ma, kunyi maganar yanzun ya wani sake ranshi."


"Ba zan iya sitirin asibiti ba, idan zaki iya boye mishi ki yi, amma zan gaya mishi wallahi domin ba zan iya kallon shi cikin damuwa ba." Ya fada yana kallon ta.
"Toh babu matsala duk inda kace haka za yi.


**
A gidan su Mohan.


Wayar shi yana kara, duba wayar yayi ya ga babban limamin masallacin Niamey, dauka yayi suka ka gaisa.
"Yallabai, na maka karambani, na daura maka aure da kanwata shekaranjiya ta fita takaba, mijinta ya rasu, kuma ba yarinya bace can dan shekarunta talatin da biyu. Kayi hakuri amma bai zama dole ka rike ta ba, idan bata maka ba"


Murmushin jin dadi yayi sannan yace mishi.
"Babu Matsala Allah yasa haka shine mafi alkhairi, nagode sosai na amshe ta baka gaya min sunan ta ba."


"Sunanta Ummu Aimana"
"Alhamdulillahi, Nagode sosai Insha Allah anjima zan turo a dauke ta, nagode ka taimaki dan dattijo"


Wallahi labarin yayi mishi dad'i, dan haka ya shiga kiran yan uwan shi da yaran shi yana gaya musu, Aikuwa Khausar ta nufi kasauwa aka shiga hidima sosai, zuwa dare Umma suka zo aka dauko amarya, mace mai mutunci da sanin ya kamata.


Washi gari kuwa aka buga walima na manyan mutane, anyi nasiha tare da tsoratarwa akan aure, sannan aka yi rabo dan abin yazo a gaggauce, bayan an watse amarya aka kaita part din Hajiya Sahiya, sannan aka watse. Sai fatar Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a dayyiba,domin bata taɓa haihuwa ba.


Da alamu su Mohan za ayi kane (🤣🙄 Wallahi ban ce kome ba)


Danne Hajiya Lateefah sosai Umma take domin kuwa, ba karamin haukacewa tai ba, domin kuwa kuka tayi musu.
"Ni zai ciwa mutunci? Ya auro sa'ar Salman Meye ya rasa idan yace min yana bukatar hakkin."


"Kinga wannan ya zama son kai, bayan baku tare Kice kar ya auro wata, wallahi baki isa ba."


"Nuratu! Bayan shi ki ke bi? Toh na fasa aurawa Mohan Yarki wallahi na fasa! Kuma zan kira Nahnah na gaya mata yanzun."


Mikewa tayi tare da cewa.
"Alhamdulillahi, haka nake so domin ina son farin cikin yarana sama da na kowa musamman Ibrahim akan son zuciyar ki zai rasa yarinyar da yake kauna Kinga maza gaya mata wallahi ban ki mata biyayya ba"


"Ni zakiwa rashin mutunci? Toh fitar min a gida, ko na ci mutuncin ki" ta faɗa tare da kumfar baki.
"Sai me? Fita kan zan fita wallahi kawai ina farin ciki ne zaki raba wannan sharrin da zaki kula"


Fada Sosai suka yi sannan ta kira mahaifiyar su, ta ce ya fasa aurawa Mohan yar Nuratu, sannan Umma ta bar gidan, kusan hauka Hajiya Lateefah tayi a daren, domin bakin ciki ya hanata barci kuma ba auren shi bane a kanta zunzurutun kishi da haukar banza.
Washi gari.


Nahnah ta kira Abba ta bashi hakuri sannan ta ce su janye maganar auren, bai damu ba domin yasa karshe haka zai iya faruwa a fasa auren, Allah sarki Jalilah ce ma tayi karamar jinya, sabida an fasa auren Mohan da yaji kan shi kamar ya sauke nauyin da ya dace.


Dan haka yayi maza ya bar ƙasar domin matukar yana ganin ta tana ganin shi ba zata tab'a barin shi ya huta da batun auren ba.
*Kuyi hakuri muna fama da rashin wuta da babu gwara babu dad'i!*


*Hmm ku Cigaba da ɗaukar labaruna kuna juyawa! Daga free har na kuɗi bai isa ba? Sai an kwashe wannan ma. Daga yau tambarin littafina zai kasance kwanar Wata Insha Allah idan kuka ga labarin da yayi daidai da nawa Fasaha ta aka dauka! Kowa mai dambu muguwa mai_dambu Shegiya amma kuma labarin mai dambu ba zai tsari ba!? Kome da lokacin sa na saka abinda ya shafi kishi amma haka aka yi ta zagina na dauki fasahar wata Toh wannan karon a bar min labarina! Masarautan JORDAN bai tsira ba, Bahaushiyah bai tsira ba HABEESHAH bai tsira ba! Yau an diro Bororoji na gama shan bakar wahala da asarar data bincike akan abu wasu dan rashin Imani sun dauka! Na hana idanuna barci ina bincike amma ban tsira ba! Ban da ma hauka idan aka dauka ba a sauya tsarin labarin haka za a tafi dashi! Yadda Safina ta shiga Jordan a spy haka aka dauke shi aka rubuta! Yadda Husnah Habib Manga ta shiga Rayuwata Family Abubakar Moddibo haka aka dauke min Bahaushiyah Na Bature Yohanna Chibok labarina ne Dr Yohanna Chibok! Shima HABEESHAH an dauke shi an mai dashi Noorah uku. Kuma ɗan rashin mutunci sayarwa suke! Munafukai da suke karanta books dina suke saya suna shiru ana zuzzuta hauka da jahilci Allah ya isa Ban yafe ba kalmar turanci nayi amfani da shi a Kwarkwarah sai da aka ce nayi satar fasaha 😓 Ni kuma an dauke nawa an hana Ni magana Allah ka bi min hakkina Bororoji ma bai tsira ba haba mana*


#Mai_Dambu
[8/15, 9:54 PM] Joindah: HAKKIN MALLAKATA
#sun-Aug-2021


BOROROJI


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


BABI NA SITTTIN DA HUDU.
*ALHAMDULILLAHI. Hhhh ashe nayi kuskuren Pagen d'azun! Mommy Sayeed da Maman Sadeeq Nagode da ankarar dani🤣*


Miami.
A yadda yake tafiya zaka fahimci ya gaji da tarin ayyukan da yayi baki daya, bude mota yayi tayi maza ta bude tare da zare madubin idanun ta, kallonta yayi sannan ya bude motar ya shiga tayi maza ta zauna a cikin motar tare da kallon shi.


"Mohan me yasa nake binka kake wulaknta Ni? Karka manta kana aiki a kasata ce kuma Ni ban damu ba, ina son muyi alaka da kai ne wanda zaka gamsu Ni din mace ce! Kai hadadden namiji ne irin wanda nake bukata"


Kallon shi tayi tare da zare jacket din Jikinta, tare da kallon shi tana murmushi, dauke kai yayi tare da Cigaba da tukin shi. Murmushi tayi tare da bude kafarta ta kai hannun yatsunta bakinta ta jika sannan ta shafa gabanta, ta kai hannun bakinta tana tsotsa.
"Mohan naga zoben hannun ka, ina da yakinin kana da aure, me zai hana ka mai da ni side chick din ka, ka maidani your slut kaji na rantse maka ba zan tab'a kallon namiji ba."


Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mai da kanshi yana tuki, yana zuwa kofar gidan su, ya tsaya.
"Saka jacket din ki, kin gani nan! Mace daya nake muradi, mace daya tal ta ishe ni, i don't care about you but I caring for her, ina masifar sonta ita daya ce nake jin zata iya wannan shigar ban far mata ba, Moonah ko a ina matukar ta bani haɗin kai zan yi da ita ko a mota, ko a jirgin kasa, ko a jirgin sama. Ko a iya matukar zata ware min tabbas zan shiga jikin mata ta. Ita daya nake jin zan iya rudewa akan ta bake ba. Idan na kuma samunki cikin motana zan baki mamaki." Ya fada mata tare da fita ya zo ya fidda ta yana cewa.
"Bana wulaknta mace, amma kar na kuma ganinki a cikin rayuwata."


Yana shiga tace mishi.
"Ban damu ba, amma wallahi sai nayi fuck dinka sai na sha kome naka, zan saka ka, ka haukace a kaina. Ina son naji jikina a cikin naka na kuma gamsar da kai nima mace ce." Daga haka ya ja motar shi ya bar gurin.
Dariya tayi tare da kallon shi yana tsalla gudu, yana isa gida abinda ya fara nima shine magani.


Ya hadiya tun bayan rabuwar shi da Maimunari, Allah ne yake kare shi da tausar zuciyar shi amma wallahi yana bukatar mace, ya bisu su gaya mishi inda matar shi take amma fir sun ki.


Bayan yai wanka ya shiga closet din shi ya sauya kaya, sannan ya fito ya nime abinda zai ci.


***
Hankalin kowa a tashi, ina rike da hannun Mommy, gabaki daya na gama razana, kuka nake son shi amma na kasa, ina ma na samu arzikin kukan.


"Mommy! Haka azabar haihuwa yake? Don Allah ke! Mommy don Allah kice ba zan iya ba, su min aiki don Allah, Mommy sau daya yayi wallahi Kinga ya jefa rayuwata, cikin mutuwa" baki daya na gigice na kuma gigita iyayena, dake Mommy ce a kusa dani.
"Wallahi bani kuma haihuwa! Idan na kuma Allah ya..." Toshe min baƙi Mommy tayi, tare da shafa kaina tana karanto min addu'a, ina amsawa, sake dubani tayi dake ta gaya musu itama babbar likita ce, kasancewar haihuwar fari yasa ta kawo ni asibiti.


Abie sai waya yake mata daga bakin kofar, ita a birkice ni na birkitatta, Abie ya birkitta domin daga waje cewa yayi.
"Nayi danasanin karanta shara'a da ba likita na karanta ta ba, Uwata da ana amsar ciwon da na amsa miki."


Takaici ya kama Mommy, tace.
"Wallahi yanzun na fahimci magana Hajja da tace min sakalci yake addabar rayuwarki, idan baki min shiru ba sai na mare ki."


"Wayyo Allah na, Abie Mommy zata buge ni" nafada ina kuka.
"Hajja Kinga Ni Ko? Yarinya na fama da ciwo wai Zainabu dukarta zata yi."


Cikin jin haushi Benazir tace.
"Gaskiya Mommy ki fito karki dake ta, haka kawai Addah Munah tana fama da ciwo zaki dake ta, haba don Allah da wanne zata ji." Ta fada cikin kuka.
"Kiyi shiru kinji Beenah ta," ita kam Baba Mari, dariya suke bata, domin tun da aka fara nakudan suka rud'e, musamman yadda ita gwanar take narkewa. Tasan akwai katon aiki, domin daga wash Abie ya rikice kanen ma kuka suke, tunda aka kawo ta Asibitin da asuba,suke tsaye sallah ce take fita dasu.


Baki daya sun kidime, kowa gani yake zata mutu, karfe goma na dare, lokacin tayi laushi babu bakin magana sai ya da kai take, kafin Allah ya nufe ta da sauke nauyin da Allah ya daura mata, ta sauke ƙatuwar yarta mace.mai masifar kama da Ubanta, dan har yanayin Hajiya Latifah take dashi. Bayan ni gyara ta aka gyara babyn.


Sannan Mommy ta miko min ita.
"Mommy nawa ce?" Na tambaye ta,ina son yi kuka. murmushi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login