Showing 162001 words to 165000 words out of 181864 words

Chapter 55 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6271

tayi min sannan ta gyada min kai, tare da mika min ita. Da sauri na amshe ta, ina kuka tare da kirari ga Ubangiji, tare da mata addu'o'in. Albarka nake saka mata, cikin wani irin farin ciki nake mata du'a, har na gama sannan na mata Huduba da Maryam, tare da kallon Mommy.
"Mommy sunanta Maryam" murmushi tayi min sannan ta kara mata addu'o'in, sannan ta fita da ita.


_Mohan ya tabbata na rasa ka kenan! Ga Maryam tazo na maka gaban kaina. Duk da na tsane ka amma har abada ba zan daina kaunarka ba_


A hankali barci yayi gaba dani, karb'an yarinyar yayi tana kallonta. Kwalla ne ya cika mishi idanun shi.
"Rabonta ya tsaga, a wannan lokacin. Da aba ayi auren ba. Da abin kunya zamu gani, soyayyar su mai karfi ce, da ba a mallaka musu junan su ba, karfin rabon zai iya sakawa su aikata abinda zai dame mu! Kai Masha Allah nayi sabuwar Amarya dole ma na gayawa Yallabai."


Mikawa Baba Mari yarinyar yayi bayan ya gama mata addu'o'in, yarinyar tasha addu'a. Baba Mari ma haka ta mata, ai a daren ya kira PM ya yaga mishi, sannan ya gayawa professor Ibrahim Dan Ba'are, kafin ya rufe Number shi ya kira Mohan. Bai shiga ba, dole ya kira Dan Ba'are.
Canja mata daki aka yi, sannan suka koma dakin bayan sun gama kallon yarinyar,
Haka suka mai da yarinyar gurin mahaifiyarta, suka maida Baba Mari dasu Beenah gida, Mommy kuma ta zauna a jikin su, tana kallon kyakyawan Yarta da jikarta, cikin wani irin yanayi. Tashi tayi ta dauro alola bayan ta sallah nafilla tayi, tana jin wani irin nutsuwa ma shigar ta, har kusan karfe biyu, ta kwanta. Da asuba kukan jaririyar ya tashe ta.


"Toh Limamiya zaki gaya min lokacin sallah yayi ne?" Ta mike tana kallon yarinyar da take kai hannunta baki, ban daki ta shiga ya dibo ruwan zafi, ta kawo wasu magungunan, ta saka a ruwan tare da auduga ta goge kirjin Maimunari da take barcin wahala, bayan ta gama, ya maida ruwan, ta dawo ta kara goge bakin nonon, sannan ta sakawa Yarinyar yadda ta zoki nonon babu shiri ta bude idanunta.


"Mommy!"
"Yi min shiru, maza dauki nonon ki bata" cikin jin kunya ta ja mayafin Mommyn ta rufe nonon ta fara bata tana sha. Sai yatsina fuska nake kamar zan fashe da kuka nace mata.
"Mommy kuma sai yaushe zata daina shan nonon ni wallahi bana son nonona ya lalace."


"Idan baki son nononki ya lalace toh karki na daurin kirji,"(🤣 Joindah ana magana)

Aikuwa na zaro mata ido, tare da cewa.
"Don Allah! Aikuwa na daina" da taga zan isheta da shirme, ta nufi ban daki kafin ta fito mun koma barci sai da ta gyara mana rufin,


Da safe aka sallame mu, bayan likitocin sun dauki hotuna da yarinyar, lokacin da muka iso Baba Mari tayi min wanka bayan ta gama min tayiwa Babyn. Bayan ta gama na yarinyar, Mommy ta shigo da abinci da kuma wasu magungunan ta bani na sha, sannan na gyara na ci abincin kadan, ina kallon su cikin so da kauna, ita da Baba Mari da suke kiranta Hajja. Suna gama shirya yarinyar suna yi suna hira,kamar ba uwa da Y'a ba, domin hiran su me muhimmanci ne kuma da fulanci. Bayan sun gama suka mika min yarinyar, shigowa Beenah tayi tare da ɗaukar hoton yarinyar dani, domin tun aka fasa auren Mohan da Jalilah suka shirya da mutuminta, daukar hoton tayi ta tura mishi,bayan ta gama tura mishi sai ga kiran shi ta WhatsApp.
"Maimunari! Barka ashe mun zama Baba" murmushi nayi bayan na gaya mishi fuskar Yarinyar.
"Kai Jama'a wannan tadoke Mohan sai dai Ammyn don Allah kuna wata ƙasa ce, muzo ganin princess."
"Kayi hakuri kawai akwai lokacin da zaka gan mu. Ba zamu zo bikin ku ba"
"Alhamdulillahi!" Addu'o'in yayi min sannan ya gaya min zai turawa Mohan da sauran yan uwan shi.


Bayan mun mun gama wayar na kwanta da yarinyar ina jin su Mommy suna hira.
"Kinga bakin kishin wancan me karamin kan sun rusawa yaron nan niman auren shi" juya musu baya nayi, domin Mommy zargina take akan nice na ziga Beenah ta saka aka fasa auren Mohan.


***
"Mohan ga abinda muka samu tashi ka gani" mika hannu yayi zai amshi Babyn da yake hannun Maimunari, wayar shi tayi kara, tashi yayi zaune, tare da dafe goshinsa. Yau kwana biyu kenan yana yawan mafarki ta, amma na yau ya ganta ta haihu ne, kara wayar shi ya kuma ya duba.
"Abbu." Ya gani a rubuce. Dauka yayi tare da sakawa a kunnen shi.
"Abbu!"
"Alhamdulillahi ina tayaka murna ka zama Uba Maimunari ta haifi Y'a mace, har tayi mata huduba da Maryam."


Murmushin jin dadi ya sake tare da shafa kanshi yana murmushi, kafin yace musu.
"Abbu! Nine na zama Uba? Alhamdulillahi Ubangiji Nagode maka" ya fada bayan ya kasa cewa kome, kashe wayar yayi tare da fashewa da kuka, yana sujadar godiya, kuka yake, Allah ya azurta shi da yar shi na kanshi babu kazamta babu kome, kiran Khalil yayi bai same shi ba, ya tashi ya shiga ban daki yayi alola bayan ya fito ya gabatar da nafilla, har lokacin sallah asuba yayi, yana gamawa ya kwanta, sai barci, cike da farin ciki dan har zuciyar shi ya tafi gare su. sai mafarkin iyalin shi yake. Kamar zai yi yaya.


Washi gari, yana isa gurin aikin shi domin yana aiki da FBI ne, kuma yana isa ya gayawa abokan aikin shi matar shi ta haihu, aikuwa floranse ta tawo cikin murna zata rungume shi ya kauce ta fadi, wajen karfe sha biyu na rana Khalil ya turo mishi hoton yarinyar da uwar Yarinyar, wani irin abu yaji ya taso mishi, kasar hoton an saka mishi Number Beenah.


Da sauri ya dauka bayan ya kira, kuwa yaki shiga, tsaki yayi tare da saving Number, ya duba aikuwa tana Whatsp da shi, dan haka yaga ta saka hoton Babyn, murmushi yayi sannan ya tura mata sako.
_Beenah Mohan yake magana_


Bata buɗe ba, sai bayan awa daya ta bude sakon dan shima ya saka hoton yarinyar kan Dp din shi ne.
*laa Hammah Mohan, kai ne gani ga Addah Munah, na dauko maka hotonta?*
_😍😌🤗😍☺️ Zan so haka idan da hali idan kuma babu kice mata ina mata barka_


Voice ta saka, tana jin ta.
"Amma dai Addah Munah bai dace ba, kawai dan nace yana ga"


"Wallahi zan sab'a miki karki sake ki tura mishi hoton yarinya na, na tsane shi kuma wallahi idan bai daina bibiyar rayuwata ba, ba sai na bashi mamaki shima da yake da uwa take son shi kar ya kuma nima na, idan ba haka ba wallhi sai na bashi mamaki." Ta fada,. murmushi yayi domin babu macen da za a ci zarafinta ta yi hakuri kamar Maimunari, ta dauki kaddarorrin mabanbanta, taga jarabawa kala kala, dan haka bai ga laifinta ba....🙄🙄 Allah yasa labarin bai fara gunduran ku na kamar yadda ya gundire ni 😂🤣 ko mun yanke ne a wuce gurin 😂🤣 Wayyo ni
#Mai_Dambu...[8/16, 2:23 PM] Yar Kasuwa👳🏻‍♀️: https://www.wattpad.com/1116236352?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=DqKeHmGUt4S00sTqK6tvHmTwBNce4WSrmwTCLuX9s0%2BZ90klAu0vYuC2%2BG9j3NPu%2BdEkCw%2BpmnVewyRnnYYsyNs%2BbDZEQEPwUVZmfNteR0xffTyfTM0XIqekJsZ5PDHF


HAKKIN MALLAKATA
#Mon-Aug-2021


BOROROJI


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


BABI NA SITTTIN DA BIYAR.


Murmushi yayi yana mai kashe datar, yaso ya ga yadda Maimoon din shi take tsiwa, yasa so yaga yadda take masifa. A hankali ya shafa kanshi yana murmushin jin dadi,yace.
"Ya Allah ka zama shedana duk ranar da Maimoon ta shiga hannuna wallahi sai na gyara mata zama yadda ya dace insha Allah"


Ya fada yana shafa kanshi, domin yayi wallahi yana jin matukar suka had'e toh ba makawa sai ya bi da ita yadda bata zata ba, sai ya nuna mata shi
namiji ne da ba'a rena shi cikin sauki, duk zai iya hakuri da kome amma ya tsani rashin kunya, musamman irin bata da ta rena shi lokaci guda, bayan yana ji a zuciyar shi da gangan jikin shi tana haukar son shi, shafa fuskar shi yayi yana murmushi.


***
Ranar beenah ta sha fada a gurina, su Mommy watsar da mu suka yi, ranar da muka cika kwana biyar Abba da Abbu suka zo, abin ya bani mamaki. Amma ganin su bai rage kome ba, sai kara min kaunar Yaron su, na gaishe su ina kuka.


"Allah ya miki albarka, Ubangiji ya raya abinda kika haifa, Ubangiji ya shiga al'amarin ku"
"Amin Ya Allah, Amin Yallabai"
Mikewa nayi na koma dakin ina kuka.
"Ka ga ikon Allah! Yarinya ta raba gardama,kaga yadda ta dauko Ubanta, har da Kakanta. " Inji Abba,shi kam Abbu kiran matar shi yayi suka gaisa. Sannan ya gaya mata gashi a gidan su Maimunari, tare da sabuwar Amaryan da yayi,


Nan suka shiga wasa,har aka kawo min wayar, sannan suka gama maganar su ne manyan, akan nan da wata wata biyu zasu tawo bikin Beenah da Khalil, anan suka ci abincin rana da na dare, sannan suka wuce,


...
Tana gefena tana waya, wallahi bana jin me take cewa, domin maganar ciki ciki ake yin shi da salon shagwaɓa. Make ta nayi tare da kallon ta.
"Ki kula min da Widad zan shiga ban daki" na fada mata ina nufar ban daki, juyawa tayi gurin Yarinyar tana mata wasa tana waya, bayan na fito, Naji tana sauke nishi a hankali.
Fisgar wayar nayi tare da sakawa a kunnena.
"Khalil karka b'ata albarkan aurenka daga waje, duk abin da zaka yi ka jira ta shigo gidanka meye na wasu abubuwa haka?"


Na cilla mata wayar ta, mik'ewa tayi tana tura baki.
"Idan ke ba zaki kula da masoyinki ba, ki bar ni na kula nawa saurayin"


"Zo nan!" Na kirata, tana zuwa na rike kunnenta.
"Na makale a zuciyar shi ce, sabida soyayyar mu babu kazamta,ina rungume shi duk lokacin da naso, sau daya na sumbace shi ranar da muka sami sab'ani, ke soyayyar ku shirme ce. Ni tawa dashi guba ce domin idan muka hadu tabbas Allah ka dai yasan me zai faru" sannan ba ture ta, dariya ta saka min tare da cewa.
"Matar nan baki da alkibla, shekaranjiya kina ce kin tsane shi yau kuma kina haukar son shi. Duk wanda ya shiga tsakanin kuzari mutu wallahi"


Share ta nayi, na cigaba da rarrashin Widad da bata gajiya da rikici.


Haka Mommy ta shigo da kayan da aka kawo mana, akwati hudu, tsayawa nayi ina mamakin wannan al'amarin, kayan yarinya kuwa babu laifi, wai dan ba a can na haihu ba, da na ga kayan jaririyar. Har da sarkar farin gold,


**
Ranar da suka dawo ya mikawa Ummul Aiman hoton Babyn.
"Yallabai yarinyar nan tafi Baban ta kyau, dube hanci har baka. Shine baka kawo mana ita ba."


"Wallahi da na turawa Ubanta kamar zai yi kuka. Tausayi yake bani." Ya fada yana cin abincin shi.
"Gaskiya ya kamata ka gaya Mishi inda suke haka ba hujja bane."


"Insha Allah, zan gaya Mishi meye zaku yi na sunan dan na gayawa Khausar taxo ku tsayar da magana." Ya tambaye ta,
"Eh duk yadda kace"


Abu ne na kuɗi dan haka ya ware masu kudin da zasu bukata, dan haka aka shirya gagarumin walima,bayan an bawa wata gidan abincin daukar nauyin girkin walima, dan haka gefe guda haka suka yi ta zirga-zirga ita da Yar gidan Babban liman da ya bata, dake budurwa ce, gashi Radiyah bata gidan tana Nigeria, hoton yarinya aka bawa wasu masu yin aikin foste suka masu aikin dake an zuba musu kudi har da kalanda, memo, book, cup ba tangaran, stickers na mannawa a bayan waya, da abubuwa dayawa. Su kuma suka shiga hidima aka raba kaya sosai.


Lokacin da Khausar ta nunawa Hajiya Lateefah tace mata.
"Ammyn kalli wannan yarinyar ta min kyau!"
Kura mata ido tai yana kallon hoton Yarinyar da ya daki zuciyarta.
"Wacece ta haifi me kama dani"
"Ai baki sani bane, ai gobe gidan nan akwai walima dukda su yau ne suna mu gobe ne zamu yi namu matar da kika tsana ce, jinin ki Allah sai ya raba gardama gashi kowa yasan yadda Hammah Mohan yake kama dake shine Allah ya tashi sai ya sakawa Maimunari jininki me mugun kama dake."


Sake wayar tayi tare da dafe kirjinta, tace.
"Ta haifi cikin?"
"Toh dama kin kifar dashi ne? Ta haifi Maryam Sunan Nahnah, Kinga kuwa dole gidan nan ayi shagali"


Kirjinta ne yayi mata nauyi dan haka tana rike da shi, sai kallon ta take.
"Ammyn ya dai?"
"Babu kawai ina mamakin kamar da yarinyar tayi ne da mu, anya ma Yar Mohan ce?" Cikin bakin ciki da takaici tace mata.
"Ammyn Ubangiji ya dube ki da rahamar shi" ta kule dakin ta, domin tana bin na Ammyn zata fadi abinda Allah zai kama ta.


Washi gari aka yi walima kuma dake bata da kunya sai gata har a gurin tana gayawa mutane, yar Mohan ɗinta ne, gashi bata san inda yake ba, surutu irin mara hankali tayi ta sake yi shi.


Bayan an watse kayan da aka kawo na suna da mugun yawa Khausar da Ummul Aiman wacce suke kira Small Mom, suna ganin kaya, tace mata.
"Small Mom, mun hada kudi zamu mishi sayayyan namu kayan, amma ina ganin zata zo bikin Kanwar ta."


"A'a dota Abbunku yace ba zata zo ba, domin tana arba'in zata koma makaranta, kuma idan tazo zata zama abin nunawa a cikin dangi dan haka kawai tayi zamanta da yarta, idan zasu koma sai a koma mata da kayan."
**
Bayan suna da kwana ashirin, Mommy suka fara hidimar su, da shiga kasuwa sayayyar kayan Beenah da ita amaryan.


Jego ya amshe ni, idan ka ga yadda nayi kyau nida yarinya na kamar me,Bama fita Baba Mari jegon da yake min, dan haka na samu kulawa ainun.


Lokacin da muka cika kwana arba'in, Abie da Mommy da Baba Mari, da Yumnah aka bari a gida, bayan an kawo min Nanny wacce zata zauna har sai sun dawo. Yumnah suna tsakiyar karatun gama primary school ne,Ni kuma Abie ya nima min makaranta zan cigaba da aji. Duk wanda ya kalle ni ya san na samu nutsuwa kibar da nayi ta boye tsawon da nake da ita.


Ranar da na fara karatu, ranar n hadu da Malam Ansar, murna kamar zanyi yayya, har gida ya kawo ni na nuna mishi Yarinya na, haba bawan Allah haka ya dauke ta yayi ta hidima da ita. Washi gari haka ya kawo maka kaya niki niki.


A lokacin nake gaya mishi ai mun rabu da Mohan, dan haka karatu ne a gabana, kuma shima ya bani goyan baya, dan haka muka kuma dinkewa sama da baya.


... A can Nijar kuwa bayan an daura aure ne.
Anyi shagali sosai ranar budar kai wata Al'amarin ya faru.


Domin kuwa Baba Mari ta rike hannun Beenah ta mikawa Nahnah, ita kuma Nahnah ta kurawa Baba Mari ido.
"Mariya!"
"Mairamu!" Sai suka sake salati tare da fashewa da kuka.
"Mariya kina raye?"
"Mairamu kina nan da ma?" Komawa cikin gidan aka yi babban falon Abba aka zauna.


"Maza ku kira min kowa, har da Mohan da yazo, kowa karku bari har da Wancan kafiran."


Bayan minti talatin aka haɗu, kallon Mohan tayi sannan ta kalli Jama'ar falon tace musu, domin har da iyaye mazan.
"Mariya kanwata ce Yar baffana."
Share kwallar idanun ta tayi sannan tace musu.


"Zuri'ar Shehu Usmanu Wodaadabe, babban zuri'a ce fa ta haɗa yammacin Afirka zuwa gabashin Afirka, domin shi din daga kasar Libya yake kuma bafulatani ne na Usul Bororo,"
(Zaku yi hakuri domin zamu leka 75yrs ne da suka wuce! Da fatan zaku bude kanyar ku, ku fahimci bayani.)
.....
75yrs ago.
Shehu Usmanu Wodaadabe ya na da tarin dukiyar dabobbin musamman shanu da raƙuma, ba a batun kananun dabobbin,


Yana da mata uku, Maimunari itace Uwargina suna kiran ta da YADIKO Munari, yana da Mai bin mata Hajara Hajjo suna kiranta Yawuro, sai ta Ukun itace Amarya suna kiran ta da Inno, sunanta Ramatu.


Dakin YADIKO Munari ita ke da Yara maza, rai shida. Kafin mata biyu.
Iro, Kalamu, Isuhu, Dahe, Kabiru, Ya'u, sai Deja da yar karamar su Laure.
Dakin Hajo tana da yara mata biyar namiji daya.
Kuluwa, Sa'ade, Sakina, sai Rabi'atu, fatsuma, da Garbati.


Dakin Amarya tana da yara biyu domin ita wabi take, Sulaimanu da Tanimu,


Dukka yaran shi nan doka sha shida, Allah ya albarkace su da tarin ilimin addinin musulunci, kuma suna bada taimako irin na laluran rashin lafiya, dan haka sai ya zama na sun yi shura a rugar baki daya. Domin daga Libya sukan tafi Mali zuwa burkina faso, suna yawo sosai.


Sannan Shehu Usmanu Wodaadabe yana da Kane maza biyu, Abdullahi da Abbas, Abbas yana burkina faso, Abdullahi yana Mali, kuma dukkan su da iyalin su.


Duk shekara suna zuwa Libya, bikin al'adar Wodaadabe, dan haka lokacin da suka zo aka tsayar da magana yar Abbas aka bawa Iro mai suna Sadiya, shi kuma Kalamu aka bashi Yar gidan Abdullahi mai suna Dayyiba. Haka aka sha bikin su,bayan sun amince da junan su.


Sai ya zamana duk shekara ana wannan haɗin,kuma ana zaman lafiya.


Bayan wasu shekaru kamar ashirin da Biyar, duk da ana zumuncin amma yayi rauni.


Zuwan da suke duk bayan shekara daya, sai ya koma bayan shekara biyu ko uku, ya zama gidajen baki daya uku auren zumuncin da aka a tsakanin su yayi baya,


Amma kuma a Zuri'ar Shehu Usmanu Wodaadabe, ba a daina auren ba, a wannan dakunan.


Dakin Hajo sun yi aure yaranta a wasu gidajen..
D'ago kai tayi sannan tace musu.
" A cikin Zuri'ar iro nice nayi saura, ban sani ba ko akwai wasu dangin nawa! A Zuri'ar Isuhu dakin YADIKO Mariyah ce tayi saura ban sani ba ko a kwai Sauran! Amma a Zuri'ar gidan Ya'u Mamman ne yayi saura ban sani ba ko akwai sauran." Sunkuya da kai Abie yayi tare da cewa.
"A Zuri'ar Kalamu Ni da kanwata Amina muka yi saura dakin YADIKO"
"A Zuri'ar Sa'ade mune muka saura dakin Hajo" inji Abban Khalil dan Ba'are
Take dakin ya dauki kabbara.


( Mu Cigaba)


Bayan kamar shekaru ashirin sai iyayen mu suka fara ganin ya dace a hada yaran su aure.
Dakin YADIKO da dakin Hajo, aka ware matasa maza da mata.


Dakin Amarya aka ware yaran suma.


Dan haka aka kira Sa'ido aka ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login