Showing 75001 words to 78000 words out of 181864 words
koma tare"
"Amma nace ba? Kai ɗaya ne ki kana da wasu yan uwan? Naga kai kawai abbu ya damu dashi sai boye ka yake kamar wani abun da za a sace mishi" na fada ina mishi gatsine, tsaki yayi tare da mik'ewa yana faɗin.
"Ina da kane maza uku mata uku mu bakwai ne, amma nine babba."
"Auw shi yasa ka zama tikeke ashe haka abin yake? Toh Gskiya idan nine kai ba zan yarda a haife ni a farko ba sabida kar na zama tikeke irinka" na fada ina kallon shi. Girgiza kai yayi yana faɗin.
"Kai kan wallahi baka da lafiya kana bukatar likitan ƙwaƙwalwa ko zaka samu lafiya." Kallon shi nayi kafin nace mishi.
"Babu kyau dai cin mutuncin mutane. Idan bai gaya maka gaskiya ba waye zai gaya maka sai kayi kuma" wucewa yayi tare da barina ina ta mita yace min mara lafiya.
"Ina wayar ka?" Dai dai zai shiga wani daki.
"Oh toh gashi nan dai ban san ya zanyi dashi ba kuma na kasa kunna shi" juyowa yayi ya zuba min ido.
"Wallahi idan ka b'ata wayar nan sai na cire a kudin aikinka"
Kura mishi ido nayi ina kallon shi, kafin na kumbura baki ina hararan gefe da gefe na, na juya mishi baya.
"Dube shi dan daudu kawai" ya faɗa yana daukar wayar, ai ban san lokacin da kuka yazo min ba.
Ina yi ina shasheka, haka ya wuce yayi wankan shi sannan ya fito ya samu ina zaune na zuba tagumi..
"Abokina! Meye Labarin?" Ko kallon shi ban yi ba.
"Toh tashi muje ka gaida Ammina" haka na mike tare da zuwa kitchen na wanke fuskana, sannan na tawo na rufa mishi baya.
Koda muka shiga falon hannun shi da casbi irin ta yana zikiri, zama yayi ban san lokacin da ya fito dashi ba, sai na ji ya kara burge ni, domin tabon sallah shi har baki yayi na gaban goshinsa. Dinning ya nufa, na rufa mishi baya, dai dai shigowar wata hamshakiyar mace, zuba mata ido nayi, kallon mu tayi. Sannan ya tsaya turus tare da kura mishi ido. Tana son tuna yaushe rabon ta saka shi a idanun ta.
"Mohan kayi tafiya ne?" Ta tambaye shi tana niman gurin zama, ina tsaye a kan su.
"Ammin kin manta dani, haka nayi jinya babu ke babu Abbu sannan ki tambaye ni kice nayi tafiya ne" ya faɗa kamar zai yi kuka, ya mike zai bar gurin cin abincin sai naji ya masifar bani tausayi. Rike hannun shi nayi tare da kallon shi.
"Kaci abincin mana" na fada kamar zanyi kuka, tab'e baki tayi sannan ta mike abinta.
"Kai tafi can sake shi ta tafi dan gidan su, kuma ka shirya sosai domin ka dawo sai aure babu b'ata lokaci"
Ta fada cikin carelessly, wani irin tausayi ya bani kamar ba uwar da ta haife shi ba, haka ya fita tare da kowa ma apartment din shi, daukar abincin nayi tare da dauka a tire.
Yana fita lokacin itama ta dawo daga nata yawon tazubar, suna yi kicibis. Sake jakarta tayi yana kallon shi, baki sake.
"Mohan kai ne da lafiyar ka?" Ranshi a b'ace yake dan haka bai bi ta kanta ba yayi tafiyar shi, ina fitowa ta tare ni.
"Bakin algungunmi haka zamu yi da kai?" Da sauri na wuce ban kulata ba, ina zuwa na samu baya falon, ajiye abincin nayi na shiga duba dakunan da suke gurin. Can backyard na same shi ya zuba hannun shi dukka biyu a cikin aljuhun wando shi ya kurawa lambun idanu.
A hankali na isa tare da tsayawa na kalli yadda fuskar shi tayi jajjur.
"Iyaye suna da matukar muhimmanci a rayuwar mu, sannan duk wanda ya rayu da iyayen shi guda biyu bai kyautata musu ba, tabbas yayi asara duniya da lahira. Ban san meye ya sanya ka damuwa ba, amma ka tuna cewa. Kome uwa zata maka ba zaka iya biyan ta ba, Uwa wata irin halitta ce da ba kowa yake iya daukar kasadar da take dauka, Uwa wata duniya ce ta y'ayanta,. don Allah karka yi fushi da Ammin ka"
"Ka min shiru!" Ya daka min tsawa, a tsora ce na ja baya, tare da kallon shi, ina jin wani irin tsoron shi.
"Kasan yadda Soyayyar uwa take? Kasan har yanzun ban sami soyayyar uwa ba? Daga Anne Mahaifiyar Khalil sai Abbuna sai Alhaji Ibrahim Ibrahim Dan Ba'are,.mahaifin Khalil Ibrahim Dan Ba'are sai Khalil iya mutanen suna tsayawa rayuwata. mahaifiyata bata da cikakkun lokacin dan ta, bata damu da dan ta ba, bata damu da kowa ba sai daukaka da kyakyawan nasaba! Tun ina yaro na taso cikin kad'aici da rashin walwala. Kasan me yasa Uwata bata samu dani ba, idan na zauna bata tab'a tambaya na matsalata. Shine zaka gaya min soyayyar da tuntuni ta kashe shi fita ka bani guri.". Da sauri na juya ina kuka.
Duk sai naji babu dad'i, har kusan karfe goma, bai fito ba dan nima ban sami damar sallah isha ba sai karfe tara, yunwa ce ta dame ni na fito ina raba idanu. Haske na gani a wani korido, dan haka na kama Bin hanyar, murmushi nayi da naga dakin motsa jiki ne. Zama nayi akan inda ake d'aga karfe.
Na fara kiciniyar d'agawa amma na kasa, hararan karfen nayi tare da tura baki.
"Dan banza karka mike mana."
Na koma kan abinda ake dan gudun nan, na kunna aikuwa na saka da mugun gudu sai ji nayi na maku da kasa, timmm. Da sauri na mike ina zare idanu. Da suke cike da kwalla.
Tare da juyawa ina dubawa ko yana gani na.
.... Fitowar shi kenan daga ban daki ya tsaya a gaban tv da yake hade da Cctv, aikuwa yaga abinda Almamoon yake da farko bai maida hankali kai ba, amma lokacin da ya tiku da kasa bai san lokacin da takaici ya sashi jan tsaki, can kuma ya sake murmushi ko babu kome ya sha kasa, kai wannan yaron yana da kayan ban haushi.
A hankali yake bin yaron da ido duk wani motsin shi, sam bai yi kama da cikakken namiji ba, inji wani shashi na zuciyar shi.
....
Tana shiga d'akinta tayi zaman yan bori, tare da sake kuka kamar karamar Yarinya.
"Ni sahiya yau aka tozarta, sai naci kutumar kaniyar wancan bakin Yaron dani yake batu."
. Nan ta kira waya tayi ta bayani kamar zata yi sujada ga mutumin da take waya dashi kafin ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya.
... Gyaran murya yayi daidai na balla wani karfe, da sauri na ajiye ina kallon shi. Wato karatu da rashin abin yi yasa Yaron nan ya soma rashin ji baki daya baya jin magana, yanzun haka karfe biyu ya karya mishi a cikin ɗakin. Washe baki nayi ina faɗin.
"Hammah na, Sannun ka gama kukan ka?" Na tambaye shi ina leka fuskar shi,
Nad'e hannu yayi a kirji nima na nad'e tare da had'e fuska.
"Hammah Mohan cikina yana kukan yunwa, kuma idan da hali muje kaci abincin" na fada ina wani tsare gida, takowa yayi gabana na fara ja da baya, ina cewa.
"Kaga ka tsaya a gurin yanzun yunwa nake ji idan na koshi zan iya samun damar tanka maka" ban san na kai jikin wani karfe ba sai da nayi da baya zan fadi naji ya saka hannun shi a bayana ya zagayo dashi k'uguna. Hannuna dukka biyu suna kirjin shi idanuna a waje kamar zasu fado kasa.
"Baka jin magana, kuma a cikin albashin ka zan cire kudin gyaran kayan motsa jiki na." Ya fada tare da juyar da Ni, sannan ya cire hannun shi yana me niman hanyar fita. Da gudu na tare kofar.
"Kasan Allah yau zan bar aikin nan na fasa tunda dai haka ne kuma na daina abotar daga yau" na fada ina hararan gefe da gefe.
"Ok haka ne?"
"Am preety sure."
"Baka jin yinwa ne?" Ya fada tare da niman hanyar wucewa.
"Kuma fa haka ne wallahi yunwa nake ji muje na saka nawa na ci tunda kai baka ci"
"Canza kayan ka mu tafi mu ci a waje" kallon shi nayi kafin nace mishi.
"A wannan tsohon daren ina zamu sami abincin Hammah ka cika tone tone, Ni babu inda zani kawai zan ci wannan ya ishe ni." Na nufi hanyar falon. Na shiga bude kulolin abincin, sun Huce babu wani zafi sai dai dumi.
Dan haka na zauna na fara zuwa, zama yayi yana kallon yadda na lakwashe kafa tare da zuba abincin na fara ci, ina gamawa na kalle shi kafin nace mishi.
"Hammah kamar akwai magana a bakin ka" na fada ina kwashe kayan. Nufar kicin nayi na ajiye, sannan na dawo.
"Jeka kwanta dare yayi" ya faɗa min, babu musu na mike ina karawa da mika. A hankali na barshi gurin bayan na mishi sai da safe.
**
Da asuba bayan ya buga min kofa, nayi sallah ina idarwa na koma na kwanta. Domin har yanzun da gajiya a jikina.
Mafarkin wata mata muna fada da ita, lallai sai tab'a Hammah Mohan,.na hana ta shine ta zaro hannun ta masu kama da kusa ta yakushe ni, sai da na farka, ajiyar zuciya nayi lokacin da naji muryan Dan Ba'are yana magana kamar rarrashin Hammah. a hankali na fito daga dakin ina kallon su.
"Barka da safiya Hammah na, Hammah Khalil ina kwana?"
"Alhamdulillahi, Mamoon ka shirya kayan ka zamu koma tare."
Mai da idanuna nayi kan Hammah Mohan, dauke kai yayi kamar baya gurin gurin kulolin abincin na nufa ba irin na jiya bane.
"Mohan ba wani abu bane idan yarinyar bata maka ba sai a hakura meye na b'ata rai? Kawai ka shirya muje." Kallon su nayi tare da cewa.
"Hammah Mohan aure zaka yi?" Na tambaye shi a sanyayye, gyada min kai yayi tare da lumshe idanun shi, alamar yana cikin damuwa.
"Toh baka son matar da zaka aura ne?" Na tambaye shi ina cika cokali da madara.
"Eh bayan son ta, shine yake son lalata niman auren" murmushi nayi tare da cewa.
"Toh Allah ya kyauta."
Mikewa Hammah Khalil yayi tare da cewa.
"Bari na je na dawo kafin mu tafi gidan ministan Noma."
Gyada kai nayi mishi, kallona yayi ba tare da yayi magana ba, ya fice daga falon. Dawowa kusa da Hammah Mohan nayi zan mishi magana kawai naji ya fisgo ni da karfi, sai da ruwan shayin ya zube, karb'an kofin yayi yana kallon yadda nake zare idanuna.
Daura ni yayi akan cinyar shi tare da juyar dani, idanun shi sun yi jajjur.
"Idan muka je haka zaka min." Jikina da yake rawa, kuwa sai gyada kai nake alamar Eh.
A hankali ya sauke ni a jikin shi tare da barin gurin, zama nayi a kasa tare da zubawa shayin ido. Ban san me yasa idan Hammah Mohan ya tab'a ni har cikin jinin jikina nake jin shi. Numfashi na sauke tare da tuna yadda ya juyar dani ina fuskarta shi. Ina jin tasirin hannun shi a cikin ruhina da jikina.
***
Karfe hudu na yamma muka shirya mu uku, sai kallona yaƙe tare da karfaffan min gwiwa, har muka isa gidan tun daga parking space na Fahimci irin gidan da Hammah Mohan ya shigo.
Falon gidan aka so ya shiga yaki dole aka tura mu garden. Muka shiga tare, Hammah Khalil kuwa yayi tafiyar shi akan idan mun gama ya kira shi.
Muna zaune aka shiga kawo abin tab'awa, babu abinda muka tab'a, can kuwa sai ga Yarinyar doguwa kyakyawa da ita kamar bugun injin, tunda na hangota. Na kalle shi lumshe idanun shi yayi tare da gyara zaman shi, kafin ta iso na haura cinyar shi tare da kai hannuna wuyar shi, fuskar mu kamar zata had'e, idanun shi cikin nawa....... Ku more abunku kuma ranar da kuka min rahin daraja na bar ku na bawa WhatsApp 🤣😛😜🤣 suma Rahin daraja suka min.....
#Mai_Dambu
[7/28, 10:10 AM] RamlatArManga: https://www.wattpad.com/1106571155?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=MGSTqUwhvG4fBdc8Tqj6OqYqeY7iy%2Bvg8ZVvU9exRM%2FT3GQPgpgjcFkI2rY8w%2BnUMqLJf147FJNMo%2B9%2FQjDN7znC%2BTjtiS3PBxbASme2UWXXFcEf8ltwj%2F4SXO5evwr1
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
_Ina ganin Comments din ku da Vote din ku Nagode sosai, amma kuma yadda kuke son wani abun ba zai iya samu ba dole sai anyi hakuri da yadda tafiyar take! Allah yasa kuna fahimta_
BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS.
Hannun shi dukka biyu ya saka tare da rike Almamoon gam, yana goga mishi hancin shi kan nashi hancin, ganin yadda Almamoon ya rintsa idanun shi yasa shi kara sauke hannun shi zuwa cinyar shi.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Ubangiji yayi min tsari da wannan kazamtar." Ta fada tare da toshe bakinta. Cikin wani irin tsana da kyamar su tace.
"Ku tashi ku bar min gidan mu na tsane ka dama ba son ka nake ba, aka sani dole kuje bana son ganinku." A hankali na mike ina kallonta a raina kuwa dad'i naji tare da kallon yadda take matsar kwallan.
Mikewa yayi sannan yace mata.
"Lover na ne, yayi miki" kamar wacce zata yi amai ta fara yunkurin amai haka muka bar gurin ya saka hannun shi daya a aljuhun wandon shi, hannu daya riƙe da waya yana niman dan Ba'are.
"Kai Man har ka gama abinda ya kawo ka?"
"Kasan sarauniyar kyau ce da zan zauna kallonta mun gama kome saura kai da Ammin ku ji da sauarn." Ya fada tare da kashe wayar yana kallon yadda na takura a gefe guda, sai harde hannuna nake baki daya na gama kosawa na koma gida.
Takowa yayi har gaba na, tare da d'ago kaina.
"Meke damunka?"
"Babu"
"Ka tabbatar?"
"Eh" na fada tare da gyada mishi kai kwalla na zuba min. Fuskar shi ya kai kamar zai sumbaci bakina, nayi baya da kaina.
"Toh meye matsalarka?" Ya tambaye ni a gajiye da abinda nake mishi.
"Don Allah ka mai dani gida na gaji Ni ba makaranta ba ni ba gida b..."
"Baka son zama dani ne?" Cikin wani irin sarewa na zuba mishi idanuna da suka yi jajjur.
"Ba haka nake nufi ba"
"Toh nace ba zan kai ka gida bane? Ko so kake mutane suce na maka wani abu! Kayi min shi kafin raina ya b'aci." Yana rufe baki sai ga Dan Ba'are ya iso a masifance ya bude motar ya shiga,.nima na shiga.
Tunda na shiga na had'a kai na da gwiwa ta, sai kuka nake.
"Meye ya same shi?" Inji dan Ba'are,ya tambaya kamar zai tsaya. Banza Mohan yayi mishi kamar baya cikin motar.
Katse kukan nayi tare da cewa.
"Hammah Khalil zaka mai dani Maradi ko?" Na tambaye shi ina kara sake kuka,
"Eh zan mai da ka." Ya fada min yana kallona ta cikin madubi. Duk da idanun shi a lumshe yake bai hana shi dakawa dan Ba'are tsawa ba.
"Dalla can ka kalli hanya karka ja min magana, ya faɗa tare da gyara zaman shi jikin kujeran. Tare da lumshe idanun shi.
Haka yayi ta masifa shi daya tare da fadin.
"Wallahi na rantse da Allah idan baka min shiru na sai na ga wanda zai kai ka Maradi" had'iye kukan da nayi kenan ban kuma ko tari ba har muka isa gidan.
Muna shiga ana kawo mana abuncin daga ɓangaren Hajiya Sahiya. Ina karb'a kitchen na kai na juye abincin. Sannan na fito tare da nufar dakina na hada kayana.
Kwalla ne ya shiga zuba min, ina had'a kayan. Har na kusan gamawa na ji motsin mutum a bayana, a hankali na mike ban juya ba. Wani irin fitar numfashi na ja, tare da sake kayan hannuna. Kwalla na kara zuba min. Hannun shi dukka biyu da ya sakalo su akan cikina, na kalla. Kwallar da suke zuba ne suka kara yawan fita tare da zuba akan hannun shi, juyar dani yayi yana mai daura kaina kan kirjin shi. Ina jin yadda zuciyar shi take bugawa very faster.
Kanshi yana saman kaina, a hankali ya shafa bayana.
"Karka zama stupid, ka mai da hankali akan abinda ya kawo ka niman Insha Allah Wata sati zan shigo duba ka.". Gyada kai nayi sannan na janye jikina, amsar kayan yayi tare da fitar dashi, ina bin bayan shi. Yana fitowa falon ta mika min wayata da jakar Laptop, sai ta card din bankin shi. Kallon shi nayi domin kuwa idan na tafi da wannan kayan gida mai hana Innah ta min Yankan rago Allah da ya halicce mu ne, na bude baki zan yi magana ya daura min yatsar hannun shi a bakina.
"Na tsani musu" ya sanin katin a cikin hannuna. Sannan ya nufi Hammah Khalil, ya cakume wuyar rigar shi cikin fushi yana faɗin.
"Dan Ubanka idan kayi mishi magana sai na karya maka muƙaminka, Allah ya tsare hanya."
"Sake ni don Allah idan baka yarda ni ba, kazo muje." Ya fada mishi cikin jin haushi.
Haka ya sake shi tare da shigewa dakin shi bai kuma fitowa na har muka bar gidan. Yana kallon motar ta dakin. Bai san wani irin mugun kaunar Yaron yake ba? Bai san lokacin da kaunar yaron ya mishi kamun kazar kuku ba.
Abinda ya sani kawai yaron yana burge shi, toh bayan nan sai ya fahimci ko tab'a Yaron aka yi sai yaji kamar zuciyar shi aka tab'a. A cikin haka ya fahimci baya son yaga yaron yana mu'amala da kowa shi, yayi imanin yadda ya koyawa yaron yadda zai iya hakuri dashi.
Ya koyawa yaron wani mugun sabon shi, wanda idan ba shi ba ba zai tab'a hira da kowa me tsayi ba sai shi, ya sakewa yaron zuciyar shi yadda ba zai iya jin dadin Kowa