Showing 42001 words to 45000 words out of 181864 words

Chapter 15 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6295

nuna kanshi s fusace yana aikin,.yaki ya saduda dan haka wutar tayi kanshi da karfi, dole ya juya tare da matsawa da baya. Cikin mugun tsoro sannan wutar ya kuma komawa cikin ƙwaryan.

Ranshi ne ya b'aci, ya shiga aikatawa su Almamoon da wasu abubuwa da ban tsoro, yana kuma diban ruwan jini a wata kwarya ya bude wata kwarya ya saka hannun shi, kwari da tsutsa ya kwaso, ya zuba a cikin jinin nan yana karanta wasu mugayen ɗalasuman tsafi, munana ya d'aga ƙwaryan sama. Wadanan kalaman har da wasu kalmomin Arabia, tare da sunan Allah, kafin ya sake ƙwaryan a tsakanin sama da kasa, yana ambaton sunan Allah.(Look da gaske akwai kitabul sihir, na niman mallakar manyan ifiritai. Dan haka a sani akwai kalmomin sihiri wanda yake basu damar mallakar djinn)


Su kansu masu nima a gurin shi hankalin su ya tashi, balle shi da yake aikin ba karamin bala'in wahala yake ci ba, kuma yaki ya nuna yana cikin damuwa, sai da ya sauke wannan shaidanin aljanin me kai kamar na maciji ta tura shi, sannan ya mishi magana akan lallai ya tafi ya shiga jikin Mohan, ajiyar zuciya ya sauke bayan aljanin ya shiga cikin ƙwaryan, ya cigaba da had'a wanda zai hana yana kallon ƙwaryan.


Bayan kamar mintinan ƙalilan, sai ga dakin da suke yana girgiza, kamar za a fasa dakin, duhu ne ya mamaye d'akin, kafin wani abu ya fado dakin kamar wani katon dutse dif.... Ya dira a gaban su.
Huuuhuuuuhuuuuu!!!!" Ya fashe da kuka, yana ihu yake yana burgima.
"Karkuzu ka aike ni gurin da aka lalata min jikina wayyo ni, wayyo ni rayuwata." Burgima yake.
"Tashi munkiri tashi mara kunya, har akwai mutanen da zasu ja dani?"


Da sauri ya b'ace rashin a b'ace. Ya kalli Mutanen cike da bakin cikin yana me jin wani matsanancin kunya da faduwar darajar shi. Ya nuna musu hanya tare da dauke kai yace.
"Ku dauki ƙwaryan jinin da zaku gani a waje ku had'a tare da jaririn mage da kuma jinjirin jaki ku binne su da ransu."


Haka suka mike tare da mishi sujada, sannan suka fita da bayan sun.
Suna fita yan matan suka wanke su da ruwan bayan sun basu wasu kananun kwarya me dauke da jini.
Kafa kansu, suka yi sai da suka shanye tass, sannan suka yi gatsa. suka fadi bukatar su tare da yarda akan shi zai iya musu, tare da barin gurin, suna isowa suka kwashi kayan su, suka bar gurin.


***
Yau kam yafi ko yaushe bani wahala, domin kuwa ban tab'a jin ko ganin tashin hankali ba tunda na bashi maganin, nake tsaye a bakin kofar. Cak naga ya mike kafin kuma ya fara amai, yana yi yana jijjiga, shigowar Malik ya sashi kura mishi ido shima, yana mamakin wannan al'amarin.


Can ya fasa ihu, wanda ya sa dakin ya amsa. Kwanciya yayi yana burgima. Kafin ya fara karkarwa can kuwa sai ga dakin ya kama jijjiga, karatun Alqur'ani muka kunna, haka muka yi tashan wahala kafin can ya lafa, bayan ya gama gwara kan shi a bango.


"Alhamdulillahi" inji Hammah Malik, ajiyar zuciya na sauke ina kallon shi, kafin nace mishi.
"Da saura fa, dan har yanzun bai dawo hayacin shi ba. Ina jin sai mun had'a da limamin masallacin Makarantar mu ne Insha Allah"


"Eh toh Allah yasa a dace."
"Amin Ya Allah," muka bar dakin bayan mun gama gyara mishi kwanciyar hankali.


* Wannan karon kudina ma gida na kai, sabida ban tafi hutu ba ne zauna a jikin Hammah Mohan, koda naje gidan Innah ta kasa ta tsare. Sai dai itama kamar Malam Ansar ce domin kuwa ce min tayi.
"Karka ganka cikin gidan kudi kayi tsammanin Allah baya ganin ka ne, kasan waye kai ka kuma san yadda halittar ka yaƙe, karka sake naji wani abu ya fito, ka kame kanka domin masu kudin nan ba kirki ce ta wadacce su ba.


Domin na lura da kwaɗayi na damun ka, nan Malam Ansar ya kawo min korafin rashin mutuncin da kake mishi Almamoon!" Ta kira sunana. Cike da tsoronta nace mata.
"Inna shima me yasa baya jan girman shi. Sai ya"


Kai mun duka tayi abinda bata tab'a yi ba, sabida Malam Ansar tayi min.
"Kai min shiru butulu kawai, kasan kanka ai, kuma da yake kwadayi ya rufe maka idanun."


Idan na fahimta malam Ansar yazo ya had'ani dasu Innah ne, lallai ka bar mutum a inda yake, ban yarda nayi wani abinda zai saka tayi fushi ba, na kwantar da kaina nayi ta bata hakuri, har ta sauko.


Muna cikin ji Baba ya kawo min maganin da zan cigaba da bashi.
"Assalamu alaikum! Sannun ku, Mamoon kana ta jirana ko?"
"A'a kawai dai zan isa da wuri yasa na kagu."


"Toh Toh,,, gasu nan dai sai dai ban sani ba ko zai amince ya ci, wannan garin maganin Insha Allah idan ka karanta suratul Yasin, zaka tofa ko ka rubuta mishi, sai wannan zaka had'a zuba a wani mazubi me kyau kayi ta bashi yana sha, wancan me suratul Yasin, duk wanda yayo mishi sharri zai koma kanshi kaikayi kenan, wannan kuma suratul Rahama zaki karanta mishi, duk inda aka nufi shi da sharri zai kasance yana kaucewa ba tare da ya sani ba.


Wannan kuma Insha Allah zai kasance mishi kamar a saka wani abu ne s jikin shi, babu karfe ko itaccen da zai yi tasiri a jikin shi.


Wannan kuma Insha Allah zai taimaka mishi gurin, gano duk me shirin cutar dashi, Allah yasa mu dace"


Haka bayan mun gama na ce mishi.
"Baba dama maganar gidan fa?"
"Eh Almamoon mun gama kome sai dai muje ka gani, ko kuma."


"A'a muje dai" na fada mishi, haka muka tafi gidan, muka duba yayi kyau kuwa, ba laifi daga nan muka sami me gidan muka zanta dashi tare da cewa.
"Kayi hakuri Insha Allah nan da kwana ashirin zan kawo maka kudin ka, Nagode"


"Karka damu, Allah ya kai mu lokacin." Haka ya faɗa tare da rufe gidan, Ni da Baba muka nufi tasha. Bayan na sami motar Maradi muka yi sallama da Baba na Danka mishi kudin hannuna dukka, sannan na shiga dama kamar ni ake jira.


**
Isar dare nayi dan haka ban yi gangancin nufar gidan Hammah Mohan ba, na nufi gidan Malam Ansar domin zan kafta mishi rashin mutinci.


Ina shiga na samu Baba tana sallah isha, zama nayi bayan nace mata.
"Wash tsohuwa bayana"


Tana idar da sallah ta mike tana murmushi.
"Sannun Angona, yau kai ne a gidan mu?"
"Tsohuwa gani nan dai"
Ban daki ta shiga ta hada min ruwan zafi,sannan ta fito. Na shiga nayi, ina fitowa ta ajiye min abincin da man shafawa me gurguwa.


A hankali na shafa sannan na zauna muka shiga hira muna gaisawa.


"Daga ina kake?" Tsam nayi da hannuna kafin nace mata.
"Naje ganin gida ne."
Kura min ido tayi kafin tace min.
"Wani gari?"
"Damagaram"


"Almamoon kana dauke min kewar Y'ata, maganar ku tafiyar ku, murmushin ku.. Almamoon idan. A ganka sai naji ina ma kai jininta ne, duniyar nan cike yake da azzalumai marasa imani, ya shigo ya lalata min rayuwar Y'a yasa kowa ya guje ta.


Kimanin shekaru goma sha tara kenan rabon da naji muryanta. Ina kewarta saboda ita na kasa komawa ko ina, na kasa bin mijina da Yarana na kasa komawa Libya gurin dangina. Ina kewar Zainabu."


Rike hannunta nayi domin ta bani tausayi, nace mata.


"Me yasa mi Addah Zainabu?" Kwalla naji ya cika min idanuna,


"Wasu daga cikin kabilar Fulani suna da wata muguwar al'ada wacce matukar ta faɗa kanka shikenan. Rayuwar mutum ya lalace"
"Baba Mari wata al'ada ce haka? A'a Almamoon kai ne yau a gidan mu"


Juyawa nayi na watsa mishi kallon banza, kafin na mai da kaina gurin Baba Mari. Da take kuka. Nima tsintar kai na nayi da kuka domin duk yadda aka yi labarin ba me dadin ji bane.


Hakuri muka yi ta bata, har tayi shiru. Sannan ta gaya mana muguwar Al'adar fulanin, kallon ta nayi cikin rawan jiki nace mata.
"Baba kina nufin da auren wani akanta ya dauke ta yayi zina da ita?" Na tambaye ta kuka na kwace min. Domin am very shock, tana matar wani zaka kwanta da ita? Taya zaka iya zama da matar aure bayan kasan igiyar wani na kanta, ban san me yasa na tsinci kaina da kuka kamar Ni aka yi wa laifin. Dan ma taki ta gaya min sauran abinda ya faru.


Shima Malam Ansar haka ne, jikin shi yayi mugun sanyi.
"Almamoon zo na baka sakon ka" kamar ba zan taso ba, na mike domin ina cike da shi kuma na sami yadda zan kafta mishi rashin mutinci, muna fita ya tsaya a gabana.
"Ya isa haka kukan nan, meye ya kawo ka nan?"
"Kai me yasa baka gane bayani da Yaren da muke yi? Me yasa ka je ka sami Iyayena da maganar da tsakanina da kai ne? Kai baka da lissafi ne? Kome aka ce nake gayawa Iyayena? Nasan ciwon su da darajar su, karka kara zuwa gaban iyayena da maganar banza domin idan ka kuma zan baka mamaki dole ne sai nayi alaka da Ni?


Wallahi ka kuma duk abinda na maka kai kasayawa kanka, duk abinda kayi min ban tanka maka ba, sabida bana son damuwa amma akan iyayena wallahi za a jimu da kai domin na nasan darajar iyayena, shine abinda ya kawo ni gidan ka, kuma zan kwana gobe na wuce don't think that ko ban san me nake yi bane ina sane dashi ka fita idanuna"


Na fada zan juya riko hannuna yayi tare da matse ni a jikin motar shi.
"Ban ji kome ba, ban ji haushin ka ba, sai ma burge ni da kayi. Amma kasan me? Zo na nuna maka wani abu." Jan hannuna yayi har cikin gidan shi, ya kunna Laptop ɗin. Yana me nuna min wasu abubuwan. Kafin yace min.
"Ina ta tura musu sako ne, sabida matsalar ka, kayi Hakuri nayi laifi zan k'iyayye gaba, amma is very important ayi maka aikin na. Domin kafi karfi ta jinsin mata."


Cikin tsannanin takaici nake kallon shi kamar zan fasa ihu.
"Toh impossible" na gaya mishi tare da barin falon shan gaban yayi tare da had'a hannun shi guri guda.
"Please and Please listen to me, idan na kawo maka zancen shirme kayi tafiyar ka, amma abinda zanyi yana da matukar muhimmanci a rayuwarka."


"Look ba zan yi ba, kuma idan ka nace sai na maka abinda ba ka zata ba, dalla bani hanya na wuce ban tab'a ganin mutum me mugun shiga abinda babu ruwan shi ba sai kai.


Ina ruwan ka da lifestyle dina? Meye matsalar ka sa rayuwata? Ina ruwanka dani ne? Yes Ni mata maza ne, doesn't mean you have right to enter my personal life. Kayi rayuwarka nayi nayi nawa dole ne sai ka shiga rayuwata? Don Allah don Allah don sanka da Allah ka rabu dani"


"Dan ban da arziki? Kodan ban da kome?" Ya tambaye ni a sanyayye, takaici ya sani rike k'uguna da hannu bibbiyu, ina kallon shi.
"You see, ji abinda ka fada? Ji abinda ya fito daga bakinka? Kalli kalaman ka marasa dad'i da kyau. Yayi maka idan ka dagama kayi tunanin kome a kaina tunda baka san yadda ake gudanar da rayuwa ba, kana tare dani but kana drag din rayuwata."


Na juya a fusace zan fita. Jin shi nayi ya wani k'amk'ame ni, kamar wani zai kwace mishi ni,
"Don Allah don Allah karka tafi Almamoon, nasan za ayi nasara akan aikin da za a maka."


Kasa motsi nayi ina matukar tausayin shi, amma bawai ina jin shi bane a raina.


Zare hannun shi nayi tare da juyawa nayi ficewa ta, daga falon. Idan na cigaba da zama zan iya kafta mishi rashin mutinci. Dan haka ina fita na nufi dakin Baba Mari, na kwanta.


***
Tun da Almamoon ya bar gidan, yake zaune a bakin kofar shiga gidan, ya zuba tagumi hannu bibbiyu, yana kallon ta inda zai fito.


Duk sun zagaye shi, domin sun san Almamoon kawai yake jira.


Har dare bai tashi ba, yana gurin Malik kuma baya nan, dan haka babu wanda yayi tunanin sashi yayi alola ko sallah kamar yadda yake kullum, tunda ya zauna yake kallon kofar harabar.


Har dare ya raba, yana zaune a gurin. Yana ta gyangyadi, wasu irin kukan abu yaji ya bude idanun shi, bai ga kome ba, dan haka kamar yaro karami da ya rasa uwayen shi haka ya mike tare da shiga falon gidan, ya zauna a saman center table dake na Kwalba ce me ƙarfi.


Haka ya zauna kamar maye har kusan asuba, kafin barci ya dauke shi a saman gurin. Washi gari masu aikin gidan ne suka ganshi a gurin.


Tsoro ya kama su, dan dole suka hakura da aikin domin sun san idan Malik ko Almamoon. Yazo zasu sha wahala musamman Almamoon ma baki daya yake shuka musu tijara.


***
Ina sallah Asuba na tashi, tare da shirya kayana.
"Sai yaushe?"
"Insha Allah zan na zuwa Asabar da lahadi."


"Toh Allah ya nuna mana" haka na tattara na bar gidan, domin bana son na hadu da Malam Ansar, zai iya karya min zuciya, jiya kwana nayi da tunanin shi, sabida yadda yake damuwa da ni. Sam Ni ban damu dashi ba.


Amma shi ya daurawa ranshi damuwa a kaina.


*
Na isa gidan lafiya.
"Assalamun Alaikum"
Zubur ya mike tare da zuba min ido, tashi yayi ya juya tare da nufar sama da gudu, irin ta me cikakken kuzari, yake tsallake step by step, har ya haura dakin shi, bin bayan shi nayi da kayana na ajiye su a d'akina.


Sannan na nufi dakin shi yana gani na ya dauke kanshi. Takawa nayi har gaban shi. Juyawa min baya yayi, durkusawa nayi a gaban shi tare da riko hannun shi.
"Kayi hakuri na dawo da dare ne sai ban karaso nan ba, muje na baka abincin kaji"


Daura kanshi yayi akan cikina, tare da k'amk'ame ni, wani irin abu naji ya mike a jikina yarrrr, da sauri na ture kanshi, ina me kallon kofar. Daidaita tsawo na nayi ina kallon shi. A karon farko da kwayar idanuna ya faɗa cikin nashi.


Wani irin abu naji yana shiga cikin nawa, lumshe idanuna nayi tare da jin wata irin faduwar gaba. Lashe bakin shi yayi yana me kumshe idanun shi, janye idanuna nayi akan shi, tare da mik'ewa, kawai naji ya riko hannuna.


Kallon shi nayi bakina a sake, na kasa magana sai sunkuyar da kai da nayi. Zuciyata tana wani irin bugawa da sauri da sauri. Kwace hannun nayi ya kuma fisgo ni, tare da yi min dabaibayi da hannun shi. Ina son nayi magana amma baki daya kome na bakina ya kare, ga wani iskar da yake cika min bakina, kwalla ne suka cika idanuna. Dakyar Allah ya bani sa'a na kira sunan shi da cewa.
"Hammah"


Lumshe idanun shi yayi yana me kara rike ni gam a jikin shi. A hankali ya birkitani daga gaban shi zuwa saman gadon. Wani abu naji ya daki kirjina. Ina ƙoƙarin mik'ewa ya kuma danne ni. Sai na tuna wani hira da naji a gidan Radio BBC Hausa da Baba Yake sauraro. inda me tambaya yake cewa a hada shi da likita yayi mishi bayani shin mahaukata suma suna da sha'awa akan mata ko maza. Nan likitan ya yi bayani tare da cewa.


"Halitta ce sha'awa, kuma tana jinin kowani irin jinsi mutum ko dabba, dan haka suma mahaukata suna da ita."


Wayyo Allah na, na faɗa a raina da sauri na fara ƙoƙarin kwace kaina. Amma ina haka ya danne ni, tare da niman kwayar idanuna.
"Hammah don Allah tashi kaji, ya hakuri ka tashi bani da karfi irin naka."
Kamar wanda yaji abinda na faɗa mishi sai gani nayi ya tashi a hankali, tare da janyewa daga jikina, da sauri na dira a gadon ina niman hanyar fita waje, ai kuwa ya biyo Ni.


Allah ya hada ni da bindi, domin duk inda nasaka kafa yana biye dani, har niman faduwa yaƙe idan yana bin bayana, haka na dafa mishi abincin duk da babu dad'i domin har yanzun ban iya girki ba, kuma dai sai a hankali baki daya rayuwana ban tab'a shiga cikin al'amarin girkin Inna sosai ba, ina yi amma ba wai ina nufin na iya bane. A'a Kawai ina yi ne sabida kar na mutu da yunwa.


Ina juye mishi na zuba nawa na fara ci, kamar yadda nake ci. Rike hannun shi nayi sabida nashi cin a haukace ake yinta, ina ci ina nuna mishi. Haka shima yake ci a hankali yana kallona.


Har na gama ci na sha ruwa sai cin nashi yaƙe, kuma abin da j fahimta shine bai san koshi ba, yayi ta durawa kamar yaro karami,dauke filet din nayi, wani irin narke min yayi da fuska sai da tsigar jikina ya mike min, ina ganin kwayar idanun shi cike da wani irin maiko, yana tara kwalla.


Murmushin jin dadi nayi tare da cewa.
"Kaga idan kaci kadan sai kasha ruwa, sai ka bar inda iska zai shiga, fadar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne, a raba ciki kashi uku daya abinci daya ruwa daya kuma iskar da zaka shaka, idan kuma ka nace sai ka cika cikin ka ina zaka samu inda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login