Showing 63001 words to 66000 words out of 181864 words

Chapter 22 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6261

Mamaki ne ya kuma rufe Dan Ba'are, sama da baya. Kafin ya kalli Almamoon.
"Shi kenan, but i'm in your side babu wanda ya isa shiga tsakanin mu ina tare da kai."


Bude mishi hannun Mohan yayi suka rungumi juna, duk da kowa yasan Dan Ba'are dan uwan Mohan ne ta gurin Uwa kuma sun tashi tare, kome nasu daya ne. Amma haka bai hana Mohan kafkafta mishi rashin daraja ba. Kuma bai tab'a fushi yace ya rabu da Mohan ba, domin kaunar su daga Allah ce.


"Toh sake ni zan tafi maganar tafiyar ku, duk da mun gama rabin aikin kawai saura naje na karasa sauran ne" inji dan Ba'are,
"Ok Yaron kirki kayi abu me kyau maza kaje" inji Mohan ya faɗa cikin zolaya,
Wani banzan kallo yayi mishi tare da barin d'akin, shi kuma ya koma jikin window yana kallon yadda ake training ta baya, kasancewar asibitin a cikin Barrack yake. Tsayawa yayi sosai yana kallon kome.


Shigowar Dan Ba'are yasa shi juyawa yana kallon shi. Mika mishi wasu takardu yayi sannan ya kuma fita. Bayan kamar minti talatin sai gashi dauke har da jakar Mohan da kayan shi ya mika mishi. Sannan yace mishi.
"Toh na gama maka kome, Allah ya bashi lafiya"


Bai rufe baki ba sai ga Nurse sun shigo da gadon marasa lafiya, daukar shi suke son yi, Mohan ya dakatar dasu ta hanyar daukar shi cak ya fitar da shi daga cikin ɗakin, lokacin da ya fitar dashi kallon su Dan Ba'are yayi tare da jin idanun shi na cika da kwalla.
*Karka manta Mohan yayi maka kome a rayuwa Mohan ya baka kome da kake nima! Dan haka ka bar shi da Yaron ko zai sake kamar kowa kafi kowa addu'o'in Allah ya sauya mishi murɗaɗɗiyar hali dan haka zaman shi da Yaron sai ka ga an dace*
Inji wani shashi na zuciyar shi yake bashi shawara. Ajiyar zuciya ya sauke tare da taka musu baya. Har gurin motar shi tun kafin Mohan ya isa sojoji sun bude motar tare da sara mishi kwantar da Almamoon yayi sannan ya shiga cikin motar dan Ba'are ya shiga gaban motar suka bar asibitin.


Cikin abinda bai wuce awa daya na suna isa airport din, shi ya fidda Mamoon yana daukar shi tare da daura kanshi daidai kirjin shi. Mamoon ya sauke ajiyar zuciya. Cak ya tsaya tare da kallon fuskar shi jikin shi yana wani irin yanayi. Kallon fuskarshi yayi na few seconds kafin ya nufi cikin airport din dashi.


"Kamar yayi motsi ko?" Dan Ba'are ya tambayi Mohan, karamin murmushi yayi tare da gyada mishi kai,
"Alhamdulillahi don Allah idan kuka isa ka saka ido akan shi kaji"


Wani banzan kallo yayi mishi tare da dauke kai kamar ba shi ba, haka yasa shi jan bakin shi yayi shiru tare da murmushi. Suna shiga dama kamar su ake jira. Dan haka suna bashi keken majinyata suka tura shi a kai, sai cikin jirgin, tare da Dan Ba'are.


Mika mishi wata jaka yayi tare da kallon shi. Da idanun Mohan ya tambaye shi.
*Meye a cikin shi?*


Shima ya mai da mishi da cewa.
_Idan ka tafi ka duba_
Gyada kai yayi tare da mika mishi hannun suka yi musabaha, kafin suka rungumi juna. Babu laifi sun ji babu dad'i da zasu rabu da juna.


Leka Almamoon yayi da yake kwance a kujera.
"Allah yasa a dace"
Mika mishi hannun yayi a karo na biyu.
"Amin Friend zaka iya tafi" ya faɗa mishi tare da tsare gida dan yaga yadda yake leka Mamoon, shi a son shi kar wani yace zai kula Mamoon.


Dan haka Dan Ba'are ya juya yana dariya.
"Khalil Ibrahim Dan Ba'are Nagode da kome"
"Allah ya tsare ya kuma saka a dace."


Dakyar suka rabu, (sai kace masu aljanun kafin zuwa wani lokaci cutar sanyin su ta motsa 🤣 Wallahi sun cika fada kamar masu ganin hanjin juna) bayan fitar Dan Ba'are, basu jima ba jirgin ya tashi.


Ya juya a hankali yaji an bangaje shi ana dariya cike da mamaki ya juya, aikuwa Yarinyar ta koma bayan shi.
"Hammah kace kar Didih ta dake ni ba zan kuma tsokanar ta ba" d'ago kai yayi tare da tsare yarinyar da bata wuce shekara goma sha biyar ba ido sai hura hanci take tare da rike k'ugunta, ranta yana kara b'aci sosai. Sake baki yayi sabida wani abin mamaki yanzun yayi sallama da Mohan da Almamoon, amma ga wata yarinyar nan me kama dashi har da tsayin fuskar.


Cikin tsiwa ta juya shiga ƙoƙarin kamo yarinyar bayan shi ya kai hannun shi tare da kare ta, wani irin haduwa jikin su yayi tare da bada Wani sabon rikittaccen al'amari na daban. Kallon cikin idanun shi tayi, sai gashi ta kasa ko magana yayi mata Kwarjini. Idanun ya ne ya cika da kwalla.


"Wallahi Yumnah zan kama ki, sai na fasa bakinki mara kunyar banza kawai" ta faɗa tare da kwace hannunta.
"Toh Didih ba naga hoton ki da na Paul bane sai ki ce min solayinki ne Kinga ga Appa can muje." Inji Ita Yumnah,


Juyawa Yar budurwan tayi tare da barin gurin, shafa kan shi yayi yana kallon ikon Allah hatta tsayin da tafiyar. Daure fuskar sai dai ita wannan fara ce sosai. Kuma da alama girman kasar Turai ce domin kanta babu dan kwali riga da wando ne a jikinta sai jacket din da ta daura a k'ugunta. Idanun shi ne ya sauka akan Boom ɗinta, da sauri ya rintsa idanun shi.


"Yumnah" ta juyo tare da kiran yarinyar, aikuwa idanun shi ya dauka akan dukiyar fulaninta, had'iye yawu yayi, tare da kura mata ido.. da gudu Yumnah ta fito a bayan shi zata wuce ya rikota.
"Meye sunan ta."
"Benazir!!" Ta fada a hankali,
"Daga ina kuke?"
"Paris" ta faɗa tana kallon shi,
"Yumnah" wata mata ta kira ta, wacce zaka ga dai ba wata babba bace dan ba zata wuce talatin da yan kai ba.


"Na'am Nanny" ta amsa da gudu, rike hannun matar tayi tare da juyawa ta d'aga mishi hannu. Murmushi yayi mata. Da sauri yabi bayan su tare da kallon Number motar. Shafa kanshi yayi yana murmushi.
"Yar kwaila" shi da kan shi kuma ya kama dariya, tare da gyada kan shi. Yana tab'a gefen kirjin shi kodan kama da Almamoon zai iya sashi bibiyar rayuwar yarinyar.
"BENAZIR!" Ya ambaci sunanta yana kallon motar su, yarinyar tayi karama kuma fa, amma kuma ai bata mishi kadan ba, indai zai sake ta zai iya kuma zai koya mata son, a tunanin shi ba zata wuce 15 to 16 ba, dai dai ya kafa gwamnatin shi kenan. Dan bakin nan da idanun. Jan hancin shi yayi, Allah sarki ya rasa Mamoon Allah ya bashi Benazir! Gyada kai yake kamar kadangaren kafin ya isa gurin motar shi ya shiga tare da rufewa suka bar gurin.


***
Niamey.


Babban Ofishin primer minister, yana kallon Chef Judge.
"Yallabai Insha Allah kome zai wuce, sai dai ban da ikon Allah na gama kome Insha Allah babu abinda zai kuma faruwa kuma matsalar na gaya maka daga cikin gidanka ne idan har zaka iya taimakawa na gidan ka zai zama tarihi."


Mika mishi hannu yayi tare da mik'ewa yana faɗin.
"Nagode sosai, sai dai har yanzun bai tuntube Ni ba" ya faɗa a dame,
"Kai ka tuntube shi." Gyada kai yayi yana kallon shi.
"Ina kewar shi a kusa dani,.Insha Allah yana dawowa aure zai yi"


"Allah yasa a dace, zan koma." Ya fada tare da mik'ewa.
"Alkali ka tawo da Iyalinka muci abincin dare mana yau" sunkuyar ka dai yayi cikin sanyin murya yace mishi.
"Bani da iyali"
"Ikon Allah sun rasu ne?"
"A'a Allah ne bai nufa ba"
"Sai yaushe? Baka kasan ka girma bane?" Idanun shi ne ya cika da kwalla, tare da jin tausayin kan shi da kanshi yace.
"Insha Allah zanyi" ya faɗa tare da barin Office din, cikin sanyin jiki.


***
Tafiyar awa uku ya kai su garin Dubai, kafin suka tsaya na tsawon awa daya, kafin jirgin su ya tashi daga birnin Abu Dhabi zuwa Riyadh, sun isa ƙarfe goma na dare, motar asibitin yana jiran su, tunda ya sa shi ya nufi wata motar ya shiga domin akwai wani kamfanin da suka bude shi da wani Yariman saudiyar anan kasar, dan haka suka nufi masaukin bakin su da yake cikin Kamfanin.


"Mohan kai a ƙasar?" Inji abokin shi.
"Abeed gani nan." Bai gaya mishi gaskiya abinda ya kawo shi ba,.wanka tayi tare da saka jallabiyar shi cream colour..sannan suka nufi babban asibitin Riyadh, yana zuwa suka shiga tattaunawa da likitocin, kafin aka shigar da shi aiki.


Tun da yayi Sallah yake zaune a gurin,.har kusan asuba. Basu fito ba, ya tafi masallaci ya dawo, har gari ya waye kafin suka fito dashi babu laifi. A yanzun yana mai da numfashin sa.


Wani daki akai shi. Tare da sauya mishi kayan shi.
"Alhamdulillahi mun yi aikin cikin nasara,. An tacce jinin shi yanzun sai huhun shi shima an saka allura da maganin zasu yi flushing dattin ko yayi amai ko yayi bayan gari."


Gyada kai yayi sannan yace.
"Mun gode" ya faɗa tare da kallon Mamoon.


Tun daga ranar kome Mohan ya dauka, ranar Alhamis ya shiga macca yayi aikin Umrah, ya dawo ranar juma'a da dare, rabin addu'o'in shi akan Almamoon da iyayen shi ne da yan uwan shi. Amma karfin addu'o'in shi akan Almamoon ne.

Duk da Asibitin ba a zama amma shi saboda yadda suka ga ya damu da majinyacin yasa suka kyale shi, yana kula da duk motsin shi. Amma ta bangaren goge mishi jiki Nurse ne suke aikin nan, dan har zuwa lokacin bai yi amai ba bai yi kuma kashin ba. Ranar Asabar yana zaune ya kifa kanshi a gaban gadon.


A hankali na fara bude idanuna, ina jin amai rike zanin gadon nayi tare da yunkurin tashi, amma na kasa jikin babu karfi. Dan haka na dan juya kadan nayi ta amai, kakarin yaji ya farka. Yana tashi ya rungume ni, na cigaba da sheka mishi amai a jikin shi da jikina, sai da nayi aman tas a jikin mu, sannan ya daura kaina a kirjin shi ina jin kwalla na zuba min. Shafa bayana yake tare da cewa.
"Sannun"
Murza kai na nayi a kirjin shi, ya tab'a wani abu, sai ga nurse sun shigo, dan haka ya basu guri suka gyara min jiki shikam fita yayi daga asibitin ya koma gida yayi wanka tare da wanke kayan, sannan ya mai da wasu kayan, ya dawo asibitin ya same ni jingine.


Gashi kayan ya fidda kirjina, sau daya ya kalle ni bai kuma kallona ba, ya mai da hankalinsa gurin rubutun da suka yi. Kallon shi nake bako daya ya cika min idanuna. Hada min tea yayi tare da zama yana diba da karamin cokali yana bani a baki, amsa nake ina me kallon shi. Har ya gama ya bani magani, sannan ya dawo inda kafana yake yana matsa min su. Mamaki yake bani babu ruwan shi da magana tun sannun da yace min bai kuma magana ba.......


_🙄 Wallahi Na kusan fara rashin Daraja hmmm bana son na dauke labarin daga Wattpad kuma wallahi idan na cire zan dakatar da rubuta shi baki daya ne na Fara na kuɗi na shi kuma zai kai Okada Insha Allah ku bani had'in kai bana son ma fara book din kudi na dakatar da Wannan kuma bana son na sayar da labarin! Idan kuka bari na dakatar tabbas zamu ji babu dad'i bana son haka shi yasa nace kuyi comments da Vote idan babu Insha Allah Ranar Monday Zan fara KISHI a tsakanin zubda jini........iya comments da Vote kawai na bukata domin akwai mutanen da suke buƙatar Bororoji ya koma na kuɗi amma nace a'a kuyi wani abu ko nima na fara rashin Daraja kuma ba iya Pagen nan ba all Pages da masu zuwa👏🙄 Wallahi na iya rashin Daraja na fitar hankali musamman akan Zanen kaddara ta 🤸😒😏😡_
[7/25, 9:44 AM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


_Eh toh nayi ritaya daga Rashin Daraja! Sai dai kuma an koma Gaba gad'i🤫_


BABI NA ASHIRIN DA HUƊU.


Kura mishi ido nayi, ina son ya kuma ce min koda Sannun ne amma fir yaki kallona, da na gaji da zaman kurame yana miko min tea din na dauke kai na. Sake tura min cokalin yayi na kauda kaina. Ajiye kofin yayi tare da mik'ewa yana duba maganin da zai mika min. Shima naki kallon shi sai ma ƙoƙarin sauka akan gadon da nake yi.


"Ina zaka?" D'ago kai nayi ina son kallon shi amma yalwataccen gashin kaina ya hanani ganin shi sosai. Sake yunkuri nayi tare da zamowa zan fad'i, cikin wani irin kulawa ya tare ni.
"Gida zan koma" na fada mishi ina maida numfashi.
"Ok ince kana da kudin jirgi?"
D'ago kai nayi ban san lokacin da kuka ya kwace min ba, tare da kokarin kwace jikina, a hankali ya mai dani saman gadon, sai shesshekar kuka nake? Daukar rigar shi yayi tare da wayar shi ta fita. Bai damu da halin da nake ciki ba. Koda ya fito shekar isa yayi tare da fesarwa. Sam bai iya rarrashi ba, asalima kanen shi basa rikici wannan da alamun shine auta a gidan su, shi yasa bai rena kuka. A hankali yake walking a cikin harabar asibitin hannun shi zube cikin aljuhun rigar shi. Karar wayar shi yaji sannan ya dauka.


"Ya?" Ya tambaya,
"Ya me jikin?"
"Am think da sauki"
"Mohan anya kana kula da lafiyar shi kuwa?" Inji dan Ba'are,
"A'a Alhaji ina ganin me zai hana ka kwashe min albarka tunda ka bani aiki na gaza" ya faɗa tare da shafa kanshi,


"Toh tunda haka ne ai gwara Ansar yazo gare shi" ya caka mishi bakar magana yadda shima zai ji zafi, tsaki yaja tare da katse kiran, yana me jin haushin Dan Ba'are kuma yadda yake ji da zai same shi dan Ubanshi sai ya kirb'a mishi naushi a fuskar shi. Da dan sassarfa ya nufi cikin asibitin.


Yana shiga ya same ni na cusa kaina a tsakanin cinyoyina ina kuka, banging kofar yayi da dan karfi wanda ya razana ni. Na d'ago kai ina kallon shi wani b'ata rai yayi sama da koyaushe.
"Oya dauki tea ko na zane ka" ya nuna min kofin, kallon shi nayi naga yana niman inda zai zauna. Bayan ya leka inda yake saka cajin shi. Wayar cajin ya dauko. Ban manta ranar da Malam Ansar ya zane ni ba, jikina yana rawa na dauki shayin. Na kafa kai na fara sha, yayi sanyi toh kuma sai na fara jin zan yi amai.


"Idan ka sake ka min amai sai na zane ka" ya zaro min idanun shi. Gyada mishi kai nayi tare da kurb'an ruwan tea din, ina sha ina shafa wuyana. Ina gamawa na je ajiye cup din kawai ya fadi kasa, ya tarwatse. Kafe ni yayi da ido.
"Kayi hakuri ba da gayya bane"
" A cikin albashin ka" ya faɗa min tare da dauke kan shi. Tunawa da nayi, ina aiki dashi ne dan na saya mana gidan da zamu zauna na budewa Babana shafi saura kadan na karasa kudin gidan ban san lokacin da na fashe da kuka ba. Domin nasan kawo ni asibitin ma da kudina ne.


"Hammah Mohan" a masifance ya kalle ni, sunkuyar da kai nayi ina kallon kasa. Share ni yayi ya cigaba da duba wasu takardun shi, yana turawa a Laptop din shi, da na gaji kwanciya nayi ban san lokacin da barci yayi gaba dani ba.


Jin ya daina sauraron kananun kukan shi ya sashi d'ago kai, sai ganin shi yayi yana barci.mikewa yayi tare da gyara mishi kwanciyar shi, ya lullube shi sannan ya koma ya cigaba da aikin shi. Wayar shi ce ta dauki kara, ya kurawa Number ido, wanda ya saka.
"Abbu" cikin sanyin jiki ya dauka tare da sallama.


"Babana ka kyauta? A ce tsawon lokaci bamu nime ka ba kai ma ba zaka nime mu ba? Toh duk inda kake ina son ganin ka cikin sati me zuwa kana jina?" Gyada kai yayi kamar yana gaban shi yace mishi.
"Afwa Abbu Insha Allah"
"Khalil ne ya bani Number ka da ba zaka tab'a niman mu ba, ina kewar ka."
"Nima haka" ya faɗa a sanyayye, kafin suka yi sallama,


Har zai ajiye wayar yace mishi.
"Abbu don Allah karka gayawa kowa na sami lafiya kawai ka bari na zo da kaina."
"Insha Allah" ya faɗa a sanyayye kamar Mohan din, kashe wayar yayi tare da kura mishi ido, yana kewar shi sosai. A fisge ya kalli inda Almamoon yake kwance yanzun dai ganin likitan da yake son ya kai Almamoon ya fasu kenan.


Tunda sun tattauna da Dr Hisham Hadid, ya haɗa shi da wani likita a China Dr Zenrog Chuo a garin Yunnan, amma babu kome insha Allah zai fara tuntubar iyayen yaron dai yana komawa dashi gida gaban iyayen shi zai kai shi kuma su saka idanu akan shi.


Kaf idanun shi yayi akan hotunan da Dan Ba'are ya gama hada mishi kome, murmushi yayi sannan yace.
"Best friend like no other" yana gama abinda zai yi ya Laptop din ya fita tare da zaga garin.


Bayan fitar shi da awa daya na farka, tashi nayi sakamakon ciwon cikin da ya dame ni, sosai nake jin ciwon kamar zan yi hauka. Haka nayi ta fama har nurse biyu suka shigo. Ganin basu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login