Showing 30001 words to 33000 words out of 181864 words

Chapter 11 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6255

su, sannan ya koma dakin shi yayi Sallah la'asar, kwanciya yayi dan har yanzun bai warware ba. Dakyar ya ke takawa, sabida ciwon jikin shi.


Karfe biyar ya fara shirin zuwa kasuwa, kowa yaje bai zauna ba, haka ya shiga niman aikin yi dakyar ya samu wani kwashe kwata,. Lokacin da ya isa bakin kwatar, kallon gurin yayi kawai ya fara jin amai, babu shiri ya matsa tare da nufar gefe ya zubda yawu, sannan ya nutsu yana tuna hiran da yaji su Innah suna yi.
"Malam maganin ya kare kuma babu kudin saya, wannan kudin na makarantar shi da."


"Adana mishi, karki tab'a Allah zai kawo yadda zamu yi"
Kwalla ne ya zubo mishi, sannan ya shiga ramin bayan ya saka takalmin aiki, ya fara kwashe kwatar, cikin juriya yake aikin har ya gama, sannan ya fita ya wanke jikin shi suka dauki CD dubu biyar suka miki mishi. Saboda sun nime mutane dayawa sai su yanka musu kudi shi kuma cewa yayi aba shi duk abinda ya samu.


Kamar ya kwanta a.kasa dan murna dauki kudin ya saka a can cikin wandon shi sannan ya koma inda suke zaune, kasancewar a bakin kofar kasuwa ne a nan yayi Sallah bai bi masalaci ba, yana idarwa yace me shayin da yake Baban Salihu Bukar.
"Baba Ina son na je na sayo maganin Babana, don Allah idan malam yazo ka gaya mishi."
"Toh babu kome" ya faɗa bayan ya amshi bayanin shi.


A gurguje ya nufi gida, ya shiga da sauri yace.
"Innah bani kwalin Maganin Baba"
"A ina"
"Inna babu lokaci bani don Allah" ya faɗa mata a wujilance, dole ta bashi tare da kallon shi, ya fita bayan kamar minti goma sha biyar ya dawo, sannan ya dauki abincin shi na dare ya tafi, duba Maganin yayi sannan yace mata.
"Yaron nan da iyayen shi sun tallafi al'amuran shi tabbas sai sun fi kowa moran shi, ina tsoron ranar da zai fahimci ainihin waye shi? Ina jin shakkar tambayar da zai mana, ban san amsar da zan bashi ba"


"Allah ya rufa asiri" inji Innah.


***
Maradi.


Kurawa wasikar idanu yayi sannan yace mata.
"Baba Almamoon mata maza ce"
"Bana tunanin haka, idan har mace ce abubuwa dayawa zasu bayyana mata, kama da cikar halittar jikin ta, sauyawar ta na girma ko na wani iri. Eh kuma na fahimci wani abu mata maza ce shi yasa jikinta bai nuna alamar mace ce ba sai dai jinin da take."


Kallonta yayi na wani lokaci kafin dafe goshinsa, idan yace baya kewar Almamoon yayi karya, bai san lokacin da son Yaron ya kama shi ba, amma tabbas zai iya kome dan samun damar rayuwar shi,


Mik'ewa yayi tare da fita daga gidan yana faɗin.
"Baba zan fita"
Ya ce mata,
"Allah ya dawo da kai lafiya"


Koda ya fita makarantar ya nufa, gidan kwanan dalibai ya nufa tare da niman wani abokin karatun. Kallon shi yayi bayan ya fito yace..
"Malam gani" shiru yayi kamar mai tunani, kafin ya juya ya kalli Yaron.
"Tambayar ka zanyi" ya faɗa haka yana kallon yaron, kamar yayi shiru. Sai kuma is very important, yasan halin da Yaron yake ciki kowa sunan garin su ne.
"Daga wani gari Yaron nan yaƙe?" Ya tambaye shi yana kallon shi.
"Eh toh gaskiya yace mana daga Damagaram yake, yayi makarantar Annur," ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce mishi.
"Bai gaya maka sunan unguwar shi ba?"
Shiru yayi sannan ya kuma kallon malam Ansar, kafin yace mishi.
"Kamar yace gidansu na kusa da makarantar ne."
"Nagode" ya faɗa har ya juya zai tafi yace mishi.
"Karka fassara da wata manufa, naga ya tafi ne babu sallama" ya faɗa tare da muzurai.
"A'a wallahi."
Ya fada ina murmushi, dan shi bai tab'a shiga wannan shiga cikin shirmen da ake yi a cikin makarantar ba, asalima shi tausayin Almamoon yake, dan haka yayi tafiyar shi.


***
Watsar da kayan wardrob din shi yake, watsarwa yake yana wasu irin surutai wanda baka gane abinda yake fada, ga bayan shi kuwa wasu mutane ne cikin bakakken kaya, juyawa yayi tare da niman inda zai cusa kanshi, sake juyawa yayi yaga tabbas matsowa kusa da shi suke.


A mugun tsora ce, ya fara kokarin shiga wardrob din. Yana daidai sun tawo zasu caka mishi wukar har ya rutsa idanun shi, kawai yaji kamar an tare shi.... Karar da yaji tare da zuɓewa a jikin shi yasa shi bude idanun shi da sauri, ya had'a zufa sosai zama yayi yana kallon cikin kasuwar, sanan ya mike tare da ɗaukar karamar buta ya zaga bayan gidan yayi alola bayan ya kama ruwa, sanan ta dawo ya fara sallah nafilla, yana idarwa ya fito, sakamakon motsin da yaji. A hankali ya zuba ido akan Baba Nasiru.
"Zauna Mamoon" zama yayi yana kallon dattijon.
"Wato kaga rayuwar mun nan! Cike yake da al'ajabi, wasu na farin ciki, wasu na dariya da ban mamaki, wasu kuma masu saka kuka. Karka yarda Allah ya jarabce ka da laluran da bata da magani, karka yarda Allah ya daure maka kaddara da bata da iyaka, duniya cike take da mugaye, kowa da ka gani son kanshi yake, kowa da ka gani son abin duniya yake, kasan dai rijiya mai gaɓɓa dubu, idan ka fada kafin a ciro ka ai kasan ka sheka lahira, toh haka tafiyar ƙaddara take, na farko ba a tanada mata guri, sannan baka shirya mishi lokacin dawowa, sannan tafiya ce da motar da baka da matuki, tafiya ce da ko kana hanya ko baka hanya idan motar ta lalace tafiyar kafa zaka koma.


Kasan yadda tafiyar yake a cikin tsannanin zafin sahara? Toh lallai wannan shine zanen ƙaddara, tafiya a cikin sahara ha zafi, ga babu guzuri, shi babu takalmi da zai rage mak ga zafi sahara, yunwa da ƙishirwa. Sai ya rage maka taki kad'an domin cimma manufar ka da burarrakinka na rayuwa, sai kuma kayi katari da alkalamin ƙaddara, wacce take rubuta fari da baƙi. A lokacin zaka ji duniya tayi maka zafi, kowa ya koma ya zuba maka ido. Allah Sarki sai ka ga lokacin duk inda zaka nufa cike yake da azzalumai.


Duk inda zaka dafa mugaye cike suke da gurin, kowa kokari zai yi domin a sami dama daya tal! Kowa yunkuri yake yaga ya shiga cikin lamarin mutum, amma sai ka tadda zuciya ta kangare sakamakon jin bakon lamari, ƙwaƙwalwar mutum ta gigita. Fansa da rashin adalci ya girmama zukatar mutanen. Miyagun mutane suna karawa juna ilimi suƙa, masoyan asali sun koma a abokan gaba, taurin zuciya da ɗaukar zafin rai, zai zama linzamin farko na jagorancin zuciya, kafiya da rashin makusantan kwarai zai zama janabi na tunkarar mutanen da suke fadi tashi domin kaucewa kusakuran su.


Yaro karka sake lokacin yayi kana me jin haka tabbas zai faru, karka yarda duniya ta baka damar amsar wasikar jaki, Rayuwar da aka gina bayan an saka Allah a cikin shi, bata lalacewa. Duk mutumin da ya dogara ga Allah baya tab'a tab'ewa, idan kaga Abu ya same shi, Ubangiji yayi haka ne domin ta tura mishi wani irin yanayi domin gyara alamarinshi.


Allah ya kawo mu lokaci ne da mutane suka rufe idanun shi da yagar namar wasu, suna taunawa. Allah ya turo mu karnin da bamu da abinda zamu yi domin kaucewa tafarkin mugaye sai Addu'a, ina ma da zaka rike wannan tatsuniyar tawa, da ka kaucewa kuskure mara iyaka. Yaro mutanen da basu san darajar damuwa ba, a duk lokacin da damuwa ta faɗa musu, sun kan dimauta su gigita, Yaro kaga duniyar nan tsoro yake bani, gani dai a cikin ta amma ina shakkar mulkin da duniya take.


Wasu mutanen basu da kirki, kana son aikata abin alkhairi, amma sabida sharrin zuciyar su, haka ,zasu yanyayemak da mugun nufin su, irin su basu barin mutanen kirki zama a kusa da mutum sabida sharrin su ya fi ta bakin maciji, fitinar su ta fi ta fitinar karni, bala'in su tafi ta annoba, kai yaro nasan ba fahimtatta kake ba.....


_Don Allah kuyi hakuri 👏👏👏 wallahi na fita ne kuma fitar gaggawa ce ya kama ni! Kuyi hakuri ban cika muku alkawari ba amma muyi Abu daya mu sauya tsarin Posting ku fada min lokacin da ya dace na muku Posting naga kamar zai fi dad'i ayi da daddare sabida kowa ya gama busy na rana, kunga sai ina baku page me yawa ya kuka ce? Ina jiran ra'ayin ku idan kuma zan cigaba da rana ne shi kenan amma idan na shiga busy ba zan iya Posting ba ina jiran ku nagode sosai_


Hmmmm Wattpad ANYA?🙄🙄 Gaskiya toh wallahi zamu sake lalle domin zan bar Posting iya Whatsp.....🚶🏾‍♀️ Maneji....
[7/14, 1:06 PM] RamlatArManga: *🐂🐂BOROROJI🫀🫀*

~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
BOOK ONE
https://www.instagram.com/batool_spices
Fatima Batool enterprise
Yaji
Ginger and garlic
Onion powder
Pepper soup
Curry
Biryani spices
Mixed spices
Indian spices
Arab spices
Chai masala
Baharat blend
Tandoori blend
Thai masala
Garam masala
Provence
Tea spice
Zobo powder
Gu garzaya Domin samun kayan kamshi na fatima Baool Enterprise. Domin samun yajin suyar na naman layya 😋


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Idris


*Hmm! Kalma ce da take kunshe da ma'anoni bila'adadin! Koda yake bana ce ba! Ba kuma zan fadi ba Amma idan har zan fadi gaskiya ku din masoyan gaskiya ne ba masoyan bogi ba. 🤣😜 Wato masoyan Mata maza, #Team Majnunu! Mukan Yan tawaye ne❤️🙄 Team Malam ANSAR*


Wata Rayuwar..
BABI NA SHA DAYA..


Dariya ce ta so subuce mishi, ya kalli Baba Nasiru, sannan ya ce.
"Ina fahimtar ka, kawai maganar ce tayi min nauyi sosai. Na gaza gane me kake son ka fahimtar dani"

Tashi yayi dakyar ya nufi ban daki yayi alola sannan ya fito yana faɗin.
"Wata rana zaka tuna da haka"
Ya fada tare da nufar masallacin. Shima sallah yayi a cikin dakin, sannan ya zauna yana nazarin, mafarkin shi da. Can ya tuna da halin da yake ciki, iskar bakin shi ya ja, yana kallon hasken da rana da yake hudowa ta gabar. Ranar yayi wani irin kyau ta bada Wani irin yanayi, a hankali ya fito waje yana kallon yadda garin yake washewa. Shaƙar iska yayi me dad'i da ni'imar safiya.


Ya lumshe idanun shi, yana kara tabbatar da kanshi, yana cikin nutsuwa.
"Kasan wata ƙaddaran tamkar hudowar rana ce, idan ta shigo bata tab'a barin ka har sai tabbata akan ka."


Kallon inda hasken ranan yake murmushi yayi sannan tacewa Baba Nasiru.
"Zan koma gida" ya dauki kayan abincin shi ya juya tare da fita a kasuwan, yana isa gidan wanka yayi, Almamoon akwai tsafta ga son kwalliya, dan haka ya gama kome yana kallon Innah, sannan ya shige dakin ya kwanta. Barci me nauyi ya dauke shi.


..... Haka rayuwar su, take tafiya cikin ikon Allah da kuma matsin rayuwa, ga jikin Baban shi sai ruruwa yake, Nana cikin wannan yanayin aka yi sata a kasuwa, ai kuwa aka kama Almamoon. Aka rufe halin kunciin ya kuma rub'anyan sama da haka, rayuwar ta kuma ta'zara.


A wannan gaɓɓar halin da Innar shi take ciki kawai ya isa ya karya maka zuciya, domin wallahi ba karamin matsanancin rashin hali take ciki ba.


Ga ciwon Baban ya matsa mishi, wasa wasa sai da Almamoon ya cika sati biyu, sannan aka sake shi ya dawo ya daku, yayi laushi ko magana baya iya yi. Kwana shi uku yayi bai san inda kanshi yake ba, sai da ta haɗa mishi ganyen Tsamiya da wasu sassake ta dafa mishi yayi wanka, yana sha kafin Allah ya bashi lafiya. Sai dai kuma halin da yake ciki na rashin abinyi ga rashin abinci sai Innar shi ta tafi Bara suke samun abinda zasu ci.


A hankali kwanaki suke tafiya, watanin suna kara nisa, abin mamaki Almamoon ya cinye zangon karatun shi a gida.


----
Burin shi nason zuwa ya duba Almamoon bai samu ba, sakamakon tura shi wani yanki da kayi na aikin zaɓe,yana dawowa kuma yayi ta faman zirga zirgan asibiti da Umman shi, baki daya yaron ya tsaya mishi a ranshi, ya rasa gane wani irin kauna yakewa Dalibin shi, a iya sanin shi. Dai kaunar da yake mishi bai kai yadda yake ji ba a baya, amma rashin dawowar shi makaranta Yasaka shi jin kamar zuciyar shi ce a Damagaram.
*
Yau ta kama lahadi.


Gyara mishi gashin kanshi dan Ba'are yake, cikin kulawa da nutsuwa. Duk da yaki tsayawa amma kuma haka bai hana shi gyara mishi sumar da yake kanshi buyayya haka nan ba.


Wayar tafi da gidanka na shine yayi kara. Dauka yayi sannan yace.
"Kaga Bama bukatar mace? Namiji muke bukata don Allah kar ya wuce nan da kwana uku, matukar ya wuce haka da akwai matsala bana son tafiya na bar mara lafiyar ne"


Kome aka gaya mishi sannan tace.
"Alhamdulillahi, ku taimaka min daga fadar shugaban ne kuma albashin akwai kyau Insha Allah babu matsala, Nagode sosai"


Sannan ya katse kiran, yana jin kamar ya janyo kwana ukun zuwa yau, dan an addabi rayuwar shi da kira, ya dawo bakin aikinshi. Bayan ya gama mishi gyaran gashin kanshi ne ya kuma dawowa kan fuskar shi, a nutse yake gyara mishi fuskar. Shi dai yana zaune sai yadda aka yi dashi, yana gamawa ya kama mishi gyaran farcen shi, har ya gama sannan ya mike ya haɗa mishi ruwan zafin wanka.


***
Ofishin shugaban jami'ar, shiru yayi sannan yace mishi.
"Yallabai yaron nan haziki ne, idan aka kore shi ba a mishi adalci ba, don Allah karka yanke hukunci Ni zan tafi garin su na duba bashi, don Allah yallabai ka du..."


Daukar wayar gaban shi yayi ya fara waya, ya jima yana magana kafin ya ajiye. Har ya manta abinda Malam Ansar yake rokon shi nan ya shiga rabtabo bayanin.
"Wai ana niman wanda zai yi jinyar wani na hannun damar shugaban kasa ne, kuma namiji matashi, sun hadani da aiki ina zan samu me wannan yanayin kuma wai basa son mace, don Allah ka taimaka min ka tayani cigiyar."


"Toh yallabai ya batun Almamoon?" Ya fada a marairece,
"Zan duba ka fara duba min yaron idan ma ta kama ma waye ka kawo min zaka nima akan aikin shi kenan, albashin sa na farko nawa ne, sauran kuma zamu yi ta kashe mu raba"


"Hmm! Toh zan duba maka. Mun gode da alfarman da kayi mana daura dari biyu a fara jarabawa, dan haka Insha Allah zan tafi har Damagaram ɗin." Ya fada tare da gyada kanshi.


Mikewa yayi tare da ɗaukar kayan shi ya fita, yana me cewa.
"Insha Allah ba zan koma gida ba dai na nimo inda kake" ya faɗa cikin motar shi, ya bata wuta. Gidan mai ya fara tsayawa ta cika tanki, sannan ya dauki hanya.


---
Karfe shida na yamma yana zaune a kofar gidan su, dake basu da nisa da Makarantar da yayi, yana hango motar kamar ya santa, Amma haka ya kura mata ido, har ta iso gare shi. Mik'ewa daga kan dakalin ya tunkari malam Ansar.
"Barka da zuwa Malam" zuba mishi ido yayi ya kara lalacewa bakin shi ya karu ainun. Fitowa yayi yana kallon shi, sunkuyar da kai yayi yana wasa da hannun shi.
"Baka iya tarba'n baki bane?"
Da sauri yace mishi,
"Kayi hakuri mu shiga daga cikin gidan."


Almamoon yana gaba Malam Ansar yana baya, har cikin gidan. Inda yayi mishi shimfid'a a kusa da inda Malam Sanda yake zaune, yana fama da sauran mikin wutar da ta kona shi.
"Barka da zuwa malam" inji Innar Almamoon tana kawo mishi ruwa, "Yawwa nagode Inna"


Gaishe gaishe suka yi, kafin dai ya kawo dalilin zuwan shi. Mik'ewa Almamoon yayi Tare da cewa.
"Ni dai bani komawa ko ina, zan zauna da iyayena babu wanda yafi dacewa da kulawa da lafiyar su sama da ni, sannan babu me taimaka sama dani, idan na tafi waye zai kula da lafiyar su? Idan na tafi waye zai nima musu abinda zasu ci? Ba kowani lokaci ake samun abinda ake so ba.


Koda zaka samu dole sai ka dandani azabar da kowa ke sha, Na gode sosai malam" ya faɗa cikin sanyin murya, duk sai son shi da kaunar shi ya cika mishi zuciya, ya kuma jin yaron ta cancanci yayi rayuwa me kyau da tsada, toh amma shima ga halin da yake ciki, mahaifiyar da duk wata take cinye sama da rabin albashin sa, ga bikin kanen shi biyu da aka saka. Duk sai yaji babu dad'i Meye ma ya kawo shi?


Kurawa Baban Almamoon yayi ido, kafin yace musu.
"Ku saka baki ya koma makaranta Insha Allah zan nima mishi aikin da zai rike kan shi da kuma baki ɗaya" dukkan su a lokaci guda suka zuba mishi ido, sabida rashin yarda da ya shiga zukatar su. Ganin irin kallon da ake mishi yasa shi gyara zaman shi sannan ya fara da basu labarin yadda suka yi a ofishin shugaban jami'ar.


"Idan har daga jikin firaminista ake niman shi toh ba makawa ba iya kune kuka huta ba, hatta wasu zasu huta a jikin ku, bawai dan na rena muku bane sai dai ina son yayi rayuwar da zata saka shi farin ciki ne, kar ku damu ni ma kamar dan ku nake, don Allah ku fahimce ni". Shiru suka yi kafin ya cigaba da cewa.
"Wani sana'a kike anan?"


Sunkuyar da kanshi yayi tare da labarta mishi ko sati biyu bai yi da fitowa ba daga ofishin yan sanda, sakamakon abinda ya faru. Idanun shi sunyi jajjur,
"Dako fa?" Ya kuma tambayar shi.
A hankali ya saka hannun shi a cikin aljuhun wando shi ya ciro kudi masu kauri, ya ajiye musu.
"Ku dubi girman Allah ku taimaka gobe ya dawo makaranta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login