Showing 33001 words to 36000 words out of 181864 words
ba nazo dan na tilasta ku bane, a'a nazo ne dan na tsayawa dan uwana kanina zan tafi Nagode ga wanna Ku sayi magani"
Duk da suna cikin damuwa da matsin rayuwa, bai hana su ce Mishi.
"A'a , bawan Allah mun gode Insha Allah zamu turo shi amma ka dauki kudin nan kai Almamoon dauka ka bishi da abinshi mun gode"
Cikin sanyin jiki ya zuba musu ido kafin yace musu.
"Baku yarda dani ba kenan?" Yadda yayi maganar yasa Malam Umaru yace mishi.
"Allah ya kara budi mun gode sosai, Allah ya tsare hanya Ubangiji ya jibanci alamarunka"
Cikin wani irin jin dadi yace mishi.
"Amin Ya Allah Nagode sosai baba Allah ya baka lafiya, Toh sai an jimanku Almamoon sai na ganka kenan" mik'ewa yayi suka fita. Mika mishi hannu yayi, amma fir ya coge, sai ma yayi kamar bai da lafiya. Shiru suka yi dukkan su.
...
Bayan fitar su, a kidime Innar Almamoon ta kalli Malam,
"Malam!" Ta kira sunan shi a sanyayye,
"Kabo, bana son damuwa akan Almamoon. Ba wai dan ina cikin tsannanin rayuwa bane, sai dai ba zan ji dadin yaron ya kare rayuwar shi anan ba, kamata yayi ya tafi koda babu aikin da zai yi a jikin masu kuɗin."
"Malam ba haka bane, na hango tashin hankali a kwayar idanun malamin, na hango kaunar Almamoon a cikin idanun shi."
"A'a ki kyautata zaton ba wai ki munanan zato ba, ban ji dadin abinda kike tunanin ba." Tana son yin magana amma sabida yadda malam yaki amsar uzurin ta, yasa tayi shiru.
....
"Almamoon!" Kasa d'ago kai yayi dan yasan yana nan yana kare mishi kallo,
"Almamoon dama irin wannan rayuwar ne ya hanaka zakewa a ko ina? Me yasa baka gaya min ba tun farkon zuwanka makaranta a nima maka aikin yi yadda zaka rike kanka da iyayen ka? Me yasa baka tab'a gaya min ba?" Ya tambaye shi cikin wani irin yanayi. Tar ya kalle shi kafin yace mishi.
"Bana niman taimako a gurin kowa sai Allah, bana son wanin da ba Allah ba ya goranta min, sannan idan daga haduwar mu nace maka ina son ka nima min aiki ya zaka ji? Dan haka ya yankewa kaina damuwar Kowa sai na iyayena, yanzun ma zan yi shawarwari dasu idan suka amince na dawo shi kenan, idan basu amince ba kayi hakuri. Na iya talaucina" ya faɗa kai tsaye ba zaka tab'a tsammanin zai iya fadar haka ba, domin babu shakka ko wani abu a ranshi sai ma tsantsar gaskiya wanda daga kin shi sai b'ata.
Shafa kan shi yayi tare da hura iskar bakin shi yace mishi.
"Ba zan yi kasa a gwiwa ba, idan har baka zo ba gobe jibi Insha Allah zan zo" daga haka ya juya tare da shiga motar shi. Har ya bar Unguwar, kallon motar Almamoon yake.
"Hm" ta faɗa tare da shiga cikin gidan. Yana shiga ya lura da Innar shi fushi take dashi.
"Inna" ya kira sunanta,
"Wato baka jin maganar mu ko? Me yasa ba zaka gane yanayin ka da na sauran mutane bane? Sai da muka baka shawara kan babu ruwanka da mutane amma kayi kunnen uwar shegu damu, Allah ya baka sa'a tunda ka jajjubo shi."
Kamar wanda aka dasa, haka yake tsaye bai tab'a ganin irin haka ko ji ba, sai gashi lokaci guda kome ya sauya.
"Kai Almamoon zoka dauki kudin nan kasayo sabulu ka wanke kayanka gobe ka koma makaranta ko baka yi aiki ba, ai bamu ke daukar dawainiyar ka ba, tallafi ka samu, ina me rokonka da ka kame kanka. Insha Allah babu abinda zai faru sai Alkhairi babu ruwanka da kowa, don Allah ka rufa mana asiri. Ka ji"
"Baba ni ba zan koma ba" ya faɗa kan shi a sunkuye, shiru ne ya ratsa tsakanin su, kafin Malam Umaru ya sake wata magana kamar saukar aradu.
"Aminatu kenan, ba sai kin gwada min karfin ikon ki akan Jinin Sama'ila ba" ya fadi haka tare da mik'ewa, ba ita ba hatta Almamoon sai da ya mike tsaye.
"Malam!!!" Ta kira suna shi jikinta na rawa.
"Ayya Ayya Ayya Malam, Ayya Malam me yasa? Malam alƙawari bai ce haka ba, Malam me yasa zaka nemi kifar min da miyar da na jima ina wahalar had'a shi? Malam me yasa zaka kunce min zani lokacin da ban shirya kuncewa ba, Ayya Malam Ayya Ka yi min adalci kuwa? Malam me yasa baka Cigaba da YAKANA ba? Malam karka tulamin kasa a idanu mana, karka sare min gwiwa ta mana, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Ubangiji."
Shi kanshi bai zata maganar zata iya fitowa a bakin shi ba, kallon su Almamoon yaƙe, kafin yace.
"Waye Sama'ila da nake amfani dashi a makaranta?"
"Sunan Baba nane" inji Malam, sabida ya dauke hankalin Almamoon daga batun, ita kuwa Innar had'iye kukan tayi lokaci guda, haka kawai Almamoon yaji a ranshi, akwai abinda suke boye mishi, amma koma meye wata rana zai fito. Daukar kudin tayi tare da yafa mayafinta ta fita, sayo sabulu, kafin ta karasa ta tsaya a wani lungu. Ta fashe da kuka, sai da ta durkusa a kasa tana wani irin kuka. Me yasa malam yayi mata haka? Me yasa ya zab'i cilla rayuwar Almamoon wata duniya, me yasa ya aikata haka? Komawa tayi tare da zama.
Tayi kuka kamar ranta zai fita, kafin ta goge idanunta, sannan ta nufi shagon, ta sayi abinda zata saya. Sannan ta juya tare da komawa gida.
Ita da kanta ta ware kayan Almamoon ta wanke mishi aka kiran magarib tana shanya kayan, sannan ta zauna bayan ta ga Almamoon yana alola.
"Gama ka bani butar na taimakawa malam"
"Toh ina"
Haka ya gama ya mika mata bayan ya cika ruwa a cikin butar, ya shiga dakin sallah.
"Malam gashi" ta faɗa tare da dauke kanta daga gare shi. Riko hannunta yayi cikin nashi yana faɗin.
"Nasan nayi laifi, amma haka ba yana nufin b'ata miki rai bane, idan har sabida kin yi fushi yace ba shi komawa makaranta waye zai gaya mishi yaji? Rayuwar shi zaki duba? Waye shi ba shi bane me muhimmanci ba, rayuwar shi na gobe shine mai muhimmanci.
Idan da ace sabida ke ce wallahi ba zan saka baki ba, amma dake saboda yaron ne dole na saka baki, yana miki wata irin kauna ce ba iya ke ba hatta ni, kaunata yaƙe, sabida mu ya sadaukar da karatun shi ashe ba zamu tsayawa rayuwar shi dan wata dama ta same shi ba? Kinsan mutanen da suke niman dama irin da ya samu yau? Wallahi ba kwadayin abin duniya ya sani amsar wannan batun ba, sai dan rayuwar shi, ai ko babu kome zaki duba ki ga waye shi?
Ina zai shiga? Meye Allah ya ƙaddara mishi, shin zai iya jure ƙaddaran shi? Shin meye mizanin ƙaddaran shi? Wannan shine abinda nake son ki Fahimta, amma idan kin fahimta idan baki fahimta ba, ki barshi yayi ya zama. Allah yayi mishi baiwa amma zai kare ta a matsayin dan dako, nasan waye na ke zaune dashi. Tunda nake da yaron nan bai tab'a ɗaukar abin wani ba, amma lokaci guda an daura mishi laifin da bana shi.
Idan muka ce kullum gudun ƙaddarar shi zamu yi wata rana ba zamu iya gudu ba, kyale shi ya fita yayi rayuwar shi kamar kowa, ya fahimci muhimmancin rayuwa, ya san yadda Goben shi zai kaya, idan muka cigaba da boye shi wata rana zai iya tambayar mu me yasa? Ina jin kunyar na gaya Mishi waye shi.
Don Allah Karki Cigaba da abinda kike aikatawa, don Allah na hadaki da shi karki kuma abinda ya sani magana."
Share kwalla tayi tare da SUNKUYAR da kanta.
"Malam don Allah karka kuma haka"
"Insha Allah ba zan kuma ba, leka karki kuma ki barni nayi iko da shi." Ya faɗa,
"Inna yau ba zaki mana abinci bane?" Ya fada tare da tura baki,
Tashi tayi tare da cewa.
"Ga tsakin can dambu ne" zama yayi tare da kallonta,
"Innah dambun kuma?"
"Ina da zogale da busheshen lawashi"
"Inna da magarib zaki mana dambun?"
Ya fada kamar zai fashe da kuka, haka ya mike.
"Toh zoka sayo maka makaroni." Da sauri ya mike, tayi mishi lissafin, bayan ya mike ya dauki kudin ya nufi shagon unguwar.
Tun daga nesa ya hango yan daban, sunan shi Shege. Cikin shi ne ya cika da ruwa, haka ya isa shagon ya gama sayayyan shi, sannan ya juya zai tafi, yaji an matse mazaunin shi. Maganar gaskiya Almamoon yana da halittar mazaunai, duwawun suna nan masu dan tudu, ba laifi abinda yake jan hankalin matasan yan daban suke bibiyar shi.
Shege dan iska, yana bin mata da maza. Tun shekara daya da ya wuce yaga Almamoon yake Masifar son ya kusanci bayan shi. Amma haka bai samu ba, sai da magarib nan yake ganin kamar zai iya shigar shi da karfin tsiya.
Kwace jikin shi yayi tare da kallon shi.
"Malam Meye haka?" Wani nishi ya sauke tare da takowa gabansa.
"Kamshin mace naji a jikinka"
"Malam bana son damuwa" ya faɗa da sauri yana ja da baya, ganin Almamoon zai subuce mishi ya kara kai mishi cafka Allah ya bashi sa'a, ya arta a guje.
Shi da yaran sa, suka mara mishi baya Allah bai basu Sa'a ba, har ya shiga cikin gidan, tare da rufe kofar gidan yana haki, kamar Mahaukaci haka ya shiga gidan yana haki.
"Lafiya?"
Nan ya basu labarin biyo shi da shege yayi, shiru Malam sanda yayi sannan yace mishi.
"Insha Allah gobe zaka bar garin nan"
Innah da cikinta ya duri ruwa kamar zata fashe da kuka.
"Eh gwara ka tafi, zaman ka a nan masifa ce gwara can"
Shima munafikin da yaji haka, ai amincewa yayi babu shiri a daren suka tafasa taliyar suka ci, wajen asuba. Ya shirya kayan shi. Sannan suka mishi addu'a, kafin suka sanya shi yayi Sallah tare da niman dacewa.
Karfe bakwai na safe ya bar gidan, cike da zulumin rayuwa,
Haka ya nufi tasha, yana zaune har motar su, ta tashi. Anan ya sauke ajiyar zuciya.
**
Karfe hudu na yamma ya same shi a quarts din malaman jami'ar, a hankali ya shiga buga kofar get din, dake yasan Almamoon zai zo shi yasa ya bude da kwarin gwiwar shi, yana buɗewa, ya shigo. Bai san lokacin da ya fisgo shi tare da rungume shi ba, yana wani irin jin dadi da nutsuwa yana saukar mishi.
(Labarin zai koma bakin Mata maza🙄🤣 Salon da na saba 🙆🏾♂️😜)
Cikin wani irin takaici na kalli Malam Ansar.
"Toh meye haka? Idan Baba Mari ta ganmu ta zarge mu da wani abu ko?"
Kamar zai sake min kuka yace min.
"Kayi hakuri nasan babu dad'i amma kuma nayi kewar ka ne sosai."
Ƙaramin tsaki kayi a raina sanan nace mishi.
"Toh Ni gaskiya bana son haka." Na ture shi tare da juyawa zan fita.
"Don Allah kayi hakuri"
Banza nayi dashi. Kamar dani yake ba,
"Toh shi kenan, ba zan kuma ba." Ya fada a sanyayye, shiga cikin gidan nayi ina wani hura hanci irin ganin nan an min laifi.
"A'a ba nan ba, BQ" na wuce da jakata ina shiga na kalli Baba Mari. Cikin wani irin murna ta taso tare da amsar kayana.
"Dan mutum kai ne a gari"
Kaunar tsohuwar ya taso min tun daga cikin raina har jinin jikina, ba zan iya cewa ga yadda nake ji akan ta ba, kwalla ne ya cika min idanuna.
"Wallahi matar gani nan". Na zauna ina kallonta, kura min ido tayi, sannan tace min.
"Idan na kalle ka sai na tuna da Abuh, yanayinku, kayi hakuri na tsare ka da surutu.."
Tashi tayi ta fara hada min abinci, tare da duk wani abun da take dashi a dakin. Cikin kauna da gata, take min.
"Maza zauna kaci" haka ta hada min na fara ciki ina janta da hira, har ma gama na kwashe kwanikan na wanke, na dawo dakin nayi sallah,haka na tattara kome na koma dakin da aka bani, na gyara shi tsaf.
Sannan na dawo dakin ta muka shiga hira, har malam Ansar ya kuma zuwa, wani shegen kallon yake min, dan haka na dauke kai na tare da b'ata rai. Haka muka sha hiran mu tare da basu labarin halin rayuwar da muka sha, wanda ma na bar su.
"Yanzun ma ai bawai na dawo bane saboda kaje, wani gantalallen mutum ne ya dame ni shine Inna da Baba suka yarda na zo."
Ya fada tare da tsume fuska, dan bakin nan ya cuno shi gaba, alamar wannan Almamoon da mace ce (🙄😜🤣) tabbas zata yi tsiwar bala'i, ina dalili dauke idanun shi yayi daga kanshi, domin kowani seconds na bugawar agogo jin bugun zuciyar shi yake yana fita kamar da sunan Almamoon, tsabar kaunar da yake mishi (Dalla can mata mazan🙄😠😏) kasa sakewa yayi dan gani yake kamar Baba tasan abinda yake yi akan Almamoon, ya tashi ya bar gurin tare da cewa.
"Baba bari na fita na dawo"
"Allah ya tsare"
Ta faɗa mishi.
***
Abinka da mara lafiya, ganin yadda agwagwan ke wanka haka shima ya tawo da mugun gudu ta dirka a cikin ruwan ji kake famjammm, ya fashe da wata irin dariya yana gurnani kamar Mahaukacin kare, bakin shi yana zubda yawu, sai buge fuskar shi yaƙe alamar kuda na binshi.
"Hrmrmrmnnnnnrrr" masu kula da lafiyar shi, ne suka taru a gurin da hodar da suke shaka mishi.
"Ku nutsu a hankali"
Inji Hurayyah, sadaddewa suka yi tare da shaka mishi hodar ta bayan shi, anan suka yi a rangama daukar shi, kai ciwo makiyin mutum.
"Amma Hurayyah idan Dan Ba'are yazo da?"
"Toh kai da mu bari ya dake mu ai gwara mu shaka mishi tunda naga ai ba laifi bane, kuma idan ba haka muka mishi ba kana ganin zamu sha lafiya ne, gwara mu shaka mishi."
Haka suka dauke shi zuwa dakin shi, aka kwantar dashi, suna kokarin cire mishi kayan Dan Ba'are ya shigo. Ganin halin da suke ciki ya shi musu wani irin banzan kallo, babu shiri suka bar d'akin, tare da nufar waje, suka shi ya kintsa shi sannan ya zauna yana kallon shi.
"Mohammed Insha Allah zaka samu lafiya ina jin haka a jikina, sai dai ta inda lafiyar zata samu ne ban sani ba" ya faɗa tare da rungume hannunsu guri guda. Tausayin shi yake, yasan idan ya samu lafiya bai zama dole ya koma bakin aikin shi ba, tunda ga halin da yake ciki. Koda ya ji sauki sai dai ya nemi wani aikin kawai. Kiran wayar shugaban jami'ar yayi suka yi magana, shafa kan shi yayi yana murmushin jin dadi.
"Nagode"
Ya fada cikin wani irin abu yaji ya tsaya mishi a raina,
Dan haka ya mike tare da nufar waje, ya kalle su dakyau.
"Insha Allah jibi za a kawo wanda zai na kula da lafiyar shi, ku sai ku tsaya akan aikinku,."
"Toh" suka fada lokaci guda, sannan ya juya tare da barin gurin su.
Ko minti biyar ba ayi ba aka kira shi, daukar wayar yayi tare da mannawa a kunnen shi.
"Akan me zaka ce su tsaya akan aiki su? Karka yarda ka kawo min wani mutum da zai kula da lafiyar Mohan domin kome na shi yana hannuna."
Murmushi yayi sannan yace mata.
"Ko Ammi bata da ikon hana ni abinda ya dace akan Mohan balle ke, dan haka ki fita idona na rufe idan na rufe dake mmm" ya kashe wayar yana tsaki, fitowa yayi tare da tara su,
"Wallahi sai na kore ku kuma na kwana lafiya, kunyi na farko kunyi na karshe kar na kuma kama wani dan iska da min tsurku, idan kuma na sami haka"
Nad'e hannun rigar shi yayi tare da kallon su, yana lashe lashe bakin shi, cikin zunzurutun masifa da bala'i. Ya tsani renin hankali. Shi yasa ake ganin kamar baya son mu'amala da mutane kananun magana ne ce ya tsaya, yan iska kawai sai ya hana Hajiya Safiya shigowa gidan da shi take zancen fita yayi tare da danna wani kararrawa, kafin kace kwabo.
Kafatan jami'an tsaron sun halara a filin gidan, haurawa saman wani dakalin yayi yana kallon su.
Kafin yace musu.
"Jibi Insha Allah zan bar garin nan zan koma gurin aikina, kuma jibin zan kawo me Kula da lafiyar Mohan, idan yazo ina bukatar a kula da lafiyar shi! A kula da duk wani abun da zai zo dashi sannan ina kyautatta zaton zai zauna anan ne zai na tafiya makaranta a bashi driven da zai kai shi ya dawo dashi. Ina son kuma a saka ido akan masu zuwa daga Fadar firaminista da sunan duba lafiyar Mohan, kowaye matukar Ba Hajiya Latifah bace ko Daya daga cikin Yaranta ko Mai Girma Shugaban kasa ban yarda a bude kofar gidan ba, idan kuka ga mutum ya matsa zai shigo ku bude mishi wuta. Sannan ku kara saka ido akan masu aikin kicin da sauran bangarorin akwai munafukai. Da fatan zaku bawa Major General Mohan Mamman Nasir Aghali Kariya da Yardan Allah"
Duk suka hada baki da cewa sun amince, zasu yi aiki tsakanin su da Allah tare da bawa shugaban su kariya da yardan Ubangiji. Sanan ya gaya musu duk wanda ya karya dokan shi tabbas shima zai karya kafaffun shi. Dan haka su bi doka da oda. Suka kuma yarda tare da amincewa.
Kafin ya sallame su, ya shiga cikin gidan, yana shiga ya kira su baki ɗaya.
Kallon shi suka yi dan sun fara razana da al'amarin shi. Duk da sun zai bai da dad'i amma kuma basa tsammanin har ya kai yadda suke tsammanin.
" Idan mai aikin yazo zan tambaye shi matukar ya iya girki ba zaku kuma dafa mishi abinci ba" a rude suka d'ago kai suna kallon shi, a ransu kuwa ba karamin kwashe mishi albarka suke ba, ayi mutum da zunzurutun masifar tsiya, kome sai ya