Showing 69001 words to 72000 words out of 181864 words

Chapter 24 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6265

shi kuma ya kalle ni kad'an yana me takowa gaba na, a tsuguna ya saka min takalmina, sannan ya dauke ni can, ta mike hana na lumshe idanuna. Shi kan shi wani abu yake ji a ranshi, idan yana tare da Yaron shi kuma ba wai dan Iskanci ba a'a kawai yana yin su kawai kamar sunyi raja'a akan abu daya ne, shi yasa yake ririta al'amarin yaron yake kuma kokarin tsayawa yaron, Har waje haka muka yi ta ratsa mutane. Har gurin motar da zata kai mu jidda, lokacin da zai sauke ni ne wani karamin abu me matuƙar tasiri. Domin a hankali yake sauke, yana isowa daidai fuskar shi ee shiga niman nawa, cikin wani irin yanayi, ya zuba min idanun shi cikin nawa, ina iya hango wasu sirrika na shi amma babu damar fadar su, ina ganin wani abu na musamman a cikin ƙwayar idanun shi, amma karfin dakiya irinta zaratan maza ya sashi boye min haka, hancina ne ya gogi nashi, bakin shi ya sauka akan goshina. Wani irin yarrr naji kamar tsutsa na tafiya a jikina, shi kan sa wani abu yaji suna mishi yawo,bai san lokacin da ya sauke ni ba, tare da bude min kofar motar na shiga, ya koma gaban motar ya zauna.


Tunda muka nufi Jidda da motar, yana waya da wani har muka isa garin kusan tafiya me dan tsawo, airport muka nufa, anan muka hadu da Abeed, kallona yayi musamman yadda Mohan yake kaf kaf dani.
"Yaushe ka fara bin maza?" Kallon juna suka yi kafin yace mishi.
"Shine yaron da na gaya maka na kawo shi."
"Kai haba na zata lover kane." Daure fuska yayi sakamakon ganin Abeed yana mikomin hannu, yasan larabawa da fitina yanzun sai ya iya makale mishi akan Yaron shi. Dan hka ya buge mishi hannu yana faɗin.
"Hannun shi yana ciwo" ya faɗa tare da ɗaukata zuwa cikin airport din, shi kuma Abeed yana dauke da kayan mu, sai zuba yake, shi kuwa yana jin shi dan har ya gundura da halin shi.


Haka suka zauna yayi ta mana surutu yana haɗawa dani, nan kuwa Hammah Mohan harara na yake tare da dauke kai, har lokacin tashin mu yayi.


"Mohan gaskiya ina son Yaron nan naka" ya faɗa lokacin da yaga Hammah ya dauke ni zuwa inda ake duba kome har kayan mu, ana gama dubawa muka wuce, ya kai ni ya ajiye ni sannan ya fito suka kuma sallama.


"Mohan baka ce min kome ba, kasan an Cigaba zaka iya mai da namiji mace please ka bani Yaron wallahi ba zaka sami matsala da Ni ba". Murmushi yayi mishi sannan yace mishi.
"Akwai lokaci" daga haka ya juya tare da komawa cikin jirgin yana yaba girman haukar Abeed. Tab'e baki yayi bayan yazo zama ya hango wani dan kasar Philippines a kusa dani, wani daure fuska yayi tare da mikar da mutumin. Yana me zabga mishi harara, tare da nuna mishi hanya.


Zama yayi kusa dani, ni kuma na mai da kaina window, ina kallon yadda jirgin zai tashi, cewa aka yi kowa yasa belt, a hankali ya sunkuya kamar zai hade bakin mu, kafin yaja belt din ya saka min.
"Wato idan nace bana son abu ba zaka kiyayye ba?" Kallon shi nayi tare da sunkuyar da kaina. Huci yake tare da mai da kallon shi kan magazine din da aka ajiye Mishi.


Ina jin jirgin zai tashi ban san lokacin da na kai mishi cafka ba, na boye fuskana a gefen damtsen hannun shi, shafa bayana yake tare da cewa.
"Nutsu tashi zai yi!" Jirgin na daidaita a sama, na mike a jikin shi.
"Matsoraci kaji kunya." Tura baki nayi ina cewa.
"Toh meye laifina?" Dan na razana ya kama ce min matsoraci.
----
Karfe biyu na asuba muka isa dubai, anan ya jani har kasuwa zamani muka yi sayayya, kayan da yayi ta dauka min sune suka bani mamaki.
"Ko baka sone?"
"Allah ya kara budi" na fada ina amsar kayan, wani wando ya miko min crazy pant, da wata ƙatuwar rigar da nake son saka irin su, amsa nayi ina murmushin jin dadi, sai da na d'aga naga wandona na mata ne, kallon shi nayi.
"Ba zan maka dole kasancewa jinsin mata ba, amma wannan wandon yayi min kyau ne, ka amshe shi a kyautana"


Murmushi nayi tare da sunkuyar da kaina, ina gyara zaman gashin kaina.
"Amma meye amfanin barin gashin nan?" D'ago kai nayi ina kallon shi.
"Muje can a yanke maka " ya faɗa tare kallon yadda na firgita.
"Tsoro kake ji?" Had'iye yawun bakina nayi tare da marairaice fuska nace mishi.
"Iyayena zasu min faɗa" murmushi yayi sannan yace min.
"Dama kana tsoron iyayen ka wancan banzan ya dake ka? Sai na kareraya mishi kafa wallahi." A tsora ce na ware idanuna, daga min gira yayi tare da cewa.
"Meye?"
"Babu" na fada ina girgiza kai, wato shi bai damu da abin da zai ja min ba, kawai yayi hukunci kawai. Kamar yasan ina tunanin da nake kawai ya tako gabana.
"Kai na musamman ne, ba yau ba na gaya maka kai kyauta ne na musamman, dan haka dole na gaya maka"


Kallon shi nake kamar wanda aka sanya mishi battery sai magana yake kamar bashi ba.
"Rufe bakin" da sauri na rufe bakin nayi da hannuna.
"Muje" ya faɗa.


Idanuna ne ya sauka akan tv ana nuna wani jirgin kasa, wanda yake bin karkashin ruwa da mutane, dafa shi nayi ina nuna mishi tv. Underground railroad.
"Hammah Mohan dama an a Dubai ne kawai akwai wannan jirgin" kallona yayi sannan yace min.
"Akwai a china, akwai a Singapore, akwai a Japan. Akwai wani dakin da yake bujr Arab dakin yana karkashin kasa ne kuma kina hango kifi mana ko zamu d'aga tafiyar ne muje ka gani" wani ware bakina nayi ina dariya.
"Zan je ko sau daya ne"


Ja na yayi tare da biyan kudin kaf, sannan ya juya muka fita, wato baki daya rayuwata a Damagaram da Maradi ya kare kai ko Niamey ban tab'a zuwa ba, sai gani a karkashin ruwa ina kallon yadda jirgin kasa yake shiga cikin ruwa, ga kifi yana ta yawo. Cikin wani irin farin cikin nake kallon jirgin tare da kallon shi.
"Hammah ka tab'a zuwa nan? Kai wajen da ban sha'awa yake." Na fada ina hada hannuna, murmushi yayi tare da sako kanshi kafadana.
"Ya burge ka?" Gyada mishi kai nayi kamar wacce aka zabure ni.
"Hammah Mohan! Kasan me gaskiya garin nan yayi kyau kane kar na koma gida," na daura hannuna a kafad'ar shi karku ga yadda na kara har da dagelgel.


"Hmm" ya nuna min kafad'ar shi,
"Ai kayi hakuri" na fada ina kallon wata irin kifi me rabi mutum rabi kifi.
"Wayyo Allah, Hammah Mohan? Wannan shine , mermaid?" Jan bakina yayi tare da nuna min wani kifi shima kato, yana zuwa gurin Meemaid din suna watsewa, dariya na saka ina dawowa ta daya window.
"Hammah sun gudu sun ga babban su." Na fada ina wani irin dariya, kukan da cikina yayi ne na kalle shi kamar zan yi kuka nace.
"Hammah cikina yana jin yunwa?" Na fada a shagwaɓe, murmushi yayi sannan yace min.
"FwpMuje ayi sallah sai a karya" nan ma wancan hotel din ya kai ni, lokacin da ya biya kudin dakin sai da na tambaye shi.
"Hammah nawa kudin dakin? Kuma naji kace wuni daya ne?" Na fada ina kallon shi.
"Kudin ba yawa sai dai zai iya daukar nauyin abincin wata iyali na tsawon wata uku." Ya fada tare da nufar hanyar da zai kai mu kofar elevator......
_Ban zata zan gama da wuri ba wallahi na zata zan kai karfe goma na dare Alhamdulillahi Ubangiji Nagode maka Sosai kuyi hakuri da rashin editing, Insha Allah gobe zai iya kaiwa karfe biyu na rana kafin nayi Posting Insha Allah sabida na goben ne na baku yau da daddare_
Karku manta sharing 😘👏
#Mai_Dambu....
[7/26, 11:18 AM] RamlatArManga: https://www.wattpad.com/1105787433?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=Ja9wL7QqFEErjgU2q%2BSBeLU5C48TPF6alEcOeA68MXjwsxZkfzIB%2B1qokdEbQ55KLRjZ93ztdNSly6DP588o1P6bkl7taWFOl0ee6BP9d%2B%2F0Yz5SwmP2bjWvOwHDMKnB


🐂🐂BOROROJI🫀🫀


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


BABI NA ASHIRIN DA SHIDA.


Shan gaban shi nayi ina kallon fuskar shi.
"Kace zai dauki tsawon watanin yana ciyar da wasu iyalin?" Tura ni cikin elevetor yayi yana me faɗin.
"Na gaji da tambayoyin, ba sai ka nuna min Dalibin lauya ne." Ya fada min tare da tsayuwa yana kallon gaban kofar, shiru nayi kafin nace mishi.
"Kasan me? Kawai garin nan ya hadu, amma ya abin yake komawa ƙasa?" Na fada ina kallon shi, gajiya yayi da tambayar toshe min baƙi yayi tare da kallon yadda nake zare ido ina ƙoƙarin sai nayi magana.


Haka muka shiga dakin tare da kallon ko ina, dakyar na shiga ban dakin nayi wanka da alola bayan na fito na samu baya d'akin amma ga kayana akan gadon dauka nayi na shafa mai, tare da saka kayan sannan na fito ina saka takalmi, kallon shi nayi domin yayi kyau cikin riga da wando sai gyara gashin da yayi, kallon shi nayi sannan nace mishi.
"Kayi kyau, amma kuma kayan nan ya mai da kai wani babba dayawa, ka saka kananun kaya zaka fi ka kyau"
Na fada ina kallon shi, bai kula ni ba sai aikin gaban shi yaƙe.
"Hammah, zo nan" na kira shi ina a kujeran sa yake falon. Daure fuska na nayi, sannan na kuma kallon shi, na mishi alama yazo da hannu na.


Shi kan shi mamaki ya gama kama shi abinda yaron nan ke mishi wallahi yana wuce gona da iri, bai musu ba. Domin ya lura Yaron na jin farin ciki ne dan haka ya nufi gurin shi cikin sauki da salama, ya tsaya yana kallon shi.
"Kawo kunnen ka!" Wallahi a tunanin shi abin arziki zai gaya mishi dan haka ya sunkuya tare da kallon bakin shi.
"Kunne nace" ya gaya mishi haka, mika mishi kunne yayi. Sai da ya gama ja mishi kunne kafin yace mishi.
"Wani ya taba gaya maka kai kyakyawa ne? Toh wallahi kai kyakyawa ne gaka kamar dan dambe gingimemme da kai kamar tsohuwar bishiyar kuka." Wato haka nayi ta yabon shi ina kuma rage mishi wani abun. Kallon fuskana yayi tare da cewa.


"Da alamu yunwa ce ta saka zuba kamar tsohuwar rediyo?" Had'iye yawu nayi tare da shafa cikina, ina kallon shi.
"Idan ka taimaki dan cikina Allah zai gina maka katon gida a aljanna domin yunwa nake ji, kuma Ni kamar mareniya ce" na fada ina had'iye yawun yunwa.


Jan hannuna yayi muka fita, muna fita ya hango wani mutum da alama shima dan Afrika ne, wani irin juyar dani yayi tare da had'a ni da bango, kafin kaina ya kai bango ya kai hannun shi, tare da daidaita tsayin shi, ya kai fuskar shi kan nawa, kamar zai sumbaci bakina, zato idanu nayi ina kallon shi. Jikinsa ya matse nawa numfashin sa yana dukar nawa, kwayar idanun shi yana cikin nawa, baki daya na kasa cire idanuna cikin nashi mamaki yake bani yadda ya iya juyar dani cikin zafin nama, *Ka manta shi din soja ne* kuma haka ne fa? . Haka mutumin yazo ya wuce da wata baturiya a gefen shi. Sai da ya tabbatar ya wuce sannan ya d'ago ni.
A tsora ce nake kallon shi jikina yana kara sanyi. Kuma na kasa magana, baki daya kamar wacce baya cinye min bakina.
"Rediyo me jini ya kai yi shiru?" Tura baki nayi ina me Cigaba da tafiya.
"Abokina babu magana ne?" Kara dauke kai nayi ina kallon cikin Elevetor da muka shiga. Daukar wayar shi yayi tare da dannawa ya manna a kunne, kafin ya fara magana,


Buzanci ya juya baki daya kamar babu Hausa a bakin shi ko French, haka yayi ta hiran har muna fito, ganin kofar ta bude naka hannun shi mu tafi wayar ta fadi kafin na dauka ya taka, kamar zai bugani da kasa ya dauki wayar yana kallon yadda screen din shi yayi daga daga, gashi suna magana me muhimmanci ne da Hammah Khalil. Ranshi yayi mugun b'aci,
"Kasan abinda ka aikata min? Kasan Meye kayi? Me yasa baka da hankali ne? Kalli wayar yadda kayi min da ita? Wallahi baka jin magana mara hankali kawai, kuma a cikin albashin ka zan cire kudin wayata na baka sauran canjinka"


A mugun tsora ce nake kallon shi jikina yana rawa, sabida har jijjiyar kanshi mik'ewa yayi, da sauri na fita tare da yankawa da gudu, saka wayar yayi a cikin aljuhun shi yabi bayana, yana fitowa bai ganni ba, sake fitowa yayi ya hango ni, ina tafiya ina share kwalla.


Bin bayana yayi tare da da karamin gudu, har ya isa jin ina kuka sosai ya sashi kallon yadda nake kokarin share kwalla da suke zubo min. Abinda na Fahimta shi mutum ne da bai iya rike ka ba, a lokacin da yayi fadar a lokacin yake manta kome. Rike hannuna yayi tare da cewa.
"Abokina kuka kake?" Ya tsare Ni da manyan idanun shi.
"Don Allah ka mai dani gida zan ga Innah" na fada tare da fashewa da kuka, na fada ina fisge hannuna, ganin na saka hannuna dukka biyu a cikin aljuhun wandona yasa shi bina tare da gyara tsayuwar shi, kauce mishi nayi, ban san mota na zuwa ta bayana ba, sai da naji ya fisgo ni tare da had'a ni da jikin shi. Yana bin fuskana da idanu. Musamman yadda na razana.. hannuna daya a kirji ina zare idanun.
"Zan cigaba da baka kariya daga yau har ranar da zan mai da ka gaban Innah." Mai da kaina nayi gefen kirjin shi ina kuka.
"Toh kukan na me?" A tsiwa ce na d'ago kai.
"Baka ce zaka tab'a min albashi" na ba" na fada ina tura baki.
"Really"
"Kwarai" na fada ina kallon shi, ga kwalla na zuba min. Shi kam ya manta da wata batun albashi, amma dake yana niman rigamar ya kare sai ya kura mishi ido, sannan yace mishi.
"Toh Yanzun kai me zaka yi da kuɗin da baka so na tab'a" da sauri na dawo gaban shi tare da rike k'uguna. Sam na manta da abinda zai fito bakina.
"Zan biya sauran kudin gidan da zan saya mana, zan budewa Baba na kanti, zan sayi Laptop zan sayi waya. Kuma saboda wasu yan iska ne zamu bar unguwar dan dayan ya tab'a tab'a."


Wani irin caccuma yayi min wanda ya sani tuna abinda Shege yayi min. Jikin shi yana rawa yace min.
"Gaya min ina ya tab'a maka"
"Hammah sake ni idan har da gaske kai abokina ne!" A hankali ya sake ni, fuskar shi tayi jajjur. Cikin wauta na fara kallon shi sannan nace mishi.
"Idan kana min haka wani sai ya dauka kana jin haushin dan an tab'a ni, kuma ai ba wani gurin ya ta b'a ba, duw..." Toshe min baƙi yayi tare da kallon cikin idanuna,, yana wani irin haki. Hannuna ya lalluba tare da sakawa a kirjin shi, yadda zuciyar shi take bugawa kamar zata fito. Dakyar yace min.
"Anan na saka ka! Ajiye ka nayi anan karka kuma bani labarin anyi muka wani abu domin babbakewa zanyi a cikin kirjina"


"Toh Yanzun idan ka babbake taya zaka rayu? Zaka gaya min gaskiya ko sai na tara maka jama'a" na fada ina had'a index fingers dina yana dan bubbuga su da juna, ina mishi kallon tsokana.


Kura min ido yayi cikin damuwa kafin ya riko hannuna, muka koma hotel din, muna shiga kai mu gurin cin abincin, inda ya kai ni babu mutane a cikin gurin, an rubuta VIP. Waiter ne ya tawo tare da memo na abincin, ya ajiye mana cikin girmamawa. Dauka nayi ina kallon abincin da yake rubuce, shi kuwa Hammah ya harde kafa yana kallona.


Kallon Hammah nayi sannan na tura mishi memo din ina faɗin.
"Ban ga kome" dubawa yayi sannan yace mishi.
"African dishi" ya nuna mishi kome sannan ya ce mishi.
"Da fruit" haka ya juya kuwa can ba shafa cikina ina faɗin.
"Hammah Mohan, wallahi yau sai na biya bashin yunwar da cikin yake bina, kuma ko zai fito sai na dura."
"Cikin ka zai fashe" gwalallo idanu nayi waje kafin nace Mishi.
"Inji wa? Ai danyen fata bata fasuwa" na fada ina kara tabbatarwa.


"Danyen fata yana fasuwa, sosai kuwa amma waye ya gaya maka?" Ya tambaye ni yana kallon fuskana,
"Innah ta mana." Murmushi yayi karami sannan yace mishi.
"Innah tafi ni gaskiya" sabida yaso ya gaya mishi wata magana amma sanin cewa Yaron shi bai da cikakken kirki yanzun sai ya kuma kara tambayar shi, zuwa an jima reni ya shiga tsakanin su. Ya sa shi gasgata Innah da yaso tace mishi. Akwai a jikin kuma tsaf zai fasu sai ya share zancen.


Bai gama nazari ba aka kawo abincin, kallon shi yake yana kallon yadda yake had'iye yawu, dan haka ana gama shirya musu table din yace mishi.
"Don Allah karka cinye da table din" gyada kai nayi, ina me daukar cokali, ina faɗin.
"Bismillah" na fara diban abincin wani irin motsi kunnena yayi, bayan hanjin cikina yace kururu.
"Karka damu ku gama ihun ku, yau zan cakaku da Abincin" ba fada ina kara cika bakina da Abincin.


Wato abin ya fahimta, yaron yana da barkwace sai dai rashin abokin da zai zauna da shi suyi hira tare da raba matsalar shi da shi, Yaron yana da kuruciya da wauta, gashi da ban dariya duk fushin sa idan yayi mishi abu zuwa an jima zai bashi dariya, d'ago kai nayi ina kallon Hammah Mohan da yake kallon yadda nake cin abincin.kunya ce kuma ya kamani, na ajiye cokalin ina faɗin.
"Ya hakuri na manta da kai ne baki ɗaya."


Girgiza min kai yayi sannan yace mishi.
"Cigaba"
Murmushi nayi mishi tare da ware fararren hakorana. Girgiza kai yayi ya fara shan fruit din yana kallon hannun shi, wayar hannu shi take haske amma babu halin dauka sabida ya bugu da kasa. Har muka gama kallon abincin nayi ina sauke ajiyar zuciya.
"Yanzun haka zamu bar abincin?" Na fada ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login