Showing 93001 words to 96000 words out of 181864 words

Chapter 32 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6284

farkon kuma kece karshen har abada ba zan tab'a yarda na juya miki baya ba, Ina rokon Allah ko a gidan Aljanna ce ki zama uwargidana a can a nan ki zama matatta ta har abada.


A shirye nake na gabatar dake a baikona da za ayi nan da wata uku insha Allah. Ki zauna dani kinji kiyi hakuri dani ina da kishi da fushi, ina da bakar zuciya, amma ko..."
"Ko kuda ne ba zan taba barin ya tab'a ka"
"Tab'aki!" Muka kai karshen alkawarin mu tare, dariya na saka bayan na cire kaina a kirjin shi ina kallon fuskar shi.
" Me yasa kika saka baki alƙawari na?"
Janye jikina nayi ina kallon shi, kafin na zauna a motar ina sauke ajiyar zuciya. Shima shiga motar yayi muka bar gurin, duk inda yasan ana bude ido sai da ya kai ni, mun shiga babban Mall muka yi sayayya, sannan muka fito. Tare muna nufi wani gurin cin abinci, muka zauna aka kawo mana abincin. A tare muka ci muna hira.


Muna gamawa ya riko hannuna muka fita, a hankali muke tafiya.
"Hammah Mohan"
"Na'am!"
"Me yasa baka tab'a yunkurin niman yi wani abu dani ba?" Dariya yayi sannan yace min.
"Kamar Ya?"
Cire hannun shi nayi tare da gyara zama ina kallon shi sannan nace mishi.
"Kamar irin soyayyar zama Ni, irin sumbtar nan a baki da tab'a ni". Dariya yayi sannan yace min.
"Koda nake rungume ki a da can baya kina sani nishadi ne, kuma kallon namiji nake miki, amma bawai bana sha'awar ki bane fa, a'a ranar da aka miki kwalliya a Dubai dakyar nayi barci, amma kin san me? Ke matar da zan aura ce bana son na kwashe albarkan auren mu a hanya ne, idan na fara sumbatarki kafin mu kai ga aure, na lalata mutuncin ki. Ni ke nake so ba wani abu ba a kan me zan yarda na lalata goben mu, gaskiya ni ko rike hannunki ina yi ne abisa al'adar turawa da muka Ara. Bayan haka ba zan iya sumbatar bakin ki ba, goshinki ma ya isa "
Kwalla ne ya cika min idanu ban san lokacin da nace mishi.
"A wannan shekarunka kake kokarin kare hakkin Allah..... Kunsan weekend ne shi yasa ban baku da wuri ba... Nagode sosai
#Mai_Dambu
[8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1108559379?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published




🐂🐂BOROROJI🫀🫀


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza.


BABI NA TALATIN DA HUƊU


Murmushi yayi sannan yana me kallon hanya.
"Sabon Allah ba a girma yake ko a shekaru ba, abu ne da kowa yanka iya aikatawa idan Allah ya zare mishi imanin shi, duk wanda kika ga bai sabawa Allah ba Toh Allah ya tsare imanin shi ne, dan haka ki daina tunanin zan miki wani abu dan kawai ina son ki. Idan har kina mata masa ban ji wani abu ba."


A hankali na jingina kaina a jikin kujeran motar, kwalla yana zuba min, na kalli rayuwata tun daga farko har zuwa yau, akan tsarin Innah yake, ko sau daya ban tab'a bijire mata ba, Toh me yasa ba zata fahimci abinda nake ji ba? Me yasa ba zata gane yadda nake ji ba? A iya sani na ban tab'a sha'awar na kwatantata kwanciya a tare da namiji, sai da ya zama dole lokacin ina mata maza ya sani kwana daki ɗaya da maza, ban tab'a tsayawa sun shirya a gabana ba, ban tab'a yarda mun shiga wanka tare ba, kafin su tashi sallah Asuba na riga su. Bana sallah a tare su, kome ma bana yi a gaban su, amma haka Innah ta jefe ni da kalmar karuwanci.


Kofar wani katafaren gida ya tsaya tare da danna horn, da sauri sojojin suka bude gidan, ya tusa kan hancin motar cikin gidan, ashe gidan shi na Maradi wasa ne, a hankali yake jan motar har muka yi ta tsalleke get by get, sannan muka shiga cikin gidan. Kallona yayi sannan yace min.
"Wannan gidan shekara biyar kenan da na fara gina shi, da Alamu kece zaki fara bude min shi. A da ban shirya kome ba, amma dawowar mu daga Dubai ya sani kara himma domin kuwa ban sami soyayyar gaskiya bane yanzun kuma na samu soyayyar gaskiya,muna ga gidanki nan da zamu shirya rayuwar mu."


Ya fada tare da parking motar shi a wani gefen,. Fita yayi sannan ya bude min motar na fito, ma'aikatan gidan duk suka fito. Tare da gaishe shi sannan suka gaishe ni. Haka muka yi ta ratsa cikin gidan, har zuwa babban falon. Katon hotona ina Almamoon ne a falon sai na shi kusa da nawa.


Kallon shi nayi sannan ya ce min.
"Tsakiyar nan hoton dan mu ko yar mu na fari zamu saka, gefen can kuma na biyu zamu saka hoton shi a can, amma nafi son idan Allah zai bamu ya bamu Y'a mace, ina son Y'a mace musamman me kama dake"


Ya ja hancina, ture hannun shi nayi ina faɗin.
"Ni mai kama dakai nake son, idan har na haifa maka."dariya yayi sannan ya nufi kitchen ya samu babu kome amma kuma alamar ana kula da gidan ya nuna, dan gaba da gidan akwai masalaci, kiran sallah aka yi na kalli agogon hannuna.


A hankali na mike tare da nufar hanyar kitchen ɗin, ina shiga na same shi ya cire rigar shi ya daura afro, ya mai da hankalinsa kan girki, nad'e hannun nayi a kirjina, ina murmushi.
"Hammah Mohan" d'ago kai yayi yana kallona,
"Zan yi sallah ashe girki kake?" Na fada ina murmushi.
"Nasan Abar kaunar nawa ba iya girki ta iya ba, shi yasa na mai da hankali akan girki mijinki yana son a raya mishi cikin shi."


Jingina nayi da bangon ina kallon yadda ya mai da hankali akan aikin.
"Sallah" na fada a hankali,
"Ok" ajiye aikin yayi tare da kai ni wani dakin ya nuna min, sannan ya dawo ya cigaba da aikin shi, lokacin da na idar da sallah kuka na sha sosai, ina ƙoƙarin tuna ta ina iyayena suke.


Ta ina zan gansu? Yaushe zasu zo gare ni tunda Innah ta gaya min gaskiya guduwa suka yi,su kuwa akan me zasu gudu su bar ni bayan ina bukatar su a rayuwata. Karan bude kofar nayi ya sani kallon hanyar da aka bude kofar, shine ya shigo yana goge hannun shi, alamar shima alolan yayi zai gabatar da sallah. Ganin ina kuka bai saka shi ya fasa ba sai da ya gama yayi min magana.


"Kukan me kike? Wani abu aka miki ban sani ba?" Goge kwallar nayi sannan na mike akan abin sallah na miki mishi, kafin na koma gefe ina kallon shi, yadda yake cika sallah sai da jikina yayi sanyi, kome nashi akan tsari yake yana idarwa ya mike tare ninke abin sallah muka fita dashi waje.


Murmushi yayi min sannan ya kai ni gurin cin abincin har ya gama.
"Yau zaki ci abinci me dad'i" kallon shi nayi sannan nayi murmushi kafin na dauki cokali, daukar abincin yayi ya zuba min,. Yana faɗin.
"Don Allah kar santi yasa ki cinyewa da kwanon."


Kamshi spicys ya sani had'iye yawun, ina da yakinin abincin ya hadu iya haduwa. Haka yayi ta zuba min kome da ya girka,sannan ya dauko cokalin shi, shima ya saka hannu muka fara cin abincin tare, na kasa magana, abincin yayi dadi. Daukar nama naje yi ya rigani dauka,hakura nayi na bar mishi na zata zai ci ne sai kaiwa yayi bakin shi ya d'an hura kad'an sannan ya kai min bakina. A hankali na bude ya saka min. Ba kome ya sa haka ba, sai yadda idan na dibi abincin na kai bakina sai na dafe kirjina, ina jin zafin har gurin. Sai ya kwace cokalin ya shiga bani abincin ina ci, ya hakura da shi sai da yaga zan sha ruwa ya barni haka, daukar cokalin nayi bayan na sha ruwa na shiga bashi, shima yana kallona kawai sai naji a raina duk yadda aka yi. Ya rayu cikin kadaici da rashin soyayya, ya bani tausayi.
"Hammah kamar kayi rayuwar kad'aici?"


Rike hannuna yayi tare da kallon yadda hannun suke, duba agogon wayar shi yayi sannan ya mike, mai aikin gidan ya shigo tare da tattara inda muka ci abincin. Fita muka yi bamu tsaya ba sai a wani babban shagon saloon. Kawo mishi littafin abubuwan da suke yi aka yi ya fara dubawa, sannan ya nuna musu abinda yake bukata, kafin ya koma gefe.


Wani daki na musamman aka kai mu, anan aka fara wanke min kafana bayan an gyara min farcen, sannan aka fara wanke min kaina da mayuka masu sanyin dad'i, haka ake wanke min kan, ana gama min wanke kafar da hannun, aka fara zana min jar lalle, kallon matar yayi sannan yace mata.
"Ki huda mata kunne domin babu hujin kunne a tare da ita,"
"Kai Hammah" na fada ina kallon shi, dage min gira yayi, wayar shi ce tayi kara, a hankali ya dauka sannan ya fita.


Koda suka zo hujin kunnen nasan da zafi fir ba hana su, sai da ya shigo d'akin, suka mishi bayani. Yana zuwa ya kura min ido, kafin ya durkusa a gaba, yana kallon zanen da ake min, d'an mik'ewa yayi, ban san taya yayi musu magana ba, amma ya kai bakin shi kamar zai sumbaci ni naji an huda daya kunnen, ihu na saka mishi tare da damke wuyar shi da hannun lalle. Kafin na dawo daga duniyar zafi an huda daya kunnen, kuka na saka mishi. Masu aikin Saloon din sai dariya suke min.


"Hammah dariya suke min" juyawa yayi tare da kallonsu.
"Akan me kuke mata dariya"
"Tayi hakuri" tura baki nayi ya dauko wayar shi, zai dauke ni hoto na ki, ina kallon shi.
"Hammah na b'ata maka riga da"
"Babu damuwa bari na sauya"
Ya wuce wani shashi na cikin shagon, ya sauya sannan ya fito da wanda ya cire. Haka ya zauna yana jirana har aka cire lallen ga gashina da aka gyara, yayi kyau sosai. Fuskana ma suka gyara min, sannan muka fito.


Tunda muka fito nake lura da yadda yake zuba idanu a gurin, kafin muka shiga motar, janyo hannun yayi yana kallon shi.
"Ina son naga mace da zanen lalle kyau yake min, ki Cigaba da zuwa nan koda ban kawo ki ba, zasu miki kome da kike bukata,"


"Toh" haka muka bar gurin ina yawan karanta irin wannan abun a cikin Novel ko films ban tab'a kawowa za a wayi gari namiji ya dauke ni domin rage min damuwa ba, wato mun yi yawo sosai bamu koma gidan ba sai dare. Sannan ya sauke ni a cikin gidan, ya taimaka min na kwashe kayan da ya sayo min, muka shiga cikin gidan.


Tunda na shiga Jalilah take kallona, Kafin ta dauke kanta gaida Umma nayi, sannan na zauna ina me sunkuyar da kai musamman yadda take min kallon tuhuma. "Ki shiga cikin dakin"


A hankali na kwashi kayan na nufi d'akin.
"Jalilah kwashe kayan ki kai mata, kai kuma biyo ni d'akina." Ya mike haka ya bi bayanta, har cikin d'akinta. Zama tayi a bakin gadon ya zauna a stool.


"Baka da hankali ne? Yarinyar da kake so zaka dauka tun la'asar baka dawo da ita ba Da karfe goma na dare, ko an ce maka so hauka ne? Kar na kuma ji ko na gani, ai ki babu kome ka gaya min zaka fita da ita, idan da wani abu ya same ta fa? Wallahi karka kuma wannan gangancin ko kamanta kana da kane ne masu mugun rawan kai, bana so kar ka yi abinda ka san idan aka maka ba zaka ji dadi ba, kuma kaje Lateefah tana niman ka domin tazo nan ganin Yarinyar."


"Toh insha Allah ba zan kuma ba, amma wallahil ban da rike hannunta sai da take kuka tace tana son jin dumin mahaifiyarta na rungume ta, wallahil billahi azim ban tab'a kallonta da mugun nufi ba, don Allah kiyi hakuri ban gaya miki dan na d'aga miki hankali ba, amma ita matar da nake burin ta zama uwar Yarana ce idan na b'ata duniyar mu goben mu ba zata yi kyau ba, shi yasa nake bin kome a tsarin Ubangiji gobe zata koma gida, sati biyu masu zuwa zata dawo ta fara aiki a nan." Ya fada tare da mata sallama.


WALLAHI sai yaji duk ya bata tausayi, ya burge ta yadda ya iya fadar abinda ya aikata, Mohan ba yaro bane, amma rashin soyayyar uwa yasa shi tashi a wani irin murɗeɗɗan hali. Sai dai fara soyayyar shi yasa ya sauya fiye da bayan idan da yana Mohan shi ne, zai iya share awa daya bai bata amsa ba, har take ganin kamar bai dace da aikin soja ba. Addu'o'in tayi musu, sannan ta mike tare da fita a d'akin. d'akina da nake ta shigo ta samu ina tattara kayan da Jalilah ta fasa min har da mayunkan da ya saya min, kallo na tayi ta ga ina share kwalla.
"Taya aka yi kayan suka watse haka?" Jan hannuna nayi domin ban iya karya ba, kuma ban san yadda zan gaya mata ba, sai nayi shiru.


"Jalilah ko?" Gyada mata kai nayi, fita tai can sai muryan ta naji tana kuka, dan Ba'are ya shigo har dakin yana bani hakuri.
"Babu kome" na gaya mishi ina tattara kayan.
"Naga wasu sun fashe"
"Eh ba kome zan gyara su" na dauki kayan na zuba a jaka na.
"Ko zan sayo miki wasu ne" kallon kayan nayi domin kayan da Masoyina ya saya min ne, ba zan iya sauya su da wani ba.
"A'a kayan da Hammah Mohan ne ya dauka min, dan haka babu wata matsala." Na fada mishi haka, ganin bani da niyyar magana ya sa shi fita daga dakin, yana mamakin wannan yanayin, ko zubar da kayan banyi ba, dan haka yana fita ya kira Mohan bai dauka ba ya tura mishi sako da fatan zai gani.


***
Cikin nutsuwa ya shiga cikin gidan, tana zaune a babban falon ta, tana kad'a kafarta. Kallon shi tayi lokacin da ya shigo da sallama.
"Waalaikumun Salam" ta amsa tana kallon shi, dama yana ganin yadda take ya fahimci kome,.taji labarin Moonah, zama yayi sannan yace mata.
"Ammyn Barka da hutawa"
"Yawwa Mohan, Ya Surukar tawa?" Kallonta yayi sannan yace mata.
"Tana lafiya"
"Dama itace kake so?" Gyada kai yayi sannan yace.
"Ammyn itace tayi jinyata kuma."
"Yar Uban waye a kasar nan?" Nan ne gaban shi ya fadi, ya rasa abinda yake mishi dad'i.
"Waye Ubanta?" Sake dukar da kai yayi.
"Ina sonta ne, ban damu da ko yar waye bane, kawai zuciyata tayi na'am da ita, bayan haka ba zan iya jure rashin ta ba, kuma ba zan iya jure tashin hankalin da zata fuskanta ba, zuciyata ta bani ita kuma na amsa hannu bibbiyu."


"Mohammed Mamman Nasir! Nace waye Ubanta?" Kallonta yayi sannan ya cigaba da cewa.
"Ba yar kowa bace!"
"Ba yar kowa bace kake b'ata mata lokaci? Bayan kasan cewar nan da wasu watanin za ayi baikon ku da Hanan?"


"Ammyn ni fa bana son hanan, ni matar da bata san darajar arziki da dukiya nake nima, matar da zan bata kudi tace min me zata yi dashi nake nima, matar da zan ce mata gabas tace min toh nake nima, matar da zan ce mata zauna ta zauna ba zan yarda na auri matar da bani da iko da ita ba, ina ji ina gani haka na rasa soyayyar ku shine xan yarda ba fada hannun wata mace? WALLAHI ba zan iya aurenta ba, iya gaskiya na gaya miki"


Cike da mamaki take kallon shi, kafin tace mishi.
"Yarinyar da ta gudo daga gidan su, sabida namiji zaka ce kana sonta kai ma idan ya gaji da kai guduwa zata yi tabi wani, yarinyar da bata san darajar Iyayen ta ba?"
"Eh amma ai duk abinda zata yi domin gobenta yayi ba dan yau ɗinta ba, ita guduwa tayi tabar gaban iyayen ta, idan har na rasata tabbas gawata za a shigo miki da shi, dan haka ki barni da abinda zuciyata take so itace farin cikina, kuma itace hasken idaniyata, don Allah karki tab'a min abinda nake so."


"Kai baka san girman darajar ka bane? Ko baka fahimci yadda Allah ya maka ni'imommin rayuwa bane? Ubanta yana da arziki ne?" Ta tambaye shi.


"Ko gidan kanshi bai mallaka ba, ni dai a haka nake son abu na" ya faɗa yana kallon ta. Abin mamaki ya kuma bata. Lallai maganar Karime gaskiya ce yarinyar bata bar Mohan haka ba, yaron da mace bata ishe shi kallo ba, shine yanzun yake fada mata itace rayuwar shi. Dama tunda taji ance mata Bororoji ce tasan dole ayi haka mutane masu mugun asirin bala'i, dan haka dole ta mike domin karkato da hankalin D'anta, zata bawa Hajiya Karime damar yadda zasu karkato hankalin shi, ina wannan ai ba zata iya dauka ba.


"Baba na, ka rabu da ita kaji ina nan ina shirya maka rayuwa me inganci, wancan yarinyar kuma ba mutuniyar kirki bace domin haka suke yiwa mutane mugun abu. Ka hakura da ita zan nima maka macen da ta dace da kai kuma ban da abinka Baga Hanan ba fara doguwa me kyau ina zaka kai wancan me duhun fatar ka hakura da ita mana.


*Nasan kuna kokari wallahi amma ku kara min yawan Vote din kunji dearies idan ba Novel din kudi ba bana hana kaina barcin safe ba, amma gashi ina idar da sallah Asuba na fara typing na gama Pagen 07:16 na cigaba da Next page kunji ku kara min sai muyi tafiyar yadda baku zata ba.... Thank You 😁💞❤️💓😍😘 Nagode*
#Mai_Dambu...
[8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1108770833?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=XvTJ715kPu2X0PivW5mr2ueQhMuyT9VxReszdcWX9iE99sEqXcVLFhnWOGRWovfKLC7i4%2FOUqPMZZ6VWIcVOpGiYhQwcVRmRXaxx6lPfK9GN9UgTFxHmNED7gtVuw37%2F


🐂🐂BOROROJI🫀🫀


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


BABI NA TALATIN DA BIYAR.


_Ina mika sakon godiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login