Showing 57001 words to 60000 words out of 181864 words
da sauri na fita daga ajin duk inda na wuce dariya ake min.
"Almamoon Isma'il Wodaadabe, tsaya ka ciwo abinda aka rubuta a bayan ka" cak na tsaya ina jin wani irin tsoro yana kamani, nasan dai ba haila bace tunda sati Daya da ya wuce nayi gama.
Cire min takardan da aka rubuta Kalmar Mata maza da manyan Haruffa. Jikina har wani irin rawa yake, na juya zan bar gurin.
"Mamoon" juyawa nayi na kalle shi.
"Kad'an daga cikin abinda kayi min kenan, kuma baka ga kome ba domin yanzun aka fara."
Dariya ya bani na tsaya sosai a gaban shi ina faɗin.
"Idan na kula ka ban san darajar kai na bane, amma idan har ka cika namiji ka tari Mohan Mamman Nasir Aghali ka ga yadda ake wasan kura da lusari irinka."
Na juya zan bar gurin ya fisgo ni,cikin fushi na kai hannuna zan mare shi, sai kuma na fasa ina kallon cikin idanun shi.
"Wallahi kaci albarkacin girman ka da nake gani da yau na mare ka a cikin makarantar nan, kuma na rantse da Allah sai na baka mamaki."
Nayi tafiya na na barshi tsaye cikin mamaki.
"Dan daudu zai bani mamaki" murmushi nayi na cigaba da tafiya, domin bani da abin da zan gaya mishi, koda na gaya mishi ba zai ji haushi ba, kuma koda ma mishi a aikace ba zai damu ba, duk wanda ya cutar da kai ba zai tab'a jin zafin dan ka rama a lokacin barshi ya manta abinda ya aikata, haka na kyale shi. Sake tare ni daliban shi suka yi.
"Kai dan dan daudu, me bin maza kawai lalatacce mara hallaci." Ban kula su ba, sai ma keb'ewa da nayi zan bar su a gurin dan basu min kama da masu hankali ba.
Ina barin gurin su, na samu kasar bishiya na zauna, ina son nayi kuka amma ba zan iya ba, bana son nayi kuka yanzun so nake na iya shanye kuka na, gashi ban san halin da Hammah Mohan yake ciki ba.
Bayan an koma aji na mike tare da shiga aji, na zauna ina sauraron darasin shi. Har ya gama zai tafi.
"Dalibai ku kasance masu tsentseni da sanin ya kamata, karku zama butulu marasa halacci."
Murmushi nayi ina kallon shi, sabida ya daina bani mamaki sai dariya.
"Kai waye kakewa dariya?" Ya tambaye ni, ware idanun nayi cikin dariyar renin hankali nace mishi.
"Ina dariyar yadda mutane suke manta waye su? Kamar Ni dai." Na nuna kai na ina dariya. Mik'ewa nayi zan fita, ya tare hanyar fita.
"Ansar Yusuf, ka bani hanya na wuce na Barka kayi rayuwar ka baka isa ka hanani tawa rayuwar ba, Ansar kayi yadda kaga ya dace amma karka shiga cikin abinda babu ruwan ka" na fada ina me barin ajin.
Da sauri na fita a makarantar.
Ban samu motar da yake zuwa dauka na ba, dan haka na tari abin hawa, sai dai ina shiga da malam Ansar nayi tozali, kamar zan fasa dan wani irin tsoro ne ya kamani, sai na shiga na zauna ina kallon shi. Kamar da wasa madadin su kai ni inda na faɗa sau suka wuce dani wani gurin.
Wani asibiti muka nufa, ban mishi musu ba, har muka shiga cikin asibitin. Tare da nufar office din wani likita, kamar Balarabe ne. Muna zuwa ya mika mishi hannu suka gaisa, Kafin ya fita.
"Ko zamu je na duba ka?" Murmushi nayi domin a yanzun nake kara hango Malam Ansar shi ya dace da kasungumin mahaukaci ba Hammah Mohan ba. Mik'ewa nayi zan fita ya mike shima.
"Kazo ka zauna na duba ka."
"Ba zan iya ba, kuma wallahi ka kuskura ka tab'a ni sai ka yanke ka." Na fasa wata Kwalba da tasa shi tsorata, na fita abina daga dakin. Na samu baya nan da haka da sauri na fita a cikin asibitin. Kamar zan tashi sama haka na bar harabar asibitin, ina isa bakin hanya ana kiran sallah la'asar, Dakyar na sami abin hawa. Na fada mishi inda zai kai ni.
Ina shiga malam Ansar yana isowa da gudu ya biyo mu.
"Malam karka tsaya sace ni yake son yi don Allah mu tafi" na fada mishi ina me jin kwalla na cika min idanuna, ai kuwa driven ya taka motar da gudu, muka bar ganin shi. Tafiyar kusan minti arba'in ya kawo mu unguwar lokacin da ya tsaya na bashi kudin shi na juya zan tafi.
"Malam kudin yayi yawa"
"Jeka kawai" na fada mishi ina ƙoƙarin shiga cikin kofar get din farko.
Rike hannuna malam Ansar yayi, a tsora ce na juya. Ina ido hudu dashi na fasa ihu, ina ƙoƙarin kwace kai na.
"Don Allah ku fito ku taimake ni, zasu sace ni" kafin sojojin su fito ya shaka min abu a hancina, komawa nayi tare da zuɓewa a jikin shi. A hankali na fara ganin kome yana juya min bibiyu kafin na koma tare da lumshe idanuna.
"Hammah Mohan" na fada a hankali.
Fitowa sojojin suka yi lokacin har ya saka Ni a motar shi, ina da gudu ya bar Unguwar. Danna wani abu suka yi take ilahirin sojojin gidan suka fito. Suna masu hango motar tana tashi da kura.
"Meye ya faru Fahad?"
"Wallahi wani da bamu sani bane ya dauki Alm.."
"Haukar banzan kuke kenan? Tsayuwar Uwar me kuke?" Inji Malik,
Ai kuwa kamar wanda ya ankarar da su, suka rufawa motar baya da hilux, amma kafin nan ya b'ace musu, kamar zasu yi hauka.
Koda suka dawo sun sami Major General Mohan Mamman Nasir Aghali a tsaye yana kallon su. Baki daya aka rasa wanda zai sauko a cikin motar zunzurutun yau sun ganshi a cikin unifoam. Yana jingine da bike kanshi sanye da hular yaki, fuskar shi tayi jajjur. Yana kallon agogon hannun shi. Tab'a bluetooth din shi yayi.
"Ina jin ka? Number guy din? Ka gayawa dakin iko, su bani bayanin inda yake nan da minti biyar"
A fusace ya kuma daka mishi tsawa.
"Dan Ba'are! Wallahi na rantse da Allah sai na harbe duk wanda ya kuskura ya shiga tsakanin mu da My Maid idan ka sake na kuma kiranka wallahi sai na dakatar da kai"
Ai sojojin da basu nimo Almamoon ba sai gasu sun zube a gaban shi cikin tashin hankali.
"Yallabai wallahi" yatsar shi ya saka a bakin shi, tare da nuna musu hanya.
A hankali ya hau kan bike din, tare da saka hular kwanon shi, ya taka machine din ya jata da mugun gudu, yana bin bayanin da ake gaya mishi. Sai da yayi tafiyar minti Talatin kafin ya isa asibitin da Almamoon ya gudo, cikin isa ya tsaya yaran shi suka iso, tare da taka mishi baya da bindiga a hannunsu, irin duk wanda ya kawo mana wargi zai sheka lahira.
Wani irin tafiya yake cikin jarumta da Izza, tare da jin shi din a bakin aikin shi yaƙe. Matashin sojan da yayi zarra sama da sauran manyan sojojin da suke saman shi. Duk inda suka wuce bin su ake da idanu, sabida yadda suke takon a nutse baka jin kome sai karan takun takalmar su, kai.daga dakuna sai leken su ake, cikin isa da jin kai ya isa bakin kofar da aka gaya mishi nan Almamoon yake, dukar kofar yayi da kafiran takalmin shi, budewa kofar tayi daidai ana ƙoƙarin cire kayan Almamoon wanda yake kwace kamar gawa.
Wata Ɓoyayyen ajiyar zuciya ya sauke kafin ya tsaya cak yana kallon fuskar Almamoon da kwalla ta bushe akai. A hankali ya ja wani kujera ya zauna yana kallon yadda Nurse din cikin dakin da kuma likitan suka yi tsuru tsuru.
"Ina yake?"
Fitowa Malam Ansar yayi tare da da kallon shi babu tsoro a fuskar shi ko nadama. Mik'ewa yayi tare da nufar shi.
"Wannan shine kashedina da kai na karshe karka tab'a Yaron nan tunda ba kai ka kawo min shi ba" inji Malam Ansar,
"Idan na ki fa?" Ya tambaye shi a gadarance.
Tare da nufar Almamoon, yana ƙoƙarin daukar shi. Wani allura ya dauka ya suka a wuyar Almamoon, kafin ya juya ruwan. Mohan ya kai mishi wani irin duka akan hannun..sai da kashin hannun shi tayi kara, yayi maza ya zare alluran. Takowa yayi gaban shi yana kallon shi. Da hannun daya ya d'ago shi.
"Idan ka kuma tab'a ko inuwar shi, wallahi na rantse da Allah sai na aikaka lahira, ina kyale ka ne sabida karatun shi nasan zai fi son shi a matsayin shi ne ba kowa ba, idan ka sake raina ya b'aci, hmm" ya faɗa tare da barin gurin shi ya juya zai dauki Almamoon.
"Wallahi ka rubuta ka ajiye, sai na raba ka dashi, wannan alƙawari na ne"
Daukar maid din shi yayi tare da tsayawa cak, yace.
"Ni kuma nayi maka alkawarin barinka a raye domin ka ga yadda zan yi da Yaronka."
"Wallahi baka isa ba! Ni zan Barka a raye domin ganin yadda zamu yi dashi." Inji malam Ansar,
"Hhhh! Ni Mohammed Mamman Mohammed Nasir Aghali Mohan na kara gaya maka na maka alkawarin kana raye zaka gan mu da idanun ka, kai ba kai ba hatta shaidanin zuciyarka sai ya gan mu a tare balle kai banza irinka... 2k Words 😁
_😌😌😌 Anya zan cigaba kuwa wallahi Vote yayi kad'an ko na ajiye shi ne na fara Kishi a tsakanin zubda jini ne dan na ga kuna mutuntta labarin kuɗi sama da free book_
[7/22, 9:49 PM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA ASHIRIN DA D'AYA.
Cikin ihu da masifa yake bin bayan Mohan tare da niman riko rigar shi, amma zaratan sojojin da suke bin bayan MG Mohan suka cafke shi, tare da shiru suna jiran Umarnin shi.
"Ku kyale shi ya rayu. Na barshi ya rayu domin idan kuka dake shi sai ya leka lahira ya dawo." Ya fada tare da cigaba da tafiyar shi,
Ganin Almamoon baya motsi ya sashi karawa da sassarfa, yana kallon fuskar shi, hular kanshi ne ya zame, lallausar gashin sa da yake tufke baki wuluk wanda yake warware. Kallon shi yake yana kara mamakin yadda namiji dashi yake da uban gashi haka.
Yana fitowa ya ajiye shi a cikin motar su, kallon Fahad yayi tare da kallon bike din shi, sara mishi yayi sannan ya koma, gurin bike din ya ja machine din da gudu, yayi da suma suka rufa mishi baya. Tab'a bluetooth din shi yayi tare da cewa.
"Malam turo min wani likita daga barikin sojan maradi."
Tab'e abin yayi tare da sauke wani irin ajiyar zuciya.
"Yallabai an tura masu wani motar da zata kwaso su."
"Hmm" ya faɗa, yana me kallon zoben hannun Almamoon, a hankali yake me jin kamar ya rufe Ansar ku baki daya, amma bai san girman da yake dashi a duniyar Almamoon ba, sai ya farka.
Suna isa gidan ya sauke shi cak, har yana mamaki.
*Dube bakin shi da ya iya zungure min goshi, nan kuwa tsiwa ce zallah babu wani karfi dube shi kamar ba namiji ba*
Ya fada a kasan ranshi, yana jin wani dariya yana niman kwace mishi, yanzun ma idan ya farka zai koma kamar da yadda zai cigaba da rena mishi hankali, dan yana son haukar yaron baki daya ya kam manta da batun shi din wani ne yayi ta shirme.
Shigowar wani likita tare da wasu mata biyu, suka fara aikin su a kan Almamoon, tashi yayi ya bar musu gurin. Can suka ci-gaba da aikin su, sai kallon juna suke musamman bayan da likitan ya gama nashi suka fara nasu. Abun mamaki ya basu. Me yasa haka?
Dan gulma sai da suka yi ta duba shi har cikin, tsoro ne ya kama su lokacin da Mohan yayi gyaran murya, da sauri suka bar shi. Juyawa suka yi. Likitan ya fara magana.
"Yallabai mun debi jikin shi, zamu bincika muga abinda yake cikin shi. Nan da awa daya."
"Amma Likita mara lafiyan yana"
"Na Fahimta muje Insha Allah zamu kara dawowa, sannan na sami sauran birbidin maganin da aka shaka mishi zamu yi bincike akai."
Suna barin gidan likitan ya balbale su da faɗa, yana gaya musu.
"Dan baku da hankali taya kuna gaban MG na soja zaku saka bakin ku a cikin maganar mu kusan waye shi?"
Shiru suka yi dan sun san halin shi masifaffen ne, har suka isa asibitin, cikin abinda bai fi awa daya ba aka gama binciken. Yana karanta abinda ya kusan da sauri ya kira Dan Ba'are ya gaya mishi.
"Don Allah ku tawo da majiyancin nan rayuwar shi tana cikin hatsari"
Zunzurutun tashin hankalin da dan Ba'are ya shiga kamar zai dira a maradi, dan haka ya kira Mohan a hanzarce.
"Yaron nan yana cikin hatsari a kai shi asibiti gani nan zuwa."
Kashe wayar Mohan yayi mishi.
"Hello Hello! Kai kai katsaya mana" babu shiri ya dauki kayan shi bai tsaya wata wata ba. Ya kira wata wayar da take cikin Office din shi, ya faɗa musu abin da yake bukata, cikin kankanin lokaci suka hada mishi kome, yana fita ya daga Office gidan shi ya nufa, ya haɗa abinda zai hada,
....
A dakile ya watsar da wayar tare da shimfid'a dogayen kafaffun shi a samar table, yana kallon Almamoon da fuskar shi yayi wani irin fayau kamar wanda aka kwashe mishi jinin jikin shi. Bakin shi kuwa fari yayi fayau.
Idan ya cigaba da rike yaron mutuwa zai yi, dan haka a zuciye ya dauke shi, yana fitowa dauke da Almamoon, sojojin da suke gidan suka mike, tare da nufar inda motar aikin su yake, suka yadda saka shi yayi tare da shiga ya zauna ya daura kanshi a kan cinyar shi.
Lumshe idanun shi yayi yana tuno yadda ya birkice yau ganin halin da ya shiga, duk yabi Cameras na cikin gidan yaga yadda yaron yayi ƙoƙarin kula da lafiyar shi. Da yadda aka yi ta had'a mishi mugun abu a cikin gidan a saka Hajiya Safiya tayi ta dukar shi. Ya rasa inda zai saka zalincin Hajiya Safiya baki daya.
Sai dai wani abu daya da ya lura dashi. Bude fararren idanun shi yayi akan kofar asibitin. Ga Nurse da suka tsaya suka jiran fitowar su, a hankali ya fita tare da bude inda Mamoon yake kwance. Ya fitar dashi,
Tunda aka shige dashi wani daki bai kuma ganin wani ya fito ba. Tun yana kirga lokacin da aka shiga har ya kai ya daina duba agogon lokacin sallah nayi suke fita da Malik.
Bayan awa biyu sai ga Dan Ba'are, kallo daya Mohan yayi mishi ya dauke kai Kamar bai tab'a ganin shi ba. Asalima haushin yadda yake bashi umarni yake sai kace irin shine a kasar shi. Wani b'ata rai yayi yana shan kamshi kamar bashi ba.
Shi kuwa bawan Allah bai fahimci halin abokin shi ba, abu daya zuwa biyu ya tambaye shi.
"Ya jikin ka? Ya jikin Almamoon?"
Wani basarwa yayi tare da mai da smart watch din shi hannun shi yana wani cin magani, dakyar bakin shi ya motsa da cewa.
"Da sauki"
Ka sake Dan Ba'are yayi yana kallon shi. Kafin jikin shi yayi wani iri, komawa gefe yayi ya zauna tare da ɗaukar wayar shi yana latsawa,shi kuwa Mohan sai wani tsare gida yake irin ba zai yiwu ba.
Fitowar likita ya sa dan Ba'are mik'ewa ya mikawa Dr Faruq hannun suka gaisa.
"Faruq meye a ke ciki?"
"Yallabai rayuwar shi ta fita daga matakin tsari, sai dai bamu da kayan aikin da zai tacce jikin shi."
"Dama kunsan baku da kayan aikin uban waye ya ce kuce a kawo ta?" Ya fada tare da watsar da su baki daya gefe yayi wucewar shi cikin dakin.
"Mohan ka tsaya ayi magana kaji yace idan da za a fita dashi kasar waje ko Saudi za a dace."
"I fuck nonsense words, taya zaka gaya min maganar banza kaniyar kasar waje hell You da kasar wajen" ya faɗa a tsawa ce. Yana bankawa dan Ba'are hararar.
Dan ya tsani duk wanda zai mishi iyayi akan Mamoon.
"Amma dai meye na zagi? Kamar wanda aka mishi wani abu? Yaron nan dai ni na kawo shi dan lura da lafiyar ka, so it's my responsibility na tsayawa rayuwar shi if not me kake tsammani za a dauke ni, don Allah kayi hakuri a dauki matakin da ya dace."
Kura musu ido yayi cikin nutsuwa ya juya zai fita daga asibitin, zuciya kawai yake dawainiya da shi, yana fita ranshi ya kuma b'aci dan haka bai tsaya a asibitin ba ya nufi gidan shi, dakin motsa jikin shi ya cire kayan shi ya rage daga shi sai farin wando. Daukar karfe yayi yana nazarin yadda dan Ba'are ya nuna mishi fin karfi akan Almamoon ne. Ba zai kuma shiga damuwar su ba.
Dan haka abinda yake gaban shi zai yi ya cigaba da boye matsalar shi,.kiran Malik yayi tare da zubawa kofar idanun shi. Wanda suke cike da masifar rikici.
Yana zuwa ya zuba mishi wasu files a gaban shi, tare da kamewa ya sara mishi tare da yin alamun yana da magana.
"Humm" yace a hankali,
"Yallabai! Na gama tattara bayanan baki daya, sai dai yaron bai da matsalar