Showing 81001 words to 84000 words out of 181864 words

Chapter 28 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6288

Ba'are, abokin Alhaji Mamman Nasir ne, abokin shine tun ma Yaranta, kuma Alhamdulillahi har yau abokin shine domin duk abinda ya taso mishi me taya shi murnar ko bakin ciki, Dan Ba'are ne.


Duk da yaso bashi matsayin minista, amma yaki amsa yace mishi.
"A'a duk abinda zaka bani duniya tace sabida Ni amininka ne, amma idan ka ajiye shi muka rike amintar mu babu me magana, kasan me zan iya yin kuskure ba zaka gaya min ba, amma a yanzun babu kome da zai sauya mu sai idan kai ne kaso haka."


Wannan haka ya kara musu dankon aminta, kuma har kwanan gobe a gidan Dan Ba'are Alhaji Mamman Nasir yake karyawa da abincin rana, sabida bai aminta da abincin da ake dafawa a cikin gidan shi ba. Wannan shine halin da yake ciki da kuma nasabar da take tsakanin Mohan da Dan Ba'are, sai Hanan HH Dogo.


Kwanciya yayi a dogon kujera, ta shiga turo min sako.
_Me yasa nake kiran ka bana samun ka? Ina son jin a Damagaram a ina kake ina son ganin ka_


_Almamoon ka dauki kirana, ina son rakiyar ka zuwa London ne! Ka shirya gani nan zuwa_


Can ya kuma kiran layin amma bai shiga ba.
Kwanciya yayi sannan ya kuma tura wani sakon.
_Kayi min magana idan ka bude wayar lafiya?*


Cikin damuwa yake kallon wayar, yau kwana biyar baya samun shi a wayar kuma koda ya shiga baya dauka.


*Insha Allah gobe ina hanya*
Ya kuma tura sakon, yana jin kamar yabi sakon shima
***
Damagaram.


Duk abinda na gayawa Innah da wanda Hammah Mohan ya bani ta amsa, amma wayar da ya saya min da ita zan ji muryan shi naki nuna mata, duk da tana min kallon akwai abinda nake boye mata.


Ina kwance naji wayar tana nishi, tashi nayi dan na hango ta a waje, tana ta sintiri. Tun ranar da tayi min shegen duka ko fita waje bana yi, dan haka ina kwance na duba wayar, sakon shi da na gani babu adadi yasani mik'ewa. Tare da ɗaukar kayana na saka. Sannan ya fita kofar gida tana kallona, bayan gidan mu na nufa, na kira layin shi duk da dare ne.


Dauka yayi yana sauke ajiyar zuciya.
"Hammah Mohan don Allah karka zo"
"Akan me?"
"Nace karka zo" na fada cikin kuka, sannan na kashe wayar na koma cikin gidan, kallona tayi bata min magana ba, nima na wuce d'akina, nayi kwanciya ta. Amma kamar yadda naga rana haka naga dare, domin bani da cikakken nutsuwa, ga bugun zuciyar da nake ji.


...
Kallon wayar yayi tare da mik'ewa, bai yi wata wata ba ya gyara kayan shi tsaf, ban daki ya shiga yayi alola. Ya fito ya gabatar da sallah nafilla, tare da addu'a Allah ya bashi sa'a a tafiyar da zai yi. Ya kuma nemi tsari daga mugun ji da mugun gani. Sannan ya koma ya kwanta.


...
Gari na wayewa ba fita niman layin shi bata shiga,


Tunda na koma cikin gida na zauna tare da fashewa da kuka,bata damu ba kuma bata tambaye ni dalilin kukan ba, ni dai ta zuba min ido da na isheta ta rufe Ni da duka domin Baba da yake karb'ana baya gida, kai Innah ta cika zafi. Ita ke dukana ita ke kuka. Haka wunin ranar nayi shi kwance da zazzaɓin.


Karfe bakwai bayan an fito masalaci har da rabi, na fito a hankali domin zazzaɓi yake damuna, kiran layin shi na fara naji tana ringing. Yana dauka na fashe da kuka.
"Hammah"
"Kayi shiru, gani nan yanzun na idar da sallah..."


"Idan zabuwa tana yawo kare na yawo dole a riski juna, Mata maza yau zan ji dadi na da kai" inji Shege.


Zaro idanu nayi tare da cire wayar, na kalle shi yana tsaye sai wari yake. A hankali na raba gefen shi zan wuce, ya kai min cafka tare da matsa ni a jikin bango.
"Dan gani asarare sai na bari ka kwace min? Yau nake son kaji yadda nake, idan ba haka na maka ba, ba zaka Fahimci yadda nake kaunar ka ba, na ci bayan ka na kuma duba gaban ka naci ramin nan da yake kara maida ka wani na musamman."


Kuka ne ya kwace min nayi ta naushinsa ko zai bar ni, amma bai saka ya barni ba, sai ma ciro abin shi da yayi yana gogawa a bayana.


Kiran Hammah ne ya shigo na hada karfina da nake da shi na ture shi sannan na fita a lungu da gudu, ya rufa min da gudu har zauren gidan mu. Tare da saka min kafa, ashe Hammah yana hango mu, fita yayi a motar da mugun gudu shima, ya shigo zaune , wayar ta fadi can nima kuma ina kwance a kasar sabida gwiwata da ta Bugu. Yana shigowa ya sauke ajiyar zuciya lokacin da yaga Shago ya kamo ni.


"Ina ga tunda uwarka ta haife ka bata tab'a baka matsayi na musamman ba, Yaron da nake ji da shi zaka tab'a."


Ya tsaya tare da jingina bayan shi da kofar gidan, sannan ya tako inda Shago yake, sannan ya kalle shi bayan ya ciro gaban shi. Wani irin Mahaukacin naushi yayi mishi a fuska sai da ya zube akan gwiwar shi, ya kuma kai kafar shi ya daki shugaban karamar hukumar wandon shi.


Wani irin ihu ya saka tare da zuɓewa yana shure shure, jan kafar shi yayi ya fitar da shi daga zauren, dakyar na mike ina dingishi, ina kallon Yadda Mohan yake dukar Shago.


_idan mutum ya tab'a ka hukuncin shi a cire hannun shi, idan kuma kaddarar shi ta saya rungume ka hukuncin shi kisa ce..._
Ban san lokacin da wani karfi yazo min ba, da gudu na rungume bayan shi, kaina a bayan shi.
"Ya isa, karka kashe shi? Karka janyo min wata kaddarar da ba zan iya dauka ba, ya tuba"


Bai fasa ba sai da nayi karan Shago shege alamar Hammah Mohan ya mishi wani ba, na juya da sauri gaban shi na ture shi.
"Nace Ya isa haka? Me kake so dani? Wannan irin rayuwa ce haka? Zaka kashe shi ne?" Na fada da karfi ina kuka.


Ji nayi ya riko hannuna, ya saka a kirjin shi. Sai numfashi yake saukewa yana kallona, ji nayi an fisgo ni, tare da kifa min mari, "tassss" gurin ya dauka. Da hanzari ya d'ago kai yana kallon Innah da ta kuma d'aga hannu zata dake ni yace mata.
"Kiyi hakuri, Yaro ne bai san kome ba."


Ya fada a sanyayye..
"Kai ne ko? Kai ka sauya mishi alkibla? Kar na kuma ganinka a kofar gidan nan ka tafi ko kuma wallahil na dauke shi na nisanta shi da ko ina, kaje bana son ganin ka karka lalata min rayuwar shi."


Haka ta ja hannuna har zuwa cikin gidan, yana tsaye bai tafi ko ina ba, Yan uwan Shago shege ne suka zo suka dauke shi bude motar shi yayi ya ciro kudi ya wurga musu, suka bar gurin.


"Wato shine ya sauya kama tuni na? Wannan abin na waye?" Ta nuna min wayar da yake yashe a wajen.


"Innah don Allah karki." Buge min baƙi tayi, sannan tace min.
"Wallahi sai naci mutuncin ku daga kai har shi"


Hada kayan tayi tare da fita dashi ta mika mishi kayan shi.
"Bana son na kuma ganin kafarka a kofar gidan nan, idan kuma haka ya faru, zan cika kalmata da maganata da abinda zai dame ka. Ka rabu min dashi. Kayi tafiyar ka bana son ganin ka a rayuwar shi, bana son kukan shi."


Tana gama fadar haka ta juya tare da komawa cikin gidan .. kuyi comments da Vote Insha Allah yau zaku samu next page da dare....💃 Amma sai na gani a ƙasa
#Mai_Dambu
[7/29, 8:27 PM] RamlatArManga: https://www.wattpad.com/1107324574?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=4ugJdhgGa4BvbsExr19Jvhrf8LWxJfS%2FSxI1B7ZzbxI65y3FAC%2F%2Bp5dONKBm%2FARRS1nZwKrYHg3%2FBE6YQ7n4aR6rGLUDTKvkAvezukOoIJGO6fac4VkMX5uB5%2FHWvZsK


🐂🐂BOROROJI🫀🫀


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


Wannan shafin gaisuwar kune Mutanen Wattpad Nagode sosai..❤️💓💞


BABI NA TALATIN.


Har malam Umaru yazo ya wuce Mohan yana jikin motar shi kayan yana gaban shi, bai saka yayi fush ba, haka yana tsaye har dare yayi sosai yana tsaye a gurin.


.....
Bayan Baba Ya dawo, bata gaya mishi ba, kuma bata nuna mishi wani abu ya faru ba, domin ta gargadi ni da babban murya, ina kallon su suka kwanta,wato suka shiga dakin su, nasan yana kofar gidan bai tafi ba, dan haka na tashi a hankali na fito tare da dauko wani abu na saka a jikin katangar gidan mu, na haura katangar na diro. Sannan na kwasa da gudu, sai gurin shi.
Ina zuwa na fada a jikin shi ina kuka.


Bude min hannun shi yayi tare da shiga cikin jikin shi.
"Hammah kayi hakuri, ka tafi"
D'ago kaina yayi tare da kallon yadda nake kuka. Sake maida kaina yayi, yana shafa bayana.


"Ina nan har sai Innah ta barni nayi magana da ita." Ya fada tare da dauke kan shi. Kallon shi nayi da gaske yake fa.


Dan haka na gyara tsayuwa na a jikin shi.
"Hammah"
"Hmm! Mamoon"
"Hammah"
"Na'am My Golden Boy" ya faɗa tare da shafa kaina.
Bayan ya riko hannuna, ya nufi kofar gidan mu dani.


"Don Allah karka buga musu kofar zata zane ni ne, don Allah karka bari tasan na fito ta katanga, please Hammah Mohan" bai saurare ni ba, ya
buga kofar yayi dakyar aka bude. Baba ne ya bude. A hankali ya ciro ni daga bayan shi.
"Maza shiga ka kwanta, ina nan har gobe."


Ya fada yana tura ni cikin gidan, tsoron Allah da tsoron Innah yasa Ni jin fitsarin tsoro, haka Baba ya kalle shi tare da cewa.
"Nagode!"
"Baba kar a dake shi don Allah."


"Idan aka dake shi zaka karya mu ne kamar yadda kayiwa Wancan Yaron?" Bai ce kome ba, ya tsaya a gurin har suka rufe kofar gidan, zama yayi a kofar gidan bayan ya ciro ƙaramar bindigar shi, ya gyara kunamarta.


Ganin yadda ina take niman abin dukana yasa Baba ya sha gabanta.
"Ya isa haka! Meye laifin shi, Kinga dukar nan da takurawa, wallahi shi zai lalata miki shi, tunda na dawo kika ki gaya min abinda ya faru nace miki wani abu ya faru ne? Kika ce min a'a, amma a can inda nake zaune aka gaya min Shago ya hadu da wanda ya fi karfinshi inda yabi Almamoon, na nuna miki na sani? Toh bari na gaya miki matukar Shago yana unguwar nan wallahil azim abinda kike boyewa zai fitar miki dashi domin ba dan Allah ya kawo shi ba sunan tattalin ki na shekaru sha takwas zai tashi a banza tsanani baya gyara sai lalatawa ba yau na fara gaya miki ba.


Sabida ina son auna girman abinda yake faruwa ne, dan haka karki sake Almamoon ya fahimci dalilin ki na hana shi abinda yake so domin kuwa goben sa zai lalata da hannun shi. Ya ga yadda zakiyi, kai kuma wuce ka bani guri."


-- Haka muka kwana zuciyar kowa babu dad'i, Allah Sarki. Hammah Mohan anan kofar gidan ya kwana. Da asuba suka nufi masalaci da Baba, sannan suka yi hira bayan ya fadi abinda ya kawo shi da abinda ya faru a baya, malam yayi godiya sannan yace mishi.
"Mun gode, sai dai kawai abar aikin nan idan hankali ya kwanta za a yi miahi kaga mahaifiyar shi hankalinta yake s tashi, sannan ina son Yaron ya koma makaranta sabida kwazon shi don Allah kayi hakuri zan kula da kome, ina son Rayuwar Almamoon ya bunkasa sosai."


"Insha Allah Baba nayi mata alkawarin ba zan kuma takura mishi ba, Yaron yayi jinya na, dan haka zan kula dashi sosai kamar kanina, kabawa Innah hakuri ba zan lalata mata Dan ta ba, wannan kudin shi da kayan shi ba zan iya kome dashi ba, ka bashi Don Allah."


"A'a yaro"
"Baba ka ɗauke ni d'anka ne, idan ba zaka nuna min iya Almamoon ka haifa ba" amsa Malam Umaru yayi yana mishi godiya da saka Albarka,


Sannan ya shiga cikin gidan,, ina kwance ya d'aga labulen tare da cewa.
"Kaje yana son zai tafi yanzun."


A hankali na mike tare da fitowa waje, na same shi yana tsaye dake garin bai gama wayewa ba, a hankali na tsaya a gaban shi. Ina wasa da hannuna.
"Zaka dawo school ko? Domin ina son zan tafi wani course na shekara daya da rabi lokacin ka gama karatun ina ga zaka attechmen lokacin."


D'ago kai nayi ina kallon shi, kafin na sunkuyar da kaina.
"Innah tace ba zan koma ba" d'ago kai na yayi yana share min kwalla,
"Zata bari idan bana tare da kai zaka yi karatun ka cikin salama, idan kuma muna tare ba zan iya hakuri ba."


Gyada mishi kai nayi ina wasa da hannuna.
"Amma me yasa zaka tafi?"
"Baka son na tafi ne?" Ya fada yana bude min hannun shi, a hankali na shiga tare da lumshe idanuna, kwallan yana zuba min.
"Hammah na"
"Mamoona, kayi karatu me kyau zan baka kyauta ranar da ka gama karatu da attechmen."


Hannun naji akan lips, da sauri na bude idanun na, sai cikin nashi.
Sumbatar goshina yayi, sannan ya cire ni jikin shi bayan ya bar Ni tsaye ina me jin sassanyar lips din shi a goshina, har zuwa lokacin ban bude idanuna ba, domin ina jin shi kamar an kunna min wuta ne a jikina, tashin motar shi yasa ni bude ido ina kallon yadda ya figeta a guje..


Yasan idan ba haka ya gaya mishi ba, Almamoon ba zai yi karatu ba, yayi danasanin koya mishi sabo da shi, yasan yaron tunda ya iya dira ta kantagar gidan babu makawa next abinda zai faru ba zai yi kyau ba, amma bari ya gani ko zai iya hakuri na shekara daya da dari bai saka shi a ido ba kai ma wata daya ma tukun. Amma babu inda zashi yana Nijar kuma yana nan yana kare Kayan shi.


***
Anyi gwagwarmayar kamar za'a tashi sama kafin Inna ta amince na koma makaranta bayan ta gama ja min kunne, na dawo makaranta bayan nayi wani irin laushi kamar bani ba.. kawai karatu na saka a gabana.


Malam Ansar yana taimaka min sosai, gashi ya tattara duk kulawar shi a kaina, wata na daya da kwana ashirin sai ga Hammah Mohan a makaranta.


Sanye da unifoam, murza Idanuna nayi tare da kallon shi, yazo a cikin motar lamborghini aventador. Kasa magana nayi ina kallon shi, bude min motar yayi da sauri na nufi inda ya bude min na shiga, sannan ya dauke ni muka wuce.


Yana tuki yana murmushi..
"Hammah Mohan yaushe ka dawo" jan hancina yayi tare da mai maida hankali akan tukin da yake.


Wani gida muka nufa a cikin Barrack din gidan ya hadu, gashi da alamar an ware gidan yafi na sauran sojojin kyau, bude min yayi, tare da cewa.
"Ina zuwa, ka shiga."


A hankali na nufi cikin gidan, tare da bude kofar, babu haske a cikin falon shiga cikin gidan nayi tare da lallubar inda makunin gidan yake, ina kunna wutar wani karamin sauti na wakar.


"Happy Birthday to you" yana tashi falon, ga wani abu da ya fashe yana fidda wasu yan kyali, an saka katon baloon na 19, sai wasu cake guda biyu, daya Blue And Pink daya kuma fari ne. Juyawa nayi tare da kallon shi. Yana jingine da kofar. takowa yayi tare da kallona.
"Barka da cika shekara goma sha tara."
"Taya kasani?"
"Takardun ka na makaranta da wasu abubuwan suka gaya min haka."
"Hammah Mohan!" Na kira sunan shi.
"Ina jin ka Mamoon"
"Nagode"


A hankali ma'aikata suka shiga fitowa tare da shirya mana falon, haka muka ci abincin tare, muka yi game. Kai na kuma jin farin cikin tun bayan dawowar mu daga Dubai, kaina na kafad'ar shi .


"Ina son xan gaya maka wata magana amma ban san ya zaka dauke shi ba, sai dai idan na samu lokaci zan gaya maka" jan hancina yayi yana faɗin.
"Anan zaka zauna, ina kai kaa makaranta akwai su Hurayyah zasu kasance da kai. Bana son kana zama a can domin naji an ce min Ansar yana kulawa da kai. Ni ba zan yi faɗa akan ka ba, amma zan nisanta kowani dan isa akan ka."


Murmushi nayi domin ina jin dadin yadda yake nuna min kome nawa special ne, haka muka sha hiran mu, da dare ya nuna min d'akina, na kwanta naga ya saya min kome.


***
Tunda suka fita yake bibiyar layin Almamoon, amma babu alamar zai dawo, dan haka ya mai da hankalin shi kan abinda yake amma kuma Toh.
.....


Zama na a gidan Hammah Mohan ya kuma kara mana shakuwar mu, shi yake kai ni makaranta idan na tashi zai zo daukana, karshen wata da kan shi ya ke kawo ni Damagaram ya sauke ni a wajen gari na shiga cikin gari a wata motar..


Tattalin duniyar nan ya dauka min, tunda nake dashi bai tab'a kawowa min wata manufa ba, bai tab'a min wani abu da zai sani cewa yana niman wani abu a jikina ne, asalima babu wannan tunanin a ranshi.


***
Bayan shekara daya


Yau muka gama jarabawar mu ta wanda daga shi sai zuwa horon da zanyi na dawo na karasa wata shidan da ya rage ina da shekara ashirin.


A hankali na fito ina kallon makarantar, ina fitowa na hango Hammah daga min hannu yayi, na nufe shi da sauri.
"Mamoon!" Naji muryan Benazir,
Kallonta nayi.
"Nagode sosai, ba dan kai ba da an kore ni"
Murmushi nayi mata, sannan na mika mata hannu.
"Kinga ni kamar kanwa nake jinki dan haka ki daina biyewa yaran nan basu da hankali."


Sannan na wuce ta, tare da nufar gurin Hammah Mohan, bude min mota yayi na zauna, sannan na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login