Showing 138001 words to 141000 words out of 181864 words

Chapter 47 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6270

kafin ya sumbaci idanun shi, na dawo kan dogon lokacin shi ba sumbata, sannan na sauko bakin shi. Jan numfashi nayi sannan daura bakina akan nashi, sai da na jima ina tsotsar bakin shi tare da janye bakina daga na shi, na juya zan fita. Na tuna ranar da aka yi baikon mu, daidai zuciyar shi na sumbata, dan haka na isa gurin na sumbaci inda aka saka wani igiyar da karfe na sumbata, sannan na mike tare da barin. Dakin.
"Allah ya bashi lafiya zan tafi" na sallame su,


Tana fita a dakin yayi wani irin jan numfashinsa na'urar da suke makale da jikin shi suka bada wani irin sauti. Da gudu Khausar ta shiga dakin tare da kiran likitocin, aka rufa mishi.


So yake ya farka amma ina abu daya yake yawo a ranshi da ƙwaƙwalwar shi, sumbatar da ta mishi ranar da zasu rabu, sak irin shi yaji, a wata duniya, yana mishi.


Haka suka mishi alluran barci Bayan sun tabbatar da bugun zuciyar shi ya daidaita.
"Kun gani ba! Idan ba maita ba meye daga fita zai kama!"


"Amma Latifah baki da hankali, godiya za kiyi da Ubangiji ya bashi lafiya ba wai ki zargi wata ba, idan ma itace. Ai ta miki gata tunda ke baki hankali" yaranta babu wanda ya damu da abinda take yi.
Fitowar Khausar tana yiwa likitocin godiya dayan yace musu.
"Akwai abinda ya tsaya ranshi kafin faduwar shi, kuma ina ga shi din ne ya kuma dawo da bugun zuciyar shi."


"Mun gode! Insha Allah zamu bincika" bayan nan ta shiga yi musu bayani tare da gaya musu abinda ya faru.


"Dan iska mara mutunci! Zan muku bayanin abinda ya faru, amma ku shiga family room" kallon shi suka yi, take ya bude data yana tura musu hoton emoji na saurayi da budurwa suna kiss, yace musu.


*Wannan shine abinda tayi mishi kafin su rabu. Kuma daga shi bata kuma yarda sun hadu ba. Ina da yakinin ta kuma sumbtar shine. Allah ya barsu tare amma gaskiya Ammyn bata hakura ba gani nake kamar akwai abinda yake shiryawa! Amma Allah yana sane da kome*


Take kuwa Family room din. Ya kuma hargitsewa. Haka suka yi ta fadan albarkacin bakik su.


***
Washi gari kafin na koma Maradi na kuma zuwa asibitin Ammyn bata nan sai Salman da Haddir, a mutunce muka gaisa har nake tambayar su.
"Ya jikin na shi har yanzun babu canji." Murmushi suka yi sannan Salman yace min.
"Eh toh jiya bamu san me kika bashi ba, daga tafiyar ki kawai malamin mu ya farka, yana barci dai yanzun."


_Kar dai sun fahimci na sumbace shi ne? Wayyo Allah na kunya_


"Amma bai ce wani abu ba ko?"
Na tambaye su ina zare ido.
"Eh toh! Ya dai ce sumbataaaa!"
"Ya ilahi!" Na daura hannu a kai.
"Amma bai ce muku na sumbace shi ba?"(🙆🏽‍♀️)
"Ai ya gaya min kome, kai Maimun!"
"Amma me yasa Hammah Mohan yayi min haka? WALLAHI ba sa gayya na sumbace shi ba, ince babu abinda ya faru dashi"


"Salman don Allah ka kyaleta haka wallahi ta fadi gaskiya! Shiga abinki Karya yaƙe miki"


"Wayyo Allah na, ka sani nayi subul da baka!" Na fada ina shiga dakin da sauri. Har bakin gadon na nufa, tare da rike hannun shi.
"Ina jiranka! Ina jiranka a karo na babu adadi! Ni kamar baiwar ka ce! Zan koma Maradi na gama abinda ya kawo ni, amma ina fatan zaka tashi daga dogon barcin da kake min ya isa haka! Maimunari mallakar kace, taka ce har abada ba zaka tab'a raba kaso da kowa ba, Maimunari kason kace! Ina kaunarka da fatan zaka tashi da izinin Ubangiji."


Ina gama fadar haka na kuma sumbatar goshin sa, sannan ya juya zan fita naji ya rike hannuna. Juyawa nayi tare da kallon shi, komawa nayi na zauna a bakin gadon, tare da kallon shi.
"Karki tafi" ya faɗa min a hankali.
"Kayi hakuri! Daga wannan satin sati biyu masu zuwa ina karkashin da'iran mulkin ka ne sai yadda kayi da Ni!"
"Zaki Aure Ni?"
"Mun wuce wannan maudu'in!"
"Da gaske?"
"Da gasken gaske!" Na fada mishi ina share kwalla.
"Ki tanada min sumbatar ranar da kika min, ki ajiye min duk wani kwarin gwiwar da na gani a cikin idanun ki ranar, ki adana min dukka wani irin nau'in kulawa a daren mu, ni kuma zan gina miki daren da ba zaki manta ba!"


Murmushi nayi tare da hade goshin mu.
"Na tara maka kome na wannan daren na adana maka kome a wannan daren, zan hada maka kome kuma zan sayo jarunta a wannan daren sabida kar na hanaka sukunin aiwatar da muradinka, Hammah Mohan daga wannan daren karka tausaya min ka fanshe duk wani soyayyar ka, a cikin shi ka nuna min sakamakon kaunar da kake min Ni kuma zan boye kuka na da kome zan baka kyautar daren, zan tsara maka daren ya zama mafi girma da darajar, zan Kawata maka shi. Zanyi kome domin ka, hmmm sannan zanyi kuka da!"


Murmushi yayi tare da zungure goshina yana dariya.
"Idan kika yi kukan zan rarrashe ki, zan baki kyauta na musamman, nan dan mallaka miki zan baki dukkan shi zuciyar taki ce, zan zame miki farin dare zan raya miki daren da so da kauna, zan shirya miki shagalin da ba zaki tab'a Mantawa, ranar zan baki kyautar kaina baki daya, zaki ganin iya ganin idanunki, zan tsaya a gaban ki na juya ki ga irin mijin da kika aura. Ubangiji ya bamu yawan rai yadda zan share miki kukan ki, Ubangiji ya nuna min yadda zan sanyaki farincikin a wannan daren ya rabbil alamina ya nuna min yadda zan kayata miki daren ki! Ina addu'ar ki same ni a yadda kika sannin kika yi fatan haka, akwai shagali yarinya babu tausayi babu ruwana da Yarantarki! Zaku hadu da katon tuzuru ne!" Rufe mishi baki nayi ina zare ido....
#Mai_Dambu...
[8/14, 8:18 AM] +234 815 778 5691: https://www.wattpad.com/1113398663?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=%2BxTW4N%2Fi3%2B1dAQX5gbjmfTxgxiRMRb8Nl%2F50OD4pV94UP35Ih%2FrlfzEmYSOqSePFjk4F6wQI4BmDexcUn1v%2B6q7S5wMuA0Uc%2FC5OPGYtcFd9ON0zvTrtgtJg8WkJ5LAn


🐂🐂BOROROJI🫀🫀


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


BABI NA HAMSIN DA HUƊU.




*Ana ta zare idanu 🙄🤡🙋🏾‍♂️*


Ni a karan kaina nasan ina son Mohan, kuma shima ya san da haka,shi yasa na b'ata lokaci ina hira dashi tare da bashi labari. Kafin na kalli agogon dakin na zare hannuna cikin nashi.


"Zan tafi!" Na fada mishi,
"Bana son kiyi nisa dani, amma babu yadda na iya, Allah ya kiyayye hanya, ki kula min da kanki" murmushi nayi mishi sannan nace.
"Insha Allah! Amma ka godewa Allah da Abbu da Abba da Wallahi sai dai ka nime wacce take." Rufe min baƙi yayi da nashi.
"Don Allah a bar zancen kawai, wallahi ina son mata ta haka." Cizon hannunsa nayi tare da kura mishi ido.
"Ahhh!" Sannan ya sumbaci gurin, yana murmushi.
"Ina sonki"
Girgiza kai nayi, tare da ɗaukar jakata na fito. Na same su har wasu sun zo.
"Don Allah, ki tuna yana da kane irin wannan sakawa a lungu, baki daya. Toh Allah yasa kar muzo cin shinkafar amarya a hana mu ganin ango."
Kasa magana nayi domin Salman yana da raha kamar dan Film.
"Toh zan tafi, na gama abinda ya kawo ni Niamey."


"Ke dai kice zaki gudu an kusan amarcewa"
"Sai anjimar ku" na musu sallama na tafi, sannan suka shiga dakin sun same shi kamar mai barci.
"Munafuki idan zaka bude ido ka bude domin yarinyar ka ta nuna mana ka farka." Inji Dan Ba'are Ya fada tare da kallon shi. Gyara kwanciyar shi yayi tare da cewa.
"Dan Ubanka idan ban tashi ba sai ka d'aga ni"


Nan suka shiga fadar su ta gado, dan zance ta gado. Kafin suka shiga taimaka mishi yayi wanka da alola, yazo ya gabatar da sallah da yake kanshi Allah Sarki. Yana yi yana huta. Haka ya sauke sallah da yake kanshi, ana hira da shi Ammyn ta. Shigo ita da Maman Hanan ko inda suke bai kalla ba, sai b'ata rai yaƙe,


A hankali sauki yake samuwa, tare da sanin kulawa daga yan uwan shi, da mahaifin su amma fir yaki amincewa Hajiya Lateefah, sosai yaki sake jiki da ita, idan ya fara waya da Maimunari kuwa kowa sai ya tashi inda yake, domin kasa kasa yake maganar kamar ba zai yi ba, baka tab'a jin abinda yake faɗa.


Satin shi daya aka sallame shi saura sati biyu bikin su. Ba karamin shiri ake ba,duk ta inda kake tsammanin abin ya wuce haka, bikin saura kwana tara aka kai kayan lefe, akwati ashirin da hudu (😏😒☹️ saura kuce zuki tamalle🤣😂) tare da kyautar motar sabuwa jaguar, kukan da Innah keyi Allah kadai ya sani, domin babu wani da zata ce danginta ne sai Al'ummar Annabi, sune suka mata kara, dama tun kafin a kawo kayan Radiyah ta turo min, da ranar da za a kawo, tuni na dawo gida na shiga Niman inda za ayi mana abincin alfarma. Tare da kayan ciye ciye dake ban san yadda ake abin ba, sai da ta gaya min.


Na kawo kayan drinks aka ajiye, sai da na gama kome tare da bawa Innah kudi me yawa ta basu tukwaici. Aikuwa haka ce ta faru. Amma Innah taki amsar motar da gwala-gwalan cikin kayan.


Atamfoffin kuwa kamar shagon sayar da kaya za a bude, haka akayi ta kirga su har suka gaji suka bari, tunda na ga kayan gabana ya tsinke, ban kuma samun kwanciyar hankali ba, ga mugayen mafarkai da suka sani a gaba, a tsakanin kwanakin har saukar Alqur'ani sai da nayi, ana saura sati za a saka ni a lalle na koma gida bani da kawa bani kowa sai su Salihu Muhmuda, sune abokaina dan haka da su muka yi ta zirga-zirga.


"Malam ina jin tsoron Allah ina jin tsoron kar wani abu ya faru, ina tausayin yarinyar nan wallahi ba zan iya daukar tashin hankalin da zata ji ko zata gani ba." Inji Innah,


"Babu abinda zai faru, sai Alkhairi." Baba ya gaya mata.
Shiru tayi tana kallon kasa, kafin ta sauke ajiyar zuciya, tana wasa da abincin da yake gabanta.
"Naji tace zai tace zata Niamey, ban san me zata je yi ba."


"Eh wannan alkalin zata kaiwa katin gayyata na bikin, kuma Insha Allah zata dawo ana saura kwana kwana uku."


"Toh Allah ya nufa, ina tsoron abinda ya faru"
"Don Allah idan ba zaki fadi Alkhairi ba kiyi shiru."


***
Washi gari da asussuba nayi sammako sai tasha. Ina zuwa motar farko zata tashi Allah ya soni na samu guri.


Ina biyar kudin tana d'agawa bakina dauke da addu'a, haka muka dauki hanya.
..
Diffa.
Juya mishi baya Uban yayi, tare da kin sauraron shi, yana jin yana magiya.
"Don Allah ka ajiye kudirinka na cutar da ita, karka manta wallahi ba dan kudirinka nake aikin nan ba, ina sonta don Allah karka cutar da ita don Allah" a fusace ya juya da sandar Azurfan shi ta tsafin ya buga mishi a goshi.
"Kai ka isa ka hanani farin cikina! Ka dauko min ita ka kasa, kayi min abinda ya dace ka gaza anya ni na haife ka kuwa? Wallahi da kai jini na ne ba zaka tab'a ɗaukar mace da daraja, macen da rigar sawarka tafita daraja itace kake rokon kar na mata kome!"


"Ita nake so ka dauko min ita, so nake ka daukota ka kawo ta nan! Idan ma soyayyar ta kake ji a ranka toh ka daina, domin ita din da ni, gumin mu ake son ya hadu guri guda, daga nan kuma ina zaune mulki zai zo min har inda nake" cike da mamaki yake kallon Mahaifin shi wato abar kaunar shi ce zai kwanta da ita.
"Tab wallahi babu wanda ya isa yayi min wannan gangancin na dauka, yarinyar da na gama cin bakar azaba da duka sabida ita, toh ai gwara ka tsine min albarka da na kawo maka ita, kai dai ka kare a gurgunta amma ita wancan kayar tawa ce.


Kuma na rantse idan kayi gangancin aikata wani abu, hmm toh wallahi sai na zame maka alakakai, kana ji kana gani zan kashe ka, kaiii Dattijo ban damu ba dan baka dauke ni a d'anka ba. Amma ita ka tab'a inuwarta wallahi sai na binne ka da ranka. Ita din guguwar sauyin ƙaddara ta ce, dama daya tak nake jira kuma Insha Allah na kusan samu idan ka gadama ciwon daji ya kashe ka ko ta zuciya"


Daga haka ya juya zai fita ya tsaya tare da cewa.
"Daga yau zan zame mata inuwarta duk inda ta shiga ina biye da ita, kai kuma zan zame maka tankar tafiyar Ajali domin duk lokacin da ka ganni tabbas mutuwarka ce tazo maka. Ba zan d'aga maka kafa kana Ubana ba, zan maka kisar munmuke da sai kayi danasanin haifata da kayi. Kaiii Wa'adi Ansar wallahi idan har jininka na mugunta da keta be bin kowa lungu da sako na jikina wallahi na rantse da wanda ya mallaki alrshi sai na maka kisar da ko gawarka sai ta bawa kowa tsoro. Karka tab'a Maimunari domin ita ruhina ce. Idan kuma kana ganin haka da sauki.... Ma gwaji ya gwada"


Yasa kai ya fita tare da dukar kofar fita daga gidan, rintsa idanun shi yayi da mugun karfi, yana jin yadda Hisham Waadi ANSAR yake mishi barna duk wani abu me daraja sai da ya lalata a gidan, sai da ya fasa kome har da motocin gidan, sannan ya kwashe kayan shi ya nufi gidan shi da yake wajen gari ya kwanta.


Bayan an mintinan wayar shi tayi kara. Kamar ba zai duba ba ya dauka.
*_Saura kwana biyar bikin Maimunari da Mohan!_*


A zabure ya mike tare da danna wayar jikin shi yana rawa.. ya kira ta.
"Maimunari! Meye nayi miki da kika tsane ni? Haba ashe soyayya zata zama k'iyayya? Ina sonki sannan ina miki fatan Alkhairi, naji zaki yi aure. Allah ya cika miki burinki."


"Malam Ansar ba wai naki ka bane, sai dai tun farko na gaya maka kai dan uwana ne, Hammah Mohan kuma Masoyina ne, shi na fara so. Kai kuma na shaku da kaine, ka fahimta mana so daban shakuwa daban. Wallahi ban tab'a jin soyayyar ka ba, amma kayi hakuri ba cin fuska bane! Wallahi kasan hali!a bana boye abinda yake raina, kayi hakuri kaji"


"Na hakura kanwata, karki manta ki dauke ni abokin shawaranki Insha Allah zan zo daurin auren da duk wani shagali da Ni za ayi."


"Kai Hammah na, nagode sosai da ka fahimce ni, kuma naji dadin haka don Allah ka gafarce ni, yanzun haka ina hanyar Niamey ne zan kai katin auren amma ina ganin gobe Insha Allah zan dawo zan bi jirgin sama."


"Ai girmanki ce, Surukar shugaban kasa, idan baki biyo jirgi ba ai nayi musu ba'a, karki manta Insha Allah duk abinda kike bukata ki gaya min Insha Allah ni kuma zan cika miki burinki, karki manta da haka ina kaunarki har kwanan gobe, amma yanzun ya koma ba yan uwana"


"Gaskiya Nagode da samun babban masoyi irinka, Ubangiji ya baka wacce ta fini don Allah kashe kiran surukinka ya kirani"
"Toh!" Ya fada da sauri bayan ya kashe kiran, very sad ya kalli wayar, sannan ya sake murmushin farin ciki, kafin ya mike ya nufi ban daki, yayi wanka sosai cikin nishadi da jin dadin.
**
Yana kashe wayar, na dauki wayar Hammah.
"Ranka ya dade! Mazaje."
"Hmm! Sarauniyar kyan zuciyar Hammah Mohan! Dawa kike waya?"
"Kai Hammah! Da abokin karatuna ne fa!"
"Ok na zata wani saurayi ne ya kira min mata nasa sojojin kasar Nijar su dira a kofar gidan su, a dauko min shi a kai!"
""Kai Hammah Mohan! Lafiya? Akan me? "
Cikin murmushin kasaita yace min.
"Sabida ya kula matar Babban sojan" dariya na saka ina kara gyara zamana, ina faɗin.
"Toh gani a hanyar garin ku, Niamey"
"Don Allah? Toh a ina zaki sauka?"
"Toh ai kaji irinta, wallahi sai gidan Abie domin na gaya mishi tun a tasha. Kuma yace min idan zan koma a jirgi zan koma!"
"Toh ni dai Allah ya gani na fara kishin wancan tsohon ina dalili ya zake dayawa da!"


"Allah Sarki,wallahi kamar mahaifina nake jin shi, idan kace na daina kula shi sai na daina." Na faɗa.
"A'a ban isa ba"
"Ka isa mana."
"Hmm! Har yanzun ban warke ba"
"Ayya dama kaji ciwo ne?" Na fada mishi ina dariya.
"Gaskiya kin jiwa zuciyata ciwo? Kuma zan rama duk ranar da zan rike ki a hannuna sai kin gane" katse wayar nayi ina dariya, kafin na share zancen shi.


Har muka isa Niamey ina jin nutsuwa a raina, Driven baba yazo daukana. Ina isa gidan na sami motar Hammah MOHAN.


"Sannun da zuwa Uwata, Sannun Uwata an kusan girma."
"Ooh Abien Moonah sonkai tsirara, ina laifin ka min kara ka maidani kamar Bature tunda nazo ruwa kawai ka bani, amma tunda Moonah tayi sallama ake jera wancan table din Abie dan ban gaya maka zan zo bane?"


"Abie Hammah Mohan kishina yake, dan yaga kafi sona" na fada ina murguda baki, kwafa yayi irin zamu hadu dake.
"Abie kaga tana murguda min baƙi!"
"A'a Abie shi yake harara na"
"Toh Mohan ya daina Harara. Maimunari ta daina murguda baki."
"Abie"
"Muje muci abinci sai kiyi wanka ki huta,"


Haka kuwa ta kasance bayan na gama cin abinci nayi wanka da alola na.gabatar da sallah da ake bina da kuma na magarib da isha.


Sannan ya tara mu, yayi mana nasiha akan rayuwar mu da kuma wanda zamu fuskanta, sannan ya kara mana da kyautar da ya bani, tare da wani katon gida a Zurich ƙatuwar gida ce, wanda har kwanan gobe ana tayawa yaki sayarwa.
"Ga waɗannan sune wanda na baki su, bansan me zan baki ba, amma ina jinki har cikin jini na, Allah ya albarkaci rayuwar ku."


Mun yi hira sai da Abie ya kore Hammah Mohan, amma sai ya tafi zai kuma dawowa, yace yayi mantuwa haka dai karshe Abie ya turo ni, tunda na shiga motar shi na bige da barci. Fitowa yayi daga daya gefen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login