Showing 171001 words to 174000 words out of 181864 words

Chapter 58 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6276

***
Bayan wata bakwai na kammala karatuna har da su Beenah da tazo da cikinta dan wata shida. Da shi kan shi dan Ba'are, ban ga Mohan ba, kiran layin shi nayi yaki shiga takaici kamar nayi ta ihu.


Zuwan Hisham ya sani tafiya gurin shi, yana tayani murna tare da cewa.
"Ban ga Mohan ba, yau babban rana ce amma kamar bai damu dake ba? Da yar shi ce da zaki ganshi jikin shi yana rawa" a hankali maganar shi ya fara tab'a zuciyata, ya shiga gaya min wasu abubuwan da nuna min yadda Khalil ya damu da matar shi.


"Ki duba ki gani mana, duk nan babu wanda bai zo ba sai shi, ke kin kare kanki,kin kama kanki amma shi.yana can yana cin amanar ki. Hmmm."


Wani irin duka aka kai mishi sai da ya fadi kasa, yana rungume da Widad. Shiga tsakanin su yayi ina kallon Mohan.
"Meye a cikin maganar shi? Meye laifin shi? Da ka damu dani ba zaka ki zuwa akan lokaci ba, ka samu matan da suka fini."
Mikawa Khalil Yarinyar yayi tare da kai mishi duka.
"Na gaya maka ka rabu min da matana amma kaki ji, nace ka fita hanyar Maimunari ka ki ji, bari na koya maka yadda ake gudanar da sha'anin rayuwa."


"Munnah kina ganin zai kashe ni, karki bari ya ya illatani"


Saka karfina baki daya nayi tare da ture shi.
"Dalla kyale shi, akan ka aka fara kishi? Ka kyale shi mana, haka kawai zaka saka shi a gaba sai kace bawan ka. Karka kuma dukan shi. Idan ba haka ba zan baka mamaki"


Haka ya mike tare da barin gurin, yana dingishi.
"Ina sonki shi yasa na kyale shi, amma wallahi sai na illata shi."


"Bana son ganinka, ka koma inda ka fito matukar haka ba zai samar min da kwanciyar hankali ba."


Haka na gaya mishi tare da barin gurin ina kuka. Shi da Khalil suka kawo mu gida dan su Abie sun rigamu dawowa. Tunda na shige dakina, khalil ya shigo dakin yana kallona, sannan ya zauna tare da bani labarin duk abinda ya faru.


***
"Ban damu ba, kome zai faru ya faru, amma ina son a kashe min shi, a kashe min shi bana son ganin shi da ita,"
"Amma ita yarinyar fa?"
"Idan ta kama da ita a kashe ta kowa ya rasa shima ya mutu."


"Lallai baka cika mugu ba, ai muguntar da zaka mishi kenan ka kashe ta ya rasa ka rasa,"


Kallon shi yayi tare da cewa.
"Ka kawo shawara, kuma Insha Allah haka zai. A'a a kashe shi kawai ina sonta a raye, ina son Ubanta yaga yadda zan aure yar shi kuma na kwanta da ita a cikin gidan shi. Dan haka daga yanzun har zuwa gobe ku kashe min dan Iska."


"Toh amma kasan Unguwar akwai tsaro, idan muka tashi kashe shi ya zamu yi?"


"Ku rufe bakin bindigar da salansa"
"Toh an gama"


Haka suka ci-gaba da bayanin yadda zasu kashe Mohan, a waje kuwa wata yar makaranta ce, taji su dan haka ta fita tare da niman Number Maimoon.


Bata samu ba kamar zata yi kuka dan haka ta kai report ga yan sanda, su kuma suka tuntube Maimoon.
#Mai_Dambu.
[8/17, 2:03 PM] Yar Kasuwa👳🏻‍♀️: HAKKIN MALLAKATA
#sun-Aug-2021


BOROROJI


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


BABI NA SITTTIN DA TARA.


"Kina Fahimta! Ansar ba kaunar ki yake ba, mutumin yake kaunarki ba zai tab'a lalata miki rayuwa da farincikin ba. Bawai ina gaya miki haka a matsayin Aminin Mohan bane, a'a ina gaya miki haka ne a matsayina na dan uwanki, kuma abokin shawaran mijinki..


Wallahi bai aiko ni domin na gaya miki, amma ita wannan ta sani, komi kashin damuwa idan ya gani a tare dake kamar zai zauce haka yake ji, ki duba takardan sakin da ya baki,wallahi bai tab'a kawowa zai sake ki ba."


Da sauri na shiga watsi da kayan na fito da takardan a kasar a kwatina.
Hannuna yana rawa, jikina sai bari yake na warware takardan.
*Ina son mata ta! Ba zan tab'a sake ta ba har abada*


Wani irin kuka na sake tare da kallon wayata da take kara, da sauri na dauka.
"Kece Mrs Mohan?"
"Eh nice!" Na fada ina toshe bakina.
"Toh ki kula domin shi bamu same shi ba, amma ana bibiyar rayuwar shi da ke, an saka a kashe shi. Dan haka duk inda yake kice mishi ya kula da rayuwar shi"


Sake wayar nayi tare da jan mayafina na rufe kaina, sannan na fita ban iya kula su ba, duk tambayar da suke min. Bani da hankalin da zan basu labarin abinda yake faruwa.


Dan haka ina fita na hango shi yana tsayawa a bakin kofar shiga gidan mu, da sauri na isa inda zai bude kofar, ba bude tare da cewa.
"Basu maka kome ba? Fito kaji." Bai fahimci me nake nufi ba yana fitowa kuwa suka fara harbi,kwantar dani yayi tare da janyo wata jaka, ya ciro bindigar shi, ya shiga bin su yana harbin su. Sun samu sun gudu dan haka ya fito tare da d'ago ni, hango wani mutum nayi. Yana tasowa ta bayan Mohan, a hankali na juya tare da Mai dashi daidai kofar gidan, sai ji nayi kaifin abu ya huda bayana har ya fito ta cikina.
"Hammah Mohan! Na gaya maka rayuwata fansa ce koda ni ba zan more ta ba? Na tab'a gaya maka ina raye ne domin kai? Hammah na, tun kana cikin laluran hauka nake tare da kai, wallahi billahi azim ina sonka da dukka rayuwata..." Na tafi zan fad'i yayi maza ya tare ni, shi kanshi mutumin da fuskar shi take rufe wani irin ihu ya kwala tare da cire abun fuskar shi.
"Hisham!" Na kira sunan shi. Ina jikin Hamma Mohan. Sai gyara mata kwanciya yayi a kirjin shi kamar baya gurin.


"Na gaya maka cewa, ni Mohan nake so!" Na fada a sanyayye.
"Ni shi nake so! Ina son shi baki daya da rayuwata, ko babu kome an kawo karshen rikicin ko? Ni matar Mohan ce, Ina son mijina sosai." Na fada ina share kwalla da ta zubo min. Daidai zuwan motar yan sanda.
"Hammah na, karka mishi kome kabar shi da ciwon da ya jiwa ranshi ya ishe shi har karshen rayuwar shi."


"Mohan a kaita asibiti mana"
"Ko an kaini bai zama dole nayi nisan kwana ba"
"Karki damu zaki rayu Wallhi" ya fada da mugun karfi ya nufin inda aka saka motar asibiti yana rungume dani.


Bayan tafiyar su, da kanshi yayiwa Yan sanda bayanin shi ya turo ayi kisan, dan haka suka makala mishi ankwa, suka nufi dashi Ofishin su.


Hankalin Mommy yayi mugun tashi, dan haka suka nufi Asibitin tunda suka iso suka sami Mohan, ya kasa tsaye ya kasa zaune, sintiri yaƙe, ya shiga Nan ya fita nan hankalin shi a mugun tashe.


Allah Sarki baby Widad tana kwance a jikin Abie hannun ta daya a bakinta tana ajiyar zuciya.
Bayan awa biyar likitocin suka fito. Tare da nufar inda Mohan yake.
"Mun yi kokarin mata aiki, amma gaskiya bamu san yadda zamu gaya maka ba, Matarka koda ta rayu bai zama dole ta mori kafaffunta ba, sabida wukar ta tsinka mata jijjiyar lakanta (spinal Code) abin da muka Fahimta a jikin wukar guba a jikin shi, shi kuma ya tab'a mata ƙwaƙwalwar ta, wanda ya tsayar da aikin zuciyarta. Gaskiya muna baku hakuri domin bai zama dole ta rayu ba."


"A'a likita! Wallahi zata rayu. Ina jin haka uwar Ƴaƴana zata rayu, wallahi bana jin mutuwa zata zo mata a wannan lokacin, kaga gaya min ina ne zan kaita a mata jinya, gaya min inda zan kaita. Don Allah kaga wancan Yarinyar watanta goma sha daya. Don Allah na hada ku da Allah ku gaya min ina zan kaita. Bani da amfani matukar ita bata numfashi, rayuwata mallakar ta ce . Don Allah ku gaya min"


Ka fada a rikice, abin gwanin ban tausayi, su kansu likitocin share kwalla suke, a hankali suka juya tare da barin gurin. Mommy ta tawo tare da rike shi, ta zaunar dashi. Sannan ta zauna itama tana faɗin.


"A lokacin da na haifi Maimunari, ban tab'a jin ko ganin wani zai kaunace ta ba, musamman ta hanyar da na haife ta, naso da a gidan aure na haife ta, sai na kasa amsar ƙaddara a kanta. Nayi ta tafiyar ƙaddara. Mohan ban zata ba yau Maimunari zata fada wannan yanayin ba, domin nafi zargin SOYAYYA ba zai tab'a wasa da rayuwarta sai gashi an samu kishi a tsakanin zubda jini, Imma Maimunari ta tashi, Imma ta mutu. Jininta ya zama sadaukar ce ga Zuri'ar mu baki daya, dan haka ka yi hakuri Maimunari koda yaushe tana ran mu, idan ta mutu muna mata fatan dace da rahamar Ubangiji."


Mikewa yayi tare da ɗaukar yar shi suka shiga dakin da aka sauya mata, ya zauna a saman kujeran da yake gabanta.
"Kin gan mu, ni da Maryam mun zama kamar marayu, bamu da amfanin kome, gamu dai a raye amma zuciyar mu ta tafi da naki. Don Allah ki tashi muna dakonki, don Allah karki tafi ki bar mu, wallahi zamu tagayyara, idan kika amince kika bamu dama ta biyu zamu."


Kuka ya fashe da shi, yana kara rungumar yar shi, tunanin kowa ya tsaya, Abie ma ya saka koda wani abu, kawai yana kallon haka a matsayin da bai tab'a zata ba, yar shi kwaya ɗaya tal itace aka mata wani irin kisar ban mamaki. Meye zai yiwa Hisham ya huta, baki daya ya kassara mishi Rayuwar shi. Haka suka zauna jigun jigun.


Mikewa yayi tare da fitowa da yarinyar. Ya mikawa Innah dan itace take cikin nutsuwar ta, duk su Mommy a birkice suke, dan haka ya nufi office din yan sanda, ya mika musu katin shi na FBI, suka sara mishi sannan suka bude kofar da Hisham yake, ya ja kujeran ya zauna, yana kallon shi. Yadda yan sanda suka ci Ubanshi.


"Ban san me yasa kayi shura akan lallai sai ka raba tsakanin mu. Shin akwai bashin da kake bin Maimunari ne?" Ya tambaye shi tare da kallon shi.
Dariya Hisham yayi sannan yace mishi.
"Na riga ka, fara sonta, yin tana siffar maza na fara sonta, zuciyata tana gaya min mace ce a gurin mai dauke da Darajojinta, sai dai lokacin da nake ƙoƙarin biyan bukatan kaina na fahimci kai har tayi nisa akan ka, taya zuciyata zata dauka? Ban san asara ba, ban san faduwa ba, abinda na sani nasara. Kai kuma ka tsaya min a gaba. Dan haka yanzun da ta mutu na rasa ka rasa."


Wani banzan naushi ya kai mishi sai da ya tintsira, ya kuma kara mishi duka. Da sauri suka bude kofar.
"Kai ku fita Rigimar mu bata ku bace" inji Hisham.
"Yallabai ko zaka fita?"
"Idan ya fito ya zama lusari. Idan ka fita sunan ka ragon maza, kuma har abada ba zaka tab'a zama cikakken namiji ba, ku fita ku barni dashi ya dake ni. Bari na gaya maka, Ni na biya Malik ya dauko min ita, Ni na saka mishi kawazucin yayi tarayya da ita, ta yadda zan kashe shi babu wanda zai damu.


Ni na dauki hoton matar ka na saka shi domin ya ruguza maka rayuwarka ka manta wasar da muka saka ne? Nasan zaka yi nasara yasa ni kaiwa mahaifiyar ka, labarin abinda Kanwar Uban Maimunari ta faɗa na Shegiya ce, tawo k dake ni, itama Mahaifiyarka na gaya mata ta bani goyan bayan zata rabaku ashe tsuhuwar banza ce, shima Babban shegen shima Ubana ya Bankad'o sirrin shi."


Lumshe idanu Mohan yayi, sannan ya bude akan shi.
"Ko ku fita"
Suna fita ya garkame kofar ya shiga gyara tsayuwar shi, kafin suka kaure da wani azzababben fada, suka yi ta jiwa junan su ciwo kamar zasu kashe kansu.


Babu wanda yayi yunkurin raba su, sai da Mohan yayi mishi dukar mutuwa yaga baya numfashi, sannan ya daki gaban shi, sai da ya fasa ihu. Kafin ta fita daga dakin, ya saka rigar shi. Sannan ya fita daga Office din yan sanda. ya nufi asibitin yana dingishi.


Yana isa ya samu su Mommy, ganin bakin shi a fashe yasa Mohan tambayar shi.
"Lafiya"
"Wancan dan iskan na koyawa hankali"
"Waye?"
"Hisham!"ya bata amsa,
"Da ka kyale shi"
Kwalla ne ya zubo mishi, sannan ya mike hankali yana kallon Mommy.
"Ba zan tab'a yafewa kaina ba,matukar na bar Hisham a raye, sabida shi matar da nake so take kwance, taya zuciyata zata nutsu? Bani da abinda na sani sai soyayyar ta, bani da abinda zan yi sai Soyayyar ta, Mommy baki ga halin da Maryam take ciki bane, daga ni har ita mun zama kamar marayu, gashi dai mata tace amma ji nake kamar rayuwata ce take niman kwacewa daga gare ni.


Wai kice na yafe mishi, bayan ga lakarta, guba ce ta tab'a kanta da zuciyarta, idan ba dan ke kika haife ta ba, sai nace ko baki kaunarta ne, amma nasan kin fi ni sonta, abin tausayi yarinyar da babu ruwanta tana shirin zama marainiya, wata irin zunubi nayi ne haka? Ban san meye na aikata ba, amma yarinyar nan tana shirin zama marainiya, sannan kice na yafe mishi. Wallahi ba zan yafe mishi ba."
Ya fada yana watsa da hannun shi, dan haushin Mommy yake ji, akan me zata ce ya yafewa Hisham, dan banza mutum da ya sani sai ya karya mishi hakarkari. Hankalin shi sai kwanta, banza kawai mara mutunci, a Yanzun haushin kowa ma yake ji, ya tsani a mishi magana dan haka ya dauke yar shi suka shige dakin, kwantar da ita yayi kusa da uwar da aka saka mata na'ura a hancinta,.ya shiga ban daki yayi wanka tare da fitowa, ya ga yarinyar tana barci, fita yayi tare da niman Khalil ya kawo mishi kayan shi.


Abie kuwa da Khalil tuntubar likitocin suke ko za a taimaka a fita da ita wani asibitin, dan haka suka shiga zirga zirga, shi kuma yana jikin matar shi. Haka ya cewa Innah.
"Innah ku dauki Maryam ku tafi da ita, ni zan zauna anan. Dan ba zai yiwu ina yawo da ita a cikin Asibitin ba, ina ga kawai a yaye ta, tunda tana tsayuwa kuma tana cin abinci, ba sai an bata na Uwarta ba, ita kuma zamu cigaba da addu'a Allah ya bata lafiya."


"Son wata goma sha daya yayi sauri me zai hana a barta!" Kamar zai yi kuka yace mata.
"Bani da tabbacin Uwar zata tashi, kar a saka mata kawazucin Uwarta tazo mu rasata, Kinga anyi biyu babu, don Allah ku tafi da ita a bata wani abu....
*Toh bari mu gani zuwa sab'ani din nan idan ya wuce sai muyi Barka idan bai wuce ba a wanke hannu a saka facemask Nagode sosai an amana👏🏼*
#Mai_Dambu
[8/18, 9:55 AM] Yar Kasuwa👳🏻‍♀️: HAKKIN MALLAKATA
#wed-Aug-2021


BOROROJI


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


BABI NA SABA'IN


*PAGE 70 NA KAMMALA ZANEN QADDARA TA, AMMA WANNAN KAMAR KUN TOFE NI😭🤣*
-----------------------------------------------
*Ina kuke matan alfarma muna da kayan ado da kawa... Musamman turaren kaya wanda zai yi awa ashirin da hudu a jikin kayan ki, muna da scentball wanda ake wurga shi a wardrob sannan muna da Oil mai dan karen kyau da dad'i! Ina uwar gidan ina Amarya, maza garzayo kar a baki labari kayan mu free order! Sannan ina uwaren gida da amare nesa tazo kusa, muna da kayan Mata ingantattun masu kyau, Muna da gumba mai kyau yar asali, muna da hadin kazar amare mai kyau yar asali sannan muna da Sha daka mai kyau na amare da uwargida! Akwai parkege na amare mace da ta yarda da kanta Hajiya taɓa Ni ta wannan Number:08130269841 sayan na gari mai da kudi gida*
Kaza
Tara bala'i-
Gumba bucket ƙarami-
Gari-
Hatsabibiyar zuma
Hatsabibin gari
Zobe-
Tsumi-,
Maina ya rikice
Zazzogau
Haɗin gigita shi
Maƙale mata


Sayan na gari mai da kudi gida..... Sai kun zo muna maraba da ku


________________________________


Kallon shi Innah tayi sannan ta maida idanun ta kan Yarinyar, da take kwance jikin Mommy.
"Zainabu mu tafi da ita gida." Bata rufe baki ba, Khalil ya isa tare da Abie.


"Zamu wuce da ita Germany, akwai likitan matsalar ta, sai dai zata iya daukar wata shida kafin yazo kanta, amma da mu zauna anan jiran gawon shanu gwara mu tafi can ko Allah zai saka ta tashi." Inji Abie, yana kallon Mohan,
"Duk yadda kace haka zamu ayi, amma ai shima Mohan din ba zai ki wannan shawaran ba, tunda abinda yake bukata kenan"


Kamar kurma haka ya zauna musu, ba tare da yace musu cikanku ba. Dafa shi Khalil yayi ya juya yana kallon Khalil.
"Idan hankalin ya b'ata hankali yake nima shi, don Allah kayi hakuri ka saka salama a zucuyarka karka damu Allah zai bata lafiya."


Janye hannun shi yayi a kafad'ar shi.
"Ni nawa hankalin ya tafi ba tare da nasan ina ya tafi ba, hankalina ya b'ata a jikina tun daga d'azun da naga Maimunari wuka ya fito ta bayanta na fahimci hauka tuburan nake, dan haka ka kyale ni karka dame ni,"


Ya fada tare da saka hannun a bakin shi yana mishi alamar kar ya tashe ta, haka ya zauna yana kallonta, bani baki daya kome nashi ya tsaya cak, yana tare da ita ne, amma yayi imani da Allah ya mutu ya kai sau dari, kuma da za a tsaga jikin shi babu ruwa a cikin shi zunzurutun tashin hankali da fargaba, a kowacce dakika bugun zuciyar shi yake kara tsananta, ji yaƙe kamar kafin ya bude idanun shi na'urar da yake makale da ita zai daina aiki alamar ya cika, wani irin yanayi mara daɗi yana kara kusanto shi, ya tsani karar abu matukar ba numfashin ta ne, zai fita ba, asalima gani yake kamar kawai yaudarar shi ake shirin yi. Domin bai ga alamar tana numfashi ba,


"Zamu tafi da ita Germany da fatan zaka bamu hadinkai.".inji Khalil,cikin wata irin masifa ya juya kan Khalil.
"Matar ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login