Showing 105001 words to 108000 words out of 181864 words

Chapter 36 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6279

Sai da nayi wanka da alola sannan na fito ina kallon yadda aka gyara min dakin, a hankali na taka na bude wardrob din da na gani a d'akin. Ikon Allah, gefen dogayen riguna daban, gefen riga da zani dabam sai riga da skirt, sai kananun kaya, masu kyau da inganci. Daukar doguwar riga na saka, tare da wata hijab a naga gefen su daban, abin sallah na dauka na gabatar da sallah azhar.


Sannan na shiga addu'o'in, ina idarwa na sha magani, kafin na kwanta. Ina nazarin abinda ya hana shi dawowa.
***
A can kuwa fadar shugaban kasa, jarida aka buga shafin Farko hoton Hammah Mohan da Maimunari, abin mamaki magana dai masu matukar zafi aka rubuta.


*SHIN ME ZAMU CE DANGANE DA MAJOR GENERAL MOHAN MAMMAN NASIR? ITA WANNAN WACECE MISHI DA YA KE RIKE DA ITA? SHIN ME YA HANA SHI AURE YANA RAYUWAR DA TAYI MISHI*


A cikin shafi na biyar na jaridar aka sake saka hoton shi da na Maimunari, wanda suka yi a Dubai tana sanye da kananun kaya musamman ranar da suka shiga club ɗin nan.
'''AN CE MANA BAI DA LAFIYA ASHE MUTUM KAWAI WATSEWAR SHI YAKE ABIN SHI TOH ITA YARINYAR YAR WAYE? KUMA IYAYEN TA SUMA SUNA INA?'''


Kallon su Primer minister yayi yana faɗin..
"Allah ya kyauta, amma ban ga abin yayatawa ba, sannan kuma ministen labarai zamu tuntubar da wannan abun tunda."


Shiru yayi sannan ya kuma kallon su yace musu.
"Ku bar zance kawai, Allah ya rufa asiri." Daga haka ya sallame su. Kiran Mohan yayi, can kuwa sai gashi. Zama yayi bayan ya gaishe shi. Tura mishi hoton yayi.
Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Abbu hoton yayi kyau sosai, wannan ne banji dadin ganin shi ba, kuma ban san me zance ba, amma itace Almamoon da tayi jinyata." Ya fada yana sunkuyar da kan shi.
"Kana Sonta ne?" Da sauri ya d'ago kan shi.
"Eh Abbuna"
"Haddir da Salman sun min magana, sai Khausar itama tayi min magana akan na tausassan Mahaifiyar ku, akan ka. Insha Allah zan yi yadda ya dace." Shiru yayi tare da jan fasali kafin ya cigaba da cewa.
"Ita Hanan fa?"
"Insha Allah zan ji da kome"


"Allah yayi muku albarka."
"Amin Ya Allah, Abbu!" Sannan ya fita.


*
Yana fita ofishin Baban shi, wayar Hajiya lateefa na shigo mishi, cikin diriricewa ya dauka.
"Ina son ganinka."
"Toh Ammyn"
A rikice ya nufi gidan, kai jama'a. Ruwan bala'i ya sha na masifa, haka ya zuba tagumi kafin ya ninke ta baibai.
"Wallahi Ammyn ni da dud duniya bani da masoyi ya irin Hanan. Daga yau dan na fita da ita har sai anyi baikon mu, ya ga Yar dangi xan kula bare. Ina yar dangina nake so"


Anan ya cinye ta da baki, yayi ta rarrashinta, sannan ya mike zai tafi tace mishi.
"Abincin ka fa"
"Ammyn a kawo min part dina."


**
Tun ina saka ran ganin shi, har na cire rai, washi gari sai ga drive yazo ya kai ni babban kotun kasar, anan nayi kome. Sannan na gama zan tafi naga sunan jikin Katsina MAIMUNARI I UMAR WODAADABE, shiru nayi kafin na sake murmushi, sannan na fara gabatar da abinda ya kawo ni.


"Don Allah nace ba?" D'ago kai tayi sannan tace min.
"Ina jinki"
"Suna na Maimunari I Umar wodaadabe."


Murmushi tayi sannan tace min .
"Rukayya Husain Adam, auta."
Mika mata hannu nayi sannan ta mika min nata.
"Ofishin justice aka turani, kuma Ni bakuwa ce"
Mikewa tayi zata rakani. "Ok tun wancan satin na fara aiki anan nuna turo ni aka yi daga Agadaz, muje na nuna miki"


"Yan mata ji mana? Ina niman barista Maimunari" ya fada daga bayana.
"Karki kula shi muje niman magana yake."
"Kinga kawar mu, ki kulani indai da gaske ne" juyawa nayi a fusace, katon teddy bear na gani, dai dai misali a hannun shi.
"Sorry" ya fada min, dauke kai nayi ina kallon shi.
"Fiancée dinki ne?"
"Kyale shi karki kula shi"
"Kiyi hakuri kin sha magani? Kin karya?"
Amsar dolin nayi tare da maka mishi ina kuka.
"Kasan yadda zuciyata ta kwana da son sanin wani hali kake? Ko kirana baka yi ba, ban sani ba karka kuma zuwa nan dube shi katon mutum kawai, muje Kinji Kawata."
"Lallai kaci duka gobe maka kara."
"Toh duk wannan fushin name? Da bance zan yi sabuwar budurwa ba" cak na tsaya, tare da juyawa na kalle shi, kamar na rufe shi da dukka, haka na share shi. Bin bayan mu yayi. Har ofishin alkali, muna zuwa muka samu masijan shi, ya shiga ya gaya mishi. Kafin mu shiga Hammah Mohan ya tare kofar, tare da shiga cikin Office din ya rufe, yana ta rubutu. Jan kujeran yayi tare da zama, sannan ya cigaba da kallon shi.
"Mai girma alkali!" D'ago manyan idanun shi yayi tare da kallon shi. Yana son tuna inda yasan fuskar shi amma ya manta,
"Suna na Mohan Mamman Nasir Aghali, yarinya ta zata zo sanin makamar aiki, toh naji ance baka tab'a aure bane, shine nazo da kaina muyi magana daya, yarinyar a karkashin da'irata take, kai kuma a karkashin da'iran mahaifina kake, ban san yadda zaka dauki batuna ba, amma tabbas zan iya kome akan Beauty. Dan haka zata shigo ayi kome cikin mutunttaka, ba sai na gaya maka ina haukar sonta ba, amma toh gargadi ne ba Shawara ba." Ya fada bayan ya mike tare da bude kofar, shigowa tayi bayan ta, buga mishi dolin tana faɗin.
"Kayi min laifi amma haka bai saka ka fahimtar yadda nake ji ba, me yasa jiya baka dawo ba, kasa barci nayi fa. Har sai da nasha magani!" Bude min hannun shi nayi.
"Hammah na, ina sonka karka manta dani, idan baso kake na mutu ba......
#Mai_Dambu
[8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1109846382?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=5APA6mJ8v7GgHSCkDwtNb1XXK%2BVFjYD5JoQuwsUbL%2BoIhl%2B1ELBymj3sVefZSm9hx7T5VudtIwohWKCgDupKfRkENVHC3lkDkAPKgEM%2Fi1YU6rlaxusjnrm2Wbfeg0Md


🐂🐂BOROROJI🫀🫀


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
_Merci beaucoup, surtout mes compatriotes nigérs qui parlent français. Merci. Merci. Incha Allah. Nagode sosai ❤️😍💓😘👏_


BABI NA TALATIN DA TARA.


"Kinga ga inda zaki yi aiki, domin munyi magana da shi, dan haka ki nutsu kiyi abinda ya kawo ki,ban da shiga damuwar Kowa. Kinji" gyada mishi kai nayi, sannan ya juyar dani, ina kallon alkali, gaba na ne ya fadi.


Lokacin da nashi ya fadi ya kura min ido. Cike da mamaki.
"Moonah! Gashi nan kiyi aiki da gaskiya karki yarda a hada kai dake a cuci wani ko shi, sannan ki nutsu babu ruwanki da kowa, ki gabatar da kanki."


Kasa magana nayi ina kallon shi, haka shima yake kallona, gyada kai kawai nake ina kallon shi, kwarjinin shi da girman shi ya cika min idanuna, sunkuyar da kai nayi kasa, ina kallon kasa.
"Itace yarinyar ka?"
Cikin karamin murmushi ya gyada mishi kai,
"Sunan ta? Ya tambaya zuciyar shi na wani irin bugu.
"Maimoon I Umar" ya faɗa.
"Toh zaku iya zuwa babban Ofishin majastiri, kuyi cike ciken da ya dace sauran kudawo nan ita daya."


"Toh" ya ja hannuna muka tafi, har na manta da Rukayyah Hussain Adam, haka muka gama kome, sannan muka koma ofishin sa, idan ban gaya muku ba. Hammah Mohan so yake ya lalace a jikina, domin baki daya wani ranar haka muka yi ta zirga-zirga, lokacin da na koma ofishin sa, na zauna yana masalaci. Ina cikin Office din ya dawo, ya shigo da sallama na amsa mishi. Ban san me yasa mutum yake min kwarjini da cika ido ba. Zama yayi tare da mai da hankali akan aikin shi. Mikewa nayi tare da cewa.
"Yallabai"
"Koma ki zauna" zama nayi cikin jin kunya.
"Baki da mafadi ne? Ko abinda iyayenki suka turoki kenan? Shi kwalliya ce a tare dashi, ke kuma abin kunya ce a gare ki, ban ji dadin yadda yake rungume a kan idanuna ba, idan mahaifin ki ya ga haka me kike dauka zai kalle ki? Karki kuma kamanta irin wannan shirmen a ofishina, ki cika wannan takardun." Ya ajiye min, jikina yana rawa na dauka, tare da cikawa na mike zan fita.
"Dawo?" Da sauri na dawo na zauna.
"Kin ci abinci?" Ya tambaye ni cikin kulawa.
"A'a. Abie" wayar da can ya danna, yayi magana cikin fulatanci. Murmushi nayi tare da cewa.
"Abie anani fulfulde?"
Murmushi yayi sannan yace min.
"Eh, Wodaadabe Bororo" ya faɗa tare da kallona, kamar na saka ihu."


"Laa nima Wodaadabe Bororo ce."
"Daga ina?"
"Niger"
"Libya Mali"
"Kai Amma Abie kai ma aiki ne ya kawo ka nan?"
Kwankwasa kofar akayi, yace a shigo, katon basket aka shigo dashi, aka ajiye Mishi, tare da mishi gaisuwa, kafin ya ciro kuɗi. Ya bata, tana fita yace min.
"Akwai goran fura da nono, ki duba can akwai kofi, sai ki zuba min sai ki kawo min, abincin kuma naki ne"


Idanuna ne ya cika da kwalla, na nutsu na fara abinda ya sani, kome na Office din tas yake, na dauraye na kawo, na zauna nayi duk abinda ya sani. Bayan na gama na mika mishi.
"Abie me yasa ba zaka ci abincin ba?" Murmushi yayi sannan yace min.
"Abincin mata uku naci a duniya na gamsu dashi, Mahaifiyata, mai sunanki dan ke sunan babata ce, sai Kanwata Kabo itama ma ina son girkinta, sai mace daya da tayi tafiyar ƙaddara da rayuwata."


Hannuna na had'a tare da kallon shi ina bubuga index fingers dina.
"Abie itace Crushed dinka?" Na fada ina kallon shi da yar murmushi.
"Ta wuce crushed sai dai rayuwata."
"Ta rasu ne?"
"Zuwa yanzun kan bana jin tana raye?"
"Ayya kayi hakuri, na fama maka ciwon da yake ranka" na dauki abincin zan fita.
"Ina zaki? Ki ci anan"
"Abie, Hammah yana waje"
"Toh jeki"


"Nagode sosai Abie"
Bai d'ago ba, kuma bai amsa min ba. A duk lokacin da ya kalle ta wani irin abu yake ji akanta, haka kawai muryanta da shiririta yake dibi da ita, idanun shi ce ta cika da kwalla, ya mike tare da tsayawa a bakin window yana kallon yadda mutane ke zirga-zirga.
*Jewel* ya ambata a hankali, yana tuno yadda tayi ta kuka da abinda yayi mata, idan ya tuno yadda take daura kanta, a kafadar shi tana kuka.
_Wai meye aka miki ne? Kawai dan na tawo dake? Meye na kuka? Toh kiyi shiru zan mai daki gida_
A lokacin dud duniya baya jin zai iya rabuwa da ita, baya jin akwai wanda ya isa raba shi da ita. Sai gashi kai tsaye mahaifinta ya karya karfin shi da yake jikin ta.


Itace yarinyar da ya fara ta'adi da ita, yasan ya saka yan mata dayawa kuka, amma baya jin kukanta zai tab'a rayuwar shi sai da ta bar jinjirin da ta haifa mishi, sai da ta tsallake su tai tafiyar shi. Bai san me zai ce ba, amma zuwan yarinyar nan yasan ya shi jin lallai yana bukatar Ahalin shi.
"Assalamu alaikum!"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa yana kallonta, kafin ya mai da kanshi gurin Mohan.
"Kayi hankali da rayuwar ka, domin wani lokacin muna tafiya ne da ƙaddaran mu, duk wanda ka ga ya sha Allah ya dibe mishi wani wa'adi ne, ka kuma kara nisanta kanka da mutanen da suke zagaye da ƙaddaran ka, wasu Alkhairi ne ke tafe dasu, wasu kuma sharri ne, malam masoyi zaka iya daukar yarinyar ka tafi da ita, amma kazamar soyayya da ake yin nan a gaban jama'a, ayi hakuri dashi sabida kimar Uwata. Domin naga wani sako a jaridar jiya."


A hankali na d'ago kai ina kallon shi, sai naji jikina yayi sanyi.
"Ban tab'a rungumar ta ɗan naji dad'i ba, ban tab'a rike ta naji dad'i ba, idan nayi haka ina yi ne sabida yanayin laluranta yana bukatar kulawar da tafi haka, amma a matsayin ka na babba kayi magana Insha Allah zan kiyayye hakkin Allah, gudun fadawa rudin shaidan, sannan karka manta da kashedina."


Dariya yabawa Alkali,ya saka hannun shi daya a aljuhun wandon shi, daya yana rike da kofin fura da nono, yana kurb'a.
"Toh ai yarinyar ka, Uba ta dauke ni dan haka karka kuma damuwa da ni." takowa yayi gaban shi cikin harshen buzanci yace mish.
"Ka kula kana mata mahaukacin soyayya, itace silar kukanku. Kayi fatan Allah ya shiga al'amarin ku. Domin ina hango guguwar da ta tunkaro."
Cikin sanyin halin ya kalle shi, kafin ya riko hannunta, yana kallon shi.
"Babu wanda ya isa tsakanin mu, domin na shirya zuwan wannan yanayin, tunda na na fara bana jin akwai abinda zai raxanani sai kalmarta kawai nake jin tsoron shi."


Daga haka ya riko hannuna,muka fita kallon shi nayi ina son nayi magana, amma tsoron shi ya hanani magana, har muka isa gidan, fushi yake tayi koda zai tafi rike hannun shi nayi.
"Kayi hakuri kaji." Na fada idanuna suna cika da kwalla. Shafa fuskana yayi.
"Babu laifi dan ya mana magana akan rayuwar mu, amma kuskure ne babba ya shiga al'amarin mu kin gaya mishi wani abu ne akan rayuwar mu"
"WALLAHI ka yarda dani ban tab'a wannan gangancin ba." Na fada kwalla na cika min idanuna,
"Ya isa, ki kula da kanki"
Gyada mishi kai nayi, tare da cewa.
"Sai gobe kenan"
"Eh nazo miki hira ne? Yawwa gobe Insha Allah Rukayyah Hussain Adam, zata dawo nan da zama. Naga kina son ƙawance da ita"
"Eh" na ɗaga mishi kai.
"Toh zata dawo nan Insha Allah"
Daga haka na rako shi har waje, sannan na koma cikin gidan, na hadu da matan gidan, muka gaisa.


***
Baki daya Mohan ya mai da Uwar shi bita can, yana zuwa gurin Hanan amma babu abinda yake hada shi da ita, ta gama haukarta, bai kula ta sai ya gama Gajiya zai tashi ya bar gidan, sannan ya kalle ta, shima bawai dan yana da abinda zai ce mata ba.


Bayan kwana goma sha biyu, ana saura kwana uku zayi bikin yancin kai, hankalin shi ya karkata akan wani abu na daban, bai da lokacin kowa sai kanshi.

Shi da dan Ba'are dan ya zo gida, kullum suna fita tare da abubuwan kan su. Sau daya yazo a kwanakin nan baki daya ya dauke kafa, a kotu ma ina zance ina fahimta abubuwan da yake faruwa, sai dai ban cika azarbabbin shiga ba, sai Abie yayi min magana nake shiga, dan ma dai ina yawan damun shi da shiririta, da wauta nayi ta dashi dariya, idan kuma muna hira kamar wasu sa'o'in juna, abinda na fahimta a tare dashi Abie ya aikata laifuka da yawa, da suke yawan dawowa rayuwar shi, sai dai wani lokaci zai ta share kwalla, tare da kallona yana fada min wasu kalmomi masu girma da daure kai dan haka tausayin shi da damuwar shi ya kara sakani cikin wani yanayi na daban, shima Hammah Mohan, idan na kira baya dauka duk da Rukayyah Hussain Adam, tana tare da ni, amma bana jin dadin yadda nake kiranshi yana kin d'agawa. Ga wani mugun mafarki da nake yawan yi akan shi. Dan haka ranar na kira shi tare da tambayar shi,yana ina?


"Karki zo inda nake kiyi zaman ki kawai" ya kashe wayar.
Takaici ya sani bin shi, bayan na kira shi, dakyar ya gaya min. Koda naje sai naga gida ne, dan haka na shiga cikin gidan, hango shi nayi, Hanan tana bashi abu a baki. Wani irin nauyi naji a kirjina, dan yasan na ganshi. Na kira shi waya.
"Nagode da abinda ka bukaci na gani."
D'ago kai yayi yana kallona, kafin yace zai mike, na juya tare da fita a gidan, ina jin zubar jini a hancina, duk lokacin da raina ya b'aci kai na yake sarawa, kafin nan na fara tari, idan banyi tari ba shine jini zai na zuba ta hancina, lokacin da ya fito har na tari abin hawa, ina kuka. Har na isa gida, shafa kanshi yayi sannan ya kira dan Ba'are.
" Ya kome na tafiya?"
"Eh amma ita fa tana cikin hatsari domin ana bibiyar kiranta"
"Ok gobe da dare Malik ya tafi da ita Maradi, itama Abokiyar aikin ta ta koma garin su, ka tabbatar sun bar garin nan gobe Insha Allah"


Sannan ya juya abin shi yana kashe wayar, kara wayar shi yayi sannan ya saka a kunne.
"Mohammed Mamman Nasir Aghali, ya kake? Baka saka hannun a wasan ba toh gani nan ina jiran Munnah a gidan da ka bata me kyau da tsada, zaka zo ne ko kuma zaka iya hakura domin nazo ne akan game ɗin."


Kashe wayar yayi tare da kiran Dan Ba'are.
"Maza kazo gidan Dogo ina jiranka, ina da abu me muhimmanci a gidan Beauty"


*
Ina komawa gida, tun a bakin get din na hango Malam Ansar, cikin kuka na kalle shi.
"Ya isa haka, dama haka rayuwa take, wanda ka damu dashi bai damu da kai ba, wanda baka damu dashi ba yana nan yana hakilo akan ka, shiga mota mu fita."


Babu musu na shiga ina goge kwallar da nake, da hanky din da da yabani, muka fito cikin garin, han gyara garin yayi kyau da ado, wani gidan abinci ya kai mu, na kasa cin kome, ruwa kawai na sha, haka yayi ta tsokanata. Tare da jana da wasa.


Dole na sake muka shiga hira. Inda ya min odar abincin da suka fi na farko kyau da tsada, ina ci ina bashi labarin gurin aikina.
"Hmm! Meye ya had'a ki dashi?"
"Babu kome!"
Naki gaya mishi, domin a tsakanin masoya akwai yafiya da boye sirrin juna, tun yanzun idan ban iya boye sirrin mu ba, yaushe zan koya dan haka muna cikin cin abinci, aka rike min hannuna.
"Ina zaka tafi da ita?" Cikin fushi ya sake hannuna ya zabga mishi naushi dai dai shigowar Alkali. Sai da bakin shi ya fashe.
"Mohan!!!" Na kira suna shi da karfi....🤣
#Mai_Dambu
[8/7, 10:03 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1110255281?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=DdYNxkS6yN8uhfrR37h62zbfOjOm1OLDDCckdNme%2BKjEwnbGDu4mL6048YMV1h%2B07%2FeXZoIeF7Jb4dl3nS6A6LUJkIqi7ROIE9bf%2BgkMcMKV8M17P9CSRPPYeYAU9QZF


🐂🐂BOROROJI🫀🫀


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


BABI NA ARBA'IN.


Tsayawa nayi a gaban shi, cikin takaici ina kallon shi, zuba min ido yayi, kafin yace min.
"Ba zan miki dole ba, amma kuma yana da kyau ki fahimci suwaye a tare dake, su waye suke son amfani dake, tashi muje gida."


Ya fada min, kasa mishi musu nayi ma mike, ashe haka ya b'atawa Malam Ansar rai yace min.
"Nagode" juyawa nake son shi yi, amma abun mamaki Mohan ya hanani, muna fitowa ya saka ni a motar shi. Muka bar gidan cin abincin kamar zanyi kuka haka nake bin shi.


Baya tafiyar shi, Malam Ansar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login