Showing 108001 words to 111000 words out of 181864 words
juya zai ya hadu da Alkali, cike da mamaki ya kalle shi. Sannan ya kasa magana, har ya fita yana kara juyawa yana duba alkali.
*Taya mutumin nan yake kuma da Munnah? Kamar ta B'aci sosai* shi daya yake zancen zuci, har ya shiga motar shi, wayar shi ya saka a kunne, yana me cewa.
"Yaki amsa sabida ya san zai fadi, dan haka duk rintsi ka dauko min ita idan ka sami damar haka, idan ka sake kuma na dauke ta, tabbas zan tafi da ita ne duk inda yayi min."
Wani murmushi yayi tare da cewa.
"Kwantar da hankalinka, yanzun zaka ji ruwa mai yawa, zan baka abinda baka zata ba, yanzun zan koma diffa, idan na dawo zan kira ka."
Kashe wayar yayi tare da sake wani murmushin gefen baki yana faɗin.
"Hmm! Ta kare maka Mohan" ya faɗa yana murmushin mugunta, a hankali ya tadda motar,tare da barin Niamey.
Abincin ya saya tare da biyan kudin, sannan ya nufi gurin da su Mohan suka tsaya, ganin wayar Maimunari yasa shi dauka, hotonta ne a kai lokacin tana Almamoon, kura mata ido yayi zuciyar shi tana bugawa, da sauri ya kashe wayar baki daya. Abincin da bai ci ba kenan, haka kawai zuciyar shi take raya mishi wani abu akan Yarinyar,duk da ya lura bata da kwaranniya irinta sauran matan, gaskiya da ban mamaki yanayin su da yake gani a tare, abu daya da yake kara fisgan shi a kanta, kafewarta akan abu. Bayan haka baya jin akwai wani abin da ya ke yanayi daya da nashi, sai fuskar shi da kuma yana yin fatar su, sai dai tafi shi washewa kaɗan, kasancewar shi mai duhun fata sosai. Lumshe idanun shi yayi.
A da baya tunanin haka sai da wani abokin shi alkali daga tahua yazo da ya ga Maimunari ne yayi ta mamaki.
"Wodaadabe wannan yarinyar yar ka ce?" Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Eh toh kasan ban da iyali dai? Aiki ya kawo ta nan bayan nan kuma gaskiya babu wani abinda ya had'a mu sai dai ina jin ta kamar wacce ta fito jikina" ya faɗa yana murmushin jin dadi. Yau an had'a shi da d'a shi da yayi kuskuren tafiya ya bar baya da kura.
Bayan abokin shi ya tafi ya tuna sakon da ya barwa yar uwan shi.
_Ban sani ba ko meye muka haifa! Ba zan iya duba shi ba, don Allah ku rike shi da amana, idan namiji ne ku bashi ilimin addinin musulunci, idan mace ce don Allah ki tayani boye sirrinta, dan kar hakkin mutane ya tambaye ni akanta na had'a ku da Allah."
Lumshe idanun shi yayi kafin ya bude sunyi jajjur har da ruwa sun cika.
"Ina namiji ta haifa, kuma tarihin shi zai rufe,mace kuwa tabbas soyayya zai bude tarihin ta, kuma de ƙaddara zata ratsa tsakanin. Allah kasa namiji ne. Allah kasa kar ya gado mugun halina, ya Allah kasa kar ya dauki halin da na jefa wasu iyayen."
Ya fada yana jin saukar kwalla akan fuskar shi, tabbas yayi kuskure sosai, kuma yayi danasanin rayuwa,domin ya cutar da yaran bayin Allah da yayi ka,abun na mishi ciwo. Gashi girma ta cimma shi babu iyali shin Zainabu tana raye ne? Takawa yayi babban falon shi yana kallon yadda rayuwa ta mike mishi, a cikin shekara ashirin yayi faffutikar niman ilimi, yayi karatun boko dan yana da ilimin addini, bayan faffutikar da yayi na yawon karatu kasa kasa, ya halarci yaki da jahilci da yake garin Kano, idan ya damu shekara biyar yana karatu, bayan ya gama ya koma Nijar yayi karamar diploma kan harshen French na shekara uku. Sannan ya nime gurbin karatu ta hanyar wani mutumin da ya tab'a yiwa taimakon sakamakon asirin da aka mishi, akan shi da yaran shi. Mutumin shi ya dauki nauyin shi tafi kasar Faransa yayi karatun lawyer, inda ya shekara takwas yana karatun, yana gamawa ya kuma komawa makarantar horon alkalai anan Faransan, idan ya samu shekara goma sha biyar yana karatun shi bai da lokacin kanshi baki daya ya kuma tafiya jami'ar Madina inda ya karanci Shari'a musulunci a can suka haɗu da Primer minister, inda ya karya mishi asirin jikin shi, sannan ya gaya mishi wasu abubuwan. Akan Yaron shi da suka haɗu dashi wato Mohan.
Yana kammala karatun shi, a Saudiya suka dauke shi aiki Nan babban Kotun musulunci, albashin da tabarkallah, haka yayi ta rayuwa ga yan mata da suke bibiyar shi, amma bai tab'a kawo su rayuwar shi, asalima mace daya yake so har kwanan gobe.
Lumshe idanun shi yayi idan ya tuna yadda yayi ta yawon niman abokin shi da Kanwar shi kamar ai yi hauka, yayi ta niman Zainab da danginta, kamar Mahaukaci. Haka yayi ta jin kamar ya tsani kowa a duniya, bayan ya dawo Nijar domin Primer minister ba karamin addabar rayuwar shi yayi ba akan lallai ya dawo kasar shi yayi musu hidima, yana dawowa aka bashi alkalin Alkalai na kasar nijar, tare da albashin mai kyau amma bai kai wanda Saudiya take biyar shi ba, idan yanzun zai ga Zainab ko dukkan dukiyar shi ya zab'a ya bata zai sallama mata indai zata zauna dashi. Numfashi yaja tare da d'aga kan shi sama, yana jin babu dadi. Ya rayu a kad'aici gashi Yanzun ma kadaicin ce ta kuma takura shi.
Buga mishi kofar gida da aka yi ya sashi bude kofar shiga gidan, manyan mutane ne baki dayan su. Shigowa suka yi bayan sun nime izinin haka. Tashi yayi tare da dauko musu ruwa, ya ajiye musu.
Ya zauna yana kallon su, bayan ya daura daya akan daya.
"Ina jin ku meke tafe da ku?"
"Muna niman goyan bayanka, kan aikin da zamu yi, kuma Alhamdulillahi mun samu nasarar wasu manyan sai dai wasu daga cikin mu sun yi kokarin kin bamu hadin kai."
Murmushi yayi yana kallon su.
"Kusha ruwa" daukar goran ruwan suka yi tare da kaiwa baki, shima ya dauki nashi yana kallon suka bude tare da kaiwa bakin su. Suka sha, rike musu ruwan yayi, a wuyar su bayan ya damke goran hannun shi.
"Kun zo kuyi min tayin na shiga kifar da gwamnati Mamman Mohammed Nasir, bayan baku san tarihina ba, tun ba yau ba nasan zaku zo. Kuma idan kuka tafi zaku iya juyowa gare ni, wannan abin da kuka yi hukuncin kisa zan yanke muku domin wallahi ba zaka yi nasara ba, koda zaku yi faduwa ce zata biyo baya, sake goran yayi suka shekar da ruwan suna tari.
"Kafin ka tunkari mutum ka fara dubar waye shi, jarumta ba a jiki yake ba a zuciya yake, idan kuma aka yi katarin haduwa da karfin jiki Magana ya kare maza ku tashi ku bar min gida idan na fito muku a asalina, mutuwa zaku yi domin da bakin ku zaku fadi abinda kuka aikata."
Mikewa suka yi tare da barin gidan a guje, domin basu tab'a tsammanin tantiri bane shi sai yau.
Murmushi yayi sannan ya fara niman wani layi, bayan sun jima suna magana sannan ya kashe, yana jin wata irin nutsuwa a ranshi.
***
Wullani yayi cikin motar ran shi na kara b'aci..
"Dalla malam karka karya musu yar mutane, ka manta kai ka daukota a gidan su? Kishin banza kishin wofi ko ce maka aka yi yar ka ce ita? Baka isa ka hanata kula samari ba, tunda ba aurenta kayi ba. Haba Mohan! Meye tayi maka da zafi haka? Meye ta tsare maka haka? Idan wani abu ta maka zai ka gaya mata. Amma ba kayi ta nuna mata abinda bai dace ba, ta baro gaban iyayenta a wahale, tazo nan kana wahalar da ita"
"Kyale shi Hammah Khalil, ban san b'ata min lokaci yake ba, sai da nagan shi da yar uwan shi, ya hanani nayi rayuwa da wani, sannan shi ya kasa fahimtar dani wacece ni? Bayan tashin hankalin da na gani nazo zan shiga gida Ansar yazo, da naso wulakanta ka da a gaban shi zan ki kula ka, na bishi amma kai a rayuwata gaskiya ne baka tab'a min gori ba, nasan kana kishina amma haka baya nufin cewa zaka wulakanta duk wanda yake tare dani ne, Hammah meye nayi maka da zafi? Dama can yar uwarka zaka aura"
"Eh ita zan aura"
"Mohan ka gaya mata gaskiya mana, meye amfanin boye mata abinda kake?" Inji Dan Ba'are,
"Ba zan gaya mata ba, idan ta gadama gobe tana dawowa aiki ta shirya zata koma Damagaram" cikin takaici na kalle shi, ban iya mishi magana ba, na dauke kaina haka muka isa gida, har na fito daga cikin motar na shiga compound na gidan. Ya biyo ni da sassarfa.
"Ki hada kayan ki nace gobe" dauke kai nayi.
"Maimunari ina magana dake" banza na bawa ajiyar shi. Hannun shi ya d'ago zai rike ni, na buge hannun.
"Karka kuma gigin tab'ani, idan ba haka ba, zan mare ka" na fada mishi ina wuce shi. Kasa motsi yayi tare da cizon lip din shi na kasa, furza da iska yayi. Wayar shi ce tayi kara ya dauka.
"Malam da alamu kome dai yana tafiya dai-dai, ko ta watsar da kai ne tayi tafiyar ta, ok kasa hannun muyi wasar mana ko kana tsoron zaka fadi ne!"
"Kai!!!! Kana ina ne?"
"Ina kofar gidan ka mana, kazo domin da shaiduna nake."
Kashe wayar yayi, sannan ya fita da mugun gudu ya shiga motar.
"Taka muje."
"Ina dan Ubanka sai kace aljanu ne suka shafe ka"
Bai kula shi ba kallon agogon hannun shi yake.
"Gidana mana" da gudu suka bar apartment din, suka isa gidan, ko tsayawa basu yi ba, ya bude motar tare da sauka, yana wani irin ciccira kamar wani lantarki yana spark, takawa yayi zuwa gaban su. Ya daki motar su,
"A'a Mohan! Karka lalata min mota na mana." Ya fito yana kurb'an wine.
Takardan ya ajiye mishi. "Ka duba mana, meye a cikin shi ban da yarjejeniyar da aka kula idan bai maka ba, sai ka rubuta wanda kake so"
Ya fada tare da kallon abokanshi biyu da suke cikin motar. Yana faɗin.
"Yan iska zaku fito ku tayani saka hannu ko ya?" Dariya suka yi tare da fitowa suna kallon Mohan.
Gira ya d'aga mishi yana nuna mishi takardan daidai fitowar dan Ba'are, tare da ciro bindiga a k'ugun shi.
"A'a. A yarjejeniyar mu babu harbi babu fada. Duba mana"
Daukar takardan dan Ba'are yayi yana kallon shi.
"Ba zai shiga ba" ya riko hannun Mohan.
"Hhhh! Kunji dan mace toh tunda ba zaka shiga ba, inji abokin ka nima dai zan maka Yaren da zaka gane"
"Zan shiga"
"Mohan"
"Zan shiga! Bani. Amma idan nayi nasara zan Barka a raye domin ganin mu shi zai kara maka fahimtar kome na Allah ne"
Cika gurin yayi, sannan ya juya zai bar gurin.
"Mohan ina maka fatan nasara"
Cak ya tsaya, sannan yayi gaba abin shi. Bai kuma kula kowa a cikin su ba, har suka shiga motar bai iya magana ba.
"Mohan"
"Please"
Yace mishi, tare da juyar da kanshi.
"Idan baka yi nasara ba zai iya daukar ta da?"
"Nasara ta Allah ce, ka yarda da faduwa. Don Allah ka barni" Ya fada mishi haka.
Murmushi yayi bayan sun bar gurin.
"Me yasa ka dage ne? Naga dai baya so kamar tilasta mishi kayi."
"A'a yana so mana, da baya so ba zai shiga ba, nasan abinda nake shima kuma ya sani, idan da bai da ilimi ba zai shiga ba, saka ido ka gani."
***
Tunda na shiga dakin nake kuka, ban san me yasa kome yake zuwa min haka ba, amma tun haduwa na da Mohan nake kuka, mik'ewa nayi tare da hada kayana ina gayawa Rukayyah Hussain Adam,
"Auta tashi ki hada kayan ki, zamu bar garin nan sai bayan bikin yancin kai zamu dawo."
"Toh lafiya?"
"WALLAHI ban sani ba, Hammah Mohan ya sani haka." Na shiga had'a kayana. Ina ƙoƙarin b'oye damuwa na. Tunda na gama muka kwanta.
*1:am
Kokarin rike jan numfashi na nake, amma baki daya ya shake ni, ya hanani sakat ban san meye manufar shi ba, sai dai hango shi da nayi ya fad'i kasa warwar ya sani farkawa da sauri ina ajiyar zuciya, ban daki na shiga nayi alola nazo na gabatar da sallah nafilla.
Har asuba idanuna yaki barci a duk lokacin da na rufe idanuna abinda ya faru a mafarki yake dawo min, har aka yi sallah asuba,nayi sallah sannan na zauna na cigaba da azkar. A hankali barci ya dauke ni.
Karfe tara na bude idanuna, ganin shi nayi zaune, ajiye min kofin shayi yayi tare da mika min brush. A hankali na tashi babu yabo babu fallasa, na nufi ban daki ina fitowa na dauki shayin da magani na sha, sannan na koma nayi wanka ban same shi a dakin ba na shirya sosai, sannan na fito, ina kallon shi suna hira da Rukayyah.
"Insha Allah karfe biyu zaku bar garin nan ki gaida iyayen ki," ya mika mata wata jaka, sannan ya kalle ni.
"Muje"
"Yan mata bari na fita"
"Toh sai kin dawo" ta ce min, haka muka fita, gabaki dayan mu jikin mu a mace yake, kamar wanda wani abu zai zame mu, gurin cin abincin ne. na zamani.
Kujera ya ja min na zauna. Sannan ya zauna yana kallona, kawo mana kayan abinci aka fara yi. Ina kallon shi.
Kasa cin kome nayi ina kallon shi.
"Ci mana"
"Na koshi" bai ci ba, ya rike hannuna.
"Ban sani ba ko zan kai labari, sai dai ina rokonki Abu daya. Don Allah koda na mutu karki auri Ansar ki, Don Allah ki auri Khalil ko Haddir, sune kadai zasu rike ki kamar yadda nake rike dake. Sune kawai zasu soki kamar yadda nasoki. Kasar da Mahaifina nake son bawa kaina don Allah ki taimaka min kinji karki Auri Ansar"
Ya fada yana dauke kan shi tare da saka bakar madubi a idanun shi, domin kwalla ce take son zuba mishi.
"Me yasa zaka gaya min haka"
"Sabida bani da zab'i, rayuwar mahaifina"
"Mohan kasan yadda nake ji akanka? Me yasa zaka gaya min haka?"
"Sha ruwa" ya mika min.
Buge hannun shi nayi, tare da mik'ewa dan kula shi ma, bata lokaci ne. Haka na barshi ya zo ya same ni a gurin.
Haka muka fita yayi ta yawo dani, kusan amanar kaina yake bani kar na auri Ansar.
*🤔🙄 Toh ya zamu yi daku domin mutanen da suka biya kishi a tsakanin zubda jini sun fara niman shi fa😌😠 🙄 wai suna jiran dan haka zan fara shi ku kuma zan mai da ku posting sai dare sau daya shima sabida nayi alƙawarin shine ɗan haka kuyi hakuri, toh ya na iya an fara tambayana 👏 kuyi hakuri ba laifina bane na mutanen da suka biya kudin su..... Nagode*
#Mai_Dambu....
[8/7, 10:04 AM] Sidrah❤️: https://www.wattpad.com/1110533172?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=aSbcpjgn9asSsm9lZXK1GTYd1hkBoALGTEin2VPj2rrHh0qsHukAEkcdgVB%2Bbd47RHlGBNNnsyrNYAxk4FDLM8zZE%2BhDR1NGlY7Kh7sDrXNrEAQA9XmoAHfTO2Lcqj9H
🐂🐂BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
BABI NA ARAB'IN DA BIYU.
Gurzawa yake cikin wani irin shauki me mugun dad'i, har yaji shi ya shige cikin jikinta kamar mahaukaci a zauce da ita, ya gigice domin bai tab'a kawowa zata kai mishi ba, dan haka lokaci guda yaji an shake mishi wuyar shi.
Ban san yadda zan kwatantata muku yadda nake ji ba, ban san wani irin yanayi nake ciki ba, sai dai duhun da na fahimta yana rufe min idanuna, karar da naji wanda ya tafi da jina da gani na baki daya, daga nan ban kuma sanin me ya faru ba, na ga dai ana tafiya dani da gudu, ina wuce wani irin haske. Sai muryan da ban san ta waye bana yana kirana can da nisa.
"Munnah!!!"
Cikin wani irin faduwar gaba ta fito bayan ta gama sauya kayan ta, tana kallon abokan. Aikin da da suke mata magana, jin su take amma ba zata ce tana sane da abin da suke fada ba.
"Dr Zainab kina lafiya?"
Wani irin bugun zuciya taji lokacin da aka shigo da wata mara lafiya, mai da kallonta tayi kan yarinya domin a hannun wani mutum take yana niman agaji.
"Ku taimaka min don Allah," da sassarfa ta isa gabanshi. "Ku kawo min gadon dauka marasa lafiya." Ta fada da karfi, yana kawowa aka daura Maimunari, kallon Dr Zainab yayi tare da cewa.
"Don Allah ko nawa ne a duba lafiyar ta, don Allah" ya faɗa kamar ya cire ciwon a jikinta ya mai da nashi, da sauri suka wuce da ita d'akin tiyata, aka fara kokarin kunna wutar da zata iya haska inda ciwon yake, domin ta ga yadda mara lafiyan take.
Domin zanin gado ce a jikinta, daga haka ya tabbatar mata da zargin da yake ranta, musamman da ta kwaye zanin da ya lulluba mata, kwalla ce ta shiga sauka daga idanunta. Tana kuka kasa kasa, kallon Nurse din dakin tayi tare da cewa.
"Kuje kawai ku kira min Dr Fadime da Dr Annah."
"Toh Dr" suka fita, a hankali ta mike tare da shafa kan Maimunari, kwalla na zuba mata, kwaso kayan aikin tayi tare da saka Safar hannun, ta fara duba ta sosai musamman gaban da ya fara alamar zai kumbura, yatsin ta gwada sakawa taga bai shiga dukka ba, da sauri ta cire tanadi mamakin yadda aka haka shigowar likitocin biyu ya sata kallon su . "Ban tab'a ganin irin wannan tashin hankali ba, ina ganin cases na Fyade, amma ban san yadda aka yi wannan case din ya tsaya min a rai ba."
"Kai Dr meye na rashin hankali, wannan case din ba sabon abu bane, idan kika yi dubi da Yadda ake samun kananun yara ma ana musu fyade balle kuma babban budurwa kamar wannan.
Ina ganin ba wani babban tashin hankali bane, kawai a dubata idan aiki ne sai mu hadu muyi mata, amma ki bar kuka haka." Inji Dr Annah.
Kallon su Dr Fadime tai sannan tace musu.
"Amma ai naga mutumin da ya kawo ta ya biya kome, idan ba ita