Showing 72001 words to 75000 words out of 181864 words

Chapter 25 - Bororoji Compelet Book Document by Mai Dambu .txt

29 Jan 2025

6251

kallon shi. Bai kula Ni ba, ya fara kokarin mik'ewa nace mishi.
"Hammah kawo kunnen ka" na fada ina yafito shi da hannu, ya gaji da shirmen yaron nan, zama yayi tare da kallona.
"Kawo mana shawara zan baka"
.kawo kunnen shi yayi na kai bakina ina dan karewa kar maganar ya fito.
"Kaga mu ce su biya mu rabin kudin mu tunda bamu cinye abincin ba ko me ka gani?"


Tashi yayi yana kallon shi idan ya bashi amsa kamar ya biye mishi ne suyi ta hauka, idan kuwa ya kyale shi ya manna mishi haukar shi daya ne dan haka ya mike tare da ciwo kudin ya saka a cikin memo din ya tawo inda nake ya d'ago ni, yasan sai na iya raba kudin biyu, aikuwa bai gama d'aga ni ba, nace mishi.
"Wallahi sai na raba biyu."


Jana yake ina kai hannuna.
"Wallahi zan sab'a maka" kwace hannun nayi ina tura baki.
"Haka kawai mutum bai cinye abinci ba ace sai ya biya Alqur'an Ubangiji da na koma sai na kwashe kuɗin." Na fada ina tura baki. Bai san ƙaddara da ta haɗa shi da Mamoon ba, amma baki daya ya hautsina mishi lissafin shi. Daga nan fita suka yi cikin garin Dubai, inda suka nufi wani shagon sayar da waya, anan ya hango irin tashi, a ciki kuwa akwai inda ake gyaran waya Sosai dan haka ya nufi gurin ya mika musu, basu jima ba suka gaya mishi abinda za saya.
"Kai haba kudin a kasa kake diba? Gaskiya gwara ka sayi sabo kawai" na fada ina hararan mutanen.
"Kasan Allah, karka hada ni da mutane." Ya fada min kamar zai make ni, dan ya fara gundura da halina. Juya mishi baya nayi tare da kallon wayoyin da suke jere. Juyawa nayi gurin Hammah Mohan na janyo shi ina nuna mishi wayar. Na sake shi tare da nuna mishi wata Sumsung S4.
"Yayi maka ne?" Kallon shi nayi sannan nace.
"Eh amma nasan ko dukkan albashina na dauka ba zai saya min ba. Ba yanzun ba idan na koma gida zan Nime wata yar Vivo, dan naji kace sai ba biyaka kudin wayar ka, shi yasa ba ce maka kawai ka sayi sabuwa."


A hankali ya kalli me sayar da wayar ya nuna mishi, yana daukowa ya mika min.
"Karb'a"
"Hmm, kawai ka barshi domin ka ga idan na koma Maradi zan koma makaranta ne, kuma hostle zan koma. Sannan kuma zan je ganin gida iyayena ina kewar su." Na fada kai na a ƙasa.


"Karb'a." Ya mika min lokacin ya mika master card din shi, kamar yadda nayi tsammani haka ce, domin kuɗi ne me mugun yawa, tura baki nayi bayan naga yawan kuɗin. Can nace mishi.
"Ina fatan kyauta ka bani? Domin ni dai ba zan iya sayan wayar nan ba, tunda ba kudin ce dani ba"


"Zaka zauna dani na wata uku kafin nan na fanshe kudin aikina." Ya fada min yana tafiya kamar ba a bakin shi maganar ta fito ba, wani Jahilin tsalle nayi, tare da dawowa gaban shi, ina raba ido.
"Ba ka sami lafiya ba?"
"Eh amma ai na saya maka waya kuma na biya kudin gyaran wayar toh me?"
"Ungo maza mai da musu bana son Alqur'an bana son, kawai ka bani sauran canjina na koma gida."
"Auw haba?" Aikuwa na takarkare murya na fasa mishi kara, sai da ya toshe min bakina, tare da ɗaukata ina, watsal watsal da kafana kamar Yaro dan shekara uku. Haka ya fitar dani daga shagon. Aikuwa na koma inda ya tsayar dani na fashe da kuka.
"Wallahi ba zan yarda ba, sai dai ka rike wayar haka kawai zaka tab'a min kudina saura dubu dari bakwai na gama biyan kudin, kace ba zaka kyale Ni ba sai ka fanshe?"


"Kwarai sai na fanshe kudina." Ya kuma faɗa min, kuka ne ya kwace min, muna tafiya sai kallon mu mutane keyi.


"Kaga akwai wani wasa da ake yi casino zan baka aron kudina idan kaci zaka iya samun sama da dallar Amurka dubu dari uku a lokaci guda, amma sai ka nutsu zan na gaya maka Number kana sakawa, sannan kuma idan aka canza shi zuwa CF kudi ne ne shegen yawa, sai ka biya kudin gidan ka."


Kallon shi nayi naga nima yake kallo.
"Caca zan buga bayan haramun ne?"
Janyo Ni yayi jikin shi.
"Karka damu akwai abinda nake son muyi a gurin muje ko ba zaka yi amfani da kudin ba amma kuma zaka ga sabon rayuwa" ya shigar Kawata min gurin babu shiri na amince, muka nufi wani hotel tare mu aka kayi tare da nuna mana inda zamu sauya kaya.
Kallona yayi sannan yace min.
"Almamoon ina son tausaya min kayi shigar mata?" Wani tsalle nayi kamar wani dan biri. Ina rufe kirjina.
"Kai haramun ne" na fada mishi,
"Toh babu damuwa bari na fita na nimo wata baturiya" ya juya zai fita da sauri na rike hannun shi.
"Amma daga yau karka kuma sani nayi shigar mata, domin ni ba mace bane" na fada mishi ina me sunkuyar da kaina.


"Good boy" ya faɗa min, wani daki ya nufa bayan ya buga kofar dakin, wani dan daudu ne ya bude kofar.
"Dame zan taimaka maka karjejjen kato"


"Sauya min shi a cikin nan da awa daya" ya tura ni.


Shiga katon dakin muka yi, da yan mata kafin kace me sun taru a kaina, sai da suka kwashe min albarka kafin suka nuna min wani daki na sauya kaya, haka nayi ta sakawa idan na kalli madubi da sauri zan dawo mishi shi.


Dakyar ka sami wata gown iya kwanjina, golen sannan suka dauko takalmin da yar pose, yan kunnewa, aka saka min wato dan daudu nan da ya rike fuskana ya shiga min paint, sai da naji kamar abu ake loda min a fuskar dakyar ya gama. Sannan ya dauko wata jacket ya daura min a ƙafadana yana faɗin.
"Kin fito kamar wata Jaruma." Murmushi nayi mishi sannan na fito, ya juya bayan shi yana waya kamar kuma me muhimmanci ne.
"Eh mana shi ne daidai da aikina kafin na iso inda zan kammala baki daya, kawai zan yi amfani da hakan ne ka gane kawai ka saka ido akan sauran sai mun iso Insha Allah." Karan sautin takalmi da yaji ne ya sashi juyawa. Tare da zubawa sarautan Allah ido, duk da yasan cewa Yaron mata maza ne amma wallahi yau ganin shi cikin kayan mata ya kara kwadaita mishi son lallai yaron ya koma mace.


Takowa yayi tare da mika min hannun, a hankali na saka a cikin nashi, muka fita a hankali domin ban iya tafiya da takalmin ba kamar zan fad'i. Shi yasa ya kange ni a jikin shi har cikin inda ake buga wasan.


Kamar zanyi kuka haka nake kallon gurin, saka min abubuwan da zan buga wasan aka yi ya ajiye Dalar Amurka har guda bakwai, sannan ya saka a gabana. Yana faɗin.
"Kai me Sa'a ne kayi amfani da sa'ar nan idan suka baka wasan ka dauki wancan silallar."


Gyada kai nayi, a hankali yana gaya min ina bin abinda yace kafin minti talatin cinye gasar, a hankali ya shiga tara min kudi ko awa daya ban yi na na zama attajira a gurin an cika min kudi a gaba na. Tab'a kunnen shi yayi tare da cewa.
"Ba'are fara"
Nan kuwa wani katon mutum ne ya fito, tare da kallon shi.
"Dama tunda na ga ana ta cin mutuncin gasar nasan Mohan ya farmake mu. Barka da zuwa." Ya fada cikin French, mika mishi hannun yayi tare da cewa.
"Wasan bai kare ba, ita Yarinyar zaka saka nima kuma zan saka abinda na mallaka. Domin zamu gwada kwanji ne?"


"Thomas jefferson ba wannan ne ya kawo ni ba, kawai akwai abinda ya kawo ni sai dai matuƙar kasa ni magana zan karya kashin hakarkarinka na kuma Cigaba da wasa na, na jima da ajiye aikin soja kawai ina da yakinin wata rana kasata zata bunkasa." Ya fada yana kallon mutumin.


"Toh haba, lallai ku tattara mishi kudin shi, na zata kana aikin ne har yanzun, muje ka sha ruwa" ya faɗa mishi.
"A'a kasan bana son giya." Haka ya ja hannuna muka nufi inda mutumin yake zaune, a hankali hira ta sarke a tsakanin su, ina gefe duk a takure nake.
"Cire rigar jikinka ka nufi wancan table din, ka zauna"


A hankali na cire jacket din na kudi inda yace na zauna, ina zaune sai ga wani dattijo, zama yayi yana kallona. Matsowa kusa dani yayi tare da cewa.
"Yan mata daga Afrika?"
"Eh" na bashi amsa ina kallon yan matan da suke rawa naked, nan ya zauna yayi ta min shirme da shiririta, har wasu mutane suna shigo gurin. Mikewa yayi suka fita. Mikewa yayi tare da zuwa inda nake ya mika min kofi tare da wani kwaya ya mika min bayan ya bar gurin dai ga mutumin.
Ajiye kofin nayi bayan na zuba lemon Kwalba a cikin kofin, na mika mishi sannan nima na sha nawa, a hankali muka hira dashi har ya mike tare da mika min hannu, kallon Hammah Mohan nayi ya gyada min kai.


Bin bayan shi nayi, muka tafi yana tangadi har dakin da yaƙe, muna shiga ya zube akan gado. Bayan kamar minti goma, naji an buga kofar, budewa nayi na gan shi.
"Babu abinda yayi maka? Toh maza wuce gani nan zuwa."


Yana shiga na bar gurin domin da kayan aikin ma'aikatan hotel din ya shiga ya gama abinda zai yi ina club ɗin sai gashi, ya mika min hannun na mike tare da nufar inda muka ajiye kan mu, muka sauya. Kallona yayi bayan na saka kayana na fito rike da jakar da ya saya min waya.


"Me yasa baka da account Number? Yanzun da kudin nan sai dai na tura maka" kallon shi nayi sannan nace mishi.
"Kudin nan zan kai asibiti da makarantun gwamanti tare da gidan marayu, akwai mutane masu makamanciyar rayuwata basu ci sau uku a rana ba, ma idan na basu zasu yi farin ciki."


Jan abinda na daure gashina yayi dashi bayan ya cire hular gashin mazan da yake saman kan nawa, ya zare min gashin. Ribom din da na kama gashin da shi ya ha, gyararren gashin ya sauka har gadon bayana.
"Me yasa baka son ayi maka aikin komawa jinsin mata?" Saka hannuna nayi tare da hautsina gashin kaina ina murmushi.
"Nafi son wannan yanayin" na fada ina kallon shi.
Shima hautsina gashin yayi yana faɗin.
"Kuma kayi kyau ba a jinsin mata"
Tsayawa nayi ina kallon shi kafin nace mishi.
"Ai kafi ni kyau"
"A'a ba dai fika farin fata ko"


"A'a kawai ba zaka fada bane"
"Gaskiyar kenan"


Na gaji gashi lokacin sallah yayi dan haka muka nufi inda muka kama, muka yi sallah bayan mun isar yace min.
"Pizza kake so ko Shawarma"


Mika nayi tare da cewa.
"Duk wanda aka kawo min matukar ba zan yi asarar shi ba yayi min" na fada ina shafa cikina.
Yayi a waya can dai gashi an kawo min, shi kan Coffee ya sha abin shi.
"Kayi sauri domin an jima zamu bar kasar nan."


"Hammah duk dai saurin unguwar zoma dole sai an haihu dan haka ka jira na gama cin abincin mana" na fada ina koda pizza a bakina. Share ni yayi tare da mai da hankalin shi kan yanayin da yake ciki, na son lallai ya shiga Nijar yau din nan.


Haka na gama dakyar shima dan yayi min barazana zai tafi ya bar ni, yasani mik'ewa da sauri na bi bayan shi, muka nufi hanyar gida.


Tunda muka iso airport, yake yawan kallona,
"Yanzun idan muka koma dole sai na maka aikin ne?" Na tambaye shi.


"A'a bai zama dole ba tunda kayi kudi sai ka rike kudinka kawai." Ya fada min magana mara dadi.
Hararan shi nayi tare da cewa.
"Wayar ka fa?"
"Zan cire a albashin ka"
Zama nayi ina kallon shi, har jirgin mu ya tashi, fushi nake dashi.


***
Alhamdulillahi mun sauka a garin Niamey.


Jerin gwanon motar gidan Primer minister ne ya zo daukar mu.
"Hammah karka manta da addu'a"


Na fada mishi ina ƙoƙarin bude motar.
"Malam ga motan da zaka zauna" juyawa nayi na kalle shi.
"Haris kyale shi P.A ne"
"Toh Kaji ai ni personal Assistant din shine ɗan haka daga yau nima Yallabai za a kirani ki kuma ba bawa kowa gurin hucin gadi."


Girgiza kai yayi yana me shiga bayan an buɗe mishi kofar, nima na bude nawa gurin zaman.
"Hammah Mohan! Kai ne primer minister ko kai dan uwan shi shine?"
Hannun shi ya kai bakin shi, nima na ja nawa na rufe, a haka muka nufi cikin garin Niamey, ina kallon garin bude min window yayi na juya tare a sake mishi murmushin jin dadi, na cigaba da kallon yadda garin yaƙe.


Sai da muka nufi fadar shugaban kasa, na gane cewa Allah yayi arziki, tun daga bakin kofar ake sarawa Hammah Mohan, sabida zuwan shi yau an dauke aikin yan gidan baki daya.


Haka muka yi ta ratsa manyan kofaffen gidan har muka isa babban gidan, Wani farin dattijo idan ka gan shi ba zaka zata ya kai shekarun shi ba, haka ya fito da wasu yan yara ƙanana, suna tari Hammah Mohan, sai murna suke, yana fitowa ya rungume Dattijon.
"Soja na Barka da dawowa, ina kewar markabu iyalin yaƙi, Barka da zuwa barden Baban shi."


"Nagode Abbu"
Sake juna suka yi, sannan ya kalli Baban shi yace mishi.
"Wannan Yarona ne Almamoon."


Murmushi yayi sannan yace.
"Khalil ya gaya min mu shiga daga cikin gidan."


Kafin kace me har an gama kome, kallon shi yayi sannan yace mishi.
"Khalil da yardaddun Yaran ka suka gyara gidan ka, sannan abincin daga mahaifiyar Khalil aka kawo maka, Baba na ina tsoron Allah ina tsoron mutanen da suke tare dani, daga kai sai Khalil nake iya yarda da ku don Allah ka saka ido akan rayuwar ku, yana da muhimmanci......
Naji wani yace yana niman kari 🤔🙄 ku gode kwana biyu ina jin daraja..... Ranar da na rashin shi ya shigo zaku ga aikin gaba gadi....4k wata cewa zata yi kamar kiftu....ta gama
#Mai_Dambu...
[7/27, 2:39 PM] RamlatArManga: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀


~The Journey of Destiny💔~


Mai_Dambu


Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....


BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI.


Juyawa yayi tare da yafito ni,da dan sassarfa na isa bayan su, suna tafiya ina take musu baya har cikin gidan, ba dan na je Dubai nayi kallon duniya ba, ba mamaki sai an daure ni, har falon Primer Ministan na shiga inda ya zauna tare da jan dan shi a jikin shi kamar zai mai dashi cikin shi.


A hankali na zauna a kasa, kallona Primer ministan yayi tare da cewa.
"Ga key din inda zaka zauna sabida na saka an ware maka maka shashin."


"Abbu dalibi ne kuma ina son dawo dashi nan da karatu sabida zan fi sanin meke yi." Da sauri na kalli bakin Hammah Mohan da yayi magana kamar bashi ba, domin yana gaban Abban shi kamar wanda yake daukar karatu wani irin nutsuwa yayi kamar ba shi ba.


"Ka tuntubi iyayen shi? Ko ka tuntubi yaron? Kar karfin ikon da Allah ya bamu yasa kayi tunanin kome mana," a hankali ya juya mishi buzanci.


Kallon Almamoon yayi da ya nutsu kamar baya gurin yace mishi.
"Tashi kaje gurin Harisu zai nuna maka inda apartment dina yake ka gyara kome kafin na iso."


"Toh" na ce tare da mikewa, na bar falon.
"Yaron nada cikar kamala, yana da nutsu. Amma bai da kwaɗayi?" Primer minister ya tambayi Mohan, gyara zama yayi sannan ya gaya mishi kome akan Yaron, amma bai gaya mishi akan jinsin shi ba, murmushi yayi irin na manyan mutane.
"Amma kai me ka gani akan Yaron ni dai a tunanina ka mai dashi makarantar shi, sannan ya koma hannun dangin shi, tunda jinya yazo maka."


Duk da sanyin Ac bai hana shi jin wani mugun zafi ba, kurawa Abbu idanu yayi sannan yayi kasa da kanshi.
"A'a dama zan cigaba da aiki na a maradin kawai, domin yadda kake ganin yaron ba wani wayo ne dashi ba, kuma akwai wani da yake takura mishi, hmm hmm kuma kuma kawai hannun kawai nake bukata."


Kallon mamaki yake mishi domin idan ya fahimta Mohan ba zai iya rabuwa da yaron ba. Sake kishingide yayi yana kallon shi kafin nan yace mishi.
"Toh ba laifi amma ba zaka zauna da namiji a gida babu mace ba, tunda ka sami lafiya idan Latifah tazo zamu san abinyi kafin ka koma Maradin."


Da mugun sauri ya d'ago kai, ganin fuskar abbu babu wasa yasa shi cewa.
"Allah yasa haka shine mafi alkhairi." Ya fada kamar zai yi kuka.
"Zaka iya tafiya kayi wanka idan yaso sai ka turo shi ya amsa maka abincin ka."


A hankali ya kara nutsuwa yana faɗin.
"Nagode Abbu" ya mike a hankali, ya fita, yana sauke ajiyar zuciya. Bai san lokacin da ya gwammace da ya zauna yayi ta gadin Mamoon har ya gama karatun shi.


Ina gama gyara ko ina yana shigowa, jallabiyar ce a jikina me hula. A hankali ya tako har inda nake tsaye, ya zaunar dani. Sannan ya durkusa a gabana.
"Wata satin zamu koma Maradi, sama an karb'a maka excuse, toh yanzun zamu koma kuma sunyi korafin kayi wasa da wancan zango, dan haka na mai da hankali sosai ganin na dawo da kai Niamey amma Abbu yaki dan haka idan na gama hutawa zamu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login