Showing 1 words to 3000 words out of 129098 words

Chapter 1 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

18

🖤

AMNA DA SAFNA

🖤



FREE BOOK 📓

Amincin Allah ya tabbata agareku da rahamarsa 'yan uwana. Littafin Amna da Safna littafi ne mai ɗauke



da abubuwa da dama, cakwakiya da sarkakiya, makirci da cin amana, zalunci da rashin imani, iantarwa da nishaɗantarwa. Kamar yadda Allah ya nufa na fara shi a sa'a, Allah yasa na ƙa re



lafiya.



GARGADI = Ban yarda kuma ban amince da a sauyamin littafina ta ko wace irin siga ba. Littafin AMNA DA SAFNA ƙirƙirarren labari ne, dan haka banyi sa don cin mutuncin wani ko wata ba, idan yayi daidai da labarin rayuwarka/ki to fa haka Allah subhanahu wata ala ya nufa.

SADAUKARWA= Na sadaukar da wannan littafi

ga mahaifana, ababen ƙaunata. Allah yaƙara muku lafiya da nisan kwana mai albarka Ameen.

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Tsira da aminci sun tabbata ga shugaban mu jagoranmu annabi Muhammad, da ahalin sa da sahabbansa.

🖤AMNA DA SAFNA🖤

Part 0️⃣1️⃣▶️0️⃣2️⃣

📱 Writing ✍🏼

Aisha G Umar {Mrs umar}👸🏽

Garin Kaduna Nasarawa,misalin ƙarfe 10am, na safiyar ranar laraba, wata kyakkyawar farar mata ce a zaune a gefen gado riƙe da jaririyarta, wacche yau taci suna Safiyya, akai wa laƙabi da (Safna) takwaran mahaifiyar ABUBAKAR MAI DARAJA. Kallon yarinyar take sosai tana jin yadda qaunarta ke ratsa duk wani ɓargo na jikin ta, murmushi ne ɗauke akan fiskarta. Juyowa tayi yayinda taji shigowar mutum.

""Anty Maryam su inna na kiran ki, wai kizo kuyi hoto"" Yarinyar da bata wuci shekara ashirin ba ta furta hakan. Amsawa tayi da ""To Zulfah zo kiɗau babyn sai muje"" ta howa tayi tana amsar jaririyar, tayi murmushi tace ""Anty Maryam kinsan me, Safna kama take da Dadyn ta sosai, "hmm Zulfah kenan haka kowa ke cewa amma nidai nasan dani take kama", dariya Zulfah tayi taƙara cewa "a'a anty badai musani ba konan gaba ta chanza" dariya Maryam tayi haɗi da miƙewa dan fita. Karar wayar Maryam ne ya tsaidasu, ganin numbern mijinta akan wayar, tace wa zulfah, "jeki da ita ina zuwa" da sallama ta amsa wayar.

"Inalillahi wa inna ilaihi raju'un" tafaɗi haɗi da sakin wayar ƙasa, ta durkushe akan capet tafara rusan kuka mai taɓa zuciya.

Da sauri Zulfah ta yo gurin cikin tashin hankali, "anty Maryam me yafaru me aka gayamiki a wayan?" Batace da ita komai ba sai aikin kuka da take, ganin bata amsa ba yasa Zulfah yin waje riƙe da Safna a hannu. Dawowa tayi tare da Inna yayar mahaifiyar Maryam. Zuwa tayi kusa da Maryam ɗin ta da fata haɗi da durƙusawa kamar yadda Maryam ɗin tayi.

"Maryama wai meke faruwa haka dan Allah ki daina kuka, kisanar da mu kin samu cikin damuwa?" Da ƙyar ta iya tsaida kukan nata ta furta "Inna Abubakar, Abubakar ne" ta kuma fashewa da kuka. Cikin tashin hankali Inna ta ce "Abubakar me, meyasa meshi?" Zulfah ta ce "Inna kiranta akayi a waya kuma ni banmasan me aka sanar da ita ba," taƙarasa faɗi idonta na kawo kwalla. Cikin damuwa Inna ta ce, "ɗauko wayar ki duba waye ya kirata?" nan mutane suka fara taruwa.



Cikin tashin hankali ta shigo ɗakin tana kuka, wanda duk mai hankali idan ya dubeta da kyau yasan ba kukan gaskiya takeba. Gabaɗaya mutanen ɗakin suka dawo da idon su gareta, "lafiya Zainab ko kinsan abunda ke faruwa ne?" Inna tafaɗi tana jiran amsa Zainab ta ce, "eh nasani Inna yanzu Abban Marwan yake sanar dani Yaya Mai Daraja yayi hatsari kuma ko gawansa ba a gani ba." Gabaɗaya sukasa salati banda Maryam da ta karawa kukanta sauti.

................Taƙaitaccen tarihin Mai Daraja.

Asalinsu fulani ne zama ne yakawo mahaifinsu IBRAHIM kaduna anan ya haɗu da mahaifiyar su HALIMA wanda ita kuma bayerabiya ce, a hannun ƙanin Babanta ta girma inda yake mata riƙon sakainan kashi. Cikin ikon Allah suka haɗu har sukayi aure. Sunan MAI DARAJA ya samo asaline daga mahaifiyar sa, ganin yadda yataso yarone mai kyauta da kuma sanin yakamata, baya da kyashi ko kaɗan, ganin halayansa masu Kyau, hakanne yasa mahaifiyarsa ta sanya masa wannan suna MAI DARAJA. Su biyu kaɗai iyayensu suka haifa Abubakar ne babba sai Jamilu, Abubakar yaba Jamilu shekara huɗu. Shekaran Abubakar goma sha biyar Jamilu sha daya iyayensu suka rasu, mahaifinsu ya fara rasuwa shekara ɗaya tsakani mahaifiyarsu tabi bayansa. Abubakar mutumne mai tausayi da jajir cewa gurin neman halak, shi yacigaba da kula da ƙaninsa, yana matukar ƙaunar ƙanin nasa sosai, duk abinda ya samu baya mantawa da shi. Baiyi karatu mai tsawo ba dan yafi mai da hankali akan ƙaninsa, shi dai aikinsa ya jajirce gurin neman kuɗi. Sunan Mai Daraja yacigaba da tasiri gun mutane domin mutumne shi mai son mutane ne, ga tai mako babu wanda baya yabonsa hakan yasa yaƙara zama Mai Daraja a idon mutane.

Cikin ikon Allah kasuwancin da yafara a hankali ya haɓaka. Sanda ya mallaki kamfanin sarrafa auduga biyu nasa na kansa daga bisani yayi aure. Wanda aka ɗaura aurensu rana ɗaya da ƙanin nasa. Inda ya auri Maryam, shikuwa jamilu ya auri Zainab. A cikin ƙayataccen gidan da ya gina musu suka zauna, gida da yaci sunan sa gida, dan ba ƙaramin kuɗi akayi asarar su a ginin ba, ɓangare uku ne gidan, amma sai dai a babban ɓangare suke tare. Gidan samane mai hawa ɗaya amma ya kasance mai girman gaske.

Sai dai Mai Daraja bai samu haihuwa da wuri ba, saboda sau biyar Maryam na samun ciki amma yake zubewa, gashi shi mutum ne mai son yara matuƙa, duk da likitoci basu samu taƙamain sanadin ɓarin ba kawai dai sun ɗaura su akan magani. Yayin da Jamilu kuma ya haifi yara hudu maza uku mace ɗaya. Bayan rokon Allah da suka sa gaba, cikin ikon buwa yi gagara misali, Maryam ta samu juna biyu. Duk da cikin baƙaramin wahala ya bata ba, dan har fargaba suke kada shima su rasa shi. Haka dai har Allah ya nufa ta haifi 'yarta kyakykyawa. Baƙaramin murna Mai Daraja yayi ba, ashe dai baida tsawon ran kasan cewa da ita..........

CIGABA

Kauyen TAKORI. Kauyene dake cikin garin Kaduna. "Amma nayi mamaki sosai Habiba, wai dama ana haifan yaro ko shekara bai cikaba a kuma haifo wani, kuma duba kwayar idon yarinyar ruwar toka, irin na matar akwatin talebijin din laure, kinsan mijinta yasai mata akwatin talebijin a birni, amma abin da mamaki wallahi kuma."

Bata kai ga ƙarasa maganar tata ba, wata matashiyar tsohuwa ta katseta da faɗin, "haba Hanne wai ke ba kya gajiya da magana ne, tun ɗazu kike cewa abin mamaki to ko jaa kike da ikon allah ne?" Hanne ta ce, "a'ah Mamma nina isa?" "To ni naga maganar taki tayi yawa ne", Mamma ta faɗi hakan tana maida dubanta gun Habiba ta ce, "Biba zo muje ɗaki mu tattuna akan sunan yarinyar nan." "To Mamma" Habiba tafaɗi cikin girmamawa, tamike tayi ɗaki. Juyowa Mamma tayi gurin Hanne ta ce, "dama hura mana wuta kikayi akan surutun nan da kike kafin sauran mutane su hallara," Hanne ta amsa da "'angama hajiya mamma."

Acikin ɗaki "Yanzu Baba wani suna kake ganin za'a sawa yarinyar nan?" Baba yace "duk sunan da kika zaɓa dai dai ne Mamma haka za'ayi". "to nidai dama sonake asa takwaran mahaifiyar Biba mutumiyar kirki Amina." Sannan ta juya taga Habiba ta ce, "hakan yayi Biba?" murmushi Habiba ta ɗan saki domin taji daɗin jin hakan, daman tana da burin hakan. Baba yace "hakan yayi sosai Mamma."

An raɗawa yarinya suna AMINA mahaifinta hussaini wanda ake kira Baba yayi mata laƙabi da (AMNA)

Bayan suna da kwana uku. zaune Mamma take a tsakar gida kan tabarma, rike da yaron da baifi wata goma da haihuwa ba, tana mishi wasa. Da sallama Baba ya shigo gidan da murmushi akan fiskarsa Mamma ta ce, "Baba an dawo daga masallacin?"

"Eh Mamma sai dai na la'asar kuma, tare kike da angon naki?" Yafaɗi haɗi da jawo kujera ya zauna kusa da ita.

Mamma ta kuma cewa "hmm Mubarak ɗan rigima ba ai ni tini na sake shi gwaramin nariki kishiyata Amina ya fimin." Dariya Baba yayi sannan yace "haba dai Mamma duk fitinan kishiyarkin nan amma kikoma gurinta?"

""Eh mana yafimin ai"" taƙarasa faɗi fiskarta ɗauke da murmushi.

Ganin yayi shiru sai ta ce, "da alama akwai magana a bakinka faɗamin ina jinka?. Kas da kai yayi, sannan yace, "dama Mamma maganar tafiyar nan ne, nace ina fatan kuna shiri?" Daɗe fiska tayi tafara zuba masifa "Baba kasani banason takura, tunda na amince zanje, miye na takura kuma, sai in fasa ma haka kawai." Jin yadda ta fusata yasa da ƙyar ya shawo kanta, dan yasan tsohuwar tasa sarai, ba ƙaramin aikin ta bane ta chanza ra'ayi, dan shi kuwa yanzu bazai so hakan ba.

...............Labarin wannan family a takaice.

Su ɗin hausawa ne. HUSAINI shi kaɗai ne, ɗa ɗaya tilo awurin iyayensa.

Duk da a Ƙauye suke amma iyayensa sunyi matuƙar ƙoƙari gurin inganta tarbiyyarsa fannin addini da na boko. Don su basu kasance cikin mutanen da ke kallon boko matsayin ɓata tarbiyya ba. Sun turashi cikin birni yayi karatu. Burinsa shine ya zama ɗan jarida don shiga ko wani lungu da saƙo ɗaukan rahoto da kuma tallafawa gurin kama masu laifi. Dan yayi yaƙinin ba aikin police ko soja bane kaɗai suke da hakkin kama masu laifi, 'yan jarida ma suna da alhakin kama mai laifi don a hukunta shi. Burinsa kuma ya cika, domin kuwa ya zama babban ɗan jarida, wanda ake alfahari dashi. Ya haɗu da Habiba ne a gurin ɗaukar wani rahoto. Haka har Allah ya ƙaddara aurensu suka zauna a cikin gari yayinda Mamma take ƙauye, domin kuwa babu yadda Baba baiyi ba dan ya dawo da Mamma wurinsu, amma ta ce ita bata san wannan ba. Allah ya azurtasu da haihuwa yayinda suka haifi yaronsu namiji suka sa masa suna Mubarak, wata goma da haihuwarsa suka sake samun haihuwa. Dai dai lokacin da a kayi masa transfer zuwa Gombe da aiki. Hakan yasa ya kawo Habiba gurin Mamma bayan ta haihu. wanda hakan ya kawo surutai a ƙauyen Takori.

Da ƙyar Mamma ta amince da komawa Gombe duk da itama baza taso tayi nisa da ɗan nata ɗaya tilo ba...............

CIGABA

BAYAN SATI DAYA

Haka sukayi shirye shiryen su sukaiwa 'yan uwa da abokan arziki sallama, yayinda wasu suke jin inaama sune Mamman. Bayan isansu garin Gombe. Gida ne mai kyau duk da ba irin na shahararrun masu kuɗi bane. Amma amatsayinsa na babban ɗan jarida gida ne na musamman a ka tanadar masa. Gidan na da madaidaicin girma akwai ciki biyu da falo a haɗe sai ɗakuna ɗadɗaya guda biyu a tsakar gida, sannan ga kitchen mai girma. Basu da matsalar ruwa dan akwai fanfo kota ina.

KADUNA

Hatta mutane sunji mutuwar Mai Daraja sosai, kowa sai faɗan alkhairin sa yake.

Tun bayan mutuwar mijinta, duniyar tayi mata zafi, tarame kamar wacce tayi wata da watanni tana rashin lafiya.

Jamilu ya nemi da ta cigaba da zama tare dasu ta girmar da 'yarta cikin kulawa. Inna ta amince da Maryam ta zauna a gidan har ta yaye Safna. Amma bata yarda da ta zauna a gidan din din din ba, tunda ba tsufa tayiba in Allah yakawo mata miji sai tayi aure. Jamilu baiji daɗin hakan ba.

Bayan Maryam tayaye Safna, jamilu ya bijiro mata da maganar aure. Kowa yayi mamaki yadda tayi saurin amincewa. Zainab tafara tada hankalinta, akan me jamilu zai mata kishiya? kishiyan ma Maryam, ya akayi sai kuma sai ta bari.

An daura auren Jamilu da Maryam. Mai Daraja bashi da wani ɗan uwa na kusa, hakan yasa Jamilu ya kasance akan kowani fanni na dukiyar sa. Dama hausawa sunce faɗuwar wani tashin wani.

SHEKARA BIYU 2

Tun tasowar Amna yarinyace mai kazar kazar, gata da fitina ga surutu karambani duk ta haɗa, sai faɗa ita da ɗan uwan nata, indai suka zauna tare, duk da a lokacin shekara biyu take da.

Safna kuwa yarinyace shiru shiru. Koh dan gwarancinnan na yara bata cika yiba, gashi babu abinda yake shiga tsakaninta da yaran Zainab sai mugunta, indai zasu ganta sai sun mata wani abun, musanman ma macen, Yazeed mai bin babban ne kawai keɗan ragamata. Sai dai Jamilu wanda suke kira Daddy yana kulawa da ita sosai.

BAYAN SHEKARU ASHIRIN 20.

Abubuwa da dama sun faru. Ciki kuwa, mahaifiyar Safna Maryam, bata iya magana sannan ga jikinta ko motsi mai kyau ba yayi. Tun ana neman mata magani har ambari. Anyi na bokon anyi na islama, mai makon ya ragu saima abinda yaƙaru. Abu kaman wasa ya zama gaske. Har shekaru suka shuɗe.

Tafiya take a cikin tsadadden jami'a mai suna, AA Royal University Kaduna. Kyakkyawa ce ajin farko. Wani dan tabo dake gefen bakinta baƙi. Farace tas Ita ba siririya ba kuma bata da jiki, sannan tana da dan tsawo amma basosai ba, gata da kyakyawan manyan ido, Idonta fari tas yayinda kwayar idonta kuma baƙi, ga siririn hancinta, ƙasa kuma ƙaramin bakinta. Sanye take da doguwan rigar atamfa, kalar purple da gelenta baki. Tayi matukar haɗuwa.

Tafiya take cikin nutsuwa. Murya tafara ji a bayanta, "Safna ke Safna tsaya mana." Dakatawa da tafiyar tayi daidai isowar mai kiran naata. Duba da yadda take fitar da numfashi sai ta ce da ita "Raheena are you ok, ya naganki haka kina fitar da numfashi kamar wacce tayi gudu?" Taƙarasa maganar cikin sanyin muryarta. "Dole kice haka, gudun nayi mana, taya zaki tafi ki kyaleni nayi ta dubaki, ashe ke kinyi tahowarki why?" Raheena ta karasa faɗi tana haɗe fiska cikin fishi.

Murmushi Safna tayi hakan yasa dimple ɗinta lotsawa ta ce, "ni ya kamata inyi fishi ai, kinsan ni bason surutu nakeba, amma kika samu wuri keda wa'ƴanchan kukai ta surutu kamar gidan radio to me zaisa bazan taho inbarkiba?" Raheena ta ce, "toh naji, nidai karki ƙara tafiya kibarni ƙawata, da ƙarfi da yaji dai nima zan zama miskila."

______________________________________________________________________________________________

Part 0️⃣3️⃣▶️0️⃣4️⃣

Ƴar harara Safna tayi mata ta ce, "nice miskila?" Dariya Raheena tayi, sannan ta ce "sorry my besty, yanzu dai muje ko." Murmushi kawai Safna tayi mata tana cigaba da tafiya, bin bayan ta tayi, suka jera suna cigaba da tafiya. Raheena ce takara faɗin "Besty ya lecture ɗin yau, wallahi ya cazamin brain sosai," hararan ta Safna ta ƙarayi akaro na biyu. "shiyasa kika manta dashi kika samu gurin surutu ai"

Raheena ta ce, "bama wannan ba ina zamu gida ne?" Karamar ajjiyar zuciya Safna ta sauke sannan ta ce "a ina kuwa zamu gida inba a adaidaita-sahu ba, hmm ni bansan lokacin da zaki zama mai ƴanci a gidan ku ba, mahaifin ki mai kuɗi amma yadda talakawa suke rayuwa haka kema kikeyi Safna"

murmushi mai ciwo Safna tayi daga bisani tac e, "Raheena kenan, kin riga da kin san komai ni ba kowa bace a gidan mu, Dady ne kawai mutumin dake ganin darajar mu, daga ni har Ammu na, itama da kanta tana buƙatan kulawa". Tafaɗi daidai fitowar su daga cikin makarantar. Raheena ta dafa ta haɗi da faɗin "hakane ƙawata ubangiji Allah yaba Ammu lafiya". "Ameen" suka ambata a tare.Taran adaidaita-sahu sukayi suka shiga.

Kafinsu zama ƙawaye an ɗau lokaci, domin Safna ta ɗauki Raheena me yawan surutu, da suka fahimci juna sai suka zama aminan juna na ƙwarai. Duk da Raheena bata iya zama shiru da Safna, haka za tayi ta zuba. Wani lokaci ta amsa mata ɗadɗaya. Ko kuma ta ce mata "uhmm ko a'a".

Daidai lokacin da aka kira Sallah. Safna aka fara saukewa a layinsu first GRA, sallama sukayi cike da kewan juna sai gobe kuma.

Tafiyarta tacigaba dayi cikin nutsuwa har izuwa ƙerarren gidan da ya ƙara shan gyara, ya ƙara haɗuwa fiye da da. ƙwanƙwasa wa ta fara, babu ɓata lokaci mai gadi ya buɗe gate ɗin.

Da murmushi à fiskarta ta gaishe da tsohon mai suna Hambali cikin ladabi. Shima amsawa yayi cikin fara a. Yarinyar tana da tarbiyya mai kyau, ita kaɗaice cikin yaran gidan take ganin darajar shi, sauran kuwa ko sannu basa ce masa, sai dai ma subishi da masifa inbai buɗe musu ƙofa yayin fita ko shigar da motan su ba, duk da tsoho ne shi, shiyasa yake bin Safna da fatan alkhairi a rayuwar ta.

Komawa gurin zamansa yayi, yayinda ita kuma ta nufi hanyar shiga ciki. Shigarta ƙayataccen falon keda wuya sai ji tayi an fincikota, gabaɗaya takardun dake hannunta suka zube, ɗaga ido tayi cikin firgita, tana duban wanda yayi mata wannan abu.

"Dama nace zaki dawo kisameni, wato harni zance ki kawomin tea da safe amma kiyi wucewanki saboda kin isa ko?" Ya ƙarasa faɗi yana saketa ƙasa, cikin firgita ta ce, "Yaya Marwan wallahi sai da na kawo maka before na tafi" tafaɗi da rawar murya. Zainab wacche suke kira da Hajiya ta sauko daga upstair, ƙarasowa inda muke tayi, da harara ta bini sannan ta ce, "Rabu da ita wurine ta samu saboda na ƙyaleta tana zuwa makarantar shiyasa, tana abinda takeso". Marwan yace "Hajiya nunawa take tafi kowa son makaranta, ko Ruki bata mai da hankali kamar yadda wawuyar nan takeyi, ince ta kaimin tea amma sai zuwa nayi naga cup emty". "Rabu da ita makarantar zan sa tabari, danni na daɗe da son ta bar zuwa, ta dawo aikin gida" hajiya tafaɗi haka.

"Ya Allah" Safna tafaɗi a zuciyarta, a fili kuwa ta ce,

"Wallahi na kai ban san wanda yasha ba", ɗakinsa ya wuce, hajiya kuma ta zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login