Showing 12001 words to 15000 words out of 129098 words
Chapter 5 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
fara shafawa, sai da ta tabbatar yayi yadda ya kamata sannan ta kai wa Habu, saboda ba tason haɗuwa da Marwan ɗin.
ɗaki ta koma ta zauna a kan gado, kusa da Ammu da ke bacci hakan yasa ta jin kewa, ba waya take rikewa ba bere ya ɗau ke mata kewa, ɗauko Alqur'ani tayi tafara karan tawa cikin muryar ta me daɗin sauraro.
Ta ɗau awa uku, ba tare da ta dena ba, Ruki ce ta bankaɗo Ƙofar ɗakin ba tare da ko sallama ba dama al'adar su kenan' saida takai aya sannan ta juya gun Ammu, ganin bata farka daga bacci ba yasa ta sauke ƙaramar a jiyar zuciya, maida kallon ta tayi gun Ruki da ke yi mata kallon banza, tana kallon ta, ta kuma maida kan ta kan Qur'anin tana ci gaba da karatu.
Wani baƙin ciki ne ya bugi zuciyar Ruki, azuciyar ta take faɗin "wato yarinyar nan girman kanta ne yayi yawa fa, saboda tsaban iskanci ni zata sha re?" A fili kuwa tace "to mai girman kan tsiya, Marwan ne ke kiran ki, kuma kina ɓata lokaci zaki sha jibga wallahi" tana gama faɗin hakan ta fice daga ɗakin.
Zuciyar ta ne ya buga jin Marwan na kiran ta to me kuma? Me zai sa ya neme ta bayan ta gama masa aikin da ya bata? To ko don ba ita ta bashi da kanta bane?.
Ijje Alqur'anin tayi ta sa himar ta fito, ganin fitar Ruki yasa ta yin hanyar fita falon saboda tasan a can yake, domin ta san Ruki sai ta ji dalilin kiran da akayi mata, dan tasan ba banza ba, tsayawa zatayi in ta ga amma Safna abun mugunta sai tayi ta dariya, haka take da ma.
Nufan inda ta gansu tayi zuciyar ta cike da far-gaba, ta ɗaura idanun ta kansa da tin ɗazu yake mata kallon tsana, wanda dukkanin su suke yimata wannan kallon inka ɗauke Dady da kuma Yazeed.
"Na'am Yaya Mar..." kan ta kaiga ƙarisawa, ya wanke mata fiska da mari wanda ya sata yin baya baya tana ƙoƙarin fa ɗi, "ke Safna wai meyasa kikayi mugun raina nine? Saboda ina ragamiki yasa haka ko? Ok Today I will teach you mindfulness".
Ƙollan da ya cika mata ido ta ma tso ya dira ra kan kumatun ta, "yaya Marwan bansan me nayi maka ba wallahi" ta ƙarashe tana hawaye, yace "ni kike cewa bakisan laifin da kikayi min ba?" Yafaɗi yana maida kallon sa gun Habu da ke gefe ya cigaba da cewa, "kai ina ta kalmin yake?" Jiki na rawa Habu ya ɗauko, saboda bayason yayi a bakin aikin sa.
Ijje Takalmin yayi a gaban Safna kamar yadda Marwan ya umurce sa, ya wuce gefen su, zaro ido waje tayi ganin Takalmin da ta sha gogewa ɗazu ya zama karmar an ciro sa daga bakin Kura, yadda ko ta ina na jikin yake da ƙura harda wani a lamu kamar ansa Wuƙa an caccaka shi, saɓanin ɗazu da yake ta walwalin yadda yaji maiƙo.
Yayin da ita kuwa Ruki kewa Safna dariyar mugunta, "Saboda tsaban renin wayo, dubi yadda kika mayarmin da shoe to yau zaki san ni Marwan kika raina, Frog jump zaki fara yi cikin ranar nan kuma sai kinyi one thousand tukunna za ki bari, Is that your punishment" cikin tashin hankali ta dube shi jin wai tsallen kwaɗo zata yi, abinda ke matuƙar bata wahala, "Wallahi ba haka na ba Habu takalmin nan ba, ka tambaye sa?" Ta ƙarashe maganar cike da damuwa.
"Ke banason iskanci za kiyi abinda na sa ki kokuma sai kin ji a jikin ki before? " Cewar Marwan harda zare mata ido, share ƙananun hawayen ta tayi, da ma tayi zaton haka daga gare shi, ƙarajin maganar sa tayi yana cewa, "Ruki ki tabbatar da ta kai adadin da nace sannan ki rabu da ita" yana gama maganar ya wuce ciki.
Inalillahi wa inna ilaihi raju'un ta faɗi a zuciyar ta, tana mai ƙa ra jin Za fin abu-buwan da yaran hajiya ke mata, Ruki ɗauko abinda za ta zauna tayi, da murmushin mugunta take bin Safna dashi, zama tayi tana faɗin "baza kiyi bane sai na kirashi?" Bata tanka mata ba ta fara yi.
Tsawon wani lokaci, gaba ɗaya ta gaji zufa sai tsatstsafo mata yake idanuwan ta duk sun canza kala, hawaye kawai suke fitarwa, jin Cinyo-yin ta take kamar ana sassara mata su, Ruki kuwa danna wayanta kawai take, inta kalle ta sai ta kwashe da dariya, ta kuma maida kanta ga wayan, domin kuwa ita ta ƙulla mata wannan.
Ana cikin hakan Baba Hambali yaji ƙarar hon, tun kan yakaiga ƙa risa buɗewa Yazeed ya danno hancin motar ciki, yanayin parking ɗin motar ya fito, sanye da wando Black jeans da kuma t-shirt blue ba ƙaramin haɗewa yayi ba, yayo gurin da Hambali yake dan yin masa masifa na rashin buɗewan da baiyi da wuri ba, Saidai ya da kata da zuwa wurin sa ganin abinda Safna take yi sannan ga Ruki gefe kenan ita ta sa ta,
A hasale yafara takawa zuwa inda suke, babu zato babu tsammani Ruki taji saukar Ma ri a kuncin ta, ƙara ta saki haɗi da yin tsallen 'yan China tayi ge fe, itama Safna da katawa tayi tana kallon inda Ruki take, jin ƙarar marin da akayi mata, ba tare da sanin yaushe yazo wurin ba, don hon kawai taji.
"Yazeed mari na fa kayi me nayi maka?" Ta ƙarashe faɗi tana sakin kuka, shima amsa ya bata da cewa, "Saboda ke ga ki shegiya za kisa mara ga lihun nan frog jump akan me?" Wani irin takaici ne ya cika Safna, ya kira ta da mara ga lihu amma yake cewa akanme aka sata frog jump.
"To ai bani na sata ba, Marwan ne kuma yace sai tayi sau dubu sannan ta bari" nanma ta ƙara faɗi tana zunɓuro Ba ki, yadda ta zunɓuro baki yasa shi ƙara kai mata tagwayen maruka, yana ce wa "ni kike zunɓurowa baki, yanzinnan sai in tattakaki anan stupid, shi kuma Marwan ɗin baida hankali ne da zaisa mutum frog jump kuma yace sai tayi thousand? Se kace dabba yasa".
Ruki kuwa sai rusan kuka ta keyi na zafin marin da yayi mata, ba'abin ta mai da mai ba, ya tattaka ta kamar yadda ya faɗi ƙaramar aikin sa kenan, "me sunan ki ma?" Cewar Yazeed yana kallon Safna da ke masa kallon ɗar-ɗar, azuciyar ta kuma tace "wai me suna na, koda yake zai iya mantawa tunda ba kiran sunan yake ba".
"wuce ciki" kawai ya faɗawa Safna, shima yana yin hanyar shiga, "to mezan cewa Marwan ɗin" Ruki ta tsaida shi da faɗi cikin muryar ta da ke nuna kukan da take bai ƙare ba, kallon da ya jefa mata ne yasa ta yin shiru, Shiga falon yayi Safna na rufa mai baya, tana tafiya da ƙyar sabida yadda ƙafafuwan ta ke yi mata zugi.
Yana shiga bai tsaya a ko ina ba sai a ɗakin Marwan, zaune gefen Bed ya tadda shi yana latsa waya da alama chat yake, dago idon sa yayi dan ganin wanda ya shigo Masa ɗaki, bazai yi mamakin rashin sallama ba saboda dukan su haka suke, sai dai kaji ƙarar dirar su.
"What kind of person you are Marwan? Akan me zaka sa yarinyar nan punishment me wahala?" Yayi masa maganar cikin ɗagun murya, Miƙewa Marwan yayi yana kallon ƙanin na sa da yaba shekara biyu da haihuwa cikin ɗagun murya shima ya fara magana, "Yazeed be careful with me! Har zaka zo kana ɗaga min murya akan kuca kan yarinyar nan akanme?"
Jin alamun masifa a ɗakin Marwan yasa Hajiya yo wa wurin, itama antayawa kawai tayi tana faɗin, "ku meyasa koda yaushe kuke sa'insa tsakanin ku ne?" "Hajiya wai ni Yazeed ke ɗagawa murya akan Safna" mayarda duban ta tayi kan Yazeed, shima cewa yayi, "Hajiya saboda tsaban mugunta sa Safna tsallen kwaɗo yayi, harda cewa sai ta yi thousand sai kace ba mutum ba? Kinga yadda ta gala-baita kuwa?".
Kallon Yazeed kawai Hajiya keyi, tana ƙara jin haushin Safna, ita tsoronta ɗaya kada wata rana Yazeed ya bijiro musu da maganar yana son Safna fa, saboda ganin abubuwan da yake wani lokaci anya kuwa? Ta tambayi kanta, afili kuwa tace, "Yazeed intambaye ka mana? Wai me ruwan ka da sheɗaniyar yarinyar nan ne?".
Kallon ta yake da mamakin tambayar, "Hajiya me kike nufi ne?" "Gani nayi kana yawan shishshigewa lamarin ta ne" "tambaye shi dai Hajiya" Cewar Marwan, a hasale Yazeed yace, "wai me kuke nufi ne?" Kawai ya furta haɗi da ficewa daga ɗakin cike da haushin abinda suka ce, daga yin magana akan musgunawar da Marwan yayi wa Safna sai su ɗauki wani tinani a ransu, nufi ma suke ko yana Son ta, to mema zaiyi da ita mtsww
Da ƙyar Safna ta iya ƙarisawa ɗaki, jikin ta Sam baya sabo da wuya, inba haka ba abinda Hajiya da 'ya'yanta suke mata tun tana ƙarama ai yaci zuwa yanzin ta dena jin zafin duk wata wahala, a ɓangare guda kuwa, tayi mamakin yadda Yazeed ya taimake ta duk da shima zai iya sata fiye da hakan saida ta ma tse Cinyo-yin ta da ruwan ɗumi tukunna taji ɗan dama dama, ga shi gobe weekend ranar Aikin ta.
#Hmm lallai, to nima dai nace Yazeed anya kuwa?
To koma dai menene zamuji a gaba.
Kukasan ce dani a part na gaba.
______________________________________________________________________________________________
Part 1️⃣5️⃣▶️1️⃣6️⃣
BAYAN KWANA UKU.
BABA, duk wani shirye shirye ya yi dan saura kwana uku tafiyar sa, gaba ɗaya mutanen gida sunyi mamakin tafiyar na sa, da suka tambaye shi sanadin tafiyar? sai yace musu, zuwa ziyarar mutanen Takori zaije yi, saboda tsawon shekarun nan babu wanda yakai ziyara.
yana zaune a ɗakin Mamma suna hira nan Mamma take ce masa "ina kai ne ka hana mu zuwa ziyarar? Sai yau kuma kace za kaje?" "Hakane Mamma amma ki fahimce ni ziyara nake son kaiwa, kuma kina faɗamin ako da yaushe zumunci na da kyau".
Kallon sa tayi da kyau sannan ta ƙara cewa, "to kaɗau kemu muje tare mana, ya kamata muma muje, nayi matuƙar kewan su sosai" ta ƙarashe maganar tana ƙoƙarin tina wani abu, "Mamma yanzu dai kiyi haƙuri sai wani lokacin, nima nasan cike kike da kewan su, amma yanzu ki amince min inje kinji?"
Haka dai ya lallaɓa ta ta amince, tabbas shima da kan sa baya son zuwa Garin Kaduna ko kaɗan, saboda wani babban dalili da ya barwa kan sa, sai dai baiji cewa zai bar yin wannan binciken ba.
WASHE GARI.
Abokin Baba Tukur ne yazo, iso yayi masa izuwa falo, bayan gaisuwa, suka fara hira "Alhaji Hussaini Baba da alama har yanzu kana da ƙwarin guiwa sosai, ranar Alhamis ɗin kenan zaka tafi?" yayi maganar cikin ɗan zolaya, murmushi Baba yayi haɗi da faɗin "ai ka riga da kasanni bazan sadaukar ba har sai nayi nasara".
Tukur Abokin Baba ne tun farkon zuwansu garin Gombe, sun shaƙu sosai hakan yasa basa ɓoyewa junan su sirrin su, sai da ya sauke ƙaramar ajiyar zuciya sannan yace, "to yanzu ai na zaka sauka idan ka isa? Ko hotel zaka ka ma?" Tukur yayi masa tambayar.
Sai da Baba ya gyara zama sannan yace "a ah ba ka ma hotel zanyi ba, akoi wani aboki na da ya ke garin, na yi masa magana kuma ya bani masauki a ɗayan gidan sa, sabida ba na son na sauka a hotel gudun wata matsalar" "da kyau tsarinka na burgeni Aboki kasan kan aiki" Cewar Tukur. Wannan zamar sun ƙare shi ne da hirar abinda Baba zai fara yi idan ya tafi.
YAU TAKE RANAR TAFIYAR BABA, gaba ɗayan su babu mai farin ciki da tafiyar ta sa, sai dai dan ya zama dole, abokin sa Tukur ne yazo yi masa rakiya, bai wani ɗau kaya da yawa ba iya ka ƙatuwar jaka ta ra ta yawa ya ɗauka.
Gaba ɗaya kallon sa suke kamar mai musu ban kwana, Fatan alkhairi suka bisa da shi, sukayi masa rakiya har izuwa ƙofar gida inda Motar Tukur take, saboda shi zai kaishi Tasha, juyowa suka yi bayan sun yi masa Addu'oi, su Baba kuwa tsayawa sukayi sunayin magana.
Kowa da sanyin jiki ya shigo gidan, Mamma ce ta shige ɗakin ta, Ummee ma haka, Amna da Mubarak ne kawai suka jingina da bango kamar masu tinani, Ummee ce tafito riƙe da waya a hannun ta tana faɗin "Amna yi maza kikaiwa Baban ki wayar sa ya manta da ita, Allah yasa basu wuce ba" Amsa Amna tayi da sauri tayi waje dashi.
"Allah yabaka nasara akan Ƙungiyar POSPA Aboki na, dan Allah duk abinda ake ciki ka rinƙa sanar da ni" "insha Allah amma yanzu ka kai ni in samu mota da wuri ko" Cewar Baba yana Murmushi, Amna da ta tsinka yi maganar na su ta shiga tinani, wa tsar da tinanin tayi da kiran sunan sa.
Tsaida shiga motar sukayi Baba yana kallon inda take, saurin zuwa inda yake tayi, "Amnan Baba lafiya kuwa?" yayi mata tambayar, "ka manta wayar ka" ta faɗi tana miƙa mai wayar, ansa yayi yana faɗin "ashe na manta shi, kuma ko kula banyi ba, thank you daughter" "yaushe zaka dawo Baba" ta kuma yi masa tambayar fiskar ta cike da damuwa.
Murmushi yayi mata yana cewa "karki damu Ƴata bazan daɗe ba, yanzu ki koma gida nizan wuce lokaci na wucewa" Murmushi tayi masa, tana tsaye a wurin har ya shiga suka wuce, sha fo ruwan da taji ya zuba mata kan kumatu tayi, "Hawaye?" Ta furta cike da mamakin yau hawaye ya fito daga idon ta, yaushe rabo.
Sai ta danganta hakan da ko don tun tasowar su bai taɓa yin tafiya kamar hakan bane? Sha re hawayen tayi ta juya zuwa Gida, Wunin ranar yin sa sukayi cikin sanyin jiki, duk da sunji isar sa lafiya.
Baba kuwa da isar sa, Abokin sa Hamza yazo ya ɗauke sa zuwa Gidan sa na biyu bayan wanda iyalan sa suke, Gida ne ƙarami, bayan tarbar da yayi masa yayi masa sallama ya rabu da shi dan ya huta, sai dai maimakon Baba ya huta, sai tashi yayi ya ɗauko jakar sa, ya firfito da duk Takardun da ya je dasu yana duba su, dan fara bincike zuwa gobe.
Kasa bacci da wuri Amna tayi, tana tinanin me yasa Baba ya ɓoye musu manufar tafiyar sa? shin wace ƙungiya taji suna magana a kai?
WASHE GARI.
Yau lecturen rana za suyi, hakan yasa su shiryawa bayan sallan Azahar suka fice ita da Mubarak, suna cikin napep Mubarak yake yi mata magana, "Amna you know what?" giɗa masa kai kawai tayi a lamar a ah, ba tare da ta ce komai ba, cigaba da magana yayi, "remain one year mu gama school, nifa na ƙosa lokacin yayi, sannan bayan mungama na samu aiki a lafiyayyen company ina zaune a ƙayataccen office ƙafa ɗaya kan ɗaya habawa ai babu wani shege wallahi" ya ƙarashe maganar yana mai kallon kan sa a wannan yanayin yana murmushi.
Dariya sosai Amna tayi harda ƙya-ƙya tawa tana rufe Baki, kallon ta Mubarak yake da mamakin me yasa ta dariya? "Ke wai me yasa ki dariya? Ko wani abun kika gani ta waje?" Tsagaita dariyar tayi tana faɗin "You are the one who's make me funny, kai matsalar ka kaɗan ne ma, kawai ka tsinci kanka a company, kamar bakasan wuyar samun aiki a ƙasar nan ba, kuma a iya matakin karatun ka kake burin zama a babban office" ta ƙarashe da murmushi.
"Haka ne nasan ƙasar nan ta mu, mutum ya gama karantu amma ya zama ɗan zaman banza, to amma ke mene ne burin ki? koda nasan bai wuce kice soldier ba" "tabbas a baya nafi son aikin soja, amma tunda Baba ya nuna min rashin amincewar sa akai na sallama, a yanzu bani da tabbacin aikin da nake son yi sai nan gaba".
Daidai lokacin da aka sauke su a ƙofar jami'an su, sa kai sukayi cikin makarantar suna ci gaba da hira "wai Mubarak kasan dalilin tafiyar Baba Kaduna kuwa?" Tayi masa tambayar dap da zuwa a jinsu, "eh mana ina Ƙauyen Mamma za shi?" Ya faɗi yana amsan littafin sa, ya wuce aji, ajiyan zuciya kawai Amna ta sauke itama tayi na su ajin.
Gurin ƙarfe 2:20 aka gama musu lecture, sabida ba wani daɗe wa sukayi ba, gaba ɗaya ƙawayen ta sun fita sun bar ta, ba tada niyyan fita in dai bawai lokacin Sallah ne yayi ba, danna wayar ta kawai takeyi yau ko sha'awan fita ba ta yi.
Mubarak kuwa bayan ya fito bai ga Amna ba, ya tambaye friends ɗin ta, nan suka sanar da shi, cewa tayi yau ba tason fita, sai lokacin Sallah za ta fito, hanyar da zai sa da shi da ajin nasu ya fara bi, saurin janyo shi da Zanga yayi ne yasa shi kusan fa ɗi, yadda suke ko da yaushe ne ya gan su, su Biyar.
Gir-giza kai kawai yayi, yana ƙoƙarin ci gaba da tafiyar sa, dan yasan neman magana ne kawai suke so, sai dai kafin ya fara tafiyar Usy ya janyoshi ta hanyar ka mo Rigar sa ta baya, luuu yayi baya, "wai me kuke so da nine?" Ya faɗi a hasale yana ƙa re musu kallo.
Dariya suka kwashe da shi