Showing 87001 words to 90000 words out of 129098 words
Chapter 30 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
da zani ba, inba haka ba wata rana fa ɗi zata yi in tana tafiya da su.
"Wannan ba abun damuwa bane 'yata, nima ya kamata ace nayi tunanin haka tun tuni, saboda na daɗe ban baki kuɗi ba, bayan mun kammala abinda ya kai mu, sai in haɗa ki da driver ya kaiki shopping da kuma gurin sayen waya" "thank you Dady" "don't worry that's my responsibility".
#Muje dai zuwa😊
____________________________________________________________________________________________
Part 8️⃣3️⃣▶️8️⃣4️⃣
Tunda Dady ya doso wannan wuri Amna ta daina ƙwaƙƙwaran motsi, kallo wanda ake kira kallo take wa wannan wurin da take ganin Dady na dosa da su, ƙofa ce ga tsawo ga kuma faɗi, sannan ga security shida, uku ta ɓangaren hagu uku ta dama, suna sanye da kaya kamar na 'yan sanda amma ba shi bane, su nasu kayan kalar brown ne saɓanin baƙi, tsaye suke ƙam yadda kasan à barikin sojoji suke.
Motar Dady na isowa wurin suka sara masa, biyu daga cikin su ne suka je dan buɗe masa ƙofar, sauke glass ɗin motar yayi yana duban sauran da suka taho suna yi masa gaisuwan girmamawa, ɗaga musu hannu kawai yayi yana ƙoƙarin danna hancin motar ciki, bayan biyun sun fara buɗe ƙofar, yana shiga ciki ta kuma ƙara zare idon ta, tana kallon girman wannan kamfanin, kamar wani unguwa ne sukutum a ciki, a haka ma acikin mota take bata gmna hango wasu gefen ba.
Can wani gefe ya nufa yayi parking ɗin motar, tun kan su ƙarasa fita daga motar, mutane uku da kuma wasu security biyar suka taho inda suke suna yi wa Alhaji gaisuwan shugaba, nan ma ɗaga musu hannu yayi kawai, sai kallon Amna suke suna kallon balarabiyar budurwa da ke tare da Dady. Ita kuwa ganin ikon Allah kawai ta ke, yadda ta ga Dady yanzu wani taƙama yake yi, itama gaisuwan suka yi mata ta amsa musu da lafiya.
Ta fiya ya fara hakan yasa ta bin bayan sa, yayin da wa'yan nan ukun ma suka rufa musu baya, amma su security kam komawa bakin aikin su sukayi, ci gaba da ba idon ta abinci tayi sosai, domin irin wannan wurin ba wanda zakawa kanka rowan gani bane, ko ƙasar da take takawa à ciki ya isa tasan ba ƙaramin kamfani bane, tana biye da Dady harya nufi wani ɓangare.
__bazan iya zanyyano muku wannan kamfani sosai ba, saboda ni kaina sai da na ruɗe, amma dai na bar muku ku kai idanuwan ku duniyar mahanga don hango kyawun M.D cotton company__
Lifta suka nufa haɗi da shiga, sauran kuwa wani liftan suka shige, hatta cikin sa Amna ƙarewa kallo tayi, ta zama 'yar ƙauye ta ɗan lokaci, sama sosai sukayi, har suka kai ga inda abun zai tsaya, yana buɗewa ya fice ta cigaba da bin bayan sa tana kuma kallon wurare, duk mutanen da suka haɗu da shi, sai sun gaishe sa cikin girmamawa amma babu abin da yake musu sai ɗagun hannu, ita ko Amna sai murmushi kawai take sakar musu.
Wani babban mutum ne ya taho gun Alhaji da sauri yana faɗin, "your welcome sir!" Shima cikin girmamawa, shine kaɗai Amna taga Dady ya amsawa da thank you, mutumin ne ya koma gaba, har suka isa wani haɗaɗɗen ƙofa, buɗe ƙofar yayi haɗi da tsayawa à gefe har sai da Alhaji da Amna suka shiga ka na ya shiga shima.
Wayyo haɗuwar office ɗin sai dai rufe baki, juyawa Dady yayi yana kallon Amna ya ce, "ga kujerar ki" saurin kai duban ta ga kujera da yake yasha bamban da irin ko wani kujerar office da ta sani, ta kuma dawo da kallon ta kan dady, fiskar ta alamar tambaya, zatayi magana ya riga ta da cewa, "je ki zauna" yana faɗin haka ta fara taku har izuwa gun kujerar, tana zama ta ji kamar ta zauna akan auduga saboda laushi.
Zuwa Dady yayi ya zauna a kujerar dake gaba da ƙayataccen table ɗin ya zauna, yana maida duban sa ga mutumin nan ya ce, "ina fatan duk abinda na sanar an gabatar da shi?" Da sauri mutumin ya amsa da, "ƙwarai kuwa mai gida, domin mutane sun fara hallara sosai" lokacin mutane ukun ɗazu suka shigo, "su Marwan sun zo?" Dady yayi tambayar, amsa masa da "eh mai gida, sai dai kamar basu da lafiya, sabo..." kafin ya ƙaraDadyya ce "its ok, nan da twenty minutes ya rage kowa ya hallara, kuje kuyi sauran shirye shiryen" "toh mai gida" gaba ɗayan su suka amsa suna wucewa.
Amna da tabi mutanen da kallo har suka ɓacewa ganin ta ta ji muryar Dady na cewa, "yata wannan shine Office ɗin ki a yanzu, minti ashirin kaɗai ya rage kowa da ke cikin wannan kamfanin ya shaida ki matsayin jagorar kamfanin, ta shi in nuna miki Office ɗinki da kyau ki gani" ba bakin magana tashi kawai tayi kamar yadda ya ce.
Zuwa wata ƙofa sukayi yana sa hannu ya buɗe ta, ciki da falo ne da kuma bayan gida à ciki, komai na cikin falon white and light blue ne, tsarin ɗakin yadda kasan à ƙasar waje, wani sabon kallo, "wannan ɗakin hutu ne, a duk lokacin da kike da buƙatar sara-rawa to sai kizo" ya faɗi yana kuma yin gaba zuwa uwaɗɗaka, shi kuma only white ne komai na ciki, aljannar duniya Amna ta furta cikin ranta tana ganin wurin da bata taɓa kwatanta ganin sa ba koda kuwa a mafarki ne.
"Harda barci in kina buƙata 'yata, dan komai da kika gani anan mallakin ki ne a yanzu" ya faɗi yana komawa, ita kuwa tafiya ta farayi à hankali tana nufan wani ƙofa da ta gani duk da tafi zaton toilet ne, aikuwa tunanin ta bai faɗi a banza ba, toilet ne amma ba muna toilet ba fa, saboda ba ƙaramin ƙera shi akayi ba, to ai idan aka ce maka ɗakin kwanan ka nema sai ka gode🙃.
Barin wurin tayi harda zama a kan gado, wani laushin da taji jikin katifan ne yasata jin ya ma fi na kujerar ɗazu, wannan kai ai ta samu gurin zuwa, kiran ta da Dady ya soma yi ne yasa ta fitowa tana amsawa, wata computer ya ɗago yana nuna mata, yadda zatayi amfani da shi, "koda ace kin shigo wannan sashin dan hutawa, idan abu ya taso na ujila ana son yi miki magana amma kina wannan sashi, zai miki ƙara da kuma alama, idan kika ji haka, sai ki dannan wannan filin dan sanin dalilin da yasa aka ne meki, idan na fito wa ne sai ki fito, saboda babu wanda zai shigo ɗakin nan, bayan masu gyara, suma sai lokacin da kike so, shima a can Office ɗin akwai in munje zan nuna miiki".
Duk da cewa koya mata amfanin wannan na'urar da yayi ba kowa bane zai ɗauka farad-ɗaya amma ita babu abin da bata fahimta ba, wata ƙofa dake can gefe wanda labule ya rufe suka je, da mamaki take ganin wurin don batayi zaton akwai wani abu mai suna ƙofa ta wurin ba, sanya wa Dady ido kawai tayi ta ga ya fara dannan wasu numbobi da ke jikin ƙofar, kawai sai ga ƙofaya buɗe, binsan tayi tana fita sai taga wani sashe ne daban amma ba ɗaki ba.
"Wannan hanya ce da zata kai ki ƙofar da zaki iya fita ta baya, amma sai da babban dalili zaki bi ta" ɗaga kai tayi alamar ta gamsu da bayanin sa, maida ƙofar yadda take yayi, sannan ya sa Amna zaɓi wasu numbobi don canza mata yadda zata yi amfani da su gurin buɗe ƙofar, tun da à yanzu ƙarƙashin ta wurin yake. Daga nan suka koma office, nuna mata yadda zata yi amfani da na office ɗin ma yai, sannan ya ce, "muje sun riga da sun haɗu yanzu" ya faɗi bayan ya duba agogon da ke hannun sa, tare da ɗaukar wayoyin sa uku da ya ijje akan table.
Marwan da Saleem ba ƙaramin mamaki sukayi ba ganin yadda aka ƙawata wannan gurin, sannan ga mutane bila adadin sun zo kamar za'a naɗa sarauta, Saleem sanye da face mask gudun kada kumburin fiskar sa ya fito, za 'à iya raina shi, shi kuma Marwan ƙafar ta sa ta dawo dai dai, sai ɗan abinda ba'a rasa ba.
Cikin masu aiki kuwa kowa na kace nace akan wacche za'a kawo, mace kuma wai itace zata ja goranci wannan kamfani, koya zata kasan ce a zubin kamanni?, wasu wa'yan da suka ga Amna kuwa tuni sun sanar wa abokan su yadda take, duk da basu da tabbacin ita ɗin ce sabuwar shugaban ta su, yayin da su kuma wa'yan da aka shafa musu yadda take suke jira don tabbatar wa don an faɗa musu ƙaramar yarinya ce. su kuma wa'yan da basu gan ta ba suna jira kawai suga yadda abun zai kasance.
Marwan da Saleem basu gama fita daga wancan mamaki ba sai ga zuwan manyan mutane sanye da kayan lauyoyi kusan su goma, suma da kan su sauran mutanen sunyi mamakin haka, abinda bai taɓa kasan cewa a cikin wannan kamfani ba. Mutanen sun zone akan naɗa 'ya ga Mai daraja jagorantar kamfanin mahaifin ta, kuma haƙƙin ta, babban abinda ya kawo su shine su tabbatar da rubutaccen wasiyyar mahaifin ta wato Mai daraja.
Kowa ya zo a yanzu ya rage su Dady kawai ake jira, bin bayan Dady kawai take yi, ba tare da ta san inda zasu ba, gani tayi sun doso inda aka ƙawata, suna tafiya har suka sha kwana nan ta ga zun-zurutun mutane wanda zata iya tabbatar da da alama ba iyaka 'yan kamfanin bane, Amna mace ce mara tsoro hakan yasa duk yawan mutanen nan bai sa taji tsoron kasan cewa a gaban su ba.
Kallon su take sosai yadda suka nutsu suna kallon ta ita da Dady, nan ta ga Marwan da Saleem a gefe, suma sai wani ƙa fafa suke yi, tuni wasu a cikin mutanen suka fara 'yan surutai, kowa na ayyana kyau da wannan baiwar Allahn ke da shi, yarinya kamar à India, ko kuwa balarabiya?
Babu ɓata lokaci Dady ya fara gaisawa da wa'yan nan lauyoyi da kuma mutanen, yayin da lauyoyin suke farin ciki da Allah ya kawo su lokacin da zasu sauke haƙƙin da ya rataya a wuyan su shekara da shekaru, wani ne ya fara gabatar wa mutane sanadin haɗuwar su a wurin duk da suma sun san haka, tun daga nan Amna ta fara ayyanawa a ranta wannan ba ƙaramin abu bane, musamman maganar da ɗayan lauyan yayi wa Dady kasan cewar suna kusa, "alhamdulillahi, Alhaji muna taya ka murna da mu kan mu akan wannan rana, da Allah subhanahu wata ala yasa za mu sauke haƙƙin da yake a kan mu tsawon shekaru"
Da turan ci yayi maganar, tun da ya faɗi hakan take tunanin wani haƙƙi suke magana a kai ne? Sannan kuma mutumin ya juyo gare ta yana yi mata murna da zagayowar ranar haihuwar ta, ita kuwa godiya kaɗai tayi masa.
Babu wani ɓata lokaci Dady ya hau munbari yana gabatar da Amna a matsayin Safna, da kuma taya ta murnar cika shekaru ishirin da uku à duniya, sannan ya ɗora da tabbatar wa da mutane ita ce zata jagoranci M.D company, wato dai ta zama C.E.O na su.
Bayan ya kammala bayanin da zaiyi ya sauka daga munbarin, sai babban lawyer wanda ya fi sauran matsayi shima ya hau ya fara magana yana kallon Amna, "muna yi miki murna da samun wannan matsayi Safiyya Abubakar mai daraja, wanda dama ƙwarya ce aka dawo da ita gurbin ta, ba ma wannan kamfanin kaɗai ba, harda sauran kamfani huɗun duk à ƙarƙashin ja gorancin ki suke a halin yanzu, sai dai wakilan ki da suke a can, Allah ya taya riƙo, yasa ki kasan ce ƙarin ci gaban wannan kamfanin na har abada".
Ji sukayi kamar anbuga musu rodi cikin ƙirji, domin har gwara maganar Dadyn su akan na wannan lawyern, ƙila da Hajiya ta zo wurin nan da tabbas suma zata yi, saboda jin kalaman mutumin nan.
Da Ameen ko wa ya amsa, amma Amna kam abin har ya fara sa mata wani tunanin, mutumin nan ya sanar cewa, gaba ɗaya kamfanunuwan shi kuma Dady abinda yace daban, abun ya matuƙar ɗaure mata kai.
Ba ta izini akayi itama akan ta tsaya a munbari dan yin magana, ba tare da wani ɗar-ɗar ba ta tsaya, duk da bata san me zata ce ba, bakin ta kawai ta buɗe ta fara cewa, "na ji daɗi sosai da Allah ya nuna min wannan rana, na kuma ƙara gode masa da ya nufi faruwar hakan, Allah ya bani nasara ya bani ikon kawo cigaba a cikin wannan kamfani mai tarin albarka".
Nan wurin ya kaure da tafi, saboda yadda tayi maganar ya burge su, musamman wani saurayi da ke gefe, wanda ya ijje maga nan sa kan kowani motsin Amna, amma fa duk wannan tafin su Marwan ko ɗaga hannu basu yi ba, bare ma Marwan, ji yake kamar ya maida wannan wurin a kaure da faɗa, Ita ko da tayi maganar ne kawai amma taji daɗin tafin da akyi mata har cikin ran ta.
Matsowa da wani computer ɗaya daga cikin lauyoyin yayi yana faɗin, "signing ne kaɗai ya rage yanzu" ya faɗi dai dai lokacin da aka kawo kujerar alfarma aka ijje a gefen ta, alamar ta zauna kafin tayi signing ɗin. Zama tayi suka miƙa mata computer ta amsa, suka kuma miƙa mata wani ƙarfe da yake kamar biro.
Sai da ta ƙare masa kallo kafin ta amsa, lauyan yana nuna mata inda zata yi, "kuɗi shegu, wato yanzu wannan ƙarfen me kama da biro, shi ɗin alƙalamin computer ne" tayi maganar cikin zuciyar ta, sai dai lokaci ɗaya zuciyar ta ta buga, signing fa akace tayi, ita da ba Safna ba taya zatayi wannan aiki? "Anan kawai zakiyi ranki shi daɗe" lauyan ya faɗi ganin tayi shiru, ita kuwa wani nyawun ta ƙare min tayi tana kallon mutane da suma acikin idon su take.
#Shin bakuyi tunanin ya akayi mai daraja ya bar rubutaccen wasiƙa ba?
Hmm Ya zata ƙare da Amna gurin yi signing? Ko asirin ta zai to nu ne?.
Koma dai ya zata kasan ce, ku kasan ce tare da Alƙalamin Aisha G Umar 👸🏽
Dan jin yadda zata kasance.
____________________________________________________________________________________________
Part 8️⃣5️⃣▶️8️⃣6️⃣
Ta rasa dabarar da zata yi, babu a bin da take sai kallon computer da ke hannun ta kawai, abun ya fara ba mutanen wurin mamaki, ganin tana ɗaukar lokaci ba tare da tayi signing ɗin ba, matsowa kusa da ita Dady yayi ya furta, "my daughter signing kawai zakiyi" ya kuma faɗi don shi a tunanin sa bata fahimci zancen ba ne.
Innalillahi wa inna ilaihi raju'un take ta na na tawa cikin ran ta, da roƙon Allah ya kawo mata mafita, ita da ko Safna bata taɓa gani ba bare signing ɗin ta, yanzu ya zatayi? Wani shirmen tunani ne yazo ran ta, to shirme mana, taya zatayi sign na ta, kuma ta canza shi da F a maimakon na ta da take yi da A? Wannan ai ba hanyar ɓillewa ba ce.
Nan zuciyarta ta bata ƙwarin guiwar yin haka, to idan hakan baiyi aiki ba kuma fa? Zuciyar ta ta kuma bata amsa, "sai kiyi tunanin warware hakan" cike da tsananin far-gaba ta kai hannun ta daidai gurin da ake buƙatar signing ɗin, nan ta fara yin sa hannun ta amma ta canza da F kamar yadda zuciyar ta bata goyon baya.
bugu sosai zuciyar ta ta fara yi kamar na tsoro, abin da bai taɓa faruwar mata ba, tana ƙarasawa ta rintse idon ta tana jiran lokacin da zata fara jin surutun da zasu fara kan signing ɗin da tayi, tun a kan computer tayi, kuma ta san zai iya yiwuwa sun riga da sun shigar da bayanan Safna a ciki, idan kuwa tayi ba daidai ba to zai nuna, gashi ita ko takardun Safna da ta amso bata duba ba, rashin sanin zuwar wannan rana.
Zuciyar ta bata daina bugawar da take yi ba, yayin da take sake tunani da zuciyar ta, akan yadda zatayi idan aka ce ba daidai tayi ba, "ko dai in suma kawai ne? Ko kuma in yi musu ƙaryar ciwon kai? A ah! To ko in faɗar da na'urar ya fashe ne? Sai ince ba da sani na nayi ba? Kaai wai wanne zan ɗauka ne?.
"Safiyya kina lafiya kuwa?" Taji muryar lawyer ɗaya, a hankali ta fara buɗe idanun ta tana kallon su, amma sai taga fiskar su babu wata matsala, saboda duka maganar da sukayi bata ji ba, "yauwa yanzu komai yayi, addu'ar da muka miki shi zamu ƙara, Allah ya taya riƙo, Allah yasa ki ɗau halin mahaifin ki Mai daraja, mai hali irin na daraja" da sauri ta kai duban ta ga computer ta ce, "babu wata matsalar da computer ya nuna?" Ta faɗi cikin ƙaguwa don jin amsar, saboda tayi mamaki da maganar ta su, kamar suna nufin Signing ɗin yayi impossible"
"Babu komai dama signing ɗin ne kaɗai ya rage don mu ƙara tabbatar wa" ajiyar zuciya ta ijje da har ya fito fili, da mamaki Dady ya kalle ta yana cewa, "kina tunanin zai yi wata matsalar ne? Ko kin yi kuskuren zanawa ne?" "No no no kawai dai na tambaya ne, saboda wani lokaci computer yana samun matsala idan ya fara ɓaci" tayi saurin taran numfashin sa da faɗin hakan tana murmushi, su ma sauran murmushin suka saki suna ci gaba da maganganu tsakanin su.
Miƙewa daga kan kujerar tayi a tsaya a gefe. Nan wannan saurayin na ɗazu da ya ƙurawa Amna ido ya iso gun yana gaida Alhaji, amsawa Dady yayi