Showing 36001 words to 39000 words out of 129098 words

Chapter 13 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

31

sannan babu iska mai daɗin da yake kaɗawa dayawa shiyasa basu cika son wurin ba, sai Safna ke zuwa saboda yadda yaran ke korar ta a wancan wurin, don lokuta da dama ma Safnan ce me gyara wurin.

Amma Allah ya rufa asiri da akan ɗan ta hakan zai faru, ɗanta da tafi ƙauna à zuciyar ta, tana matuƙar son Yazeed fiye da sauran 'ya'yan ta, duk da cewa bashi bane babba amma ya zama mafi soyuwa a ranta, sannan Yazeed yafi bata respect a kan sauran, duk da bata son wasu halayen sa, koda bawai muna na bane, kawai dai indai tayi abinda yake ganin ba daidai bane to fa sai ya faɗa mata, duk da cewa wasu tarbiyar gidan yana kansa, in kuwa tasa shi aikin da bai game shi ba tofa zaice mata tayi haƙuri bazai yi ba.

Ruki ce ta taho ta zauna kusa da Hajiya haɗida dafa ta tana faɗin "Hajiya wallahi nasan makirci ta haɗa masa, inba haka ba duk abinda muke mata ya bari ta cece shi, nasan tayi ne dan ya fa ɗa soyayyar ta, kuma ya fa ɗa baki ga yadda ya zama a kan ta ba?" "Ke da Allah rufan ba ki, inji da abinda ke damuna ne kokuwa ki ƙara min?" Hajiya ta faɗi cikin ƙarin takaici ta miƙe ta haye sama.

Saleem da Ruki me makon suyi shirin sallah sai suka zauna suka dasa hira wanda yawancin ta duk zagin Safna ne.

Bayan Ammu tayi ƙoƙarin yin sallah tayi musu addu'a da ga ita har 'yar ta a zuciya, sannan ta dawo kusa da Safna tana cigaba da hawaye, lokacin shima Yazeed ya shigo, ƙarasowa kusa da su yayi, sai da ya ijje ledar daya shigo da ita sannan ya zauna gefen gadon, sai kuma ya tashi ganin idon Ammu na zubar da hawaye.

Tissue ya fitar daga aljuhun sa ya hau share mata yana cewa "Anty Maryam na fa ce miki babu abin da zai same ta zata farka, likita ya tabbatar min da haka, kinga ma takeaway nayi muku, bari inbaki na ki, inyaso ita in ta tashi sai taci nata" ya faɗi yana ɗago ledar.

Murmushi Ammu tayi masa lokacin da ya ciri takeaway ɗaya, ya buɗe yafara miƙa mata a baki tana ci, shima yana bata yana yi mata labarin da zai sanyaya mata zuciya daga damuwar da take, ana haka Safna ta farka à hankali ta fara buɗe idon ta, juyawa gefen ta tayi jin maganar Yazeed ta wannan gefen.

Ba ƙaramin burge ta yayi ba yau ɗin nan dan tsintar kanta tayi cikin farinciki sosai, ganin yadda yake kula mata da farin cikin ta, murmushi take yi sosai tana kallon su, har yagama ba Ammu abin ci, "Anty Maryam ruwa ko tea kike so yanzu? Sai in dafa miki tea yanzu, ko kuma ina ga in haɗa miki duka zai fi ko?" Yazeed yayi maganar kamar Ammu zata basa amsa.

"Aa ruwan ma ya yi" Safna tayi maganar ba tare da murmushin fiskar ta ya ɓace ba, da sauri ya juyo yana kallon inda take, ganin yadda take murmushi yasa shima maida mata da martanin murmushin, yayin da gefe guda kuma Ammu itama ɗauke da na ta murmushin tana bin fiskokin kowannen su da kallo.

Ta shi tayi ta zauna tana shirin sauka a gadon, miƙewa yayi yana faɗin "ya kike ƙoƙarin tashi kuma bayan kina buƙatar hutu?" "Zanyi sallah ne" ta bashi amsa a taƙaice, "ok let me help you" yayi maganar yana zuwa kusa da ita, tayi saurin faɗin "a'a zan iya" tana takawa, aikuwa rashin ƙarfin jikin ta ya sata yin baya zata faɗi.

Da zafin nama ya taro ta kan ta ƙarasa, "kin gani ko? Nasan baza ki iya ba ai" tashi daga hannun sa tayi duk da bai sake ta ba ta ce, "ni dai ka barni in tafi da ƙafa ta" "ƙafar ta ki daba ƙwari?" Yayi mata maganar yana dariya, kallon Ammu tayi taga ta yi ƙasa da kanta, sai kunya ya kamata ganin da alama Ammu taga abinda ya faru ɗazu.

Wucewa tayi duk da ƙafar ta ba ƙwari sosai amma ta daure dan kada ya ƙara taɓa ta, sai da dariya ya kusa kuɓuce masa ganin yadda tayi tafiyar tangal-tangal kamar me koyon ta ta ta, sannan yace "Anty Maryam bari in kawo miki ruwan" ya faɗi yana fita daga ɗakin ya nufa kitchen, ruwan gora mara sanyi ya ɗauko sannan ya koma ɗakin.

Bawa Ammu yayi saida tayi alamar ya ishe ta, sannan ta rufe ya ijje kan table ɗin dake gefe, lokacin Safna ta fito daga toilet, ta tarar har ya shimfiɗa mata garduma da kuma himar a kai, har da carbi, ɗauka tayi ta sanya himar ɗin ta tada Sallah.

Yadda take aiwatar da Sallahr cikin natsuwa ne yasa shi tsayawa kallon ta, ba ƙaramin birge shi tayi ba.

Toh fah Hajiya dai sai dai ince miki sorry, domin kuwa ina ga abun ya fara fa😀

______________________________________________________________________________________________

Part 3️⃣9️⃣▶️4️⃣0️⃣

Har ta idar da Sallar yana kallon ta, tana idar wa ta zauna zaman lazumi, "to malama Safna ai ya ci ace dai an yi sallama ko? Ya kamata kici abincin nan before yayi sanyi" Yazeed yayi maganar ganin bata da niyyar tashi, sosai taji saukar furta sunan ta cikin zuciyar ta, domin kuwa sautin ya fito daban da yadda kowa ke kiran ta.

Sai da ta lumshe ido ka na ta buɗe, ji take gaba ɗaya tsoron da take masa ya disashe, kamar an tsige mata daga cikin zuciya, sai da ta gama tasbihi kafin ta miƙe tana naɗe garduman duk da Isha'i ma ya kusa, "zauna nan" ya faɗa yana nuna mata mazauni kan kujera, zama tayi ba musu tana binsa da ido inda yake ƙoƙarin buɗe takeaway.

"Yi haƙuri ka ƙyaleni inci da kaina please Yaya Yazeed" ta faɗa masa hakan ganin yadda yake neman miƙa mata cokali zuwa baki, shima ce mata yayi "dube ki fah, har yanzu jikin ki ba ƙwari yayi ba, dan haka banason musu" saida ta juya inda Ammu take taga idon ta ba'awannan gefen yake ba, badon taso ba ta amince.

Yana kammala bata abincin ya ɗaura mata da magungunan da Doctor ya bata sannan yayi musu sallama da cewa gobe da Safe zai zo duba su, da kallo Safna ta bisa har ya fice a falon suna idar da sallahr Isha'i Safna ta shiga wanka saboda tsaftace jikin ta ko zata ji daɗi.

Bayan ya dawo daga sallah kai tsaye ya nufi haɗaɗɗen bed room ɗin sa, sai da ya watsa ruwa yasa kayan bacci sannan ya zauna gefen gado ya janyo laptop ɗin sa, sai dai hankalin sa ya ƙi tsayawa guri guda, yayin da idanun zuciyar sa fiskar Safna kawai yake gani.

Mayar da laptop ɗin yayi inda ya ɗauko shi, ya kwanta yana mai tinanin Safna, "ita ɗin yarinyar kirki ce, duk abubuwan da ake mata bai hana ta taimako na ba, tana da halaye masu kyau, tsawon shekarun nan ban taɓa fiskantar hakan ba sai yau, kash! I forgot ban bata haƙuri ba" shine maganar da yake a zuciyar sa.

Sai kuma ya tashi ya zauna yana murmushi a fili yace "gobe zanje inyi mata godiya, zance mata Safna ki yafe min, zan roƙe ta yafiyar abunda na jima ina yi mata na rashin kyautata wa, bazan damu da duk abinda Hajiya za tace ba, sannan daga yau bazan ƙara bari wani yaci zarafin ta ba, wannan alƙawari ne nayi wa kaina, zan zame mata ɗan uwa, zan zame mata majinginan ƙuncin ta da yardar Allah" shine abinda ya faɗi yana komawa ya kwanta, yana mai cigaba da tunanin ta sai murmushi yake kamar tana ganin sa.

Ɓangaren Safna itama kusan hakan yake, domin kuwa yadda Yazeed ya bata kulawa yau ba ƙaramin burge ta yayi ba, "dama yana da irin wannan zuciyar? Duk da cewa yana raga min kuma yana taimako na lokuta da dama, amma ban taɓa tunanin zai iya kulawa dani haka ba, ban taɓa tunanin yana da wannan fiskar ba" shine abinda take faɗawa kanta daga zuciya.

Juyawa tayi ɗayan gefen da take kwance tana kallon fiskar Ammu, hakan yasa ta sakin murmushi tana tuna kulawan da Yazeed yayiwa Ammun ɗazu, da kuma murmushin daya yi mata lokacin da tace ruwan ma ya isa, "da ma murmushi kada ya taɓa yanke wa daga fiskar sa, sabida ba ƙaramin kyau yake masa ba" sai kuma ta giɗa kanta tana kara cewa "Safna karkiyi saurin tinanin haka, ta yu yayi hakanne kawai dan kin taimake sa shine kawai" duk wannan maganar a zuciyar ta tayi ta.

WASHE GARI DA SAFE.

Kamar yadda ya ce gurin ƙarfe bakwai ya nufi sashin su, kamar yadda ɗabi'arsu take ko sallama baiba yafaɗa cikin ɗakin, bacci ya samu Ammu na yi, waige-waige ya hauyi yana tinanin inda Safna take, ko toilet take ne? Nan kuwa ya tina yau tana nan tana aikin gida saboda yau Asabar, zuciyar sa ce ta buga bayan ya tina hakan, duk da ba tada lafiya amma Hajiya ta sa ta aiki bayan ko doctor sai da yace abar ta sai sati ɗaya kafin tayi wani abu.

Yana gama wannan surutun ya fice yana dudduba ta, haɗuwa da Ruki yayi bayan ta fito daga kitchen da kofin tea a hannun ta, bakinta duk yawun bacci, ido kuwa duk kwantsa, sai sosa ƙeyar ta take yi, saboda barcin ba isan ta yayi ba, dama fitowa break fast tayi tana gamawa ta koma, "keh! Where is Safna?" Yayi mata tambayar ba tare da dogon zance ba.

Duk da cewa tayi mamakin sa na neman Safna da yake, da kuma yawan ambatan sunanta daya fara daga jiya zuwa yau amma tayi saurin cewa, "kamar naga fitar ta waje" domin kuwa tasan ƙara tambayar da zai yi mata inba ta yi saurin amsa wa ba mari ne, dan Yazeed ya tsani yayi maka tambaya ko magana ka tsaya ɓata lokaci gurin amsawa, ɗaukar hakan yake da raini.

Ba tare da ya kalleta ba ya doshi hanyar wajen, chan harabar ƙofar falo ya isketa tana shara, "me kike yi haka?" Safna da take shara a galabaice saboda rashin ƙarfin jiki ta tsinkayi muryar Yazeed, kuma babu alamar farin ciki a muryar, saurin ɗagowa tayi tana kallon sa a razane, "what are you doing here?" Ya ƙara yi mata tambaya.

Duk da cewa tayi mamakin maganar saboda yasan da duk weekend tana hakan amma sai tace "aiki nakeyi" haba ai sai ya fara zuba masifa, "kinsan baki da lafiya amma kike wannan aikin, baza ki iya haƙuri bane? Maza yanzun nan ki ijje tsintsiyan nan ki wuce ciki, kije kiyi break fast ki kwanta".

Mamaki ne ya ƙara fa ɗaɗa a fiskar ta, "yaya Yazeed bazan iya ba saboda....!" Ya katse ta "bana son musu ki ijje tsintsiyar nan kiwuce ciki nace, inba haka ba zan iya marin ki" ya faɗi cikin ɓacin rai, "kamar ya ta shiga ciki? Gama aikin tayi ne?" Marwan da ya fito yanzu ya faɗi hakan, shima da mamakin abunda yaga Yazeed ya yi, juyowa Yazeed yayi yana cewa "bata gama ba kuma baza ta gama ba".

Yayi masa maganar yana juyawa inda Safna take ya ƙara cewa "tsaye kike har yanzu?" Da sauri ta bar wurin jiki na rawa, ganin yadda fiskar sa yake a haɗe ne yasa ta jin tsoron ya dawo "lallai Yazeed wato so kake kawai kace ka fara son ta" "eh na fara son ta, I love her then what?" Yazeed ya faɗi hakan yana wucewa ciki, cike da zafin rai.

Shima Marwan ransa ne ya ɓaci "lallai Yazeed abun na ka ya fara yawa, dole Hajiya taji wannan labarin tun kafin yafi ƙarfin ta" yayi maganar yana komawa ciki shima dan zuwa ɓangaren Hajiya.

Yazeed kuwa zuwa kitchen yayi yaga Safna na ƙoƙarin haɗa breakfast ɗin kamar yadda yace da ita, tsayawa yayi yana kallon ta yadda jikin ta yake rawa da kagan ta kasan ba ƙalau take ba, hakan yasa shi cewa "kije ɗaki za'a kawo muku break fast ɗin" tun kafin tayi magana ya bar kitchen ɗin, hakan yasa ta yin ɗakin su dan bata son wani abun ɓacin rai ya faru kuma.

Yazeed kuma fitan da yayi yasa masu girki su haɗa mata break fast, Marwan ne ya fito yana kallon inda Yazeed yake zaune a falo, sai da yaji haushi a ransa domin yadda Hajiya take yawan nuna fifita wa tsakanin su, "Hajiya na kiran ka, kuma inaso ka sani, in ka manta intuna maka I'm your brother, dan haka baka da damar yimin kowani maganar da yazo bakin ka" Marwan ya ƙarashe maganar yana kallon Yazeed cikin isa.

Sai da Yazeed ya miƙe sannan ya murmusa, irin lallai ɗin nan, yana kallon Marwan yace "a baɗini haka ne amma a zahiri ba haka bane, kasan meyasa? Saboda ba ka kama girman ka, ba ka da tausayi kai ko da yaushe baƙin hali ne a ranka, da 'ace baka da duk wannan ƙila da ka zama yayan na gaske".

Cike da ɓacin rai shima Marwan yace "naji duk abinda kace indai hakane kuwa ita kanta wacce ta haif...." ai sai yayi saurin da katawa jin maganar Hajiya tana cewa "wai me Yazeed ɗin ke jira bayan na kira shi?" Tayi maganar tana ƙarasowa, kallon ta dukan su biyu sukayi sannan Marwan ya fita.

Allah ya taimaka da fa cewa zai yi, "ita kanta wacce ta haife ka hakan take don a wurin ta na koya" hmm ashe da yau yasha ƙanin tsinuwa wurin Hajiya, cab zuciya za ta sashi ɓaran-ɓarama duk da gaskiya ne, ya sauke ajiyar zuciya sannan ya shige motar sa.

Fannin Hajiya kuwa tana saukowa ta fara aikawa Yazeed wani irin kallo da saida ya kauda idon sa, "kiran nawan ne baza kazoba ko kuwa?" Ta jefa masa tambayar tana cigaba da kallon sa, "Hajiya maganar banza yake faɗamin shi ya hana ni zuwa kiran da kika min" "to na ji! Amma me yasa ka hana shegiyar nan aikin da take yi a duk ranar Asabar da Lahadi? A wani dalili zaka ce ta bari eh?"

Ta ƙara yi masa tambayar ba tare da ta zauna ba, "haba Hajiya kamar baki san abinda ya faru da jiya ba? Har yanzu jikin Safna fa bai warware ba, kuma kina ji doctor yace a ƙalla a barta tayi one week tana hutawa, ko makaranta ma so nake ta barshi har ta warware, amma sai tayi aikin gida haka".

Kallon mamakin sauyawar sa take matuƙa, sai da ta ɗan ni sa tace "shakka babu Yazeed ka sauya, kuma na ji duk abinda kace, yayi mai tausayi, ah dole na yiwa tifkar hanci, iyyeh!" tayi faɗi tana samun wuri ta zauna, ba tare da ya fahimci inda maganar ta ya dosa ba ya wuce kitchen, ya samu sun gama haɗa komai.

Ɗaukar tray ɗin abincin yayi ba tare da yayi musu wata magana ba, ya fice, Hajiya na zaune Yazeed ya wuce da abinci a hannun sa ya nufi side ɗin su Safna, ai batasan lokacin da ta miƙe ba, ta fara muzurai, ba tama sanin abinda bakin ta ke cewa, saboda yadda take zuba masifa, duk da shi Yazeed ba ya ma jin maganar don bata ɗaga murya sosai ba.

"Wai yaron nan me yake buƙata ne? Yanzu abinci fa zai kai musu, lallai sai na ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki akan tsinanniyar yarinyar nan, inba haka ba to ni zan kwana a ciki. Barin surutan tayi ta nufi ɗakin ta, da sauri ta ɗauki wayar ta dake kan miro ta fara duba numbern aminiyar ta Ladingo, bugu ɗaya ta ɗaga kamar me jira, ko sallama Hajiya bata yi ba ta fara magana.

"Ƙawata Ladingo akwai matsala fah" "matsalar me kenan Hajiya?" Ladingo tayi tambayar, sai da Hajiya ta sauke ƙaramar ajiyar zuciya haɗi da zama gefen gado ta ce, "ina faɗa miki Yazeed ya fara ƙaunar shegiyar yarinyar nan, alamu sun fara bayyana, yanzu ni ya zanyi?".

"Haba Hajiya me yasa kike saurin zato ne, kece kika sanar dani abinda ya faru jiya, tayiwu ko don hakan ne kawai yake bata kulawa, kema fa kinsan ɗan na ki ba wawa bane duk da kyawun da yarinyar take da amma shi ba class ɗin ta bane, don't worry about criticism".

"Kin ga Ladingo yi min hausa na fi gane wa, na rasa gane miki duk da sunan ki na ƙauyawa ne amma kin iya turan ci" murmushi kawai tayiwa Hajiya daga wayar, don ta san ƙawar ta da je fawa mutum baƙar magana kuma ita baigame ta ba, haka dai har suka ka mo wata maganar daban.

#Ya kuke tunanin zata kasance a wannan gida cikin 'yan kwanaki masu zuwa?

______________________________________________________________________________________________

Part 4️⃣1️⃣▶️4️⃣2️⃣

Yana isa ɗakin ya tadda Safna na wa Ammu tausa a ƙafa, wato tana ɗan mammatse mata ƙafar ta, suna zaune kan lallausan kafet ɗin ɗakin "ita da ko ƙarfin jiki ba tada amma matse ma Anty Maryam ƙafa take wai" yayi maganar daga zuciyar sa yana ƙa rasowa ciki.

Juyawa tayi tana kallon sa har lokacin da ya ijje tray ɗin kusa dasu, -hmm Safna kam akoi kallo fa wani zubin- saurin kauda kanta tayi lokacin da ya dawo da hankalin sa gare su, duk da mamaki ne ke ƙara cika ta a karo na babu adadi dan gane da shi.

Sai da ya gaishe da Ammu sannan ya ce "nima yunwa nake ji ban karya ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login