Showing 42001 words to 45000 words out of 129098 words

Chapter 15 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

30

ke tambayar Safna dalilin sauryawar da tayi sosai, wanda ke son ya taɓa karatun ta. Duk da ba yau bane tambayar da tayi mata na farko, ganin yauma bata niyyar bata amsa ne yasa ta yin fushi tana cewa "shi kenan besty na daina tambayar ki damuwar ki daga yau, tunda ban cancanci in sani ba, kuma nima bazan ƙara sanar dake komai game da ni ba, tunda a yamzu bani da wanni mahimmanci à gare ki, thank you".

Ta faɗi tana ƙoƙarin tashi daga kan ɗaya daga cikin kujerun hutawar makarantar, saurin riƙo hannun ta Safna tayi tana marai-raice mata fiska, "please sit my Rahee" ba tare da tayi magana ba ta zauna fiska a haɗe, cikin sigar rarrashi Safna ta fara magana "Raheena kar kiyi fushi please, dalilin da yasa naƙi sanar dake damuwa ta bakomai bane sai sanin halinki da nayi, nasan zaki ɗaurawa kanki damuwa ne sosai, shiyasa badon banason ki sani ba".

Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "amma kinsan rashin sanar dani ya fi saka ni cikin damuwa, kwanan nan Momy take tambayana wai meyasa na sauya? Ni kuma nace mata 'yarki Safna ce ke sani cikin damuwa" ƙaramar dariya Safna tayi wanda har kyawawan haƙoran ta suka bayyana tace "wato dai na sawa Momy ɗiya cikin damuwa?".

Dariya Raheena tayi tana cewa "kinji yadda hausar ki ta fito kuwa? Kamar bahaushiya" "to dama ni mecece yanzu ai hausawa kun ƙwace ni" Raheena ta ƙara yin dariya tace "Allah? Kenan yanzu ba kyajin fulatan ci?" Tayi murmushi ta bata amsa "inaji amma yaushe rabon da inyi, tun fa kafin Ammu ta fara rashin lafiya".

"Allah sarki to yanzu dai tell me abinda kesa besty na cikin damuwa?" Sanar da ita duk abinda ya faru tayi, banda soyayyar Yazeed tun da dama Raheena tasan dashi, tana gama sanar da ita tace "hmm wallahi Safna ni na ƙosa bawan Allahn nan ya dawo, koda yake koya dawo babu abin da zai gane tunda nasan ba sanar da shi zaki yi ba".

"Raheena kenan taya ya zan haɗa tsakanin ɗa da uwa, ko kuma tsakanin sa da 'yan uwansa ba abu mai kyau bane" "eh ai dama na sani ke adila ce, amma ni kam zanso inga auren ki da Yazeed wallahi inga wai Hajiya suma zatayi ko mutuwa?" Sai da Safna ta juyo ta kalle ta tace, "nifa bana tunanin hakan zai faru, kuma bai sanar dani yana sona ba".

"haba Basty wani sanarwa zaiyi bayan kin fiskanci duk abinda zuciyar sa ke son isar wa? Kamar yadda kema kika isar da na ki, Allah na tare dake insha Allahu komai zai wuce, inaji a jiki na zaki zamewa su Hajiya abinda basu taɓa tinani ba, kuma duk abinda suke miki sai ya koma kansu by the grace of God" da amin Safna ta amsa suka tashi suka wuce class.

Bayan Alhaji shima yayi tafiya Istanbul, Hajiya ta samu dama dan aiwatar da abunda take buƙata, Safna ta shiga tashin hankali lokacin da Hajiya ta sanar da ita cewa wai dama Alhaji nason sanar da ita ya manta akan zata je gurin dangin mahaifin ta da suke Nijer, dan kai musu ziyara, dan haka ta shirya jibi za ta tafi.

Ta roƙi Hajiya da tayiwa Dady magana akan in ta tafi bamai kula da Ammun ta, amma Hajiya sai rufe ta da masifa tayi, wai so take taƙi bin umarnin sa saboda bashi ya haife ta ba? Bayan duk kulawan da yake bata fiye da 'ya'yan da ya haifa? Ko gidan kango ne babu mutanen da suke a ciki bere su kula mata da mahaifiyar ta ta?.

Haka ta sun kuyar da kai ganin Hajiyar nason kai mata bugu, washe gari haka ta zana jarabawar ta na ƙarshe badon tasan abinda ta za na ba, don gaba ɗaya hankalin ta baya kan komi sai tinanin da yayi mata zaune a zuciya, koda ta sanar wa Raheena itama ta shiga kotankwacin yadda Safnan ta shiga, amma ya zatayi tunda ba tada hanyar ceton ta, don wani lokaci ta kan ji haushi idan ta tuna yadda Safna take azabtuwa a gidan su, ita kuma ba tada hanyar tai maka mata.

RANAR TAFIYA.

Doguwan riga atamfa da kuma gele mai faɗi Safna ta sa, tayi kuka sosai kamar ranta zai fita, ita ma Ammu hawaye masu raɗaɗi ne ke ta zarya a kumatum ta, ba tada bakin magana da ta sanar da 'yarta cewa mahaifin ta baida wasu 'yan'uwa a Nijar, amma ina, riƙe hannun Safna tayi sosai kamar yadda itama ta riƙe na Ammun.

"Ba shakka! Naga alama dan kin ga ina shige miki gaba akan tafiyar nan shiyasa kike min iskan ci ko Safna? Tun yaushe aka ce miki lokacin tashin motar na ku ya kusa? Shikenan baza ki dawo bane in kin tafi? Dazaki tisa uwar ki a gaba kina kuka?" Hajiya Tayi maganar tana shigowa ɗakin, wanda ta daɗe bata taka ko ƙofar shi ba.

#Hmm ana wata ga wata, kai amma muguntar Hajiya sai dai addu'a, koya zuwa Nijar zai kasance?

______________________________________________________________________________________________

Part 4️⃣5️⃣▶️4️⃣6️⃣

Sai da ta rungume Ammun ta sannan ta fara ja baya a hankali tana jan akwatin ta tana ci gaba da kuka har suka bar ɗakin, sai da Hajiya ta gallawa Ammu harara tana ayyana abinda yakamata tayi mata itama a ranta sannan ta fice, direba ne ya amshi akwatin yasa shi a bayan mota Hajiya na jadda da masa kada yabar wurin har sai yaga tafiyar su Safna.

Haka kuwa akayi don tunda ya ijje ta kuma ya sauke mata jaka bai matsa a wurin ba. Wai Safna 'yar gidan Mai daraja ce zata yi tafiya a mota, motar ma irin lalatattun nan, wanda yaran Hajiya ko a mafarki baza su yarda da hakan ba, koda yake dama ba tafiyar Allah da Annabi bane.

Ana cikin loda kayan mutane a motar tafiyar wayan direban yayi ƙara, Ruki ce ta kira sa take ce masa ya zo tana da buƙatar shi, akoi inda take son zuwa, koda ya fara sanar da ita abin da Hajiya tace, sai cewa tayi wallahi inbai zoba sai ta sa ankore shi, kuma sauran ya faɗawa Hajiya ta kira shi, Dan dole yabar wurin, yabar Safna ta rafka uban ta gumi.

Motar baza ta je Nijer kai tsaye ba, a ƙalla sai ta canza mota ko sau ɗaya ne kafin ta hau na zuwa cikin Nijar ɗin, amma Hajiya tasan yadda tayi aka nuna wa Safna direct zuwa Nijar ne, ita kuma ba sani tayi ba bare tayi tinanin da wata a ƙasa, ita da daga gida sai makaranta? Ko cikin Kadunan bata taɓa zuwa wuri mai nisa ba bere barin gari.

Babu abinda take juyawa a hannun ta sai dubu biyar ɗin da Hajiya ta ba ta akan na abincin hanya, da kuma 'yar takarda wai adreshin da zata sauka ne, ta rasa meyasa Hajiya ta nuna tana son tafiyar?. Buɗe zip ɗin akwatin tayi ta sanya papern da kuma kuɗin a ciki tunda ba jakar hannu ta riƙo ba, tana zaune gefen har aka gama lodi, saiji tayi ana maganar azo ashiga mota zata ta shi, da sauri ta shige ba tare da ta lura da ba'a saka akwatin ta aciki ba, saboda tsabar tinanin da take ciki.

Bayan mota ta fara tafiya kusan minti talatin dan har anfara shiga dajin fitar gari, lokacin ta tuna ba a saka mata akwatin ta ciki ba, to kuma adreshin fa? Ai nan ta fara yi wa mai motan magiya da ya tsaya ta manta jakar ta, da ƙyar ta samu ya tsaida motar, mutanen ciki kuma suka fara mi ta, su baza su tsaya jiranta ba, ba tada hankaline da baza ta tsaya ta kula da ansa mata kaya a mota ba har mota ya tashi? Kowa dai da abunda yake faɗa.

Ƙarshe dai haka aka sauke ta su kuma su kayi gaba, sai lokacin ta ga ashe a daji aka sauke ta, rasa abinyi tayi domin babu abinda yake hannun ta, tana cikin tinanin abinyi kunnen ta ya fara jiye mata kamar sautin maganganu can ciki ciki.

Maida hankalin ta guri ɗaya tayi dan ta tabbatar da abinda take ji, "kamar, kamar ta cikin dajin nan ne nakeji fah" tayi wa kan ta maganar tana duban inda take kyautata zaton nan ne ake haya niyar, kuma da dukkanin a lama masu wannan surutu suna can cikin dajin.

"Bari inje induba" Ta ƙara yiwa kanta magana, ba tare da ta jira zuciyarta ta bata yaƙinin shiga ba, ta fara sanya ƙafa ciki, tana kan tafiya a ɗar-ɗar ta ga wata baƙar mota duk ta dagargaji, da alama accident mai muni motar tayi, sai da ta jinjina kan ta yanzu wannan hatsarin bil'adama ne su kayi, ko sun fita da rai? Ta yi maganar a zuciyar ta cike da far-gaba, -wannan motar ta su Zilla ce lokacin da sukayi hatsari ta wun tsula wurin, gawar su kam ba abun magana bane, don ko alamar sa babu-

Barin wurin tayi tana ci gaba da tafiya sai dube-dube cikin dajin ta keyi, duk da har yanzu daga nesa take jin sautin, zuciyar ta na yi mata gargaɗi a kan ta fice daga wannan dajin, amma sai take jin tana da buƙatar zuwa dan ganin me mutane suke yi cikin daji haka? Sannan me yasa suke magana da ƙarfi? Koda itama tasan da ba don kunnen ta da jiye-jiyen magana koda daga ne sa ba ne, da ba abunda zai sa taji hakan.

Tun tana hango kan hanya inda aka ijje ta har ta dena hangowa, Tafiya mai nisa tayi dan harta gaji sosai amma har yanzu bata ƙa rasa inda take jin sautin ba, bata sa re ba dan tafiyar ta cigaba da yi haɗi da waige waige, domin ko kukan wani tsuntsu taji sai zuciyar ta ya tsinke, amma fa sai kace wacche aka sa.

Ta samu nasarar isa gurin mutanen, amma duk ta bi ta galabai ta, dan da ƙyar take fitar da numfashi, laɓewa tayi a bayan wani bango wanda yake kewaye da ciya yi, dan da ba don sun shagala da wasu maganganu ba da babu abinda zai hanasu jin alamar zuwanta, koda ace baka tawar da mutane a wurin ba, zaka iya tabbatar da wannan gurin bana ƙalau bane.

Saboda yadda aka daddasa duwatsu da kuma banguna suka kewaye wurin, duwatsun jajaye ne sai bangwayen kuma kewaye suke da ciyawu kore shar, mutanen suna da yawa, dan zasu kusa talatin, kuma gaba ɗayan su sanye suke da fararen tufafi, kamar sababbin gawawwaki, sai ƙyalle baƙi da suka rufe fiskar su banda ido, tsaye suke gaban wata shirgegiyar Bishiya baƙa ƙirin kamar ansha fa mata baƙin penti.

A tsorace Safna take binsu da kallo, saboda gaba ɗaya ba suyi kama da mutanen ƙorai ba, ɗaya daga cikin su ne yayi gefe, wanda ɗazu bata hangesa ba, ƙatoton mutum ga jiki ga kuma tsawo ya haye kan wata doguwar dutse wacche akayi mata rubutu wanda ita kanta Safnar bata fiskan ci wani iri bane, tsayawa akai yayi yana duban sauran mutanen da ƙananun idanun sa, sai dai shi na sa baƙin ƙyallen mixed da ja ne ruwan kafirai, wanda haka ke iya nuna maka shine babba a cikin su.

Magana ya fara yi musu cikin wata ƙatuwar murya, -da innace zan kotan ta muku tofah hannuna ce zai tsaya- "wannan mutumin maci amana ne, kamar yadda hukuncin maci amanar Ƙungiyar mu ta POSPA shine mu ra taye mutum jikin baƙar Bishiya har sai mun raba kansa da gangar jikin sa, to hakan shima zamuyi masa, ƙarƙashin jagorancina ni Vapi shugaban tsakiyar rukunin ƙungiyar POSPA, dan ya ƙara zama izina akan masu wannan niyyar a gaba, kun riga da kunsan cewa mai gida ZABBA BA ba ya tsoron maci amana, sai dai shi ba ya yafe duk wanda yayi masa laifi, kamar yadda a dokar sa take babu ɓata lokaci zamu aiwatar da hakan".

Yana ƙa re maganar sai gashi an gurfa nar da maci amanar a gaban su, mutumne da bazai gaza shekaru hamsin ba, domin gashin kansa har ya fara fari-fari a lamar tsufa ya fara bayyana, shi kuma sanye yake da baƙin kaya, gumi ne yake tsatstsafo masa daga tsakiyar ka har zuwa ƙafafuwan sa, saboda tsabar tsoro, duk da yasan yau babu abinda zai hana shi ba ƙuntar lahira, babu ɓata lokaci aka rataye wuyar sa cikin jar igiya, igiyar da ka gan ta ka san ita kanta sheɗaniya ce.

Take jikin Safna ya hau kyarma saboda ganin yadda marasa imanin nan suke yiwa mutumin, domin bayan sun saƙala masa igiyar a wuya sai suka fara jan wata igiyar kuma, yana fara yin sama igiyar ta fara yanke masa wuta, yadda kasan reza, shima mutumin sai ihu yake yana neman ya fiya, haka har ya dena motsi.

Yana dena motsin suka ja igiyar da ƙarfi, hakan yasa maganar da suka ce farko ya bayyana, Safna bata san lokacin da tasa ihu ba ganin munin a binda ya faru a idanuwan ta, wanda ko a labarin mafarki ko tatsuniya bata taɓa jin hakan ba, saurin mannewa jikin ginin tayi, tana toshe baki, dukkan su suka dawo da kallon su inda su kaji wannan sautin, ganin bakinta ya riga yayi suɓul da baka ne yasa ta zaro ido, sannan ga shirun da mutanen su kayi alamar hankalin su ya dawo kan ta.

ba tare da gajiyan zuwa wurin ya fita a jikin ta ba, amma ta fara ƙoƙarin barin gurin, gusawa daga jikin bangon tayi ta fara gudu cikin ta shin hankali, umarni shugaban na su yaba mutane biyar a ciki akan su kama wanda yayi wannan ƙarar su kashe shi kan su kawo masa gawar, amsa umarnin sa sukayi suka fara gudu neman ta.

HAJIYA.

"Nace miki ta tafi, direban dana sa ya kaita ya tabbatar min sun tashi, nidai burina ya cika shine kawai" cewar Hajiya dake waya da Ladingo, itama Ladingon cewa tayi "ai baki da matsala tun da dai kin tabbatar da ta tafi, dan bokan cewa yayi yadda zata bar garin nan to baza ta taɓa sha'awar dawowa ba, ko sunan shi sai dai taji a bakin wani ba dai ita ta furta ba bere sunan ku, indai Safna ce to ki cire babin ta a rayuwar ku".

Murmushi cike da jin daɗi Hajiya tayi tana ƙara cewa, "shakka babu kin min ƙawata, amma kinsan wasu-wasin da nake?" "A ah sai kin faɗa ƙawata" Ladingo ta amsa tana jiran abinda Hajiya zata ce, sai da tace hmmm sannan ta cigaba da cewa, "cewa fa kika yi yace inta bar gari, sai nake ganin kamar abun da ƙyar ya kai labari".

"Haba ke kuwa Hajiya Zainab me yasa kike yawan kawo rashin nasara a lamarin ki ne? Kuma yanzu kika san yadda rayuwar ta zai kasan ce? Ƙila ma mutuwa za tayi idan ta gaji da gararin ta, Shifa wannan bokan na musamman ne, ba ɗaya yake da sauran ba" "to ƙawata Ladingo ni ina nasan na ƙorai a cikin su, kinsan wannan ne karo na farko dana fara bi ta filin boka" Ladingo ta kuma cewa "Haka ne amma nasan zaki ji daɗin fa rawa da shi da ki kayi, to ya maganar gurguwar fa?".

"Itama ina nan ina tinanin yadda zan ɓullowa lamarin" cewar Hajiya dan sai ta rabu da Ammu kafin zata kasance cikin sala ma, "kada lamarin ta ya dame ki, ai yunwa kaɗai ya isa ya kashe ta tun da mai kula da ita ba ta nan, amma fa ya kamata a cika masa alƙawarin sauran kuɗin" Ladingo ta faɗi hakan tana murmushi mara ƙara da Hajiya batasan ta yi ba, duk da a waya ne amma bai hana Hajiya yin shewa ba saboda farin ciki tana faɗin "karki damu indai wannan ne, tunda har burina ya ya cika" lokacin Ruki ta shigo, zama tayi gefen mahaifiyar ta tana cewa.

"Hajiya me kika samu haka tun daga ƙasa nake jin shewar ki?" Saida Hajiya tayi Sallama da ƙawar ta, sannan ta juyo kan Ruki, "ina kikaje ɗazu kika bar motar ki?" Cewar Hajiya tana kallon Ruki, kamar baza tayi magana ba sai kuma tace "Hajiya ni na rasa meyasa kwanan nan kike sa min ido, nifa yanzu ba ƙaramar yarinya bace" tayi maganar cike da rashin kunya.

#Tashin hankali gobarar gemu, wa'ennan mutanen zasu kama Safna kuwa? ko ya ya?

Gashi ita Hajiya tinanin ta Safna ta bar garin Kaduna, amma mu mun san bata bari ba, to ya zata kasance?.

______________________________________________________________________________________________

Part 4️⃣7️⃣▶️4️⃣8️⃣

Ba tare da taji rashin daɗin yanayin yadda 'yarta tayi mata magana ba tace "haba autana! bawai sa miki ido nake ba, gani nayi kwanan nan kin samu sabbin ƙawaye shiyasa nake son ji ko gurin su kika je? jiya ma kusan magriba naga kin fita" "ok, zuwa partyn ɗan Gomna mu kayi jiya" "Allah ɗan Gomna?" Hajiya Tayi tambayar tana Washe baki.

Hakan yasa Ruki farr da ido tana ƙara cewa "of course har cewa ma yayi yana sona, kuma sai kinga yadda yake ɓarin kuɗi a kaina, wanda ko Dady ba ya yi mini haka, yanzu haka ya bani wata zoben gol..." ai tun kan ta ƙarasa Hajiya dake washe da baki ta katseta da cewa "zoben gol?".

Tayi tambayar dan wannan labarin ya faran ta ranta sosai, dan ita duk abinda akace na kuɗi ne tofa tana sonshi, duk da kuwa a cikin kogin dukiya take, sannan dama so take 'yarta ta auri mai dumus, duk da tasan koshi mahaifin yaron Gomna bazai fi su dukiya ba sai dai ma su fisa, amma yadai fi wasu samarin da Rukin take da su.

"Eh Hajiya duk da ina sakawa amma wannan ta birge ni, mai tsada ce zan kawo miki ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login