Showing 63001 words to 66000 words out of 129098 words
Chapter 22 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
shine a tsakanin mu kowa zai bada labarin kowa, yanzu misali, ni ba Safna bace idan nace ki bani labarin ƙawar ki Safna zaki iya bani?".
Murmushi Raheena tayi sannan ta ce, "sosai ma! Bayan Ammu nice wacche zan bada cikakken labarin ki Safna" "to bismillah ina jinki" cewar Amna tana ƙara gyara zama da kyau, Raheena ta fara magana kamar haka, "sunan ƙawata Safiyya amma ana kiran ta (Safna) tana da ɗabi'u masu kyau da ya kamata ayi koyi dasu, bata da girman kai bata da fitina, ba ta da yawan surutu wanda wasu zasu iya kiran hakan da girman kai, saboda bata cika shiga abinda ba'a gayyace ta ba, koda kuwa an gayyace ta to bata da shishshigi, ba ta kula samari bare tayi wasu dogon magana da su"
Sai da ta sauke numfashi ta cigaba da cewa, "tun tana da shekaru biyar a duniya mahaifiyarta ta kamu da wata cuta wanda ba ada tabbacin wani iri ne shi, duk da kasan cewar ta mai ƙananun shekaru amma a haka take kula da mahaifiyar ta, domin idan ba ita ba babu mai kula mata da ita, mahaifin ta ya rasu ba tare da ta san shi ba illa a hoto kawai, ya kasance mai kuɗi sosai amma ita da mahaifiyar ta suka zama marasa ga lihu a cikin gidan da suke da haƙƙi a ciki, domin kuwa na mahaifin ta ne, musgunawa iri daban-daban take fiskan ta acikin gidan su tsawon shekaru".
Amna ko ƙyafta ido ba tayi a kan kallon Raheena, "kinyi mamaki da na ƙara sanin wasu abubuwan ko?" Amna da ta maida hankalin ta gaba ɗaya wajan Raheena tana jin labari, taji Raheena ta faɗi haka, amsa ta bawa Raheena da faɗin, "eh nayi mamaki amma yanzu dai ki cigaba da min bayani" tayi maganar domin ita so take ta ƙare mata labarin Safna.
"Toh! Sai dai wani lokaci tana bani haushi" kan ta kuma wani maganar Amna ta katseta da faɗin, "me yasa take baki haushi?" Ci gaba da magana Raheena tayi, "duk da cewa haƙuri abune mai kyau amma na ta yayi yawa" nan dai Raheena ta sanar da ita duk abinda ta sani game da Safna.
Ita da kanta Amna taji takaicin abubuwa da dama musamman yadda su Hajiya suka rinƙa musgunawa Safna amma babu abinda tayi, "amma ita wannan Safnan wace iriyar mutum ce? Sai kace babu zuciya a jikin ta" cikin zuciyarta ta faɗa, "kuma duk Hajiya da 'ya'yan ta sukayiwa Safna hakan?" Kallon mamakin da Raheena ta bita dashi ne yasa ta dabur cewa kar dai ta fiskanci wani abun ta ce "kar kimin wata fahimtar, ba ce miki nayi à misali ni wata ce ba? To shiyasa".
Sai da Raheena ta ɗan share ƙwallan da yaɗan zubo mata na labarin da ta ba Amna ta kwashe da dariya tace, "nima ramawa nayi naga react ɗinki" murmushi Amna tayi ta ƙara cewa, "amma ya akayi kika san duk wannan?" "Ita ƙawar tawa ce ta sanar da ni, domin ta kura mata nayi ta bani tarihin ta bayan na bata nawa".
"Da kyau gaskiya ku ɗin aminai ne na haƙiƙa" cewar Amna tana murmushi, ƙawancen n'a su ya burge ta sosai, duk da ita dasu Zarah ƙawaye ne amma bata faɗa musu sirrin ta kamar haka, "wato shiyasa nima suke min irin cin kashin da suke mata kenan? Saboda sun zata ita ɗin ce, sannan kuma cikin yaran Hajiya akwai mai matuƙar son Safna? Lallai! Amma yadda Hajiya ta tsani baiwar Allahn nan zata iya bari ta auri ɗan ta kuwa? Cab ashe akoi aiki a gabanki Amna".
Katse mata tunani Raheena tayi da faɗin, "keh malama baza fa kimin wayo ba, naga kinyi shiru to nima sai kin bani labarin Raheen, ni na gama nawa saura naki" "sai da Amna ta haɗiya nyawun ta ƙa re min sannan ta ce, "shirun da nayi kai na ne yaɗan harba min shiyasa, ciwo yake min" ta faɗi domin kaucewa Raheena, domin ita ko hanyar gidan su bata sani ba bare tasan labarin ta.
Da sauri Raheena ta miƙe cikin damuwa ta ɗaura hannun ta kan goshin Amna tana cewa, "sorry besty na, kuma babu alamar zafi, to ko ta ciki ne yake miki ciwo?" "Eh kamar kin sani ta ciki ne" cewar Amna harda rufe ido ita ga mai ciwon kai, "sannu! muje ɗaki ki sha magani".
Zaunar da Amna tayi à kan kujera vayan sun isa ɗakin, ta nufi inda tasan Safna na ijje magun-guna ta ɗauko, "wato har ɗakin ta san shi sosai" cewar Amna a zuciya da taga Raheena ta ɗauko maganin, "ba wani matsala besty idan na ɗan rintsa kaɗan zai bari" ta faɗi bayan Raheena ta miƙo mata maganin, Raheena ta ce, "toh shikenan ki konta ɗin". Kwantawa Amna tayi gefen Ammu da ta samu damar rintsawa.
"Ni zan koma, Allah ya ƙara sauƙi" "komawa kuma? Ina cewa kikayi sai azahar?" Raheena ta kuma cewa, "so nake in barku ku huta sosai, ko kina da buƙatar wani abun?" Da à ah Amna ta amsa mata, "toh shikenan besty ni zan tafi Allah ya ƙara sauƙi ki gaida min da Ammu in ta tashi" cewar Raheena tana wucewa cike da damuwa domin ba tason abinda zai taɓa lafiyar bestyn ta.
Raheena tana fita Amna ta tashi ta zauna, ƙurawa fiskar Ammu ido tayi tana jin wani irin haushin su Hajiya a cikin ranta, su wasu irin marasa imani ne? Mutane da gidan su amma su maida su bayi, duk laifin Jamilu ƙanin mahaifin safna ne, duk da baya musguna musu yana ɗan basu kulawa amma ya kamata ya sai musu daraja a idon sauran" a binda ta faɗi a fili kenan cike da ɓacin rai.
Bankaɗo ƙofan Hajiya tayi, take kan Amna tayi, ji kake taas taas ta sakewa Amna tagwayen maruka biyu a kumatu, a fisace Amna ta miƙe tana kallon Hajiya da tayi mata wannan marin.
#Amna ta san wasu daga cikin labarin Safna yanzu,
Ga Hajiya kuma ta mare ta ba ɗaya ba har biyu, kuna ganin zata haƙura?
Toohh muje dai zuwa.
______________________________________________________________________________________________
Part 6️⃣5️⃣
▶️
6️⃣6️⃣
Guri ne mai kama da kogo, domin kuwa gaba ɗaya wurin duwatsu ne da aka sarrafa su da ƙasa, sai wasu abubuwa mai kama da na tsafi a mammane jikin bangon, da kuma rubuce-rubuce da baza kasan wani yare bane, hanyar shigan sa siriri ne sosai, kuma yana da matuƙar nisa kafin zuwa ciki bayan kona-kona masu tarin yawa, da ace wanda baisan wurin ba ya shiga tabbas zai ɓace ɓat aciki, bayan haka da ƙyar yayi awa ɗaya mai kyau ba tareda ya gommace da acikin ramin kunamu aka sa shi ba, domin yadda wannan kogon yake da matuƙar hatsari, amma idan da sanin mai kogon ka shigo to babu abinda zai sameka.
Mutane huɗu ne gurfane a ƙasa cikin wannan kogon, kowannen su guiwar sa a ƙasa hannayen sa kuma a haɗe ɗaure guri guda kuma ta baya, kan su kuma a ƙol-ƙole ba gashi, yayin da jikin su keta kyarma saboda tsananin tsoro da tashin hankalin da yake ziyartan kowannen su, tunda aka nufo su wannan kogon suka kasance cikin tashin hankali, bare bayan shigan su, abinda basu taɓa gani ba, ai ko ziyara akace suyi cikin wannan kogon abin tsoro ne, bare laifi sukayi aka kawo su ciki. gurin na da sanyi sosai amma yanayin da suke n'a tashin hankali yasa gaba ɗayan su zufa sukeyi mai matuƙar yawa kai kace tsomasu a ruwa akeyi.
Gefe guda kuma shugaban nasu ne tsaye, sai hular da yake kasan cewa a kansa kamar kullum wato hula mai malafa baƙi, kayan sa kuma ash colour bayan sa kuma PA ɗin sa ne Salman shima tsaye.
Ɗayan gefen kuwa wani gajeren mutum ne zaune kan kujerar sa mai kamar ƙashi da kuma wasu sur ƙulle à jikin kujerar, ƙugun sa ne kaɗai da yadi jawur dogo kamar wanda ya ɗaura zani, sai wasu abubuwa masu kama da layoyi a wuyar sa da damatsan hannun sa, sai wasu irin abubuwa kuma masu kama da jigida suma a ƙugun na sa, launin fatarsa kuwa kamar ansha fa mata launin blue, sai jajayen ƙananun idanun sa mai kama da idon 'yan China, fiskar sa a tamƙe babu alamar annuri ko ɗigo kamar bai taɓa dariya a duniya ba, yanayin sa dakuma shigen gaba ɗaya yafi kama da boka ko kuwa ince matsafi.
Shine matsafin dake jagorantar ƙungiyar POSPA, domin kuwa babu abinda maigida ZABBA BA yakeyi ba tareda sun bashi izini ba, sanadiyyar wannan matsafin ne ya ƙidaye wa muƙarraban sa sanya tifafin tsafi, dik abinda zasu aiwatar to shima na tsafi ne, domin ko kisa zasuyi sai sunbi dokar da Zabba ba ya ijiye musu ta hanyar bin wata hanya ta tsafi.
Misali. Idan zasu aiwatar da kisa to sai suyi amfani da bishiyar da aka sihirce ta. A cewar matsafin ƙahon tsafi ne ke shan jinin ta wannan hanyar, Rukunuwan muƙarraban Zabba ba guda uku ne, kuma babu sunan da suke kiran wannan rukenin face.
RUKUNIN FARKO.
RUKUNIN TSAKIYA.
RUKUNIN ƘARSHE.
A haka kawai suke kiran su, kuma kowani Rukini an ƙawata shi ne da surƙullen tsafi, ko wanne kogo ne masarrafan su, amma fa ko kusa sunfi wannan kogon kyan gani, domin ko gurin shigar sa kaɗai ma abin tsoro ne.
Mutane ti ƙa-ti ƙa ne kewaye da su, suma ƙugun su ne kaɗai da marufi, amma su na su farare ne, suma suna sanye da nasu kalar layun.
Zabba ba ne ya miƙe yana kallon wannan bokan ya ce, "maganar ka ne kaɗai muke jira a halin yanzu, dan a aiwatar da abun da ya kamata" ya faɗi yana zuwa inda mutanen suke sai da ya ƙare musu kallo dukkan su sannan ya ce, "dama na riga da na sanar da ku, in har kuka kuskure min to fa bazan bari ba" ɗaya daga cikin wa'yanda ke gurfanen ya fara magana a ɗar-ɗar yana cewa, "shugaba dan Allah kayi mana rai, wallahi bamu san abin zai yi haka ba, a gafarce mu baza mu sake ba" ya kai ƙarshe yana nishin da ya haɗe masa da komai, wahalar da yasha kafin zuwansa wurin, da kuma tsoro da fargaba.
Dariya Zabba-ba ya saki irin na bosen nan hahhahahahha, matsafi kuwa saida ya ja wani gurnani mai kamar zaki da ya dakatar dasu gaba ɗaya kowa yayi tsit, sannan ya fara magana kalma-kalma da muryar sa mai kamar gargada ba daɗin ji yace, "dole ne. Ayi wa ƙaho. Sadaukarwar su. Yanzu. Kafin lokacin hakan. Ya wuce".
"Yadda kace mtsafin matsafa" Zabba ba yayi masa maganar sigar kirari, da kallo kaɗai matsafi ya umurci wa'yannan ti ƙa-ti ƙan mutanen na shi, hakan yasa su zuwa suka ɗauke mutane huɗun nan sukayi wata hanya cikin kogon dasu, yayinda su kuma mutanen suke ta kuru-ruwan neman ɗauki.
"Ku wuce. Yanzu. Sai na gaba kuma." Cewar matsafin wa Zabba ba, murmushin gefen baki Zabba ba yayi daga bisani suka fice shi da PA ɗin sa. Motar dake parke a ƙofar kogon suka shige bayan sun fito.
AMNA.
A fisace ta miƙe tana kallon Hajiya da tayi mata wannan marin, Ruki ta shigo tana share hawayen munafurci, "ko ramawa zakiyi ne? Naga kina min kallon hakan, to ko cinyeni zakiyi? To wallahi kurwata tafi ƙarfin ki shegiya" cewar Hajiya tana kallon Amna, "niba mayya bace" Amna ta furta cikin muryar ta ta ɓacin rai, sakin baki Hajiya tayi tana cigaba da kallon ta, matsowa kusa Ruki tayi tana faɗin, "kin gani ko Hajiya? Dama nace miki sheɗanu ne suka shiga kanta, yanzu duk abin da take so take firzar wa mutane, shiyasa ta zuba min ruwan sanyi a jiki, wallahi Hajiya sai kin nemi abinyi tun kan iskar su sa ta kashe mu".
"Ba shakka wato shiyasa take abubuwan rashin hankali yanzu ko? To tayi kaɗan tsinanna, koda kuwa matattaran aljanun ne kanta to nida zuri'ata munfi ƙarfin ta wallahi" wani irin ƙullutun baƙin ciki ne ke tahowa Amna tun daga ƙasan zuciya, idon ta dake ƙasa rufe ne t'a buɗe, hannun ta da ta dunƙule saboda ɓacin rai ne t'a kuma damƙe shi, Hajiya kuwa tana shirin ƙara yiwa Amna masifa wayar dake hannun ta ya fara ƙara.
Amna ta ɗaga hannun ta cikin fitar hankalin ɓacin rai zata kaiwa Hajiya bugu kenan Hajiya ta juya dan fita zuwa ɗakin ta, saboda kiran Alhaji ne, memakon bugun Hajiya sai ta bugi iska, Idon Ruki na kan mahaifiyar ta dake fita hakan yasa bata ga abinda Amna tayi ba, Hajiya na fita Ruki ta rufa mata baya, Amna da idon ta ya fara rikiɗewa zuwa launin ja ne, ta nufi zuwa mirror, kayan dake kai gaba ɗaya ta zubda su, haka drawern dake gefe ma tayi wulli dashi, zuwa gurin kujera tayi shima ta ɗaga shi da ƙarfi ya kife, ƙara kawai take sakewa saboda yadda zuciyar ta take yi mata.
Jin kanta take yi a wani yanayi, saboda barin abunda aka mata dactayi, ya tafi a banza kenan? ko Mubarak ne yayi mata abu bata iya ƙyale shi saita rama koda kuwa kaɗan ne, iyayen ta kaɗai ne wa'yanda zasu iya sata gaba suyi mata duk abinda suke so ba tareda ta ce ko ihhim ba, amma sai gashi yanzu saboda gudun kar a cutar mata dasu tana jure abubuwa da dama, anya anya zata iya ci gaba da jurewa kuwa? Da badon Hajiya ta wuce ba da tabbas yau ta koya mata hankali, tun da ta ce ita baza ta kama girman ta ba, amma dole ta san abinyi, dole ta taka musu birki dan kar sukaita maƙura.
Ammu da komai ya faru a idon ta ne ta rintse ido, saboda ƙarar zubar da abubuwan da Amna take yi, domin tun bayan da Hajiya ta mari Amna ta farka, buɗe idon tayi jin shiru, ganin Amna tayi zaune gefen ta, ta damƙe katakon gaban gado sai saukar da numfashi kawai take, saboda yadda zuciyar ta ke tafar-fasa, har ta fara jima kawai taje ta sami Hajiyar ko kuwa Ruki da tana da tabbacin ita ta haɗa hakan, ta sauke ɓacin ran da ke damun ta.
Ji kawai tayi ana shafar mata gashin ta a hankali, tasan Ammu ce amma batayi yunƙurin hana ta ba, dan tana da buƙatar tausasawa yanzu, kanta Ammu take shafawa sosai duk da kuwa yadda hannun ta ke rawa, amma yau ta samu damar motsi da hannun ta da yafi na da da take yinsa kamar tafiyar tsohon kunkuru, lumshe ido Amna tayi tana mai jin natsuwa na shigan ta, a hankali ta konta kan cinyar Ammu ba tareda tayi niyyar hakan ba.
Ammu bata tsaya da abinda take yi mata ba har barci ya ɗauki Amna, kallon fiskar Amna take sosai tana ganin ikon Allah ƙarara dangane da wannan yarinyar, da ta sanar da ita sunan ta Amna, tana da saurin hasala sosai, halayyar ta da Safna akoi bambanci dayawa. Abinda Ammu ke tinani a ranta kenan. Taƙi natsuwa tun ɗazu da yarinyar ta sanar da ita gaskiyar komi, itama da so samu ne da tasami wanda zai taushe ta, amma baza ta samu ba.
Few moment letter. Kiran sallar azahar sama-sama Ammu taji, hakan ya sata kiciniyar tashi bayan tayi ƙoƙarin saukar da Amna daga ƙafan ta da ƙyar, ji kawai tayi an kama ta ana taimaka mata dan zuwa toilet, sai da Amna ta tabbatar ta kula da Ammu gurin yin alwala sannan ta fito da ita, ta shimfiɗa mata darduma ta zaunar da ita dan ta gabatar da sallah, kallon ta Ammu tayi, yau ta yi mata abinda bata taɓa ba a kwanakin da tazo.
Ita kuwa Amna shigewa bayi tayi dan aiwatar da na ta alwalar, bata san meyasa ba, amma ɗan kulawar da matar ta bata ɗazu yasa taji son ta ya shige ta, kuma tana jin yanzu zata iya yi mata komai a matsayin 'yarta. Bayan ta idar da sallah Amna ta fita zuwa kitchen dan kawo musu abinci, yauma dai-dai lokacin da suke sa abinci ta isa.
Ba tare da tace dasu ko kuci kan ku ba, ta fara zuzzuba abincin cikin plate, Saida ta ɗibi duk kalan abincin da sukayi tasa ko wanne a ƙaramin plate, duk da tasan ko kusa ita da Ammu baza su iya cinye abincin ba, sannan ta ɗauki ruwan gora ta fice, ko wa da ido kawai ya bita saboda sunga wannan Safnan ta sha ban-ban da wacche suka sani.
Tana isa ta tarar da Ammu har tanzu bata idar da sallah ba, hakan yasa ta zama jiran ta, bata ɗau lokaci ba ta idar, tana ganin Ammu ta idar da sallah ta miƙe ta ɗauki plate din ta kai gaban Ammu, itama tana zama gefen ta, hankalin Ammu ne ya koma kan ƙatoton tiren da Amna ta kawo gaban ta, ganin ƙananun plates tayi kusan bakwai sannan kowanne da abinci ciki, a hankali ta maida kallon ta kan Amna.
"Mada..." sai kuma ta dakata da kiran Madam ɗin tayi murmushi tana ƙara cewa, "daga yau n'a daina kiranki Madam inason nima inkira ki da Ammu kamar yadda Safna take kiran ki" murmushi Ammu tayi domin koba komai taji daɗin hakan, "daga yau muma zamu rinƙa cin dukkanin abinda suke ci Ammu, domin gidannan na ki ne ba nasu ba" cewar Amna cikin dakewa kai kace gidan su ne. Sai da ta tabbatar da Ammu ta ƙoshi sannan ita ta fara ci, tana ci Ammu na kallon ta, kallon jin daɗi.
Bayan ta mayar da Kwanukan kitchen ta dawo ta mayar da Ammu kan gado ta zauna kusa da ita tana faɗin, "iyayena ne aka