Showing 90001 words to 93000 words out of 129098 words
Chapter 31 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
yana tambayar sa mahaifin sa ya dawo ne? Sai ya amsa masa da sai gobe zai dawo. juyawa Dady yayi gurin ta ya fara gabatar mata da saurayin, "yata wannan sunan shi Aliyu, yaron aboki na ne, ku kasan ce tare kaɗan ina zuwa" Dady na gama faɗin haka ya wuce gurin wasu mutanen.
Matsowa kusa da ita yayi yana sakar mata murmushi, itama murmushin take masa na iyaka baki, "barka dai beauty" ya faɗi yana ƙara fa ɗaɗa murmushin sa, yana cigaba da cewa, "yau n'a fara ganin ki amma kika sa ce min zuciya" "iimm" ta faɗi cikin baki, "ƙorai kuwa a yanzu haka zuciya ta ba a tattare da ni take ba" "to tana ina?" Amna tayi masa tambayar, tana ganin daga haɗuwar su yau sai ya fara yi mata magana mara ma'ama?.
Shi kuwa ci gaba da magana yayi, "kin sa ce min zuciyar mana". "Kamar ya na sace maka zuciya? Ni da haɗuwa ta da kai ko minti biyar bai yi ba?" Tayi masa maganar tana mai kallon yana raina mata wayo, duk da ta san inda maganar ta sa ya dosa, murmushin dai ya kuma sakar mata yana cewa, "a gurin ki yake haka, ni kuwa tun lokacin da nayi tozali da ke, sai nake jin kamar na ɗauki shekaru da yawa a tare da ke".
Tsaki tayi cikin zuciyar ta, shi yasa ta tsani soyayya, domin haka yake sa mutane ƙare-rayi ba gaira babu dalili, wato shi wannan da yake a haka ya ganta shine ya zo, "ba sai na kai maganar da ni sa ba, i love you ina sonki kamar raina" ji tayi kamar ta kwashe masa fiska da maruka kyawawa amma ina babu hali.
Ya kuma cewa, "don Allah ki faɗamin wata kalma ko guda ce wacche zanji daɗin ta" a zuciya ta kuma cewa, "wato wannan shine daga ganin rago ya yanke shawarar ta layya ce, inba haka ba da ka ga sarkin fawa sai miya tayi zaƙi?" Ta faɗi tana ƙare masa kallo, gashi dai yana da kyau kaɗan, kuma baƙi ne, sannan bashi da jiki ko ƙonjin sa basu fito ba, daga ganin shi ragon maza ne, ita kuwa me zatayi da irin sa? Ko da ma wai zatayi soyayyar, abunda bata taɓa sawa ran ta ba.
Jira yake kawai yaji furucin da zata yi, duk da ya ga sai ƙa re masa kallo take, amma fa idan ya haɗa ido da ita wani kwarjini take yi masa, saboda ko ƙyafta idon ta ba tayi, kafin tayi magana Dady ya zo wurin yana faɗin "muje in haɗa ki da drivern yanzu" "komawa gida za tayi ne uncle? Indai wannan ne sai in maida ta" Cewar Aliyu don wannan wata hanyar samun damar sa ne ai.
Kafin Dady ya amsa Amna tayi saurin cewa, "no don't worry, akwai wani abun da zanyi ne" ganin yana son sake magana ne yasa ta ƙara saurin cewa, "Dady muje ko?" Ta furta tana yin gaba, shi kuwa da kallo ya bi ta, yana murmushi don shifa ya samu mata.
"Dubi yadda Dady ya mayar da Safna kamar wata gold, ko kula mu baiyi ba fa, ka lura da hakan?" Cewar Saleem bayan sun ga wucewar Dady, tsaki Marwan ya ja sannan ya ce, "kai wannan ne matsalar ka? Ni abun da ke damu ns shine wannan babban matsayi da aka damƙa mata, kuma mamaki na Dady bai sanar mana da abunda za a gabatar a nan babba bane, Dubi manya-manayan mutanen da suka halarta a filin nan, kuma wai duk saboda ita su kazo, duk da cewa na san wannan dukiyar ta mahaifin ta ne, amma nayi mamaki da aka mallaka mata duka wannan kamfanin a lokavi ɗaya, ko Dady fa babu sunan sa akan ko da kuwa ƙaramin cikin kamfanin ne".
"Nima mamakin da na ke kenan, shiyasa idan nace Dady na da kuɗi ya ke faɗar magan-ganu ashe dai saboda wannan ɗin ne" ya faɗi cike da damuwa da kuma baƙin ciki.
Nuna mata mota Dady yayi ya ce ta shiga, ya kuma bata katin sa yana cewa, "wannan katin da zakiyi amfani da shi gurin biyan kuɗin kayan da kika saya ne" ya faɗi tare da ƙara sanar da ita nombobin sa. Sakar mata ac driver yayi a motan, mutuniyar ku sai la pewa tayi bayan kujera, tana jin daɗin wannan ac da kuma ƙamshin da ke fotowa duka ta jikin ac ɗin.
Ganin yadda drivern ke tafiya da motar cikin hankali yasa ta ɗaga daga jinginen da take tana cewa, "ya kake taka motar kamar wa'yan da suke ciki barci su keyi an ce karka tashe su? Kuma kai ba tsoho ba" da sauri ya ce, "yi haƙuri Hajiya" "ba haƙuri ba, ƙara gudun motar za kayi, kuma ba sosai ba fa, saboda kar kaji na ce ka ƙara kasa mana gudu kamar zamu tashi sama".
"To Hajiya" cewar driver, duk da ɗazu ganin saliha yayi mata amma yanzu ya tabbatar da masifaffiya ce ita, "yauwa ko kai fa? Yanzu kai da kanka baka ji tafiyar yafi yi maka daɗi ba ne? Ai da ni zanyi tuƙin da kaga abu wallahi" ta faɗi tana komar da kan ta jikin kujerar motar.
A bakin wata ƙatuwar shopping ya tsaida motar, juyawa wurin ta yayi yana faɗin, "Hajiya mun iso" ba tare da ta amsa masa ba ta sauko daga motar tana duban shopping ɗin, ta riga da ta kalli ƙarshen mamaki, wato haɗuwar Mai daraja company, don haka yanzu duk haɗuwar abun da zata gani ba zai sa tayi mamaki sosai ba, shi yasa duk haɗuwar wannan shopping ɗin bai sa ta zura mai idon ta ba.
Kaya masu kyau ta zaɓa bayan ta shiga ciki, da a ce Zuby za tazo ta ga wannan shopping ɗin da ta ƙaryata kan ta, ita da ke son yin bagu. Kuɗi sosai kayan suka ci, duk da dayawa ta zaɓa amma masu tsada ne sosai. Sa kayan a mota driver yayi yana kuma jan motar zuwa gurin siyan waya. Nan ma mai tsada ta ɗauka duk da saboda ya burgeta ta zaɓe shi, Bayan ta biya kuɗin ta hanyar katin da Dady ya bata suka juyo gida.
Driver ya ɗauki kayan yana bin bayan ta da shi zuwa falo, yayin da Hajiya da ɗiyar ta suke tattaunawa, "ke Autah, wai ina labarin ɗan Gomna ne kam? Kin daina yi min maganar sa" cewar Hajiya, Ruki ta ce, "ai baki sani ba Hajiya, tun yaushe muka rabu da ɗan Gom..." saurin katseta Hajiya tayi da faɗin, "me kike cewa ne? Akan me zaki rabu da shi?".
"Kwantar da hankalin ki Hajiya, ke fa kika ce min in na samu wani in rabu da shi" Hajiya ta kuma cewa, "haka na ce in kin samu wani, to akan me yanzu kika yi hakan?" Sai da Ruki tayi murmushi sannan ta cigaba da cewa, "to yanzu ɗin samun wani nayi, mutumin ya ci kuɗi, ya sha kuɗi, kai harma yayi wanka da kuɗi" gyara zama Hajiya tayi tana cewa, "ke bana son baganar hauka, to inba hauka ba, taya mutum zai ci ya sha kuma yayi wanka duk da kuɗi?".
"Kai Hajiya, daɗi na da ke wani lokaci kamar 'yar ƙauye kike, ba fa ina nufin ya ci kuɗi ba, ina nufin ya ci ya sha abinci mai tsada saboda dukiyar da yake da shi, don a yadda naji daga bakin sa, zai iya yin ta kara da Dady gurin dukiya" ba tare da ta ji rashin daɗin furucin Ruki na farko ba ta saki murmushi har cikin ƙasan zuciyarta ka na ta ce, "keh haba? Ashe dai ina zaune nan ina wani sabga Auta na na can tana kankaro min mutunci cikin ƙawaye?".
"Hmm ba shakka Hajiya faɗin ta ki, tun tuni nake son in sanar miki amma bamu samu zama ba, kin ga nima na daɗe ban fita chilling da manyan gayu na ba saboda rashin natsuwar da ba muyi ba sanadiyyar yarinyar nan" faɗin Ruki. Lokacin Amna ta danno kai ciki bayan sallamar da ta gabatar, shiru Hajiya tayi kamar an ɗauke wuta, domin har yanzu ba ta manta komai ba, to taya ma zata manta? Ita da ga abun ɗuriya ƙa ƙabe da wuyar ta kamar da shi aka haife ta.
Amna kuwa tsayawa tayi tana kallon su, "Hajiya ina za'a kai?" Cewar driver domin ya ga kamar Amna bata da niyyar yi masa magana, don tun da ta sanar da shi ya ɗauko kayan ya yi mata magana amma bata amsa mai ba, haka ya ɗauko kayan duk da kasancewar sa babban driver a kamfani kuma da ɗadɗe.
Bata amsa masa ba yanzun ma saboda kallon su Hajiya da take yi, sai kuma ta ce tana kallon su Hajiyar, "am Ruki na ce bah" kallon ta Ruki tayi haɗi da yi mata kallon banza, wani shu'umin murmushi ta saki, a zuciyar ta ta ce, "dama ke kin samu bonus babu abin da nayi miki shiyasa kike jin kan ki a hayaƙi har yanzu, a fili ta furta, "zo ki taimaki mutumin nan ki kai min kaya na ɗaki, saboda hannuna na riƙe da wasu" sai a lokacin Ruki ta kai duban ta kan kayan da mutumin ya riƙo masu uban yawa.
"Cabb! Hajiya kinga yawan kayan da ta dawo da su kuwa?" Da azarɓaɓi Hajiya ta juya don tabbatar da maganar Ruki, sai dai yadda wuyar ta ya bada wani ƙara sakamakon juyawa da tayi da sauri yasa ta miƙe tana sakin ƙarar a zaba, Amna bata kula da Hajiya ba ta kuma yi wa Ruki da ke riƙe da Hajiya magana, "Ruki mutumin nan ya gaji fa" "bazan kai ba! Aikin ki nake yi ne? Dubi halin da Hajiya ke ciki, amma kina yi min maganar banza", cewar Ruki cikin ɗagun murya harda jan tsaki.
"Ijje kayan kayi wucewar ka" Amna ta faɗiwa drivern bayan ta ijje jakar wayar da ke hannun ta, ficewa driver yayi bayan ya musu sallama, ta ku tayi har tana zuwa gaban su, yayin da Hajiya kuwa ta ke zare da ido tun da taga ta fara ta ku izuwa gaban su, ita Ruki kam ko kallon ta bata ƙara yi ba, Amna tana zuwa ta kama hannun Ruki ta fara jan ta, tana yin upstair da ita, ita kuwa sai masifa take yi tana cewa Amna ta sake ta ko kuwa ta fasa mata kai yanzu".
Sai da Amna ta kai ta dai dai saman Upstair sannan ta tsaya, kallon ta Ruki ta fara yi cikin fargaba, domin tayi duk yadda zatayi don kuɓutar da hannun ta amma abun ya ci tura, domin ji tayi kamar harda gam a hannun Amnan, sannan kuma ga zafi da hannun yake mata, ba tare da Amna tayi mata magana ba ta hankaɗa ta kan matattakalan.
#TOOOHH RUKI TA SHIGA HANNU.
GOBE AMNA ZATA FARA AIKIN OFFICE.
SAI MUN KASANCE GABA DON JIN YADDA ZATA KASANCE.
______________________________________________________________________________________________
Part 8️⃣7️⃣▶️8️⃣8️⃣
Hajiya kuwa da ta biyo su ta fara roƙon aljanin jikin Amna ita duk a tunanin ta aljanin ne yazo don Ruki ta ɓata mata rai, tsayawa tayi ba tare da ta hau matattakalan ba, sai dai hankaɗawar da Amna tayi wa autar ta ne yasa ta shiga tashin hankali, ƙara ta saki sai dai wuyar ta shaƙe.
Ruki kuwa Amna na hankaɗa ta da zuciyar ta ya bada bugu arba'in a take, sakin ƙara tayi dai dai faɗawar ta goshin nan ya bugu da tayis, tana ci gaba da ƙara kuma tana gangarawa, ihu Hajiya ta cigaba da yi murya can ciki, sai dai batayi ni sa da gangrawar ba Amna ta dakatar da ita ta hanyar sa mata hannu.
Ɗago ta tayi ta dire ta ƙasan upstair ɗin, da sauri Hajiya ta zo tana tsugunnawa kan Ruki, lokacin bakin ta ya buɗe sai ba Amna haƙuri take, Ruki kuwa da azaba ya isheta ta saki kuka, musamman yadda taga jini na ta zuba daga goshin ta, daka mata tsawa Amna tayi cikin muryar da ta ɗan canza, amma bai bada kalmar tsoro sosai ba, tunda babu kofin da tasa wancan karon, "zaki rufa mana baki ko kuwa mu haɗiye kii? Donma mun ji tausayin ki? Da mun barki kin ƙaraso ƙasa da kin yi kukan da dalilii, ko kuma yanzu ma bata ɓaci ba sai mu maida ki".
"A a a a" Ruki tayi saurin faɗi kamar zata ari baki, wucewa Amna tayi ta bar su, zuwa tayi ta ɗauki kayan ta wuce ɗakin Ammu da shi, ta so ta bar Ruki ta gangara a step ɗin gaba ɗaya, amma sai kuma taga kada abun yayi yawa domin yadda ta tura ta da ƙarfi idan har ta takai ƙasa zata iya karyewa ma.
Tana shiga cikin ɗakin ta tarar da Jummala na kwantar da Ammu kan gado, ijje kayan tayi kan kujera ta sakarwa Jummala murmushi, tare da yi mata godiyar kula da Ammu da tayi, "Safna'u ai ni na ɗauka ma zaku daɗe, ashe ba wani daɗewa zaku yi ba" cewar Jummala, Amna ta ce, "eh dama ba aiki naje ba sai gobe zan fara" "masha Allah, amma naji daɗi sosai 'yata, yanzu baki da matsalar ta kura a wannan gidan, dama ina faɗa miki komai da lokaci, kinga lokacin yayi".
Murmushi kawai Amna tayi mata ita kuwa tayi musu sallama ta tafi. Zuwa Amna tayi kusa da Ammu ra fara nuna mata kayan da ta siya, murmushi kawai Ammu take mata, sai da ta gama nuna mata kayan duka amma banda wani ƙaton leda dake gefe, ɗaukar sa tayi tana faɗin, "Ammu kin san me nene a cikin nan?" Ta faɗi tana murmushi, "kayan da na siya miki ne a ciki" ta faɗi tana fitar da su, "na fison dogayen riguna Ammu shiyasa na siya miki su kema" ta faɗi tana nunawa Ammu su, masu matuƙar kyau sosai, harda takalma ta siya mata da kuma himar ɗin kanti.
Idan Ammu ta ce batayi farin ciki da hakan ba to tayi ƙarya, har ƙara jin ƙaunar yarinyar tayi cikin ran ta, murmushin dake kan fuskar ta ya ƙara bayyana, Amna ta fiskanci hakan, shiyasa itama taji daɗi a ranta, saboda Ammu taji daɗin abunda ta siya mata. Sai kuma ta zauna gefen gadon tana mai tuno da ahalin ta, tana tuna lokacin da Ummee ta siyo mata kaya ita da Mubarak.
Murmushi mai cike da kewan su tayi, sai kuma ta sauke numfashi, haɗi da kwantawa kan katifa, sai da ta ɗau minti goma a haka kafin ta ɗaga kanta, mamakin abunda ya faru ne ya dawo mata, musamman wannan signing ɗin, wannan wani'irin abun mamaki ne? Taya sa hannun ta da Safna zai zama iri ɗaya? Abunda bata taɓa ji ko ganin faruwar sa ba, wannan sai kace a tatsuniyar almara? Hannunta ta dunƙula hannun ta tayi tasa a ƙasan gemun ta, alamar ƙara zurfafa mamakin ta.
Na na ta mamakin signing ɗin tayi-tayi a cikin zuciyar ta, juyawa tayi inda Ammu take Ammu kuwa dama tun ɗazu take binta da ido, "Ammu kin taɓa jin inda signing yazo ɗaya?" Ta faɗi tare da matsawa gun Ammun, ta bata labarin abunda ya faru bayan tafiyar ta, sai dai Ammu bata nuna wani alama da zai sa ta fahimtar Ammu tayi mamakin abinda ya faru ba.
"Ammu kamar bakiyi mamaki ba, ko fiddo idon ki bakiyo ba, kamar yadda ranar da na sanar dake cewa ni ba Safna bace kikayi" Ammu tayi mata murmushi, "to ko dai dama kin san da maganar ne?" Rufe ido Ammu tayi ta kuma buɗewa, ƙara kaɗan ta saki tana cewa, "Ammu yau kin bani amsa, kenan kin sani? Hakan yayi, amma nifa haryanzu mamakin signing ɗin Safna da yake irin nawa nake, koda yake babu abinda Allah baya yi" cewar Amna tana ɗauko jakar wayar da ta siya ta buɗe haɗi da ciro wayar.
Kunna shi tayi domin ta riga da ta ce suyi masa setting ɗin sa ta yadda idan ta buɗe amfani kawai zatayi da shi, nunawa Ammu tayi tana faɗin, "yayi kyau?" Idonta ne ya fa ɗa kan time and date, murmushi tayi tana furta "my birthday" cikin zuciya, sai kuma ta zare ido a fili ta furta, "my birthday? My birthday!! my birthday and Safna's birthday".
Ta faɗi da ƙarfi cikin wani mamakin tana miƙewa, nan ta fara sintiri a cikin ɗakin taje ta dawo, idon Ammu biye da ita, don bata gama fiskartar abun da yasa Amna miƙewar ba, saurin zuwa gun Ammu tayi tana faɗin, "Ammu my birthday! My birthday Ammu! Kuma kuma ranar haihuwar Safna!" Ta faɗi cikin ƙara shiga wani mamaki sabo fill, "ranar haihuwar mu ɗaya kenan? Taya hakan zaiyu?" Ta faɗi tana kuma zama gefen Ammu, Ammu ma mamakin ne ya cika ta matuƙa, taya hakan zai faru?
Ba tare da ta tambayi Ammu ba ta fara bincike ƙananun drawers ɗin gado tana faɗin, "ina hotunan ku suke Ammu? Suna nan?" Tana tambayar ba tare da kallon Ammun ba, haka ta rinƙa firfito da kayan ciki, babu akwati bare tayi tunanin ansaka a ciki, ta ɗau 'yan mintuna tana binciken hotun har ta gano su, "yauwa ga sunan!" ta faɗi tana zuwa gaban Ammu da su, baje su a ƙasa tayi ta fara gani.
Ture hoton tayi cikin gigicewa da ya wuce na lokacin da ta fara kallon hoton Safnan, ba komai bane ya haddasa mata wannan abu sai ganin hoton Safna da ta gani lokacin da take ƙarama, zuwa kusa da Ammu tayi cikin ruɗani