Showing 9001 words to 12000 words out of 129098 words
Chapter 4 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
wacche da ita gwara babu, to in baki sani ba bari in faɗa miki, Cewa akayi ita ta cinye ubanki" ta ƙarashe maganar suna dariya ita da Saleem wanda take bi.
Rintse ido tayi saboda yadda maganar ya bugi zuciyar ta, batasan lokacin da kuka ya kufce mata ba tayi waje, tafawa sukayi Saleem yace "shegiya". A ɗaya daga cikin kujerun hutawar da ke garden ta zauna, ta na cigaba da kuka, ta zaɓi zuwa wurin ne domin bata son Ammu take ganin ta cikin damuwa, gudun karta ƙara sata cikin tinani.
Babbar mata ce tazo kusa da ita, Ɗaya daga cikin masu shara da goge-goge Jummala, zama tayi a gefen ta cikin kulawa tace mata, "Safna'u kiyi haƙuri kinji, ki daina sa yawan damuwa à ranki tun kina ƙanƙanuwa dake, ki fauwa-lawa Allah komai, insha Allahu komai mai wuce wa ne".
dago manyan idanun ta tayi, daya fara can zawa izuwa launin ja, tana kallon Matar, daga ita sai baba Hambali mai gadi ne kaɗai masu tausayin ta cikin masu aiki, share hawayen ta tayi, ba tare da cewa komi ba, Jummala ta ƙara cewa "ki ci gaba da haƙuri Safna'u mai haƙuri yana tare da Allah duk da nasan ke mace ce maihaƙuri" "Na gode Inna Jummala, amma ki koma ɗakin ki, kar a ganki tare da ni, kar nayi sanadin barin aikin ki" "to nabar ki lafiya 'yata".
Kontar da kan ta tayi a jikin kujerar, tana mai ƙara jin zafin abinda Ruki tayi mata, tabbas da ace yau tana da kwarin guiwa da yau tayi maganin Ruki, sai dai bata da wannan ƙwarin guiwar.
Bayan ya dawo, ya watsa ruwa yasa Riga marar nauyi fari da gajeren wando da yafi guiwa, yana da kyau sosai duk da baida haske sosai, duk à cikin yaran zainab yafi su kyau, haka kawai yaji yana da buƙatar zuwa garden don ya shaƙi sassanyar iskar da ke kaɗawa ta kyawawan shukokin masu ban sha'awa.
Yana isowa gurin yagan ta zaune ta kwantar da kanta jikin kujerar, sannan ga hawayen da ke zuba kan kyakykyawar fiskar ta, a hankali ya isa izuwa inda take, haɗe fiska yayi sannan yace "ke!, meya saki kuka?" A razane ta ɗago tana ƙoƙarin share hawayen ta.
Yakuma cewa, "ba magana nake miki ba?" "Yaya Yazeed am dama babu komai" "inga kina kuka amma kice bakomai?" Ya ƙarasa faɗi yana ƙure ta da idanun sa dake ƙara daburar da ita, "ba komai" ta ƙara faɗi a matuƙar tsorace,
"Bar wurin nan tun da bazaki faɗa ba" kamar mai jiran umarni, ta mike jikin ta har rawa yake yi, saboda ba ƙaramin tsoron Yazeed take ba, dan zata ita cewa tafi tsoron sa a cikin sauran 'yan uwan ta, shi kuwa binta yayi da kallo yayin da take tafiya harda wani harɗe ƙafa saboda tsoro, bai san meyasa yaji zafi lokacin da ya ga hawaye a idon ta ba.
AMNA.
Gwalo yayi mata yace, "ai dama nace ni zan cinye ki" war watsar da duwatsun da suke wasa Amna tayi, tana hararar sa sannan tace "wallahi rinto kamin kuma bazan yarda ba" ta faɗi tana miƙewa, shima miƙewar yayi ya kalle ta yana dariya yace
"ba wani nan" ya faɗa yana ƙoƙarin nufan ƙofar gida, dan yasan ta yanzu sai ta tada bala'i akan wasan Dara kawai.
Ai kuwa binsa ta fara yi "ina zaka!?" Tafur ta tana jin haushin cinye ta wasa da yayi, kan ya kai bakin ƙofa Ummee ta dawo daga maƙota, saurin zuwa bayan ta yayi yana faɗin "Ummee kiga Amna mugun ta take son yi min" ya ƙara she maganar yana nuna ta da yatsa.
"Wai ku bakwa girma ne?" "Ummee wallahi cuta na yayi à wasa" ta ƙarashe maganar tana bin sa, nan suka fara zagaye Ummee, tun tana kallon su tana daka tar dasu har ta fara jin jiri, saboda yadda itama take juyawa.
"Kai! Kaaai!" Ta furta da ƙarfi, hakan yasa su daka tawa, "miƙomin kujera" ta ƙara faɗi tana riƙe kanta dake juyawa, riƙo ta Amna tayi daidai lokacin da Mubarak ya kawo mata kujerar, ta zaunar da ita suna faɗin "sannu Ummee".
Kitchen Amna tayi ta ɗibo ruwa a glass cup, ta kawo wa Ummee, ta miƙa mata kana tace, "sannu Ummee baki da lafiya ne?" Saida tasha ruwa rabin kofin sannan tace, "eh" ta faɗi tana haki kamar ita ce tayi gudun,
Suka haɗa baki gurin faɗin "menene ke damun ki Ummee" sai da ta kallesu tace, "ku mana!" "Mu kuma" nan ma suka furta a tare.
______________________________________________________________________________________________
Part 1️⃣1️⃣▶️1️⃣2️⃣
"Mu kuma?" nan ma suka furta tare haɗi da shiga damuwa saboda jin Ummee tace su ne damuwar ta. Ganin yadda sukayi kicin kicin da fuska yasa ta cewa, "eh kune matsala ta!, kullum girma kuke amma sai ƙara cin ƙasa kukeyi har yaushe eh? kai Mubarak kamar ba kaine babba ba, ke kuma Amna dube ki yanzu ke in a Ƙauye kike ba har da ƳaƳa ba?"
"Ummee Aure fa!" Amna ta faɗa tana ɗan turo baki kaɗan, "Auren fa!" Ummee ta faɗa mata haka, tin tsirewa da dariya Mubarak yayi, "Ummee da ma Auren kukayi mata wallahi" yana ƙara kwashe da dariya, "Ummee kin gani ko?" Tafaɗi tana ƙoƙarin kamo shi, ɗaukar sandar daya ke kusa da ita tayi tana ƙoƙarin zuba musu, suka sa gudu, suna faɗin "sorry sorry Ummee for give us please".
Ɗakin Mamma suka nufa, sukayi kan ta, "wayyoo kon-koso ta wayyo kun-kuru ta, Biba zo da Ruwan ɗumi ki matse min, kafin a kira mai ɗoriya" Mamma ta faɗi jin yadda suka faɗo kan ta. Ai kuwa sai suka kwashe da dariya jin yadda Mamma tayi maganar, Ummee ma tsayawa tayi tana dariyar ta ciki-ciki.
ganin dariyar da suke mata ya ƙara sata faɗin "kai ba na son ɗiban albarka kun kusa karya ni kuma kuman dariya?" "Biba duba min yaran nan fah" ta faɗi haɗi da juyawa gun Ummee, "au kema dariyar kike?" dena dariyar Ummee tayi da cewa "a ah Mamma nifa biyo mutanen kin nan ne nayi sun isheni da sangarci", "au to kice kece kika sa su karya ni?, kinji yadda kon-koso ta ke zugi kuwa?" Cewar Mamma.
Mubarak yace, "Mamma daɗina da ke raguwa ce" "naji niɗin raguwa ce, kai da kake jarumi ai gudun bula-la kayi" darawa suka ƙara yi, "Ummee Allah ya ƙara miki lafiya, kiyi haƙuri baza a sake ba" Amna ta faɗi harda sinnan da kai, hararar ta Ummee tayi, "ke dama ai babu wanda yakai ki, sallon iya bada haƙuri" ta faɗi tana ficewa daga ɗakin, harar Mubarak Amna tayi tace "zamu haɗe wataran ai kuma sai na rama rinton da ka mini" "oho dai" ya faɗi tare da fita waje, Mamma ce tace "oh Allah ni talatu ina ganin ikon Allah yara ne iya kaji".
DARE mahutar Ba wa.
Baba, Ko alamun bacci babu a idanun sa saboda tsaban yadda tinani yayi masa cunkushe a Zuciya, wannan aikin da ya ɗauko yasan ba ƙaramin aiki bane, "ta'ina zan fa ra? ina zan ka ma? waye ZABBA BA shugaban ƙungiyar safara da ƙwayoyi ta POSPA?.Ƴan ta'adda masu ɓa ta rayuwar Samari da Ƴan-mata cikin halin Shaye-Shaye" duk wannan tambayar kansa yake wa.
Jin alamun motsi da Ummee taji ne yasa ta buɗe ida nuwan ta, haɗi da juyowa inda yake, ganin sa a zaune yasa ta ta shi ta zauna, tana kai duban ta kan a gogon da ke maƙale a bangon ɗakin, sannan ta juyo da duban ta gare shi, cike da mamaki da tinanin me yahana mai gidan ta barci har tsawon wannan lokacin ƙarfe biyu na dare?
"Abban Mubarak! Abban Mubarak!" Sai da ta kira sunan sa sau biyu sannan ya juyo da sauri, saboda yadda ya nutse cikin kogin tinani, "na'am" ya amsa mata "Abban Mubarak lafiya kuwa har yanzu baka kwanta ba?" "Lafiya ƙalau!" "haba dai lafiya, na lura tun da ka dawo daga wurin aiki yanayin ka yake wani iri, dan Allah sanar dani", "kar kisa kanki à damuwa bawani abu bane kawai tinanin yadda zan war-ware wani matsala nake yi, amma ba wani abu bane".
Ba don ta gamsu da maganar sa ba ta rabu da shi saboda yadda yaƙi ba ta damar sa ke yi masa wata tambayar, shi kuwa Baba har yanzu bajin bacci yake ba, saidai ya konta ganin Mai-ɗakin sa nason shiga damuwa sanadin ganin sa haka.
WASHE GARI.
Sammakon fita aiki yayi, saboda akoi binciken da yasa ayi masa, sai dai duk sammakon da yayi, Abokin na sa bai samu zuwa da wuri ba, zaune yake à office ko aiki ya ka sa yi, don ya ƙagu yaji daga ba kin mai binciken. Sai da aka shuɗe awa biyar ƙarfe goma tukunna Tukur yazo.
Yana sallama Baba yayi saurin miƙewa daga zaunen da yake, izinin shiga ya basa, suka gaisa Tukur ya ɗora da cewa, "I'm sorry Aboki na, rashin gani na da bakayi da wuri ba, wata matsala ce ta tsaida ni", "ba damuwa Tukur tunda ka zo yanzu shikenan, kawai sanar dani abinda nakeson ji", Baba yayi maganar yakoma mazaunin sa, tare da yi masa alama da ya zauna.
Zama yayi tare da fito da wasu takardu daga cikin jakan da ke rataye a kafaɗar sa, ya ijje a gaban sa kan tebur sannan ya fara magana, kamar haka, "kamar yadda na fara sanar da kai a waya, shugaban Ƙungiyar POSPA mutum ne mai matuƙar hatsari, kuma su karan kansu muƙarraban na sa ba sanin sa sukayi ba, sai manyan cikin su, su ma manyan da kansu kusan tar su hatsari ne babba, a yadda naji, bawai daga wata ƙasar ake kawo ƙwayoyin ba, amma babu wanda zai faɗa maka inda ake buga kwayoyin bere inda suka dasa wannan Ƙungiyar".
Yafaɗi yana buɗe file ɗin yana nunawa Baba, yacigaba da cewa, "sannan wannan Ƙungiyar ba wai lalata tarbiyya kaɗai tayi ba, tayi Sanadiyyar mutuwar matasa da da ma". za ro file ɗaya yayi Yace, "wannan file ɗin cases ne na mutanen da suka rasa rayukan su sanadin POSPA".
Yaƙarashe maganar yana maida kallon sa kan Baba, saida Baba yaja dogon numfashi daga bisani yace, "na ji gaba ɗaya abubuwan da kace kuma nagode da ƙoƙarin da kayimin, amma abun da na keson sani yanzu shine a ina akafi sayarda ƙwayoyin? saboda a tinani na inda akafi safaran nan Ƙungiyar take".
"a ah bayadda kake tinani bane, saboda a koi abinda na fiskanta game da lamarin, ana saida wannan ƙwayoyin a ƙasashe ka ma daga nan Arewa maso gabas, Arewa maso kudu, kai harma da ƙasashen ƙetare, amma abin mamakin shine, garin Kaduna, kokusa babu wata hanya da ake shigo da ita wannan garin".
Cike da mamaki Baba yace, "amma ya akayi duk cikin garu-ruwan nan Garin KD yafita zakka cikin su?" "Nima abinda ya ban mamaki kenan, amma abinda nakeso da kai Hussaini, a matsayi na abokin ka ina baka shawara, da ka ijje wannan binciken da kakeyi, saboda kamar kana ƙoƙarin cusa kanka ne cikin rijiya me ɗauke da Macizai".
Miƙewa Baba yayi yafara magana "Tukur yakama ta kabani ƙwarin guiwa ba wai ka kashe min guiwa ba, kamar yadda kasa ni ne na shiga aikin Jarida ne badon in rinƙa nemo labarai na shirme ba, nashiga aikin Jarida dan nemo labaran muggan mutane masu ɓa ta mana ƙasa, to har ila yau ban canza daga wannan manufar ba".
Shima Tukur miƙewa yayi yana mai cewa, "hakane dan ni kaina shaida ne akan jajircewa da kayi, gurin tai makawa jami'an tsaro, amma ina so kasa ni wannan yasha bam-bam da sauran, ta yu ni kaina da na taimaka maka gurin sa mo en wa'ennan sirrikan zan iya kasan cewa cikin hatsari, bare ace kai, dan Allah ka nisanci duk wata matsala da zata sa rayuwar ka cikin hatsari".
"A ah Aboki na, ban fara wannan aikin dan na bari ba, saboda haka ba zanyi maka alƙawarin bari ba, dan haka kwanan nan zan shirya zuwa garin Kaduna dan yin bincike acan, dan nasan Ruwa baya tsami banza, tabbas akoi dalilin da yasa Ƙungiyar miyagu ta POSPA basa safarar su a can". ya ƙarashe maganar cike da yaƙini.
Ajiyar zuciya Tukur ya sauke, Abokin na sa na da kafiya, yasan babu wanda ya isa dakatar da Hussaini akan wannan binciken tunda har ya da ge, fatan nasara kawai yayi masa, suka fara taɓa wani hira.
AMNA.
Wa'en nan 5 guys ɗin ne suka yo inda suke, sai dai da ganin su Amna ta cewa friends ɗinta da su sha re su kada su kula su, cigaba da tafiyar su sukayi ba tare sun kalla inda suke ba.
shan gaban su sukayi, wani irin warin shaye shaye ne ke tashi a jikin su, wanda wannan warin ya haddasa wa Amna ta shin zuciya, da sauri ta durƙusa a wurin tana kora ro Amai, sannu Abokan ta na kullum Wali, Zarah, da kuma, Nabila, sukayi mata cikin kulawa.
Inda su kuwa su Jalo suke mata kallon Ƴar renin wayo, wato kenan Amna ta nuna su ke wa ri, "ke Ƴar renin hankali kina nufin mu ke wa ri, lallai ma kincika shegiyar mara kunya, ba cewa ake kina da ƙarfi a Makarantar nan ba to yau zuwa mukayi musauke miki jiji-da-kanki".
Jalo wanda shine bos ɗin su Yafaɗi hakan, miƙewa Amna tayi bayan ta wanke bakinta da ruwan da Zarah ta bata, takawa ta fara yi, Abokan ta ne suka fara tausan ta, saboda sanin halin ta da sukayi, tsayawa tayi jin an riƙe mata hannu, "please Zakanyan Baba ki taushi zuciyar ki, dan Allah kar ki biye su" Nabila ta faɗi hakan, sai dai kafin Amna tayi mata wata magana, ɗaya daga cikin yaran Jalo, Zanga ya kwashe Nabila da mari, yana faɗin.
"A gaban buss ɗin mu kike kiran wata Zakanya, ba wani Zaki daya wuce Bos Jalo" shima yana kai aya Amna ta kai masha nushi a baki, har sai da bakin sa ya fashe, saurin ja da baya yayi haɗi da riƙe baki, yana jin zugi kamar wanda aka bugawa ƙarfe a wurin, shafo wurin yayi aikuwa saiga jini,.
Gaba ɗayan su suka zaro ido waje, ƙawayen Amna suka haɗa baki gurin faɗin, "Amna please let's go". Cikin fusata Jalo yace, "ke! To bari kiji ɗan wannan abun da kikayi bazai sa naji tsoron ki ba" Yafaɗi yana ƙoƙarin yowa kanta, saidai ya dakata saboda ganin police sun shigo Makaran tar, suka juya sunai mata kallon zamu haɗe.
Dariya suka ba ta, hakan ya sata murmusawa, hakan yayi dai-dai da lotsawar kumatun ta, wato dimple, wanda ke ƙara tsatso da kyawun ta, Wali, yace, "yan iska matsoratan banza, ashe duk iskancin su suna tsoron 'Ƴan-sanda".
"Hmm rabu da su tantirai kawai, bansan dalilin da yasa suka sawa Amna ido ba", cewar Zarah, Nabila ma tace, "neman rigima kawai mana" dai-dai isowar Mubarak, har lokacin kuwa Amna bata sanya musu baki a maganar da suke ba, dan ita haushi ne ma ya cika ta, dan so tayi ace yau sun cire raini tsakanin ta da Jalo, saboda tun ba yauba suke neman abunda zai haɗasu faɗa da ita,.....
#Ƴan-uwa na kunji dai yadda Jalo suka gudu saboda ganin Folisawa, to ya zata kasan ce in suka gamu akaro na gaba?
Ga binciken da Baba ya jefa kansa a ciki, shin zai je Kaduna?, shin zaiyi nasara?, ko ya ya.
Nasan kuma zaku so sanin waye ZABBA BA shugaban ƙungiyar POSPA, da kuma ita karan-kanta Ƙungiyar.
kuci gaba da bin Alƙalami na, dan jin abu-buwan da zasu faru cikin labarin AMNA DA SAFNA.
______________________________________________________________________________________________
Part 1️⃣⃣3️⃣▶️1️⃣4️⃣
SAFNA.
Tana dawowa daga Makaranta ɗaya daga cikin ma su aikin flower Habu, ya ba ta saƙon Marwan cewa, "ya ce ki kai masa takalmin sa a wanke masa kan ya dawo, saboda shi zaisa da yamma, sannan...." tsaida shi Safna tayi da cewa "where is the shoe?" "ehh?" Ya furta saboda bai fahimci inda maganar ta dosa ba, "ina takalmin yake?" takalmin mai matuƙar tsada brown colour ya ɗauko, ya miƙa mata yana ƙoƙarin sake magana, sai dai wucewar Safna ne yasa shi ƙunshe bakin na sa.
Safna kuwa, tasan Marwan ya bar mata aikin ne bawai haka kawai ba, ɗan kwanan nan da akayi ba tare da ya mata komi ba, ba daɗi yayi masa ba, tasan hanya ce kawai ta musguna mata da yake son yi, inba haka ba ko kuɗin aikin bai bata ba, sannan ga masu aiki da su ya dace ya bawa amma ya zaɓi ya ba ta.
Shiga gefen su tayi, tana gama dik abinda zatayi ta ɗauki kuɗin ta tafita dan kaiwa wani mai wankin takalmi da yake kusa da gidan, sai dai ta yi rashin sa'a saboda bata tadda shi ba.
cikin rashin jin daɗi ta dawo gida, da tinani meza tayi yanzu, aikuwa sai shawara yazo mata, na ta goge masa takalmin da tsumma da ruwa, wata zuciyar ta ce mata 'inkuma yaga baiyi ƙyalli ba fa?' aikuwa taba zuciyar ta amsa a fili, "sai in sha fa masa Mai".
Nan ta fara goge sa saida ya fita tas sannan ta je kitchen ta ɗibo Man-gyaɗa takoma gyafen ɗaki ta