Showing 96001 words to 99000 words out of 129098 words

Chapter 33 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

47

yana nufar hanyar gida kamar yadda ta bashi umurni, yana yin parking bata jira ya buɗe mata ƙofa ba ta fice, nufar falon tayi hannun ta riƙe da jakan ta, tana tunanin abin da zata ce wa Dady na rashin dawowa da batayi da baƙon sa ba, sannan ga shi bata dawo da wuri ba bere ta sanar da shi abin da yasa hakan.

Shiga tayi tana ƙara fa ɗaɗa abin da zata cewa Dady cikin ranta, me yasa ma bata karɓi layin sa ba? Da abin ya zo da sauƙi, muryar Dady ta ji kamar yana hira da wani, sai dai muryar sa ne kaɗai yake tashi, ba tare da tsoron ko bazai ji daɗin ya sata aiki bata yi ba ta nufi inda yake, ganin mutum tayi, kasan cewa ya bata baya sannan kuma yanayin yadda ya zauna kan kujerar kamar kwanciya ne yasa bata ga wani alama ta kayan sa ba, fa ce kwantaccen gashin sa da ta hango.

Sallama karo na biyu tayi tana kuma nitsawa cikin falon, amsa mata sallama Dady yayi tare da furta, "yata ga baƙon da nace ki tarba ya riga ki ƙarasowa" ya faɗi yana murmushi da cewa baƙon, "ka ga wacche na ce ta je tarban ka nan, eh ai ina ganin ko kuskure aka samu, amma bazan barka ka dawo kai kaɗai ba, saboda ni da kaina naso inzo, amma da yake wani uzuri ya riƙeni shi ya hana ni zuwa" ya faɗi yana murmushi sosai, dan wannan baƙon ba na rainawa bane.

Ita kuwa Amna ƙarasowa ta cigaba da yi don ganin wannan mai girman kan, to idan ba ɗan girman kai ba, taya bayan ance ga wanda aka aika dan ɗauko shi amma bazai iya juyowa ya ga wacece ba, dan da alama ma tun ɗazu da Dady yake magana shi kaɗai ke kiɗa da rawar sa baya ba sa amsa.

Sai da ta zauna akan kujerar sannan ta kai duban ta gare sa don ganin sa da kyau, hakan yayi daidai da ɗagowar sa setin da take, idon su ya kuma haɗewa guri ɗaya, tashi daga zaman tayi tana kallon sa cikin mamaki, saurayin da ta tsaida ɗazu a filin jirgi! A zuciyarta ta furta, "innalillahi.. a she shine wanda nake nema ɗazu!" shi kuwa bai nuna wani mamaki a ganin ta ba sai ma ɗauke kai daga kallon ta da yayi ya maida kan wayar da yake latsawa, "ya dai my daughter? Ya da ganin sa kin tashi alamar mamaki?" Cewar Dady ganin abinda da tayi.

Saurin ya ƙe baki tayi ta dawo da duban ta ga Dady tana shirin magana, Shuraim ya ce, "dama mun haɗu da ita a airport, That's why she was surprised to see me here, right?" Ya faɗi da murmushin gefen baki idon sa ga Amna, "au haba? Ashe ma kun haɗu, amma rashin sani ya sa baku gane ba". Wannan karon Amna ta kauda idon ta gare shi, ta ce "eh Dady, na rasa numbern da ka bani ne" "ok good 'yata, wannan sunan shi Shuraim ɗan wani abokina daga ƙasar London" ya faɗi yana maida kallon sa gun Shuraim ya kuma cewa, "wannan 'yata ce Safna kenan, sauran ma suna nan zaka gan su daga baya".

Lokacin Hajiya ta zo da masu aiki bayan ta ɗauke da kayan abinci da na marmari da kuma na sha, ijjewa sukayi Hajiya kuma harda rusunar da kai tana gaishe da baƙon cikin girmamawa, "Shuraim ko? Maraba-maraba sannu da zuwa" shi kuwa da fine kawai ya amsa yana cigaba da latsa wayar sa, "cab ɗi! Dubi yadda Hajiya ke wani gaidashi kamar ɗan sarki, amma ko ɗan girman nan bai bata ba, amma wannan akwai mugun hali" Amna ta furta acikin zuciyar ta.

"Da kun ijje masa a dining ai, ku ɗauka ku kai masa dining, ko kuma kana da buƙatar inda za'a kai maka tsakanin dining da ɗaki ne Shuraim? Take this house as yours" cewar Dady yana kallon baƙon na sa cikin girmamawa. Amna kam kallo kawai take bin su dashi, tana kallon ikon Allah domin yadda su kewa mutumin da Dadyn ya kira Shuraim magana cikin girmamawa.

'Yan aikin sun sa hannu zasu ɗauka abubuwan da suka kawon kenan Shuraim ya fara magana cikin muryar ta ƙama ya ce, "ku bar shi!" ya faɗi yana kallon inda Amna take ya kuma cewa, "Safna can you take it?" Kallon sa tayi na rainin wayon maganar sa a kan ta, kuma ta tabbata da ita yake tun da gefen ta ya kalla, kan tayi wani magana Dady ya ce, "of course me zai hana? 'yata ɗauka kayan duka ki kai masa dining ɗin kin ji?" Ya faɗi yana cigaba da washe baki.

Wucewa Hajiya tayi lura da yadda fiskar Amna yayi kamar ɓacin rai, to kuwa gwara ta bar wurin, don har yanzu bata gama warkewa ba, kuma ga audugar a wuyan ta. Amna kuma kallon Shuraim tayi a ranta ta furta, "lallai ma wannan mutumin!"

Shin ya kuke ganin Amna zata kasan ce da Shuraim? Ga dai abin da ya fara faruwa a tsakanin su.

Koma dai wace tuya za'ayi? Ku kasan ce da Alƙalamin {Mrs Umar}👸🏽

Na san kuna nan kuna jiran jin abun da ya faru da Safna, ta mutu ne? Ko tana raye?

Kar ku damu, zaku ji komai lokacin da ya dace🥰

___________________________________________________________________________________________________________

Part 9️⃣1️⃣▶️9️⃣2️⃣

Miƙewa tayi bayan Dady ya kuma yi mata maganar, ɗaukar kayan abincin take tana binsa da kallon haushi, yadda yake wani jiji da kai me yake ɗauka a zuciyar sa ne? Saboda renin wayo har da sa ta aiki, to ko don abun da ya faru ne yasa ya raina mata wayo? Sai da ta kammala gaba ɗaya ɗaukar kayan sannan ta dawo ta sanar da Dady ta kammala, juyawa Dady yayi gun Shuraim ya ce, "zaka iya zuwa yanzu komai a kammale yake ɗana, idan ka gama kuma Safna zata nuna maka ɗakin na ka" zaro ido Amna tayi da jin abun da Dady yace, "Dady me zai sa sai ni zan nuna masa? Da ace zaka sa su Marwan da hakan zaifi" tayi maganar cikin sanyin murya.

Ɗago ido Shuraim yayi yana duban ta, jin kamar tana nufin baza ta iya kai sa ɗakin ba sai dai a nemi wani, lallai wato itama tana ji da kanta kenan?abin da ya faɗi a cikin zuciyar sa kenan, duk da kuwa maganar da tayi ba na ɓacin rai bane, "duk kansu ba sa nan 'yata, ita kuwa Auta har yanzu ba tada lafiya, kuma ban san abin da ya sameta ba, daga ita har Hajiya babu wanda ya sanar min da abin da ya faru" cewar Dady ita kuma ta amsa masa da cewa, "ba damuwa Dady zanyi kamar yadda kace".

A ranta kuma tana tunanin wato tun hankaɗar jiya da tayi wa Ruki shine ya sa har yanzu ba tada lafiya, Dady kuwa juyawa gurin Shuraim da ya miƙe yayi yana cigaba da sakin fiska ya ce, "ɗana muje in nuna maka dining ɗin ko, saboda idan ka kammala ka samu hutu, kamar Shuraim ba zaiyi magana ba, sai kuma ya ce, "I prefer she takes me there" yanzu ma ya faɗi yana kallon ta, haɗe fiska kaɗan tayi tana yi masa kallon ka raina min hankali, kan tayi magana Dady ya ce, "'yata ɗan zo kaɗan".

Gefe sukayi shi da Amna yana cewa, "don Allah kar ki ɓatawa wannan yaron rai kinji? He's my special guest, ki gabatar masa da abinci cikin girmawa, sannan ki nuna masa ɗakin nan na gefen hanyar can cikin kulawa, I’d love for Shuraim to feel happy and comfortable in this house, kin ji 'yata?" ya faɗi yana nuna mata ɗaki da yake ɗayan gefen, ba hanyar da ɗakin Ammu yake ba, a jiyar zuciya Amna ta sauke bayan ta gama jin maganar Dady, murmushin zanyi hakan tayi masa, sannan suka dawo.

Murmushin da iyakar sa fatar baki tayi masa, sannan ta ce "can we go to the dining now?" Ta faɗi cikin dauriya saboda ba ƙaramin girma maganar yayi mata ba, don ta ga kamar so yake ya maida ta baiwar sa, ai kuwa gwara ta taka masa birki, idan ma don abinda ya faru ɗazu ne yake mata haka.

Ta fiya ta farayi yana binta baya, taku yake kamar baya son taka ƙasn, kuma hankalin sa na kan wayar sa, sai ɗan ɗago kan sa da yake kaɗan, Amna kam sai tayi gaba sai ta juya ta ganshi a baya, yana tafiya kan tayis kamar wanda aka sa dole, "lallai, kuma wai Dady cewa yayi in basa kulawa, abin da ba zaiyu ba kenan" ta faɗi tana hararan inda yake, a haka har suka ƙarasa dining.

Juyawa tayi ta ga babu alamar Dady a wurin, don yanzu bata hango shi kamar ɗazu, hakan yasa kafin ya kaiga zama a kan kujerar wurin ta furta, "kai malam" ba tare da ya kalle ta ba ya zauna a kan kujerar, hakan da yayi kuwa ba ƙaramin ɓata mata rai yayi ba, matsowa kusa da shi tayi ta ƙara faɗin, "kai Malam da kai fa nake" ta faɗi da ƙarfi, ɗago idon sa yayi yana kallon ta ya furta, "are you talking to me?".

Ya faɗi yana kafe ta da ido, cikin haushin tambayar renin wayon da yayi mata ta ce, "who else do you think I'm talking to? Of course you!" Murmushin gefen baki kawai yayi yana kallon ta yadda take masa magana kamar wata isassa.

Fiska da murya cikin gargaɗi ta fara cewa, "ka ga Malam! Kada abun da ya faru ɗazu ka ɗauke shi a zuciyar ka, saboda naga sai wani take-take kakeyi, ni banyi kama maka da wanda zata yi soyayya da kai ba, idan ma don wannan ne kake nuna wani hali, to yafi maka tun wuri ka sani ni ba wacche za'a raina bace, don bazan ɗauki hakan ba" dariya ta bashi hakan yasa ya miƙe yana duban tsawon ta da murmushi ya ce,

"Da gaske ba kyason raini jaruma?" Daga idon ta tayi tana kallon sa yadda fiskar ta yake ƙasan kan sa, don ya fita tsawo, "ni dai na faɗa maka" ta furta kawai tayi hanyar tafiya, "a ah Safna har Ya gama cin abincin ne?" Cewar Dady daya taho wurin, "a ah Dady dama zuwa zanyi in ɗan huta, saboda a gajiye na dawo" ta faɗi don baza ta iya tsayawa da wannan dogon ba.

Alamar mantuwa Dady ya nuna sannan ya ce, "Oh i forgot, kinga na manta da yau kin fara zuwa company, kuma nasan kin sha aiki a can, to kije ki huta 'yata" "thank you Dady" ta faɗi tare da sakin murmushin jin daɗi ta wuce, amma wannan bawan Allahn yana da fahimta sosai. Zama Dady yayi kan ɗayan kujerar yana cigaba da sakewa Shuraim fiska ya zauna don ya taya shi hira.

Amna kuwa tana zuwa ɗakin ta tarar da Ammu kan darduma, ɗaki kuma Jummala ta ƙara tsabtace shi kamar yadda tace mata, ijje jaka da mayafin ta tayi, ta shiga toilet dan watsa ruwa.

Dady. "Eh ta fara zuwa company dan gudanar da aiki, a matsayin ta na C.E.O" cewar Dady, sai da Shuraim ya jin jina kai ka na ya ce, "But why would you give her such a position when she’s still so young? The job will be too hard for her."

"Yes that's right, amma idan ba damuwa ko zan iya roƙan alfarma a wurin ka?" Cikin mamaki Shuraim da hankalin sa yake a waya ya dawo da hankalin sa gun Dady ya ce, "alfarma wani iri!?" Ya faɗi cikin ƙasaita. Sai da Dady ya ji nauyin maganar da ya ke son yi masa sannan ya fara faɗin, "tun da ka sanar da ni cewa, aikin da kazo yi ba yanzu zaka fara ba, shine nake neman alfarma akan kayi aiki a company na, a matsayin rage lokaci, amma kafin kace komai Shuraim, please don’t take my words as disrespect toward your position."

Ya faɗi cikin sanyin murya don Shuraim ya amince, idan har ya samu wannan damar to kamar wata hanya ce ta samun muradin sa akan mahaifin Shuraim ɗin, shiru Shuraim yayi kamar mai nazari sannan ya ce, "ok i understood, so there's no need for me to think, if you want i can start from tomorrow" ya faɗi cikin nuna alfarma yayi wa Dadyn.

Shi kuwa Dady wani irin farin ciki ya gauraye masa zuciya, duk da yanayin maganar da Shuraim yayi masa, amma ya san yana da sauƙin kai, da alama ya fara irga damar sa, "thank you so much my son, I'm so happy, n'a ji daɗi da ka karɓi alfarmata, kuma har zaka iya farawa daga gobe, amma na gode" Shuraim bai amsa ba.

ƘARFE HUƊU.

Ruki ce ta sauko ƙasa tana tafiya kamar wacche aka yiwa dukan tsiya, sabida har yanzu jikinta cikin tsami yake mata, kallon Dady tayi da ke ta hira à waya, da alama da wannan abokin na sa na London yake waya, zuwa tayi ta zauna kusa da shi, fiskarta alamar shogoɓa, dai dai lokacin Dady ya sauke wayar daga kunnen sa, duban ta yayi yana faɗin, "my Autah me yake damunki ne?" Sai da ta sauya fiska ta ce, "Dad kawai wani zazzaɓi ne ya kamani, but da sauƙi yanzu".

Cikin kulawa ya kuma cewa, "Oh sorry dear, ko zamu je hospital ne?" "No Dady, na ji sauƙi yanzu" ta faɗi don tasan babu buƙatar zuwa asibiti, iyaka dai ta sha maganin tsamin jiki.

Shuraim ne ya taho falon cikin wannan takun n'a sa na ƙasaita, tun da Ruki ta ga tahowar sa ta saki baki tana kallon wannan balaraben, duk da cewa ba baƙonta bane kallon mai launin fata haka, bisa tayi rayuwa a ƙasar wajen itama, amma wannan ya burgeta sosai, "ki rufe bakin ki mana Hajiya Ruki" cewar Amna bayan ta taho wurin bayan kiran da Dady yayi mata, sai kuma ta ga Ruki nawa Shuraim kallon ƙurilla, juyowa da sauri Ruki tayi gun Amnan tana haɗiye wani nyawun tunowa da abin da tayi mata.

Zama Amna tayi dai dai da zamar Shuraim shima a gefe, da wannan halin na sa na rashin kula, sakewa Dady murmushi tayi haɗi da sake gaishesa, amsawa yayi da murmushi shima, sannan ya gabatar da Ruki gun Shuraim, barin wurin Ruki tayi, don ita harga Allah ba ta ƙaunar ta haɗu da Amna yanzu, juyowa Dady yayi gun Amna ya ce, "yata kasancewarki sabuwa a fannin company, kuma kike da babban matsayi, naga ya kamata ki samu wanda zai taya ki da kuma nuna miki yadda zaki gudanar da aikin ki cikin ƙwarewa".

Jin jina kai Amna tayi don ya kamata ta samu hakan ƙwarai, saboda ta san yadda zata gudanar da komai cikin kulawa, "hakane Dady, zanyi farin ciki da haka" cewar Amna, sai dai fa tun da ta zauna ko kai idon ta batayi inda Shuraim yake ba, Dady ya cigaba da cewa, "na ji daɗi da kika fahimta, saboda haka na roƙi alfarmar ɗana Shuraim, kuma ya amince, harya bani tabbacin gobe zai fara".

Amna da tun da Dady ya ambaci sunan Shuraim ta zaro ido, ta katse numfashin sa da faɗin, "Dady wani Shuraim kake magana?" Sai da Dady ya juya gurin Shuraim yayi murmushi sannan ya dawo da kansa gun Amna da murmushin ya ce, "Shuraim dai wannan 'yata, kuma na tabbata zai baki gudunmawa kafin ya bar aikin" kallon Shuraim tayi, ya sakar mata murmushin cikin baki, haɗe masa fiska tayi ta maida kallon ta ga Dady, kiran da ya shigo wayar Dady ne yasa ya furta, "excuse me" ya faɗi yana barin wurin da sauri.

Juyawa Amna tayi zata wuce cikin ɓacin ran rashin daɗin abin da Dady ya faɗa, "da alama kina da girman kai 'yammata" taji muryar Shuraim bayan ta, juyowa tayi tana kallon sa da mamakin furucin na sa, miƙewa yayi yana kuma cewa, "don kin samu zan taimaka miki kike wani ɗagun kai? Amma nayi mamaki da kika kasance mai hali biyu" yayi maganar yana kallon inda take, ba tace da shi komai ba sai kallon sa da take kawai, shi kuma ya cigaba da cewa,

"Then listen to me! Kar ki ɗauka zaki iya sake yin amfani da ni kamar yadda kika aikata, wai don ki tsira da mutuncin ki à gaban wani, I'm not a liar" Shima yayi mata maganar cikin gargaɗi, matsowa à hankali tayi wurinsa, cikin mamaki da kuma haushin kalaman sa ta fara magana itama cikin n'a ta salon, "dama a tunanin ka ni ɗin nayi arha har haka ne? To bari kaji, kar ka ɗauka don na gwada amfani da kai, zan zamo wata ballagazar mace a idon ka! Kamar yadda na faɗa maka da fari, nayi amfani da kai ne kawai a matsayin mafita gareni, idan ba haka ba me zaisa nayi mu'amala da mutum irinka? mai girman kai! Kuma don ance zaka taimaka min a company ba shi ke nuna zan buƙaci wata taimako daga gare kaba! Saboda bazan taɓa yin hakan ba".

Tana ida maganar ta kuma juyawa zata wuce taji ya kuma cewa, "tabbas zaki buƙaci tai mako na Safnah!" Ya faɗi da yaƙini, "never!" Ta furta ba tare da ta juyo ba ta wuce abun ta. Tana isa ɗaki ta zauna kusa da Ammu tana cewa, "Ammu kina jin wani abun ɓacin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login