Showing 105001 words to 108000 words out of 129098 words

Chapter 36 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

53

kasa da na fi ki ƙuri'u yau ɗin nan" hararansa kaɗan tayi ta dawo da duban ta ga mutanen ta ce, "I think abun da zamu tattauna akai kenan, amma inason naji daga bakin kowanne a cikin ku, na cewa ya kawo wata matsala da ya ci ace an gyara, ko kuma ɗaukar mataki, domin salo zamu canza akan yadda ake gudanar da companyn a baya".

Nan dai kowa da maganar da yake faɗi har aka kammala, suma da kansu wa'yannan manyan ma'aikatan sun jinjinawa Amna, duk da cewarta mai ƙananun shekaru amma ta iya tsara abu na hankali, gefe ɗaya kuma sun jinjinawa Shuraim kan ƙoƙarin da yayi. Tashi Amna tayi ta nufi hanyar fita, wasu biye da ita, tsayawa tayi a wurin réceptionist tana yi mata wasu maganganu akan ta nema mata gurin da ake motsa jiki mai inganci, tana gama faɗa mata ta wuce office. Daga nan ta wuce ɗakin hutu don ta samu damar natsuwa akan aikin da zata yi.

"Madam C.E.O ya da gajiya da wuri haka?" Cewar Shuraim bayan ya shigo yaga tana ƙoƙarin shiga wannan side ɗin, "ba a san shugaba da sarewa dayawa haka ba, ko da yake may be ita ɗin raguwa ce" takowa tayi zuwa inda yake tana bin sa da kallon haushi, shima yana binta da kallon sannu da haushi, mintuna huɗu suka shafe suna wannan kallon sa'insan a tsakanin su, kamar Amna zata yi magana sai suma ta wuce ta koma kan kujerar ta, ta fasa shiga ɗakin, ta fara duba computer.

ai zauna ba saima cigaba da magana da yayi, "to ya kike ganin za mu tsara sabbin tsare-tsaren?" Ganin bata amsa masa ba yasa ya zauna ya fara rubuta abun da ya dace, ya tura gaban ta ya ce, "gashi na rubuta abun da ya dace, sai ki ƙara naki ciki" nan ma bata amsa masa ba, shi kuwa miƙewa yayi ya nufi ƙofar fita, yana ƙara cewa, "ya kamata ki zagaye duk wata kafa ta companyn ki, domin ki san cikakken abun da ke wakana a ciki, daganan sai ki kuma sanya tsarin ki" yana faɗi ya fita, da sauri ta jawo note ɗin da yayi, ta fara dubawa, domin dama kawai nuna masa rashin kula ne take, amma duk mganar da yake cak take ijje su a kanta.

Kamar yadda ya ce, tafiya take wasu ma'aikata na yi mata ja gora gurin nuna mata komai na kamfanin, hatta masarrafan duk san da ta bibiya, zuwa yayi ya iske ta a cikin masarrafar ana yi mata bayani akan komai, domin har ta gaji ma sabida kasancewar wurin da girma sosai, haka ko wani sashe yake. "Madam C.E.O ta karɓi shawarar assistant ɗin ta karo na farko, shin farinciki zaiyi ko kuma?" Ya faɗi tare da murmusawa, sauran mutane kuwa kallon su kawai su ke.

Bayan sun koma gida.

Amna ce cikin ɗaki tana zaune kan kujera tana duba computern da ta dawo da shi gida, tana ƙara har haɗa duk abubuwan da zatayi, wayar ta ƙarama da ta ɓoye à drawer ne ya fara ƙara, kamar kullum da gudu taje ta ɗauka tana karawa a kunnen ta haɗi da sallama, amsawa yayi ya ɗora da faɗin, "aikin ki na kyau C.E.O, kina bin komai cikin tsari kamar dama kin san da aikin, duk da wannan mai taimakon na ki yana baki gudummawa sosai" "a ah ranka ya daɗe MR, ba ya taimako na, kuma bana buƙatar taimakon sa, kai kasan waye shi kuwa? Sai jiji da kai, sannan shi fa ɗauka yake yafi kowa basir.."

"Wait Amna!" MR ya tsaidata, shiru tayi Tana maida numfashi, don ita haushi taji da ya ce wai Shuraim na taimaka mata, "kamar yanzu ya daina nuna miki girman kan ko?" "Eh ya bari amma ba duka ba, kuma ya akayi kasan..." nan ma ya sake tsayar da ita, "na kira ki ne don in tunatar da ke akan aikin da na baki a baya, don kamar kin manta da komai, na ce ki rinƙa sawa Jamilu ido, amma ba kya hakan" ita tama manta da wannan batu amma saboda ta nuna masa kamar tana yi sai ta ce.

"Gani nayi babu amfanin sawa mai hali irin na Alhaji ido, saboda mutum ne mai kirki" "Babu ruwan ki da halin sa ko kuma yadda yake, so nake ki cigaba da sa masa ido akan duk abin da yake yi, koda ma ace kiran waya ne!" "Toh insha Allah zan cigaba da hakan MR" kashe wayar kawai MR yayi ita kuma ta kwantar da kanta jikin kujerar, "shima da kanshi ɗan girman kai ne kamar wancan Shuraim ɗin" ta furta aranta, ko yaushe komai zaizo ƙarshe?.

DARE.

Suna zaune suna cin abinci, lokaci-lokaci Amna na kai duban ta kan Dady, yayin da take ciyar da Ammu, "Dady dama ina son in roƙi wani abu" "faɗi 'yata ina jinki" ya ba Amna amsa, ta cigaba da magana da cewa "dama so nake nace maka ina son ni da Ammu mu tashi daga ɗakin da muke ciki yanzu, mu koma sama muma" furzar da shayin da ta shigar baki Hajiya tayi, harda ƙwa-rewa tana kallon Amna cike da mamaki.

Sai da Hajiya ta tsagaita da tarin da take sannan hankalin kowa ya sake dawowa kan Amna saɓanin Shuraim, ita kuwa kamar bata san suna yi mata kallon mamaki ba ta cigaba da cewa, "na so na faɗa maka amma ban ganka da safe ba, saboda wancan ɗakin kama yake da na masu aiki, ko da ma ace masu aiki irin na gidan nan ne bai kamata su kasance a ciki ba, kuma asama zaifi iska da kuma nishaɗi a wurin Ammu, domin har na sa a kawo mana kayan da zamu zuba cikin ɗakin".

"Amma kin isa isassa yanzu, wato kin samu dama har zaki..' sai kuma Hajiya ta tsaya da maganar da take faɗa, ganin ɓacin rai na shirin mantar da ita kwakwan da ta sha a hannun Safna, Amna kuwa dama kallonta kawai take ta ji zancen da zata ƙarisa, sauran gudan jinin Hajiya kuwa zaro ido su kayi ganin Hajiya na shirin taɓara, wani murmushi mai haɗe da takaici da kuma ya ƙe Hajiya ta saki tana cewa, "am am am so nake nace ai dama ke isassa ce yanzu, kuma kina da damar yin tunanin da kike so, ko?" Girgiza kai su Saleem su kayi alamar eh gaskiya ne.

Shuraim kam bai ɗago komai ba, Dady ya ce, "eh lallai gaskiya ne 'yata, kina da damar ki zauna a duk inda kike so cikin gidan nan" "wow hakane Dady?" "Sosai kuwa Safna" sai da ta ni sa kaɗan ka na ta kuma cewa, "to idan kuwa haka ne ina son ni da Ammu mu koma ɗakin Hajiya da zam.." "ehhhhh! Me kike cewa Safna?! Akan me zaku dawo ɗaki na da zama? Kenan mu haɗu mu uku a ɗaki ɗaya ko me?" "A ah Hajiya baki gama fahimta na bane, so nake na ce ni da Ammu ɗakin ki zai zama na mu, ke kuma sai ki zaɓi wani ɗakin, idan yaso ma ɗakin da muke ciki yanzun kike so falillahil hamdu".

Hajiya bata iya ƙara cewa komai ba, sai sakin baki da tayi, suma sauran yaran mamaki suke sosai yadda Safna ta sauya a lokaci kaɗan, Dady kuwa cewa yayi ai hakan ba wani abun damuwa bane tun da gidan akwai ɗakuna dayawa, sai Hajiyar ta zaɓi ɗaya daga ciki, wayyo Allah zo kuji yadda zuciyar Hajiya ke ɗagawa saboda baƙin ciki, barin wurin tayi harda yin tuntuɓe. Ita ko Amna yin hakan tayi domin so take ta kasance ɗakin ta kusa da na Alhajin ko ƙila zata fi sa masa ido kamar yadda MR ya ce, kuma ɗakin Hajiyar ne wanda yake ɗan kusa da shi, domin ko wani ɗaki da ɗan ta zara kan kaje wani.

Dady kuwa sanja magana yayi da batun auren Marwan, "tooh! Ashe Marwan an kusa angwan cewa? Masha Allah kuma saura kwanaki ƙalilan" cewar Amna a zuciya.

Washe gari aka cire duk wani kaya dake cikin ɗakin Hajiya aka mai da mata wani ɗaki da yake saman Upstair ɗin, aka kuma gyara ɗakin Hajiya, aka zuba kayan ɗaki, masu kyau masu tsada, wa 'yan da suka fi na Hajiyar ma, ɗakin ya zama kamar na matar sarki, kasa zaune Hajiya tayi, bata san lokacin da ta saɓi jakarta ba sai gidan Ladingo abokiyar ƙulla sharri.

"Ƙawata please calm down, yaushe zaki ta da hankalin ki har haka? Kije ki ɗaura wa kanki ciwon zuciya, kinga in kika mutu sai Safna ta cigaba da cin karenta babu babbaka, ni na kira ki musamman na sanar dake na samu wani sabon malami, amma kikace afurr ke ba bu wanda zai ƙara cin kuɗin ki" cewar Ladingo, "naji-naji to yanzu na amince, idan ba haka wallahi duk mafarki na zai zama tarihi idan banyi da gaske ba".

"Ai kuwa ta zo gidan sauƙi tun da har kika amince, kinga sai mu ba malamin umarni ya sa aljanin da ke jikin ta ya lahanta mana ita" Hajiya ta amshe, "faƙat wallahi da na huta" ta faɗi tana saukar da numfashi, domin baza ta ƙyale yarinyar nan haka ba, kuma a yanzu kome zata iya yi don ta gama da babin ta.

Amna.

Tafiya zuwa company tayi, ta bar masu aikin decorating suna kammala komai. tana shiga company ta tarar da Shuraim ya kammala mata duk abun da ya kamata fannin doka da dabaru, murmushi ta saki wan da bata san lokacin fitan shi ba, domin komai yadda ya tsara ya burgeta.

Ranar aka ƙaddamar da duk tsare-tsaren, inda yayi wa wasu daɗi wasu kuma ƙunci, amma dolen su su bi idan ba haka ba kuma sai dai su bar companyn kamar yadda sabuwar Shugaba Safna ta faɗi, duk wanda bazai bi doka ba to hanya ce mai sauƙi ya bar company kawai, sannan duk wanda ya karya wata doka, za'a aikata mishi hukunci daidai da yadda laifin sa yake.

AFTER THREE DAYS.

Hajiya ce ke ta shirin kai kayan auren Marwan yau, ita da mutane da abokan arziƙi, duk da kasancewar ta mara son mutane saboda tana da kuɗi, amma mutane sun zo ,kama daga dangin kusa.

SHURAIM.

Kwanan nan duka Amna ba ta komawa gida da wuri, kuma ya lura da tana ɗaukan lokaci kafin ta dawo, hakan yasa yau yake son sanya mata ido yaga ina take zuwa? a gaban idon sa ta shige mota driver ya ha, shima shigar motan sa yayi don yanzu shi da kansa yake tuƙa motar. Tafiya suke yana bin su a baya.

Shin ko mene ne manufar MR akan Dady?

Amna zata iya wannan sa'idon kuwa?

Ina ne Amna me zuwa? Shuraim zai cimma ta?

Hajiya zata cimma burin ta?

Mu kasance a part next don jin yadda

zata kasance

✌🏼

___________________________________________________________________________________________________________

Part 9️⃣9️⃣▶️1️⃣0️⃣0️⃣

Tafiya suke yana bin su a baya, har suka yi tafiya mai ɗan ni sa, fitowa yayi yana kallon inda Amnan ta shiga, rubutun da aka rubuta a bangon wurin ne ya bashi amsar tambayar sa, gurin exercise, da mamaki ya karanta rubutun bangon, "me ya kawo ta gurin motsa jiki kuma!" Ya tambayi kansa cikin mamaki, zuwa gurin drivern yayi, driver ya gaishe sa cikin girmamawa, "me ya kawo ku nan?" Yayiwa driver tambayan, sai dai ya bashi amsa da shima bai sani ba, kawai madam C.E.O ce ta bashi damar ya kawo ta. Wucewa kawai yayi ba tare da ya sake tambayar sa komai ba, yana shiga ma'aikatan suka tarbe shi.

Amna kuwa da shigan ta taje ɗakin sauya kaya, ta canza ta sanya riga da wando irin na sport ta kuma ɗaure gashinta da kyau, yanda zai sa ta taji daɗin exercise, ta daɗe da son ta rinƙa motsa jiki amma bata samu ba, don ko da idan tana yin haka a gida sai su Ummee su hanata, amma yanzu ta samu dama, shiyasa take amfani da lokacin tashi office tazo ba tare da kowa ya sani ba, ita kaɗaice a wurin saboda ita ta buƙaci hakan, zata fara kenan taji tafi a bayanta, da mamakin jin haka ta juya don ganin waye, "kai ne?!" Ta faɗi da mamaki, Shuraim kuwa tsaida tafin yayi da ƙarasawa inda take.

Kallon ta yake sosai ganin ko irin kinyar nan bata ji ba, na ya gan ta ba yadda ya saba ba "me kake min kallo haka? Ko a London ɗin ba sa sa riga da wando ne?" Murmushi yayi yana faɗin, kin burge ni ne, shiyasa nake kallonki, ko zan iya sanin dalili?" Ƙaramar tsaki taja, ta fara training ɗin ta, "abun mamaki! Da alama kina son zama jaruma" "Me kake nufi?" "Ina nufin kina son ki zama jaruma kamar dai ne" tsayawa tayi ta miƙe tana kallon sa, ta ce, "kai jarumi ne?" "fiye da haka! Kina tantama ne?" Murmushi mai ƙara ta yi masa "Ko zamu gwada? Sai in cire tan-tamar" ta faɗi dama yana raina mata wayo da yawa, don haka yau ta cire shakkun Dady kawai ta nuna masa ita ba sa arsa ba ce.

Shi kuwa dariya maganar ta ya bashi, sai da ya dara sannan ya kuma cewa "mu gwada me? Wai faɗa kike nufi?" "Eeh!" Amna ta faɗi idon ta kansa babu tsoro, da mamaki ya ce, "kina ganin zaki iya faɗa da ni?" Ta bashi amsa "fiye da haka" ta faɗi idanuwan ta kansa ko gezau babu, kallonta Shuraim ya cigaba da yi da mamaki sosai a ransa, da alama tana da ƙwarin guiwa, saboda kallon da take yi masa ya tabbatar masa da hakan, to amma me yasa zatayi irin wannan furucin? Bayan ta san baza ta iya ba?

Lura da yadda yake mata kallon maki yasa ta cewa, "tunanin bazan iya ba kake yi? To gwara ka cire wannan tunanin, kawai mu gwada mu fitar da zakaran ne ko kuwa zakanya" wani dariya yayi irin na ta ƙara bashi dariyan nan, sannan ya kuma faɗin, "jarumtar ki gurin magana yana burgeni, but ina son ki sani, ba anan ne yake nuna ke jaruma ba c..." kan ya ƙarisa maganar ta kai masa nushi a fiska yayi saurin kaucewa, juyowa yayi yana kallonta cikin tsantsar mamakin yadda ta kawo masa wannan hannun kamar wata ƙwararra.

Nan ta fara kai masa nushi yana kaucewa, shima yana kai mata tana kaucewa, sun ɗau minti bakwai suna wannan faɗar, wanda ni zan kirashi da exercise na musamman, sai dai mintuna nan babu wanda aka kaiwa nushi, ganin tabbas wannan yarinyar fa ta iya faɗa, hakan yasa shi canza mata wani salon, saurin yin bayanta yayi kan ta juyo ya ɗauki wani dogon ƙyalle da yake saman kan ƙarfen tafiya, ya riƙe da hannu biyu ya saƙala mata shi a jiki, sannan ya janyo ta yayi saurin baya da ita sai jikin gini, amma ba tare da hannun sa ya taɓa jikin ta ba.

Amna kuwa da ya shammace ta, zata juya ta kai masa wani hannun, taji ya saƙale mata abu a jiki da sauri kuma ya tura ta jikin bango, sai dai bata bugu sosai ba, kallon sa take da mamaki ganin fa shima soja ne, murmushi yayi mata yana faɗin, "na jinjina miki 'yammata, but you can't!" Yana yin maganar taji wani haushi a ran ta, bata yarda da rashin nasara a gasa ba. Ture sa tayi da sauri, kan ya juyo ta sa ƙafanta ta kai masa tokari a ƙafa, ƙasa kafafuwan su kayi, sai dai kan su ƙarasa ya miƙe, daidai da ta kai masa dunƙulen hannun, yana juyowa kawai nushin na ta ya sauka a gefen idon sa.

Hannun sa yasa a wurin sakamakon à gefen idon sa hannun n'a ta ya sauka, domin har ji yayi kamar har idon m'a ya samu, saurin zuwa wurin sa Amna tayi cikin damuwa ta furta, "Oh sorry, ba à idon ka na so nayi ba" ƙyallen nan ya kuma ɗauka da sauri, ya ta ɗe mata ƙafa itama tayi ƙasa, matsawa kusa da ita yayi ya furta, "da a ina kika so kiyimin naushin?" "A bakin nan na ka mai tsokanan mutane!" Ta faɗi fiska a haɗe, Shuraim ya kuma cewa, "sorry 'yammata amma fa da'alama kin bugu sosai gurin zaunuwa a ƙasan nan ko?" Ya faɗi yana dariya.

Miƙewa tayi da sauri zata kuma kai masa cafka ya kauce da faɗin, "you are already lost C.E.O, but don't worry na san kin nuna jarumta" hararan sa tayi don tayi mamakin da ta kasa warewa sosai tayi faɗa dashi a asalin ƙashin ta, amma nan gaba zata yi hakan, sai ta ragar-gaza masa fiska, daganan zai gane, ta faɗi cikin ran ta harda ƙofa.

Wucewa yayi ya ƙyale ta a wurin, sai dai fa zuciyar sa cike yake da tsantsar mamaki sosai, "tabbas yau na ƙara tabbatarwa, duk da naga ta kasa yi min haƙiƙanin asalin yadda takeyin, to ko don ba wai ranta a ɓace yake ba?" Ya faɗi ƙasan laɓɓa, Amma fa duk da haka inda tayi masa wannan nushin yana yi masa zugi, saboda yadda yaji hannun n'a ta kamar wani ƙarfe, lallai sai kace ƙarfe ne a madadin ƙashin jikin ta?. Sakin wani murmushin jin daɗi Shuraim yayi, sannan ya shige motar ya ja ya bar wurin.

Amna kuwa bata iya cigaba da abun da ya kawo ta ba, ta koma ta maida kayan da tazo da shi ta bar wurin, tana tunanin inda tayi masa wannan naushi, tabbas ta san yana yi masa zafi yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login