Showing 45001 words to 48000 words out of 129098 words

Chapter 16 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

23

ki gani" "ai dama ke matar manya ce 'yarlele na, kamar yadda kike 'yar manya, amma fa kina samun wanda ya fisa to fa bazan lamunci ki aure shi ba, yanzu dai ki lallaɓa da shi kafin hamshaƙi na hamshaƙai yazo" cewar Hajiya tana shafa ƙarin gashin atach ɗin Ruki.

Dama ba yaune farau ɗin Hajiya akan yimata khuɗuba na cewa itafah matar manya ce kuma ko acikin yaran masu kuɗi itaɗin ta musamman ce, hakanne ke ƙara sanya Ruki jin itafa ta musamman ɗin ce.

SAFNA.

Gelen ta kam ma batada labarin inda ya faɗi saboda gudu take sosai da iya ƙarfin ta, wanda bata tinanin ta taɓa kotan-kocin irin sa, to gudun cetan rai ina ma zaka san lokacin da kake yin sa, yadda take gudu haka wa'ennan mutanen suke biye da ita, saurin jan birki tayi lokacin da ta iso wani ƙatoton rami, a ƙoƙarin ta na dakatawa sai da ta kusa faɗawa domin sai da ƙasa da kuma ƙananun duwantsun da ta ture da ƙafar ta suka gangara ciki.

Rami ne me matuƙar tsawo yayin da ruwa ke gan gangarawa à ɗaya gefen, hakan yasa ƙasan kuma yazama kogi mai gudu sosai, kallon gurin takeyi a matuƙar tsorace sai fitar da a zababben nishi take, jin ƙirjin ta take tamkar zai bulluƙo waje saboda yadda zuciyar ta take bugawa da matsanancin sauri.

Jin alamar tsayawar mutanen tayi a bayan ta, ba ta san lokacin ta za ro manyan idanuwan ta da suka canza izuwa launin firgita ba, cike da tsoro, fargaba, tsananin tashin hankali ta fara juyowa bayan ta a hankali, yayin da jikin ta keta famar rawa tamkar mazari.

Tana juyowa inda suke ta kuma shiga sabuwar tashin hankali, dariya suka sake lokaci guda cikin razanannun muryar su, ɗaya daga cikin su ne ya tsagaita dariyar sa da cewa "yarinya wace tsautsayi ne ya kawo ki dajin tsakiyar rukuni?" Sai ya kuma ɓalllewa da dariya, "dan Allah dan Allah... ku rabu... da ni... kawai hanya ce... ta biyo da ni... bansan ya akayi ba... please ku ƙyaleni inyi tafiya ta" Tayi musu maganar a rarrabe cike da magiya da kuma tsoro, sobada yadda numfashin ta ke kai ka wo.

"Hahahahha yaro man kaza, yarinya taki ta ƙare, tunda har ƙafafuwar ki suka kawoki i zuwa ajalin ki a wannan dajin, ina miki albishir da kiyi murna da yau kika same mu a waje, dan da acikin ma'aiwata kika same mu da anmiki kisa mafi muni, amma yanzu kyakykyawar wuƙa ce kawai zata kai ziyara izuwa cikin ki" cewar ɗaya daga cikin su kuma, yayin da duka su biyar ɗin suka fiddo da wasu kafuran wuƙa da gigicewar Safna bai barta taga daga inda suka fito dasu ba.

Nufan ta suka fara yi da wa'ennan wuƙaƙen suna ci gaba da darawar su, jin dariyar da suke take kamar gaba ɗaya dajin yana juye mata, dan dariyar amsa kuwa take mata a gaba ɗaya kunnuwan ta, girgiza musu kai kawai take yi tana waige-waige hawaye sai aikin su suke yi a idon ta. Basu dai na matsowa gareta ba kamar yadda bata dena girgiza musu kai tana roƙon su kuma tana kuka ba.

Ganin sun kusa isketa ne ya sata fara ja baya, ja da baya take har ƙafarta yakusa zuwa gab bakin ramin, ba tare da ankarewa ba ƙafar ta yayi tuntuɓe da wata jijiyar bishiya, hakan yasa ta sakin ƙara me tsananin sauti sakamakon yadda zafin tuntuɓen ya ziyarce ta, sai dai da ƙarar da kuma afkawan ta cikin ramin sunyi daidaito, saida ta ɗan ɗauki secondes sannan ta kaiga isa cikin ruwan, ji kake timbil ta faɗa ciki "amma yarinyar nan mai sa'a ce, mutuwar ruwa ai bonus ne" suka faɗi suna ƙara dariya yayin da wasu suke cewa, "kai amma munyi babbar à sara fa" suna faɗi suka juya suna wucewa.

Safna na faɗawa cikin ruwan numfashin ta ya ɗauke n'a wucin gadi, dama tana da tsoron ruwa, to ina ga tafaɗa kogi? take ruwan yafara jan ta sai tafiya da ita yake tana yawo saman ruwa, to ko aina koginnan zai ajje Safna?

YAMMACI.

Wani mutum ne zaune kan kujera mai ɗaya wanda aka sarrafa shi da zinare, siffar sa yana da jiki amma bai zama ɗan lukuti ba, yadda yake a zaune ne ya hanani kalon tsawon da yake dashi, sanye yake da kaya pich ɗin riga da wando irin wa'enda ake kira court, ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, sai hula mai malafa dake sanye kansa, sannan baƙar gilas toshe ga idanun sa.

ZABBA BA kenan shugaban ƙungiyar POSPA mutum mara imani number ɗaya, wanda bai ɗauki ran bil'adama ba a bakin komai ba, wanda yake iya aikata komi dan cikar miradin sa, wanda ya tara dukiyar sa ta hanyar haramun, wanda yake da goyon bayan wasu daga cikin manyan ƙasa, yayinda à tsakanka nin sa dasu suke cuɗeni incuɗe ka.

Wani ne daban kuma ya zo inda yake, a bayan sa ya tsaya yana miƙo masa sallama irin wanda ake yiwa bosawan nan, sunan sa Salman wanda za'a iya kiran sa da PA ɗin Zabba ba, kuma wanda shugaba Zabba ba ya amince da shi sosai fiye da ɗanda ya haifa, kuma shine me sa masa ido akan duk abin da ya shafi ƙungiyar, kuma yake kawo masa rahoto a duk sanda yake da buƙatar ji, duk da ya amince da shi amma fa shi Zabba ba baya son wasa, hakan yasa kowa yake matuƙar tsoronsa.

"shugaba barka da hutawa" ya faɗi yana risinar da kai alamar girmamawa kamar yana ganin sa, sai dai maimakon ya amsa masa sai cewa yayi cikin muryar sa ta ta ƙama "Zabba ba bai da buƙatar gaisuwar ka a halin yanzu" "a gafarce ni shugaba, tsakiyar rukuni ta aiwatar da hukuncin ka akan wani maci amanar mu, sannan akoi yarinyar da abin ya faru a idon ta...."

katsesa ya ƙarayi da faɗin "bana son ɓata lokaci, kawai yi abinda ya kawo ka" Jiki na rawa ya fara zayyano masa bayani kamar haka, "shugaba kamar yadda ka umurta sabbin ƙwayoyin mu sun isa duk inda ka ambata, kuma nan da wasu kwanaki zasu fara aiki kamar yadda aka haɗasu dan hakan, a iya kacin wasu garuruwan da ke cikin Nigeria kamar yadda ka tsara, yanzu kwana uku kawai zamu jira, indai sun karɓu to zamuyi mafi munin abinda muka aikata a baya"

"Yayi kyau" ya furta yana Miƙewa, hakan yasa ni gano tsawon sa, yana da tsawo kam, ya jawo wata sandar zinare dake jingine gefen kujerar yana ƙara cewa "amma bana buƙatar jin ansamu matsala, kasanar wa sauran ma'aikatan, indai har aka samu wani problem to su kuka da kansu da kuma ahalin su, dan ni bana ɗaukar asara" "kamar yadda kace shugaba" ya faɗi cikin girmamawa yana risinar da kai kan ya tafi.

"Nigeria Nigeria, kwanan nan zaku amshi kyakykyawar kyauta daga gareni" Zabba ba yayi maganar haɗi da yin murmushin da shi kaɗai yasan manufar sa.

BAYAN KWANA HUƊU.

FANNIN AMNA.

Tsawon watannin nan sun matuƙar dagewa da karatu daga ita har Mubarak, duk da wani lokaci sukan taɓa faɗan na su amma ba kamar baya ba, saboda yadda haryanzu gidan baya musu wani daɗi saboda rashin jigon su da sukayi. Suna zana jarabawa dan yau saura musu kwana biyar su kammala.

Safiyar litinin. Mamma ce zaune gefen gado tana manne da radio à kunne tana sauraron labarai, gefe kuma Amna ce ke shiryawar zuwa makaranta, ganin yadda tsohuwar ta maida gaba ɗaya hankalin ta kan radion ne yasa ta cewa, "Mamma ta me kike sauraro cikin radion nan ne?" "Yi shiru kar ki katseni ina jin wani labarin tashin hankali" Mamma tayi maganar tana ƙara manna radion ga kunnen ta. Jin abinda suka ƙara faɗa ne yasa ta cewa, "daman nasan dole asa dokar zauna gidanka".

Saida ta haɗe gashin ta sannan ta maida hankalin ta gun Mamma jin abinda tace sannan yanayin ta ya sauya alamar abinda take ji babbane, "to Mamma ki ƙara volume nima inji" "sai kin hanani ji kenan? Kinsan dai radio ɗin nan ya kwarkwance ta ina zan ƙara bolum ɗin?" Matsowa Amna tayi2 dan itama taji abu-buwan da suke faɗa, itama zaro ido tayi sakamakon abinda taji, jawo wayar ta dake ƙasa tayi tana kunna data, nan ta lula internet dan ganewa idon ta abunda taji cikin radion Mamma, nanma sai da zuciyarta ta ya buga sakamakon abinda ta gani.

Vidiyoyi ne da yawa wanda ake nuna mutane, kamar wata cuta ta kamasu, shiga ɗaya daga ciki Amna tayi dan ganin menene silar?" Polisawa da Likitoci ne ke ta zarya kan mutanen, sun galabaita sai jini yake zuba musu ta hanci ta baki, yayinda wasu kam da ka gansu da ƙyar su kai labari, saboda yadda suke kamar basa numfashi.

Ba tare da ta ƙarasa gani ba Mubarak ya shigo yana cewa "Amna ki fito muje mana kar a fara exam bamu isa ba" fita daga wurin tayi tana miƙewa daga zaunen da take tana ƙarasa shiryawa, tana gamawa sukayiwa Mamma sallama suka fita, a waje suka tadda Ummee itama ta bisu da fatan alkhairi Allah ya basu nasara, da ameen suka amsa haɗi da yi mata murmushi suka fice.

Babu abinda Amna take gani a idanuwan ta sai videon da ta gani ɗazu, yau dai hira batayi tsawo tsakanin Mubarak da Amna a hanyar tafiya ba, saboda yayi ta mata hira amma hankalin ta yana can wani wurin daban, dan tinani take bayan jarabawa zataso taji menene sababin rashin lafiyar wa'ennan mutanen?.

__garuruwa kusan biyar ne samari da dama suka faɗa cikin rashin lafiya lokaci ɗaya, sai kaga hancin mutum ya fara fitar da jini tamkar haƙo, daganan kuma sai baki ya fara zubar jini, daga ƙarshe kuma mutumin baya iya jurewa tsayawa sai ya faɗi ƙasa, hakan ya tayarwa mutane hankali sosai, sannan har yanzu ba'a ce ga silar hakan ba, koda kuma yawancin masu shan kayan maye ne hhakan ke faruwa dasu, ɗinbin mutane ne suke faɗuwa, sannan abun tafiya yake a hankali, domin kuwa daga wannan garin ya faru sai kaji wani gari ya amsa__

Bayan sun isa makaranta suka tarar da yawanci maganar ake tayi, bata samu mai yi mata cikakken bayani ba saboda basu daɗe da isa ba akashiga class, haka har akayi papern farko, basu fita waje ba daga ita har ƙawayen ta.

Su kaɗai a cikin class domin kowa ya fita, juyawa tayi tana facing ɗin Wali tana cewa "haba Wali meyasa zaka jefa rayuwar ka a irin wannan halin? Koda yaushe kakar ka tana maka nashiha akan ka kula da rayuwar ka, amma me yasa ka zaɓi bin gurɓatacciyar hanya bayan kai karan kanka kasan da hakan?".



#To to too, 'yan uwan ƙorai ruwa dai ya tafi da Safna, to ta mutu ne ko kuwa suma tayi? Saboda ramin nan fa mai tsawo ne, to koma dai me nene yana gaba.

Yau dai munga Zabba ba, me yasa yake zaɓar garuruwa dan aiwatar da manufar sa? Shin sabon al'amarin daya dayafara kasancewa daga wasu garuruwa shirin da yayi ɗin ne?

Me zai kasance a gaba? Kamar kullum alƙamin ✍🏼 {Mrs Umar} ne kaɗai keda wannan amsoshin✌🏼

______________________________________________________________________________________________

Part 4️⃣9️⃣▶️5️⃣0️⃣

Tayi masa maganar tana miƙewa domin kuwa ba ƙaramin zafi a rai taji ba lokacin da taji labarin Wali ya fara shaye-shaye, sanadiyyar wasu banzayen a bokan da ya haɗu da su a unguwar su, cigaba da magana tayi "kai ne mutumin da ya kira ni wancan ranar, duk da cewa nasan ƙazafi akai wa mahaifina amma har yanzu ciwon dake raina bai gushe ba, toya kenan daya kasance kazama mai aikatawa?"

Sai da ta juya ta kalli sauran ƙawayen na ta Zarah da Nabila sannan ta cigaba da cewa "kunce zaku ban ƙwarin guiwa, ko ba haka kuka ce ba?" Maida kallonta gun Walin ta ƙara yi wanda tun da tafara maganar kansa yake a ƙasa, tace "kunce zaku ban duk wani gudunmawa dan fiddo da gaskiyar abinda ya kashe Baba na, amma me yasa kake son rusa na ka alƙawarin, saboda fa ɗawar ka cikin wannan halin kamar nunawa kake baza ka iya taimako na ba" ta faɗi tareda dafa kujerar ajin dake kusa da ita, tana sauke numfashin rashin jin daɗi.

A hankali ya miƙe yafara cewa, "hakane maganar ki Amna, nima da kaina nasan ba abu mai kyau nake yi ba, amma ya zanyi? Ba da son raina bane" "kamar ya bada son ranka ba? Kana nufin ɗure ake maka kenan? Haba Wali me yasa kake ƙoƙarin canzawa ne?" Cewar Zarah cikin damuwa, dan dukkan su babu wanda yaji daɗin hakan, amsa ya bata da cewa.

"Tsundumawa n'a cikin wannan hali bai daɗe ba hasalima kwana shidda da suka wuce ya faru, samin magani sukayi a abinsha bayan sun rinjaye ni zuwa inda suke da ƙarya, nima saida nasha sannan na gane ɗandanon lemon da bambanci da wanda nasaba sha, ina gama sha suka kwashe da dariya wai yau dai sun ƙure ni, duk rashin so n'a da biye musu sai gashi yau n'a sha ƙwaya, sai da muka haure da faɗa akan abinda sukamin" saida ya share hawayen daya gangaro masa ka na yacigaba da magana.

"Amma abin takaicin tun bayan kwana ɗaya da faruwar hakan na tsinci kaina da ƙara son sake shan wannan ƙwayar, duk dauriyar da nake wa kaina akan ƙin hakan amma yaci tura, dan jin kaina nake kamar zan haukace, a ƙarshe dai sai da na samesu harda roƙo sannan suka bani, ina shansa kuwa na samu hankalina, wallahi abokai ni da kaina tsanar kaina nake a wannan hali amma na rasa abinyi" ya kai ƙarshen maganar yana ƙara share hawayen sa.

Yayinda Amna da sauran suke yi masa kallon tausayawa, dan su Zarah masu rarraunar zuciya har idon su ya fara kawo ƙolla, ita ko haɗa kallon tayi da nazarin maganar, "wani irin kayan maye ne? Ko kuma ince me suke kiran ta?" Tayi masa tambayar ba tare da ta kauda idonta daga gareshi ba, saida yayi shiru yana nazari sannan yane "bansan cikakkiyar sunan ba, amma naji suna mata laƙabi da (PO..." "POSPA?" Ta katseshi da ƙarashe faɗin abinda yake son faɗa.

Sai kuma ta riƙe bakin ta jin ta furta da sauti, cike da mamaki dukkan su suke kallon ta dan bata sanar dasu magana makamancin wannan ba, "eh shine amma ya akayi kika sanshi?" Wali yayi mata tambayar, saida ta wawwaiga cikin ajin, ganin babu wanda ya dawo ajin har yanzu su ya su ne aciki yasata samun guri ta zauna, tana ƙara tattara gaba ɗaya hankalin kan Wali tace.

"Babu buƙata dan maganar mai tsawoce, amma Kana nufin shine ƙwayar da ka sha suma suke sha?" "Tabbas amma nima saida na fara shiga mummunar hanyar nan na gane ashe kusan rabin makarantar nan suna shan kayan maye kuma wannan ƙwayar da kuma wasu kayan maye da suka haɗa na wannan sunan su akafi amfani da su".

Zaro ido su kayi jin abinda ya faɗa musamman Amna dan sai da ta miƙe tsaye, "hakan na nufin da ma ana amfani da ƙwayoyin wannan ƙungiyar a makarantar nan? Kuma kamar yadda uncle Tukur yamin bayani ne, ƙwayar tana zama jaraba ga wanda yake shan ta, amma ya akayi hatsarinta yayi yawa har haka? Ace mutum daga shan sa sau ɗaya shikenan ya zamar masa bala'i? Menene abinda ya kamata nayi dan kuɓutar da abokina daga cikin wannan halin?".

Shine maganar da tayi daga zuciyar ta. Dan bata sanar dasu maganar da ta shafi POSPA ba, juyowa tayi zuwa kan sauran tana faɗin "ko kuma kun san da hakan?" "A ah gaskiya ni ban taɓa cin arba da magana makamancin wannan ba, bansan ko Zarah ba" cewar Nabila tana kallon Zarah, Zarah ta giɗa kai haɗi da cewa "a ah nima hakan take, dan mamaki ma nake taya hakan yake faruwa ba tareda kowa ya sani ba?".

"Babu wanda ya sani sai wanda yake mu'amala da miyagun ƙwayoyi, domin a ɓoye suke shigar da koman su, kuma ba ƙaramin kuɗi suke tarawa ba, ni kaina saida suka min gargaɗi akan karna sake na faɗawa kowa, dan zan iya samun matsala" "to meyasa kake faɗan?" Cewar Nabila "saboda bazan iya ɓoye muku abu ba indai kuka tambaya, musamman zakanyar Baba" ya bata amsa.

"yanzu dai ku tsaya" ta furta hakan tana ɗaga musu hannu sai ta kuma cewa, "Wali abinda nakeso yanzu shine dan Allah kasan yadda zaka daina wannan mugun abun" "Wallahi abun da nake ƙoƙarin yi kenan Amna, dukda yanzu bayamin kamar kwana huɗu da suka wuce amma har ayanzu inban sha sa ba inajin ƙoƙƙwalwata kamar zata fashe, suma wa'enda suka jefa ni cikin halin cewa sukayi ƙwayar ta fi ƙarfi akan sauran wanda suka sa ba sha, sabuwar fitowa ce, amma insha Allah zanyi iya ƙoƙarina dan inraba kaina daga hakan, sannan ku ma kusani à addu'a".

Suka haɗa baki gurin faɗin Allah ya yaye masa Amna ta kuma cewa "bayan haka in aka gama exam ɗin yau zaka kaini gurin wa'enda sukayi silar shigar da kai cikin mummunar hanyar nan, dan wallahi sainayi maganin su, sai sun faɗamin à inda suka koyi jagaliyanci" ta ƙarashe maganar haushi na cika mata zuciya, yace "nasan hakan shiyasa naƙi sanar daku tun da fari, banason inzama sanadiyyar tarzoma sai dai inzama silar lafawar ta, dan Allah kar hakan ya dame ki, addu'a kawai nake da buƙata a gareki please".

Juyowa Amna tayi tana kallon sa tace "hmmm lallai, ai barin su kamar nunawa yake abu mai kyau suka aikata kenan, kuma su samu damar ƙara aikatawa wani haka, to

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login