Showing 3001 words to 6000 words out of 129098 words

Chapter 2 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

17

a ɗaya daga cikin kujerun falon. Batare da sun saurareta ba, kwashe takardun ta tayi, jiki a sanyaye ta nufi gefen ɗakin su. Tana share ƙananun hawayen da suka fito daga manyan idon ta.

Buɗe ƙofar tayi da sallama ta isa ciki. Tarar da Ammunta tayi zaune akan garduma da alama sallar La'asar ta idar, ajiye littafan hannunta da gyalenta tayi a kujerar dake ɗakin, sannan ta ƙaraso gun farincikinta, durƙusawa a gabanta tayi, hawayen da bataso fitan suba suka fara zubowa, Kwantar da kanta tayi a kan ƙafar Ammu, Ammun ma binta tayi da kallo cikin tausayawa, a hankali ta ɗaura hannunta a saman kan Safnan saboda yana yin jikinta,

"Meyasa hakan, ke faruwa da mu?, Shin ko munyiwa su Hajiya laifine, shiyasa suke yimana haka, Dady ne kawai ke sonmu?" Ta ƙarasa faɗi haɗi da matso ƙwallan da yacika mata idonta. Da ƙyar Ammu ta fara share mata hawaye, tana mai jin zafi a ranta, akan duk abinda ke faruwa, amma babu yadda ta iya.

Ganin hawaye yafara zuba daga idon mahaifiyar ta, tayi saurin ta shi cikin damuwa, hannu tasa ta share mata hawayen tana girgiza kai "no my Ammu don't cry, banaso inganki cikin damuwa bare inga hawayen ki. Bazan iya juran gani ba". Ta ƙarasa faɗi tana rungumeta.

Taimaka mata tayi ta kwantar da ita a kan gado. Ta ce, "Ammu bari inyi sallah sai inkawo miki abinci nasan kinajin yunwa," ta wuce toilet dan yin alwala.

Daddy na ɗawainiya da su iya ƙoƙarinsa. Ita kaɗai ce ke kula da mahaifiyar ta sosai. Babu me leƙo Ammu yaga ya take idan bata nan. Bayan masu gadi biyu da kuma masu gyaran flowers. Akwai masu girki huɗu, masu wanki mata biyu maza biyu. Sannan sai masu shara da goge-goge. Duk kansu kuma suna da ɗakunan su, amma fa Safna ko Ammu basu da iko dasu, iyaka dai Hajiya da 'ya'yanta kaɗai suke da iko akansu.

Bayan ta idar sallah kitchen ta nufa, saidai bata samu komi ba, illa jalof na taliya, ɗiba tayi a plate tayo ɗakin da shi, taso da Ammu tayi, ƙoƙarin kaimata tayi a baki amma ta kauda kai , idon Ammun ta gani sannan ta ce, "Nasan baki cika son spaghetti ba Ammu, amma ki daure kici saboda na sani kinajin yunwa."

Ƙara kau da kai tayi akaro na biyu, ajiye plate ɗin Safna tayi akan drawern gefen gado ta miƙe haɗi da faɗin "to bari inje na samo miki wani abun"

"A a Ammu bazan ɗaɗe ba, zan dafa mana ko kuskus ne, kin san bazan iya cin abinci ba in ke bakici ba" taƙara faɗi bayan taga idon Ammun nata,tsawon shekarun da tayi da mahaifiyar ta a haka, tana iya fahimtar abunda take ƙoƙarin faɗi ta ido, wucewa tayi don dafawa Ammu kuskus.

Bari mu leƙa garin Gombe.

Kyakykyawa ce na hango cikin wani Ƙaton shopping mai suna Haleem shoprite, tana matsakaicin tsawo, sannan kuma fara ce, wajen launin fata, ga shi tana da karan hanci sosai, wannan yasa ake mata laƙabi da wanke hannu kataɓa kawai. Manyan idanunta farare tas tas, glass ta sanya wanda yasa har ba a iya ganin kwayar idanunta, don baza kace idonta nada wani launi ba inka ganta. Sanye take da kayan kanti riga da wando, irin dogin rigunan da ake kiransu da gown, blue colour ta sanya, wacce ta sauƙa mata har gwiwar ta, sannan ta yafa ɗan gyalenta milk colour, wanda yazo dai dai colour ɗaya da flate shoes ɗinta. Ya nayin haɗuwarta da shigarta sai tabarkallah kawai.

Tsaye take agurin biyan kuɗi bayan ta zaɓo takalma black and red. Wani ɗan saurayi ne a gefenta da shekarunsu zai iya zuwa kusan ɗaya. Amma sai dai ɗan ɗara ta tsawo kaɗan. Shima kyakykyawa ne, Kusan 30 minute suke tsaye a gurin ga layin mutanen da ta tara a bayanta, akan takalma ɗaya da ta keson zaɓa tsakanin baƙi da ja.

Kallonta saurayin yayi cike da takaici yace "ke nifa nagaji haba, da yanzu ina gida ina cin daddaɗan girkin Ummee, amma kin jawoni nan tin ɗazu kina abu ɗaya, dan Allah kisai takalmin nan mu wuce, duba bayan ki fa mutane ne ke jira"

hararansa tayi, sannan ta juya ta dubi mutanen da suma cike suke da ita, taƙara juyowa ta dubeshi ta ce, "dama ba ce maka nayi kawuce ka ƙyaleni ba, harda cewa ƙafa ta-ƙafar ki, to ma mutum da kuɗinsa bazai zaɓa ya darje ba, ha'a" ta ƙarasa faɗi tana tattaɓe baƙin takalmin, Inta ɗaga jan sai ta girgiza kai, "a'a kamar wancan yafi kyau" sai ta ɗaga baƙi kuma.

"To ki zaɓa ɗin mana, kuma da kike cewa nace ƙafa ta-ƙafar ki ai kinsan wannan tsohuwar, dana koma ba tare da keba zata hanani sukuni", tafara faɗin, "kai Mubaraka ina kabaro min jika ta Aminatu, saboda Allah kataho kabar yarinyar da babu ruwan ta, in wani abu yasa meta fa, haka zatai ta min sababi, Mubarak ɗin ma bata iya faɗi in tana masifa sai ta kirani da sunan mace wai Mubaraka".

Bata tanka masa ba sai ma cigaba da abinda take tayi, gyaran murya yayi da alama ma shi ake biyan kuɗin a wurinsa, ɗago idanun ta dake cikin glashi tayi tana duban sa, shima kallonta yayi sannan yace "biwar Allah me kike nema ne anan, akan takalma biyu kike wasting time ɗin mutane, inba siya zakiyi ba kiba mutane wuri".

Kamar zata cire glass ɗin sai kuma ta fasa sannan ta ce, "kaga malam kuɗi zan bada fa, ko so kake in siya takalmin da bai da lasting, toma tinda bason ciniki kukeyi ba nafasa siya, ku sayar a wani" ta ajiye takalmin, tayi fitowar ta, take mutanen wurin suka hau surutu, haƙuri Mubarak ya basu, sannan ya biyota yana faɗin.

"Amma ke Amna ko, yanzu duk wasting time ɗin da mukayi ba ki siya komi ba". "Dama ce maka akayi siya zanyi?" ta furta hakan tana kwashewa da dariya. Yace "what me kike nufi, ba cemin kikayi kintara wasu kuɗi ba?" Amina ta ce, "ba wani kuɗin da natara, ƙure ƙaryan me ƙarya nayi, Zubi ce ke cewa "ai Haleem shoprite na manyan masu kuɗi ne, waini takewa bagu, shine nace yau zanzo in ƙure ƙarya"

Yace "wato shiyasa ta biyoki kenan?" "eh mana ba kaga tana ganin abin bana ƙare bane ta ware" ta kuma kwashewa da dariya. dariya yayi shima yace "kuma wai a haka mamma take cewa ba ruwanki, duk abinda zan faɗa mata sai taki yarda", Amina ta ce "kai kuma gashi baƙin ciki kakeji in ta faɗi hakan ba mai gulma" tafaɗi tana ɗan sa gudu-gudu, shima bin bayan ta yayi yana faɗin "nine magulmaci?"

______________________________________________________________________________________________

Part 0️⃣5️⃣▶️0️⃣6️⃣

Tsayawa napep ɗin yayi a daidai kofar gidansu. Amna ta fara sauka "kefa zaki biya kuɗin" mubarak Yafaɗi hakan, tace "bazan biya ba, ai nina biya jiya" takarashe faɗi tana buɗe gate ɗin gidan ta shige da sauri, ƙofa yayi sannan ya ciro kuɗi yana miƙawa me napep ɗin.

Jikin tsufa sai a hankali hakan yasa ta ɗan kishin gida, dan tasamu damar hutawa, jin an faɗi akanta yasa ta ƙoƙarin tashi a hankali, "ke Aminatu karyani kikeson yi?, ina ganin sai kin karyani murƙuƙus tukunna zaki huta ko?" Tsohuwar ta faɗi haka, cikin shogoɓa Amna tace, "haba dai Mamma, ni ɗin nawa nake da zan karyaki, kuma ma ai ke Tsohuwa ce mai ran ƙarfe" Mamma tace "bawani mai ran ƙarfe, yadda kike ƙashi ɗayan nan"

"Kaii Mamma!, Aminatun kice fah" "Aminatun nawa fa, yadda kike ƙaƙƙarfiyan nan, ya akayi yau kuka Daɗe, baku dawo da wuriba, ina Mubarak ɗin?" Amna tace"Tare dashi muke, kuma wahalar abun hawa akayi a cikin gari fa yau, shiyasa bamu dawo da wuriba"

Shigowa Mubarak yayi yana cewa "sannu Zubaida wato" miƙewa Amna tayi ta katseshi da faɗin, "wato kai inba ka haɗa ni da tsohuwa taba bakajin Daɗi ko?, to muje dama bacci take son yi" ta ƙarashe faɗi haɗi da kama hannun sa ta jashi waje.

"Wai ke Amna in tambaye ki mana?, meyasa bakya tsoron yin ƙarya ne?" Mubarak ya faɗi mata, bayan sun fito daga ɗakin, sai da tayi masa kallon tara saura kwata, sannan tace, "menene matsalarka dani?, ƙaryar tawa cutar da wani zatayi ne?"

"Akan me kuke magana, wace ƙaryar?" Matashiyar matar ta furta hakan yayinda ta fito daga ɗakin ta, da sauri dukkansu biyu suka dawo da dubansu gareta Amna ta ɗan zaro ido kaɗan, "ummee dama, daman Amna" "Ummee magana nake akan abinci, kada yunwa ya cutar damu saboda da yunwa muka dawo" tayi saurin faɗin haka saboda tasan Mubarak yanzun nan sai ya konce mata zani a kasuwa, kuma tasan Ummee bason shashanci take ba.

"Toh me yakawo cutarwa ta yunwa kuma tunda kun iso gida, sai kuje ku watsa ruwa kuzo kuci ai" taƙarashe maganar tana juyawa. Ƙaramar ajiyan zuciya Amna ta sauke tana mai kallon Mubarak, "maƙaryaciya!" "Magulmaci!" Suka furtawa junansu. Suka juyawa kowa yayi hanyar dakinsu.



SALLAHR MAGRIBA

Bayan sallahr magriba, gaba ɗayan su suna zaune a gefen tsakar gida kan babban tabarma, yayin da iska me tattare da ni'ima ke kaɗawa, baƙaramin jin daɗin yanayin suke ba, jin ƙarar motan mahaifin su yasa Mubarak miƙewa dan buɗe masa gate, fitowa yayi daga motar bayan shigowan sa ciki, amsan jakar dake hannun Baba Mubarak ɗin yayi haɗi da yi masa barka da



dawowa.

Nufo wurin su yayi fiskarsa da murmushi me haɗe da gajiya, zama

yayi ak

an tabarma, s

annu da dawowa Ummee tayi masa, Amna ma tayi masa.

Juyowa yayi gurin Mamma.

"Mamma kin wuni lafiya ya jiki jikin

?

" "Lafiya ƙalau alhmdllh Baba ya aikin da alama yau ba ƙaramin gajiya kayi ba daga ganin fiskar" murmushi yayi sanna yace "Mammata kenan harkin gane ina tattare da gajiya" dukkan su sukayi murmushi, yacigaba da faɗin, "wani aiki ne ke ƙoƙarin bani wahala, aikine me ɗauke da sarƙaƙiya, narasa gano ta inda zan fahimci lamarin"

"Baba nima ka sani a cikin aikin, zan taimaka muku please" ta ƙarashe faɗi tana haɗe hannu alamar roƙo, dariya Mubarak yayi yana nunata da yatsa yace "sannu akaran bana mai karan bani" haɗe fiska tayi tana hararan sa. Mamma tace "kai banason iskanci fa, kasan dai Aminatu na jaruma ce shiyasa takejin zata iya komi"

"yauwa Mammata" Amna ta faɗi tana murmushi. Haɗi da yimasa gwalo, Ummee tace "Mamma kullum abayan Amna kike" shikuwa Baba kallo kawai yake binsu da shi yana murmushi, musamman ma Amina yana matuƙar mamakin yarinyar,

tunba yauba indai za taji labarin da akace akoi wahala to sai tace itama zatayi,Tun tasowar ta yarinya ce meson kasada, ko labari ake bata indai bana gwagwar maya ba, bata tsayawa jinsa, kuma ita bawani abu bane a wurinta, tayi faɗa da yaro namiji, har Mubarak ita take tare masa faɗa, dukda kuwa namijine shi.

tafison wasan maza, har mamaki sukeyi a inda take koyon faɗa, don yasha kamata tana faɗa da wa'enda suka fita, kuma tayi galaba akansu bata neman tsokana ammafa in aka taɓo ta, batasan yafiya ba saita rama, dan bata barin kota kwana, dan ma a haka yana taka mata birki.

gashi kwayar idon ta launin toka, ganin bakin mutane nason yawa a kanta yasa ta sa glass, indai zata fita waje sai ta saka kafin ta fita, ganin babu abinda yake mata yasa su barinta ta cigaba da sawa, basa zaman 10 minute da Mubarak batare da sun yi faɗa ba, ammafa bakaramin ƙaunar junan su a matsayinsu na en uwa suke ba.

shigar ta kuwa, atamfa baya daga cikin abunda takeso, sai dai tasa dan wani shagali, barta da kayan kanti, dogon riga ko riga da wando, musamman ma riga da wandon, shine 80% ɗin kayanta, dukda kuwa bata taɓa sa rigar da bata wuce gwuiwa ba, kuma hannunsa mai tsawo. Sannan ba matsatstse ba.

Idan ya tam bayeta, "What do you want to be?" Sai ta bashi amsa da "Soldier" sai yace mata lawyer yakeson ta zama, idan Yafaɗi haka kuwa, bata ƙara ce masa komi, sannan bata manta da matsayinta na Ƴa mace ba, gurin kare mutuncin ta da Ƴan uwanta, da kuma riƙe addinin ta. Amna yarinyace da kowasu irin ahali zasu so zama tare dasu.

"Baba Baba!" Mamma ta furta ganin yadda yayi shiru yana nazari, shima dawowa yayi daga duniyar nazarin da yake wa Amna, "na'am Mamma, kutayani da addu'a akan wannan aikin da nasa gaba" "kullum cikib addu'a muke daman, amma zamu ƙara bi iznil lahi" Mamma ta faɗi hakan bayan jin maganar sa.Suma sauran da addu'ar samun nasara suka bishi daga bisani ya wuce ciki.

WASHE GARI

Gurin ƙarfe 07:00am, tana shirin zuwa makaranta, yauma sanye take da riga da wando, saidai design da colour sun ban banta dana jiya ashcolor, haɗe baƙin dogon gashinta tayi da rimbom, sannan tayi rolling ɗin ƙaramin gelen ta, sallama tayi wa Mamma.binta da adawo lfy tayi,

ɗaukar madai daicin bag ɗin ta tayi, da kuma, glass ɗin ta, sannan ta fito, nufar ƙofan ɗakin Mubarak tayi, saida ta duba agogon dake ɗaure a tsintsiyan hannunta tukunna ta fara magana cikin ɗan ɓacin rai.

"Matsala na da kai kenan, baka daraja lokaci ko kaɗan, kuma fa na faɗa maka yau wannan malamin me kunnuwa kamar na jaki shi zai yi mana lecture 08:00am, yakamata in rigashi zuwa amma kai" tsayarda maganar tayi ganin fitowan Baba.

Cikin shigarsa dake nuna tabbacin shi ɗin babban ɗan jarida ne, "cigaba da faɗa mana, wato malaminki kike cewa kunnuwa kamar na jaki ko?" Yakarashe faɗi yana ƙureta da idanu fiskarsa a haɗe, ƙasa da kai tayi a tinanin ta yariga da yafita, "a ah Baba daman sonake yafito muje kar mu makara."

Alokacin Mubarak ya fito shima cikin shigarsa ta riga dark blue da wando black, harda hula black facing cap, riƙe da wasu takardu a hannun sa, "to sai ku wuce ai" baba Yafaɗi hakan dai dai fitowan Ummee da Mamma, Amna tace "Baba tare zamu?, zaka ijjemu a makaranta ne?".

"A a kuyi tafiyarku ni sai anjima zan wuce, kuyi karatu da kyau, kunga yanzu ana kan gaɓan hutu" ya miƙa musu kuɗi,Ummee ma fatan alkhairi tayi musu daga bisani suka fito, Mubarak ya sa littafansa cikin jakan Amna, amma da masifa tabarshi yasa, haka yake mata kullum, sai lokacin da yakeso yazo ya amsa, wani lokaci tace ita bazata riƙe jakan ba saidai ya riƙe, baza tarinƙa yi masa dakoba kullum, hakan kuma bazai hana gobe ma yasa ba.

Shiga cikin S K U university jamian nasu sukayi, amsan littafi da biro ɗaya yayi, yana yin ɓangaren su yayin da itama tasu ɓangaren tayi, tana shiga ajin ya kwashe da tafi, suna yi mata kirarin, "barka dai barka dai, wanke hannu kataɓa, barka da shigowa, Ƴar baba zakanya"

Taku tafara yi cikin isa, har izuwa mazaunin ta, tana mai jin farinciki à ranta, "yakuke friends" ta faɗi tana mai kai dubanta ta ko ina a ajin, tana ganin masu ƙaunar ta da masu yi mata kishi, amsa mata sukayi "lafiya sanyi ƙalau zakanya" ɗaya daga cikin mutanen da tsakanin su ba nisa yace "ya kika gano mana Haleem shoprite?" Shu'umin murmushi tayi. Tana kai duban ta inda zubi take tareda abokan tafiyar ta, sannan tace,

"I'm telling you Wali, jiya na ƙure ƙaryan me ƙarya, wato yadda naji labarin wannan shoprite ɗin, bahaka na sameshi ba" Wali "kice Zubi ta samu a buhu kenan" dariya Amina tayi tana kuma cewa, "buhun masara ma kuwa" gaba ɗayan su suka maida kallonsu kan Zubi. Suna faɗin "ooo anji kunya masu bagun banza" Zubi kuwa ji tayi kamar ta shaƙo wuyan Amna saboda baƙin ciki, zama kowa yayi a mazauninsa ganin malami yashigo."

KADUNA

Sai da ta tabbatar ta kula da farin cikin ta wato Ammun ta, sannan ta shirya cikin Atamfa riga da skirt da kuma himar iya gwuiwa, tukunnan ta fito riƙe da jakar ta, sallama tayiwa Ammu tukunna tafito, da maganar Hajiya ta kwana, cikin tafiyar ta ta nutsuwa tafara taka falon, saidai tatsaya yayinda ta ga Ruki a gabanta.

budurwace ta ba Safna shekara uku, kuma tafi Safna jiki da tsawo, tanada 'yar kyanta daidai, baƙar riga da wando na bacci ne a jikin ta, Ga tsinanniyar gashin atach ɗin da ta ƙara à ƙoiƙoi-don gashinta, daka ga idon ta kaga hamshakiyar mara kunya.

Safna kuwa jira take kawai taji dame Ruki tazo kuma, saida ta ƙarewa Safna kallo uku saura kota, sannan tace "dady yace kije room ɗin sa" kawai ta furta, sannan ta nufi hanyar fita daga falon. Simi simi Safna ta fara tafiya zuciyar ta cike da tsoro, ko me yafaru yau kuma.

Bayan sallamar da tayi yabata izinin shiga haɗaɗɗiyar ɗakin, ganin inda yake zaune gefe kan kujera, yasa ta nufan wurin haɗi da durƙusawa, saida ta gaishesa bayan ya amsa yace, "my daughter menene yasa kikace kinason barin school, keda nasanki da jajircewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login