Showing 39001 words to 42000 words out of 129098 words
Chapter 14 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
zamu iya ci tare?" Yayi maganar kamar da Ammu yake, duk da Safna ba taso hakan ba amma suka ci tare, inda shine ma ya ciyar da Ammu, bayan sun gama ya mayar da tray kitchen da kan sa, tinawa yayi da bai gode mata akan abunda yafaru jiya ba, hakan yasa shi ƙara komawa ɗakin.
Lokacin ya tarar da Ammu kan Kujera ita kuma tana shimfiɗa Gado, sai da ya tsaya kamar bazai yi magana ba sai kuma ya kira sunan ta, ƙara maida hankalin ta tayi kansa bayan ta amsa, "am, kin sha maganin ki kuwa?" "Eh nasha tun ɗazu" "ok tom, to jikin na ki fa?" Shima ta bashi amsa da "yayi sauki sosai yanzu" ta bashi amsa tana tinanin meyasa yake tambayar ta haka? Kuma kamar ba abinda yake son faɗa ba?.
Saida ya maida kallon sa inda Ammu take ka na yace, "nagode da taimako na da kikayi min jiya" yana faɗi ya juya zai fita, nan yaji tace "nima na gode da kulawan da ka bani" saurin juyowa yayi yana kallon ta, yayinda tayi ƙasa da kanta, murmushi mai ƙara ya saki sannan ya wuce, Ita da bata san sanda tayi masa wannan godiyar ba itama tayi murmushi.
Kamar yadda doctor yace Yazeed ya kasa ya tsare Safna ko tsinke baya barin ta ta ɗaga da niyyar aikin gida saidai na ɗakin su, hatta makarantar ya hana ta zuwa duk da ta sanar dashi cewa babu abin da ke damun ta, amma yace ina maganar doctor zai bi, cikin wannan kwanakin koda yaushe yana zuwa ɗakin su Safna, domin ko fita bai cika yi ba, saboda dabara ce ta ya hana mahaifiyar sa da 'yan uwan sa ƙuntata mata har ta gama warwarewa.
Ita ko tun tana ɗar-ɗar da shi har ta fara sabawa, saboda ba ƙaramin sauyawa Yazeed yayi ba, zama yake yana musu hira sosai ita da Ammu, wani lokaci har takan taɓa hirar itama, shi da kansa yake mata jagora gurin fitar da Ammu waje, cikin sati ɗaya alaƙa mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin Yazeed da Safna, duk da rashin maganar ta.
A yanzu Yazeed ya tabbatar wa da kansa haƙiƙa tsawon lokacin nan da kon soyayyar Safna yake, saboda yadda da ya yi nisa da ita yake tinanin ta, hakan yasa shi siyan mata waya domin ko ya koma ɗaki sai ya rinƙa jin muryar ta, duk da kuwa ba wani maganar azo a gani take ba.
Hajiya gani tayi abun Yazeed yayi yawa, koda yaushe yana manne da Safna da nakashashshiyar uwar ta, sannan Ruki ko Saleem basu isa suyiwa Safna wata banzar magana ba sai yayi maganin su, da tayiwa Alhaji magana kuma cewa yayi wai to me abun damuwa, rashin kwanciyar hankali ne cikin 'yan kwanakin nan yayi mata yawa hakan yasa ta yi wa Yazeed kira na musamman zuwa ɗakin ta.
Bayan ya shigo gaishe da ita ya fara yi cike da girma-mawa haɗi da zama kan kujerar da ke cikin ɗakin, fari t'as sai ɗaukar ido yake, yayin da ita kuma take tsaye kansa, yadda ya same ta lokacin da ya shigo, ɗakin Hajiya zan iya cewa shine ɗakin da yafi ko wani ɗaki a gidan kyau domin yadda aka zuba kayan a latu à ciki.
Amsa masa gaisuwan tayi kamar dole, ganin yadda tayi masa ba yadda yasa ba gani bane yasa shi cewa "Hajiya hope are you ok? Ya n'a ganki tsaye ko akoi abinda kike buƙata ne?" Sai da ta jefa masa hararar jin haushi sannan ta fara yi masa magana cikin ƙa ra ji.
"Koma dai Me kake tinani can maka, ka sani cewa duk cikin 'ya'yana kai nafi so, amma meyasa ko da yaushe cikin bani kunya kake?" Cikin rashin fahimtar inda zancen na ta ya dosa yace "Hajiya I'm not understand, me kike son faɗa ne?" "Kai ba nason iskanci yimin magana da yare na kana ji ko? Ba cewa nayi kaimin zancen turawa ba" nan ma ta faɗi a hasale.
Tana ƙara cewa "abinda nake so da kai yanzu shine, ka raba kanka da yarinyar nan, kada na ƙara ganin ka inda suke, ina ce likita sati ɗaya ya ba ta? to satin yayi, dan haka bana buƙatar ƙara ji ko ganin abu maka mancin wanda kayi cikin satin..." "Hajiya i can't bazan iya ba" ya katseta da faɗin hakan yana miƙewa yayin da ita kuma babu abinda tayi sai kallon sa da take.
Cigaba da cewa yayi "cikin 'yan kwanakin nan ne na tabbatar da cewa akoi abinda nakeji a game da Safna, wanda ban fahimci hakan ba sai yanzu, ko baki kira ni yau ba ina da niyyar zuwa in sanar dake...." "Yazeed!" Ta dakatar dashi cikin tsawa hatta idon ta sai da ta rufe.
Ba ƙaramin shock yaji ba yadda ta furta sunan na sa, hakan yasa shi saurin ɗago idon sa gare ta, duk da bai kamata yayi mamaki ba, sai lokacin ta buɗe idon ta tana cewa, "kar kaga ina lallaɓa ka fiye da 'yan uwan ka kayi tinanin zan zuba ido akan duk abinda kake so, yanzu menene cikakken abinda kake son sanar dani? Ina jinka faɗa min?".
"Hajiya me nene yasa kika ɗauki wannan maganar babba haka? i love her ina matuƙar ƙaunar ta, ba tada mugun hali, sai dai ma..." ta ƙara saurin katse shi tana ƙara yi masa magana cikin tsawa "ya isa! Ai ka riga da ka faɗa min abinda ke ranka, to kasani gwara tun wuri ka janye, saboda ni dai Hajiya Zainab kuma mahaifiyar ka bazan taɓa bari ka auri Safna ba, koda kuwa ita ce matar da ta rage maka kaɗai a duniyar nan".
Shima cikin haushin furucin na ta yace "Hajiya kamar yadda nace ina son ta, to inason ta nake nufi, kuma bazan iya rabuwa da ita akan wani dalilin ki wanda ni bansan shi ba" yana ƙarasa faɗa ya fice cike da ɓacin rai, bai taɓa tinanin zai wa Safna irin wannan soyayyar ba, amma a halin yanzu ji yake bazai taɓa rabuwa da ita ba, duk da bai sanar mata ba, bai kuma san cikakken abin da ita take ji game dashi ba.
Zama tayi a kan kujera inda Yazeed ya tashi, sai furzar da iskar takaici take daga bakin ta, saida ta sauke wata ƙatuwar ajiyar zuciya sannan ta fara magana da kanta "ba shakka! hakan na nufin mai afkuwa ta afku kenan? Abinda Yazeed zai min kenan? Duk taka tsantsan ɗin da nake yi duk ya tafi a banza? yanzu wai Yazeed da bakin sa yake cewa yana matuƙar son Safna? So wanda bazai iya rabuwa da ita ba? Acikin sati ɗaya kawai? Kuma duk laifi nane, da ban hana Alhaji sawa ayi gyara a kan ƙarfen nan ba da duk hakan bai faru ba. A ah ba laifi na bane, laifin sheɗaniyar yarinyar nan ne, to wallahi baza ta saɓuba, ba zaiyu uwarta ta aure min miji itama ta auren ɗa ba, dole insan abinyi, ƙorai kuwa".
Tana ƙarashe maganar da takewa kanta ta miƙe har zata fita sai kuma ta dawo, ɗaukar wayar ta tayi tana neman numbern Ladingo, tayi kira na biyu amma bata ɗaga ba, ba ƙaramin ƙara tinzira tayi ba, cikin kira na Uku ta amsa, "Haba Ladingo wai ina kika ijje wayar ne? Sai ayi ta kiran ki amma bakya amsa waya?" Hajiya ta hau zuba wa ƙawarta masifa.
"Hajiya Zainab ki kwantar da hankalin ki dan Allah, kiran da kikayi min fa ina toilet ne, amma me nene ya sa ki hasala haka?" Ƙara sauke ajiyar zuciya a karo na biyu tayi sannan ta fara ba ƙawar ta labarin abinda ya faru, bayan Ladingo ta gama jin komai tace "kinga Hajiya Zainab nifa yanzu akoi tinanin da yazo raina, to indai har da gaske Yazeed na son ta me zai dame ki..." "bangane me zai dame ni ba? Ko wai bakiji abinda nace miki da kyau bane?.
Sai da Ladingo ta taɓe baki a can gefen sannan race, "to ai baki tsaya na ƙara sa ba, abinda nake nufi shine karki manta fa wannan dukiyar da kuke fa ca ka dashi na ta ne, saboda na mahaifin ta ne, kuma ke da kanki kika sanar dani shekarun da zata fara aiki a kan kamfanonin ya kusa, kuma dai kinsan mijin ki ba hana ta zaiyi ba, dan yana bata kulawa, to mezai hana baza ki bar ɗan ki ya aure ta ba? kinga daga nan sai ku ƙwace ragamar dukiyar gaba ɗaya a hannun ta".
Sai da Hajiya ta ni sa sannan tace "hmmm ba shakka ƙawata maganarki m'a na da amfani, to amma kinsan Yazeed fa, tunda yace yana ƙaunar ta to bazai taɓa cutar da ita ba, kwanan nan ma baki ga yadda yake bata kulawa ba, rannan auta na zuwamin tayi tana kuka wai Yazeed ya duke ta akan yarinyar".
"Komai zai zame mana mai sauƙi idan har ya aure tan, kibari bayan ya dawo daga ƙasar da yake son zuwa sai mu shirya komai, zuwa yaushe zai tafi ne?" Amsa Hajiya ta bata "ina jin cikin watannan zai tafi, kuma zai ɗan jima kan yadawo, dan ina ga zai yi shekara ko fin haka ma" Ladingo ta ƙara cewa, "yauwa to ki bari sai ya dawo mu tsara komai, abinda nake so dake yanzu ki nuna masa kina tare da shi".
Hajiya tace "kina ganin hakan zaiyi?" "Haba ƙawata shekaru nawa muke tare dake, komai fa tare muka ƙulla shi, wannan ma zamu yi nasara kamar baya, ke dai mujira lokaci".
-a haka dai suka cigaba da wasu hirar su wanda ni ban tsaya jin su ba-
Hajiya ta nuna wa Yazeed goyon bayan ta akai, kuma tace zata bashi duk wata gudunmawa, amma tace masa yayi haƙuri da maganar hai izuwa lokacin da zai dawo daga turai, kuma kada ya sanar wa Alhaji har sai lokacin, ganin yadda ta nuna masa amincewar ta akan lamarin yasa shi amincewa da abinda tace.
Haka suka cigaba da hira da Safna duk da bai sanar da ita yana son ta ba, haka itama, domin fa itama fa ta shaida da cewa soyayyar sa ta shige ta, musamman yadda yake bata kulawa, har ta fara jin daɗin zama a gidan domin yanzu ko Hajiya ta rage wasu abubuwan da take mata, Ruki da Saleem kuwa sai harara ne ke rabasu indai zasu haɗa ido da ita, kai ko himar ɗin ta suka hango sai sunja tsaki, domin yanzu basu isa suyi mata wani abunba don Yazeed na nan.
Marwan ne ke mata wani cin kashin, da zarar hakan ya faru gaban Yazeed kuma to fa kusan faɗa suke yi, halin Yazeed ya ɗan fara sauyawa, domin yanzu duk fa inda zai shiga to sai yayi sallama.
#Too 'Ƴan-uwan arziƙi kun dai ji yadda soyayyar Yazeed da kuma Safna ta fara kasan cewa, shin kuna ganin zai kai labari kuwa?
Me Hajiya da ƙawar ta Ladingo suka shirya a baya? Me kuma zasu ƙara shiryawa a gaba?
Me zai faru bayan Yazeed yayi tafiya?
______________________________________________________________________________________________
Part 4️⃣3️⃣▶️4️⃣4️⃣
Marwan ne ke mata wani cin kashin, da zarar hakan ya faru gaban Yazeed kuma to fa kusan faɗa suke yi, halin Yazeed ya ɗan fara sauyawa, domin yanzu duk fa inda zai shiga to sai yayi sallama, hakan ya fara kasan cewa ne wani lokaci bayan ya shiga ɗakin su Safna kamar yadda ya sa ba.
A natse tayi masa bayanin badai dai bane abinda yake yi, sallama abu ne me kyau, idan da so samune ma bayan sallama kane mi izini kafin kashiga, wannan shine abinda manzon Allah (S.A.W) ya koyar, sai da tayi masa gamsashshen bayani sosai, duk da tana jin tsoron abinda zaice mata.
Amma a mamakin ta sai ya karɓi gyaran kuma yayi da nasanin rashin yin hakan abaya ma, yadda ya karɓi laifin sa hakan ya ƙara sanya mata sonsa a zuciya, a yanzu babu wata maganar tsoro tsakanin Safna da Yazeed, duk da har yanzu babu wanda yayi wa ɗan uwan sa bayanin yadda yake ji a ransa, amma alamu duk sun nu na.
Safna sosai take jin daɗin yadda rayuwa ta fara sauya mata, wanda ba kowa bane sila fa ce Yazeed, Yazeed ɗin nan dai wanda a baya take ɗaukar sa kamar dodon ta, wanda ko muryar sa taji sai jikin ta ya amsa, amma sai gashi Allah ya haɗa zuciyoyin su guri guda yanzu, fatan da take shine wannan farin cikin ya dauwama a gare su baki ɗaya, sai dai ta kanji fargaba in ta tuna zancen tafiyar da zaiyi, duk da shekara ne, amma sai take ganin kamar wata hanya ce ta ƙara fa ɗa wa cikin wata matsalar fiye da na baya.
Haka haka har lokacin tafiyar Yazeed yayi, da sassafe yazo dan yi musu sallama, Safna ta sha kuka sosai, kuka ne me cike da kewar masoyin ta, da kuma tinanin halin da zata shiga bayan tafiyar sa, shima da kansa ji yake kamar yafa sa tafiyar, to amma babu da ma, domin tafiyar na da matuƙar mahimmanci à gare sa, lallaɓar ta yayi tayi akan zasu rinƙa chat ko bayan ya tafi, addu'a daga ita har Ammu sukayi masa.
Haka dai ya wuce rai babu daɗi, duk da yayiwa su Saleem warning akan kada ya ji sun yiwa Safna wani abun da bai da ce ba amma baiji daɗi ba, ƙarfe 07:00 daidai jirgin su ta ɗaga sai ƙasar UK 🇬🇧
Sai dai tun bayar tafiyar Yazeed ta cigaba da ansan mugunta daga wurin Hajiya da 'ya'yan ta wanda yafi na da ma, domin sabon fanni suka ƙara buɗe mata ta fannin musguna wa.
BAYAN WATA TAKWAS DA TAFIYAR YAZEED
Safna na zana exam na ƙarshe a jami'an su.
Wayan da ya siya mata tuni Ruki ta ƙwace shi, kuma ba tada bakin magana,Yazeed kuwa hankalin sa ya tashi lokacin da ya dena samun Safna a waya, idan ya tambayi su Hajiya kuma cewa suke basu san me dalilin ba, ƙila ma blocking ɗin sa tayi, a haka dai har yade na tambayar su ita. Ya ƙara zama ko yaushe ba tada aiki sai hawaye ko kuka, shi kuma Alhaji ba sa idon sa yake akan al'amuran ba
Musamman Hajiya tayi takanas zuwa gidan Ladingo. Gidan Ladingo ba wani na azo a gani bane, domin gidan gadon 'ya'yan ta ne, shi kuma mijin dama ba wani kuɗin kirki yake da ba, dan duk abinda zataci ma 'ya'yan ta maza ne masu kawo mata, ita yanzu bata da aiki sai musguna wa matan yaran ta, duk da ba gida ɗaya suke ba, amma tana matuƙar ta kura musu,
Ladingo da Hajiya ƙawaye ne tun suna 'yan mata, kuma masu mugun hali, wanda hakan ya bisu har izuwa girman su, Ladingo tana zuwa gurin boka don yanzu ma yiwa 'ya'yan ta take akan kada su kula da matan su sai ita kawai, abunda Hajiya bata sani ba Ladingo kishi take da ita, yadda take zaune gidan dukiya tana fachaka ga shi kuma ba ta bata komai, dan dama Zainab maƙon tsiya gare ta, ƙila da badon ta su tazo ɗaya ɓangaren mugunta ba da ba sa tare.
Suna zaune a falon ta bayan Hajiya ta ɗan taɓa kayan marmarin da aka kawo mata sai ta fara cewa, "kinga Ladingo nifa ba na tinanin shawara akan Yazeed ya auri Safna hanya ce mai ɓillewa, dan haka ni dai na samo wata shawarar, in tura ta can wani wuri da niyyar zataje gurin dangin su, kinga daga can sai musan abinda za muyi mu kora ta karta dawo, inyaso lokacin da ya dawo dole ya haƙura in bai ganta ba, kuma maganar dukiya kuma ai ta zama na wa, koya kike ganin shawarar?"
Sai da Ladingo ta sauke ƙafar ta da ta ɗora kan ɗaya ƙafar sannan tace "shawarar yayi to amma kinsan dai zata dawo, tunda ba haukacewa tayi ba, ko kuma ta mutu" "kinga Ladingo nifa bana son maganar mutuwa kuma kin sani" sai da ta murmusa ka na tace, "hmm Hajiya Zainab kenan, ke dai kiyi muguntar ki amma banda kisa?" Hajiya tace "to kinga laifi na? A dai illata mutum banda kisa kada zunubin yayi yawa ah toh".
"To ma duk ba wannan ba, yadda za'a kora tan da baza ta dawo ba yakama ta muyi tinani a kai yanzu, kuma dai ke baki cika son harka da bokaye ba yanzu ya za'ayi kenan?" Hajiya ta amshe "ai dole yanzu na amince amma fa inaso sai bayan Alhaji ya yi tafiya kafin nan, dan ya sanar da ni shima za shi ƙasar waje ko ista ko me?" "Istanbul kenan ai ƙasar Turkish ne" Ladingo tayi maganar.
Hajiya tace "yauwa nan, shima zai ɗan jima, dan haka nake son mu aiwatar da komai bayan shima ya tafi, wannan karon ko gurin bokan ne aje nidai insamu biyan buƙata, saboda wallahi ina ga indai Yazeed ya auri Safna bansan yadda zanyi ba, ke wallahi gwara na ƙare rayuwa ta a nakashe akan hakan ta fa ru".
Giɗa kai Ladingo tayi tana mai ƙara jinjina tsanar da Hajiya take wa wannan Yarinyar sannan tace "kar ki damu kedai ki bani isashshen kuɗi ta yadda za'a miki aiki ba wasa shine kawai" "kar ki damu indai kuɗi ne baki da matsala, zanbaje su kamar yadda nakeson amin aikin" murmushi Ladingo tayi tana jin daɗi a ranta koba komai hanyar samun kuɗin ta yayi, domin kuwa sai tasan yadda zatayi ta tatse Hajiya ko kaɗan ne itama ta lasa rabon ta.
Sai da suka ƙara tattauna wasu abubuwan yau ma sannan Hajiya ta koma gida.
WASHE GARI.
Bayan sun fito daga exam kafin su ƙara komawa Raheena ce