Showing 33001 words to 36000 words out of 129098 words

Chapter 12 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

25

tayi tana kallon sa ba tare da ta yi yunƙurin yi masa magana ba "keh! wani irin iskanci ne haka? Baza kiyi wa mutum magana lokacin da ya tambaye ki ba" Sai da ta razana saboda yadda yayi mata maganar a tsawace.

Ni dai yau banda tacewa sai dai kuma ince ku cigaba da kasan cewa tare da Alƙalamin ✍🏼 taku {Mrs Umar} 👸🏽 dan jin yadda zata kasance ✌🏼

______________________________________________________________________________________________

Part 3️⃣5️⃣▶️3️⃣6️⃣

Sai da ta matse ƙwallan da ya cika mata a ido sannan tace "I'm sorry Yaya Yazeed, dama nayi tunanin ko nayi maka laifi ne" "to shi hawayen fa?" Saurin share hawayen tayi tana faɗin "babu..." ya katse ta, "babu komai shine abinda zaki ce ko? To lafiya ƙalau, na amsa gaisuwan na ki you can go". Yayi maganar yana zuwa kujera ya zauna, ita kam kuka baya mata wuya ne? Ya tambayi kansa.

WASHE GARI.

Yau Ruki tayi niyyar zuwa school, da ma makarantar su ɗaya da Safna, ya kamata ace ta gama makarantar yanzu ma, amma saboda daƙiƙanci da kuma rashin maida hankali yasa ta kasance har yanzu, sakamakon kowani aji faɗuwa take, hakan yasa Hajiya kashe kuɗi dan ta kasance a gaba, amma fa duk aikin banza ne wai anzubawa kwando ruwa, domin kuwa yanzu ma haka Safna ta fita a aji dan ita watanni kaɗan ya rage mata.

Cikin shigar riga da wando matsatstsu ta fito, ta shiga motar ta sai makaranta, bata da zuciyar alfarma bare tace wa Safna suje tare.

Bayan sun ɗan sarara, wato dai bayan sun fito daga lecture, tsaye Ruki take tare da tawagar daƙiƙan ƙawayen ta su shidda maza huɗu da mata biyu da ita bakwai, kowannen su sai taunar cingom yake, "Ruk baby kwana biyu kimbar Safna ta sarara dayawa, gaskiya munyi missing ɗin ki over, da kinanan da mun rinƙa kallon film ba tare da munje sinima ba". Cewar ɗaya daga cikin mazan, saida Ruki ta murmusa sannan ta ce, "rabu da ita shegiya ai gasa mata aya a hannu nake à achan gidan ma".

"Ruk baby muguntar ki na ba ni citta wallahi, ga tanan ma sun fito ita da manne matan ƙawar nan ta ta" Jemsy ta ƙare maganar tana nuna wa Ruki inda su Safna suke, juyawa inda su Safna suke Ruki tayi sannan ta ce, "yauwa, yauma tafe nake da wata muguntar, ta tozarcin da zan mata ai".

Ta faɗi tana juyawa inda Halil yake tace "Halil where is my bag?" "Ga shi nan" ya faɗi yana miƙa mata, ta amsa tana wucewa inda su Safna suke, abokan ta na take mata baya.

Safna na cikin tafiya kawai taji an janyo ta, tana juyawa Ruki ta antaya mata garin baƙin gawayi a fiska, dariya mutanen da abun ya faru a idon su suka hauyi, "ke Ruki!" Raheena ta faɗi cikin ɓacin ran abinda akayiwa aminiyar ta, Safna kuwa tsayawa kawai tayi kamar wacce aka dasa a wurin.

"Wace ke? ki kiyaye ni yarinya ba dake nake ba, bana son shishshigi faɗi ba'a tambaye ki ba, kuma indai mayyar yarinyar nan kike ta kawa baya to kin kama gaibu, domin kuwa sai ta cinye ki daga ke har dangin ki". Cewar Ruki haɗi da hararar inda Safna take.

"Ashe baki san waye maye ba akwai mayyar da ta fiki ne? kuma wallahi ni na fi ƙarfin ki nan gani nan ƙyalewa". Raheena ta faɗa mata hakan.

Shiru abokan Ruki sukayi jin yadda Raheena tayi maganar cikin ɓacin rai, dan ita kanta Safnan haushi take ba ta, ace ayi ta yi mata abu ba ta ramawa, ita ga damo sarkin haƙuri?.

"Ruki amma gaskiya kin iya niƙa gawayi, ga yadda kika maida ita ta zama kamar aljana sabuwar kamu?" Sasu ya faɗi haka, sauran suka kwashe da dariya, harda wa'yanda suke wurin.

Jin yadda suke yi mata dariya ne, ya sanya ta cigaba da jin rashin daɗi a ranta sai lokacin hawaye suka fara zuba daga idanuwan ta, ɗaukar tissue Raheena tayi ta fara sharewa Safna hawayen harda fiska.

Dariya Ruki tasa wanda yafi na sauran ƙara tana cewa "dube ta wawuya dik a gidan mu ita ce 'yar aiki, sannan ɓarauniya ce, ƙoƙarin da take dashi a makaranta ba na ta bane magani ta karɓa.." Tun kan ta ƙarasa Raheena ta katse ta da faɗin, "ya kama ta kema kije ki amsa ai dan kina da buƙata irin wannan daƙiƙancin da kike da shi".

"Raheena karki biye ta muje kawai" Safna ta faɗi tana ƙoƙarin jan ta, Saukan ruwan leda suka ji daga Safna har Raheena, Ruki na matsa ledan ruwa kan su, hankaɗa ta Raheena tayi, Safna ta ja ta suka bar wurin, nan suka tsinkayi muryar Ruki na faɗin "be careful with me Raheena, wallahi zan yi maganin ki, saboda na fi ƙarfin ki" ta faɗi da ƙarfi.

Juyowa Raheena tayi itama tace " kin san dai rijiya ba wurin wasan yaro bane, ki dai faɗawa wa'ƴanda kika raina" "please Raheena ki daina tanka mata" "ba zan dai na ba, let me ask you wai nikam ba kyajiin komai a zuciyar ki idan ana miki abu ne?" "Ina ji mana amma to ya kike so nayi Raheena, ko so kike zaman gidan ma ya gagareni?"

Ta faɗi idon ta na zubar da hawaye, "no Safna kar kiyi kuka ba wai na faɗa miki maganar dan ta ɓata miki rai bane, for give me please" ta ƙarashe faɗi haɗi da kama kunnuwan ta alamar na tuba, murmushi Safna tayi tare da cire hannun ta a kan kunnen, tabbas Ruki ta tozarta ta yau sosai fiye da abunda take mata a makarantar, amma to ya zata yi.

Nufar school toilet sukayi, duk wanda ya kalli Safna sai yayi dariya, saboda yadda fiskar ta da koma gaban himar ɗin ta ya ɓaci da baƙi, duk da aminryarta ta share mata amma raguwa kawai yayi, Hijab ɗin kuwa fitar sa sai ruwa da sabulu, gashi lokacin tashi makaranta bai yi ba, Raheena ce me musu magana dan ita Safna komai a zuciyarta ta bari,

"Mtsew wallahi babu mai ƙara cin ƙwandala na acikin ku, yanzu à gaban ku tsigalalliyar yarinyar nan Raheena ta faɗamin maganganu amma kuka bi ta da ido. Da a ce kashe kuɗi na ne kam ai kune kan gaba" Ruki ta faɗi tana binsu da harara, dan ita kashe musu kuɗin da take badon komai bane sai dan ta zama buss a cikin su, amma bata san me yasa basa mata yadda take so ba, saidai su taya ta dariya idan tawa Safna abin mugunta, dama itace marainiyar wayon ta.

"Haba Ruk beb" gaba ɗayan su suka haɗa baki gurin faɗa, Jemsy tace "haba Ruk beb kinsan ba girman ki bane ace wasu ne zasu tare miki faɗa, sabida ke jaruma ce, kinga kuwa ai tare miki faɗa kamar abun kunya ne a gare ki, ko ba haka bane abokai?" Tana tambayar sauran, "yes yes "suka haɗa baki gurin faɗi, domin kuwa baza su so ta dai na basu kuɗin da suke samu daga wurin ta ba.

"Ai bansan haka lamarin yake ba" "ai ya ma wuce haka, kawai dai baki sani bane" suka ƙara faɗin hakan, habawa sai mutuniyar ku ta fara ƙa fa fa ta juya suna binta a baya sai ƙara fasa mata kai suke, ƙasan bakin su kuma dariya suke mata

"Cire Hijab ɗinki kiban insa ke kuma kisa gele na" cewar Raheena tana ƙoƙarin cire gelen data ya fa, "tsaya no kar ki damu zan zauna a haka" "a'a ba nason inga ana miki dariya kinga bai fita ba" "ni ma hakan take ba zanso ayima besty na dariya ba" Safna ta faɗi tana wucewa, "to mai besty a jira ni mana" Raheena ta faɗi tana bin bayan Safna tana murmushi.

Bayan sun koma Gida.

Waje wanda dama nan ta nufa, zama tayi a kujeran garden ɗin haɗi da kwantar da kanta jikin kujerar, lumshe ido tayi tana mai jin yadda sassanyar iska ke kaɗawa, gefe guda kuma ga kukan wasu daga cikin nau'ukan tsuntsaye.

Shima tahowa wurin yayi riƙe da laptop a hannun sa, domin kuwa a daidai lokaci irin wannan shima ya kanzo wurin indai yana gida, tsayawa yayi lokacin da idon sa yayi masa nuni da ita, daidai lokacin da iskar dake kaɗawa ta yi baya da gelen ta, hakan yasa fiskar na ta ya fito fayau dashi.

"Woow" shine abun da ya furta a fili, yana kusan towa inda take a hankali, ganin cewa ta ɗago kanta sannan tana ƙoƙarin buɗe idonta yasa shi juyawa kamar bashi ne keson ƙarewa kyakykyawar fiskar ta kallo ba.

Tana buɗe ido taga kamar wulgawar mutum, "waye wannan mutumin?" Sai kuma tayi burus da tambayar kanta da take, ta kuma maida kan ta kan Kujerar, sai kuma ta tashi kamar an tsikare ta, "oh no! Na manta ban ba Ammu medicine ɗin ta na yamma ba" ta ƙarashe maganar tana da fe kanta alamar kash! "Gwara naje na bata yanzu kafin dare yayi" tayi maganar tana tafiya.

Chan ta hangi Yazeed na nufar ɗaya garden ɗin, zuciyarta ce ta tsinke saboda bataso faruwar hakan ba, "me zai kaishi? Bayan ya tsani zuwa gurin?" Shine tambayar da tayi wa kanta, domin kuwa tasan dai baya zuwa, ba ma shi kaɗai ba harda sauran, saboda kasancewar wurin ba'a ƙa watashi kamar wanchan ba, itace me yawan zuwa, domin wani lokaci ko ta zauna a garden mai flowers sai yaran Hajiyar su kore ta, ko Yazeed ɗin ma yana ce mata ta bashi wuri yasarara. 'Yan aiki kuwa dama basu da damar zama a waje sosai indai bawai aiki zasu yi ba.

To bama wannan ne yasa damuwar ba, akwai wani babban ƙarfen dake tsaye a wurin, kuma kwanaki da taje ta ga ƙarfen ya haɗu da igiyar wuta, dan tsuntsuwa da ta taɓa shi sai da ta kusa wullawa, hankalin ne ya tashi lokacin da taga faruwar hakan, shiyasa ta daina zuwa, ta yiwa masu aiki magana akan kada su kusanci wurin koda dole aiki ya kaisu wurin su kiyaye, tama Dady magana ma yace za'a gyara, amma shiru tafi tinanin ma ya manta. To kuma ga Yaya Yazeed ya nufi wurin.

Ganin yayi kwanan wurin ne yasa ta yin gudu dan tayi masa bayani, shi kuwa dama ya zaɓi zuwa wurin ne domin ganin ta da yayi a ɗaya bangaren kuma baya son ya kore ta yau kuma so yake ya natsu yayi aikin sa, saboda yana son yin tafiya ƙasar waje dan wani buƙatar sa.

Yana isa wurin ya ijje laptop ɗin sa kan ɗaya daga cikin kujerun wurin masu kyau suma, gurin yana da kyau kawai dai ba'acika kula da wurin bane, sai kuma rashin ƙa watuwa da kuma rashin kaɗawar iska sosai domin wancan yafi faɗi.

Ciro wayar sa a aljihu yayi yana latsawa ba tare da ya zauna ba, ɗayan hannun sa ya ɗaga yana shirin ɗaura shi kan ƙarfen, kawai yaji an ture sa, don ya ma kusa faɗi, Safna kuwa tana hankaɗa sa hannun ta yakai kan ƙarfen, nan shocking ɗin ya kama ta, sai da ta saki ƙara dan yadda take jin wani yanayi a gaba ɗaya jikin ta.

Yazeed kuwa juyawan da zaiyi dan ganin wanda yayi masa wannan hankaɗar, kawai idon sa yayi arba da Safna shocking na jan ta, cikin tsananin tashin hankali ya nufa in da take da gudu, tayi sa'a saboda ƙarfen ya sake ta, dan kan ya ƙara so ta fa ɗi ƙasa.

#Toh fah garin taimako ita ya same ta, koya zata ƙare?

______________________________________________________________________________________________

Part 3️⃣7️⃣▶️3️⃣8️⃣

Yana isowa ya ɗaga kan ta zuwa kan ƙafansa yana ta kiran sunan ta daya daɗe bai ambata shi a gaban ta ba, kiran sunan yake cikin matsanancin ta shin hankali, duk da idon ta na son rufewa saboda yanayin yadda jikin tan yayi bai hana ta yin murmushi ba, saboda ta ji daɗin kiran sunan tan da yayi, wanda bata san dalili ba.

Idon ta ne ke ƙoƙarin rufewa, hannun sa yasa yana tattataɓa kumatun ta yana faɗin "no dont close your eyes, Safnaa!" Sai dai ina domin kuwa idon ta ne ya kulle alamar suma, ƙara ƙolalo ido yayi cikin ta shin hankalin da bai taɓa tsintar kanshi ciki ba, hatta idanun sa sunyi jazir suna fiddo da ƙwalla.

Ɗaga ta yayi ya nufi falon da sauri gudu-gudu, sai da ya bangaje Saleem a hanyar shiga falon, yayin da shi kuma Saleem yake binsa da kallo kawai, akan kujera mai uku ya ijje ta, yana murmur za mata hannu yana hawaye, yana faɗin "wake up wake up, Safna babu abin da zai same ki kinji?" Faɗi yake kamar wanda baya cikin hankalin sa, saboda ko tinanin Hospital bai ba.

Saleem ne ya fara tafiya dan zuwa kai wa Hajiya gulmar abinda ya gani, "don uban ka ina zaka je? Yi sauri ka kira min doctor Mujaheed" Yazeed ya katse sa da fadin hakan cikin tsawa yana maida hankalin sa kan Safna dake kwance shiruu.

Da sauri Saleem ya zo kusa dashi yana faɗin "ina wayar?" Yama manta da wayar ta faɗi tun lokacin da Safna ta ture sa, "kira sa da wayar ka mana" da sauri Saleem ya fara neman numbern, dan jin yadda ya ƙara yi masa maganar da tsawa, saboda daga shi har Ruki sunfi tsoron Yazeed akan Marwan, dan shi baya son reni, hatta Marwan shiru yake inya masa wani maganar.

After some minute

Doctor ne ya gama duba Safna wanda har lokacin bata farka daga sumar da tayi ba, gefe guda kuma Yazeed a gefen ta riƙe da hannun ta cikin damuwa, daka ga fiskar sa kasan ɗauke ya ke da damuwa, ɗayan ɓangaren kuma Hajiya ce da 'ya'yan ta inka ɗauke Marwan da baya nan.

Gaba ɗaya sun zubawa Yazeed ido yadda ya susuce akan Safna gaba ɗaya yaƙi kwantar da hankalin sa, ita kuwa Hajiya baƙin ciki ne yayi matuƙar cika mata zuciya, musamman ma lokacin da tazo ta tadda shi yana hawaye akan Safna, tabbas abun da take gudu ya afku domin kuwa yadda Yazeed ya damu da yarinyar nan yau ya tabbatar mata da hakan, in hakane kuwa tsugunno bai ƙare ba.

"Doctor are sure babu abinda zai same ta? Ba fa ta motsawa har yanzu" "hakane amma kar da ka damu zata tashi zuwa anjima kaɗan, wutan lantarkin ya shige ta sosai, amma komai zai dai daita kamar yadda nace maka, sannan in ta tashi ai mata kamar yadda na faɗa babu surutu dayawa a kusa da ita, da dai sauran".

"Insha Allah Doctor na gode da kulawa" Cewar Yazeed sai lokacin ya saki hannun ta ya fita raka Doctor, yadda ya barsu haka ya dawo yasame su, Ruki da Saleem sai taɓe baki suke suna faɗin "hi'im!".

Yana shigowa Hajiya ta fara yi masa magana, "Yazeed ban taɓa tinanin haka daga greka ba, yanzu duk kashedi da kuma maganganun da nake maka duk ka share su da tsintsiya ko? Yanzu wannan me kama da mayyar ka gigice akanta dan bata da lafiya? Abinda ko ni uwarka baka taɓa yimin ba?" Ta ƙarashe maganar tana mai ƙara jin takaicin hakan a ranta, ji take kamar tayi kuka, saboda takaici.

Saleem yace "Hajiya ku koreta daga gidan kuhuta da bala'i" Ruki ma tace "wallahi kuwa da kun rabu da alaƙaƙai idan ba haka ba...." "enough!" Ya katse su da faɗi cikin tsawa.

Ya juya ya ɗauki Safna ya mayar da ita ɗakin Ammu, dan baya son ayi surutu à kusa da ita kamar yadda Doctor yace, zuciyar Ammu ne yayi mugun bugawa ganin yadda aka shigo mata da Safna ko motsi ba tayi, lura da hakan yasa Yazeed zuwa kusa da ita, ya durƙusa yana faɗin "Anty Maryam kar kiyi tinanin wani abu, likita ya duba ta zata farka nan bada jimawa ba kinji?".

Tambaya take yi masa akan me yasa me ta? Amma bai fahimta ba dan haka ya miƙe yayi hanyar fita, ita kuwa ƙoƙarin matsawa kusa da Safna tayi idon ta na zubar da ruwa, wai har yaushe fitina da tashin hankali zaiyi hijra daga gare su? Har yaushe Safna zata kasance cikin farin ciki kamar kowani ɗa?. Shine tambayar da Ammu take wa kanta, wanda Allah subhahu wata ala ne kaɗai yasan wannan amsar.

Bayan Yazeed ya dawo falon Hajiya ta rufe shi da masifa, yana nufin Safna ta fi ta kenan da har zatai masa magana yayi burus da ita, saboda bata da mahimmanci à gare sa kenan?. Gajiya da maganar na ta Yazeed yayi dan haka yace "Hajiya kinsan da yanzu ni ne a kwancen nan?" Ya ƙara she maganar yana ganin inda take.

"Eh ba shakka! Saboda nayi maka maganar ne kake cewa da kaine à kwance?" Ganin bata fahimci zancen bane yasa shi matsowa kusa da ita yace, "Hajiya! Ƙarfen da ke silent garden igiyar wuta ya sauka akai, ban sani ba nazo ɗaura hannu na akai ta tura ni hannun ta ya taɓa" "me?" Ta faɗi hakan dan batayi zaton jin hakan ba.

"Yes Hajiya, da yanzu nine kwance madadin ita, amma saboda tsabar tsanan da kuka yi mata ne yasa komai na ta kuke ganin sa baƙi, amma yau ni ta ceta" yana ƙarasa maganar ya fice waje sakamakon kiraye-kirayen sallahn magrib da ake yi.

Samun wuri Hajiya tayi ta zauna, ba tare da ta ce komai ba, saboda ita ce ta hana Alhaji gyarawa lokacin da Safnan ta faɗa masa, saboda tasan babu wanda yafi zuwa wurin fa ce Safna, kasancewar wurin babu wasu shukoki masu kyau,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login