Showing 111001 words to 114000 words out of 129098 words
Chapter 38 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
nan sai a hankali" "haba Ladingo! Kema kin san bazan iya shiga motar haya ba, bere ma motar zuwa ƙauye, ana tafiya mota na rawa saboda tsabar kwarkwancewa", "shikenan muje" Ladingo ta faɗi, suna ficewa daga gidan Ladingon suka shige motar da Hajiya tazo da shi.
Tafiya sosai su kayi har wata ƙaramar ƙauye dake cikin garin, motar ta su tayi datti sosai na ƙurar hanya, yadda kasan sahara motar ta shiga. Fitowa daga motar su kayi Ladingo na tafe Hajiya biye da ita, bayan ta ba driver umurnin ya jira su.
Hajiya sai wani sauye-sauyen fiska take yi, tana duba ko ina na wurin da suka dosa da ƙyama, wani bukka suka tsaya wani mutum da carbuna kusan goma a wuyar sa yana alwala, Ladingo ce mai gaishe da malamin, amma Hajiya kuwa ba ma tason buɗe bakinta, don gani take ƙudajen dake shawagi a wurin tsaf zasu shige cikin bakinta.
Iso yayi musu zuwaga cikin bukkansa, kamar Hajiya baza ta shiga ba sai kuma ta shige, wai Hausawa sunce ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba, shiga bukkan su kayi, wanda ke wani tashin wararraki, don ba ma wari ɗaya ba. Magana malamin ya fara yi, "ina sauraron ku Hajiya, ku sanar da ni buƙatun ku yanzu kuga aiki da cikawa gurin Malam mai carbi goma, ai ni tuni nake maraba da zuwan mutane irin ku, saboda na san bada wasa kuke tafe ba", "hakane Malam mai carbi goma, to ni dai kawo ƙawata nayi, don haka zatayi maka bayani daga bakinta" faɗin Ladingo.
Hajiya kuwa da ta maƙe bakinta tayiwa Ladingo na kurma, akan ba damuwa ita tayi masa bayanin, da ƙyar Ladingo ta gane me take nufi, "amma Hajiya sanadin da kika ce muzo tare kenan, ya kamata kiyi masa magana kamar yadda kika ce" girgiza mata kai Hajiya tayi alamar, ke dai yi masa bayanin kawi, nan dai Ladingo ta fara sanar da shi, manufar da ya kawo su garesa.
Sai dai kan Malam mai carbi goma ya bada amsa, su kaji wani ruguu-ruguu a ƙofar bukka, suna juyawa su kaga wasu ƙattin maza a bayansu, fiskarsu a rufe. Wani irin zaro idanu sukayi, domin da ganin su ba mutanen alkhairi bane sunfi kama da ɓarayi, Ladingo da Hajiya suka juya gurin malam, sai dai ganin sa su kayi tsamo-tsamo cikin gumi sharkaf.
"Ku fito da su wajen nan! Domin bukkan yayi mana kaɗan mu aiwatar da abun da mukeso, domin yau babban kamu mukayi cikin sauƙi" cewar ɗaya daga cikin mutanen cikin ƙatuwar muryar sa yana fita daga, Hajiya batasan lokacin da ta buɗe bakinta ba, cikin tsananin tashin hankali ta furta, "innalillahiii wa inna ilaihi raju'uunn".
Suna fita suka tadda drivern Hajiya yana tsugunne, gefen kansa a fashe. Wani irin dimm zuciyoyin Hajiya su kayi, musamman ma Hajiyar da take da mugun tsoro, zare ido na tsoro kam ba a magana, kai kace idon su na neman fita daga gidansa.
Shin ko ya zata ƙare wa Hajiya hannun ɓarayin ƙauye? Kardai Hajiya tayi garin neman gira an rasa ido fa😃
Kome zai faru gaba?
Mu kasance a next part.
_________________________________________________________________________________________________________
Part 1️⃣0️⃣3️⃣▶️1️⃣0️⃣4️⃣
Zare ido na tsoro kam ba a magana, kai kace idon su na neman fita daga gidansa.
Ko wanne a cikin mutanen nan riƙe da irin ta sa wuƙa, wasu kam harda adda a hannun su, "Maza ku sanya guiwo-winku a ƙasa!" cewar babban cikin na su, babu ɓata lokaci su Hajiya suka kai guiwo-winsu ƙasa kamar masu neman gafara, babban cikin na su ne ya dubi Malam mai carbi goma, da ya jiƙe ya kuma jiƙewa da gumin tsoro, "kai Malam yaufa ka yi mana abin arziƙi, irin wannan kamu da kayi haka!"
Sharɓe gumi Malam yayi, baki na rawa ya fara cewa, "ku taimaka ku rabu da mu, idan har kukayi mana haka, to fa yau wallahi raba dare zanyi ina yi muku magani da kuma addu'ar Allah ya baku nasara akan wannan sana'ar da kuke, don ai sana'a ce satar ma" Hajiya da Ladingo suka fara kallon Malam da mamakin maganar sa, "kar ka ka rena mana wayo, wannan ai magana ce kake faɗa mana ma!", ɗaya cikin ɓarayin ya faɗi haka.
Harara Hajiya ta jefawa Malam sannan ta fara magana ƙasa-ƙasa ta ce, "haba Malam! Kai da muke sa ran zakayi mana maganin su, bayan kana da magunguna da kuma na sihiri? Amma kuma sai kana yin wannan maganar? Ashe kaima tsoron ɓarayin kake, da nayi asarar kuɗi na kenan?" "Ke Hajiya sufa irin wa'yannan ɓarayin da kike gani, babu irin surkun da basu da shi, dama can sun addabe mutan ƙauye, to ni kuwa me zan iya? Kuma da kike cewa asarar kuɗin ki zaki yi, inba kiyi a wuri na ba zakiyi a wurin su, na tabbata sai sun kwashe komai naki, ni kuma yau saita Allah" Cewar Malam fiska kamar mai son yin kuka, itama Hajiyar ji tayi kamar tsala ihu sabida takaici ta ce, "bakin ka ya sari ɗanyen kashi!"
"Ke wacece Hajiyar a cikin ku? Mai motar can?" Babban na su ya tambaya idon sa kan su Hajiya, wani irin tashin hankali Hajiya ta kuma shiga, jin ɓarayin na tambayar wace Hajiya? Gashi tana ganin sun fasa kan drivernta, ƙila in suka kama itace Hajiyar to ƙila itama hakan zasu yi mata, Ladingo kuwa ganin Hajiya na nazari yasa ta ce, "Hajiya tambaya fa suke" cikin takaici Hajiya ta ce, "toh sannu muguwa!.." kan Hajiya ta kuma yin magana ɓarayin suka daka musu tsawa.
"Ba tambayar ku muke ba? Ko sai mun fara nuna muku ikon mu kafin ku gasgata?" "A ah wallahi munji, ni ce nan Hajiya, amma suna ne kawai ba wai yana nufin ni Hajiyar ba ce" "oho kece Hajiyar kenan?" "Eh ni ce, amma kamar yadda na faɗa muku, ba wai sunan na nufin asalin Hajiyar ba, ni talaka ce mai sunan girma" Hajiya ta kuma faɗi don tabbatar musu bata da kuɗin, babban cikin su ya kuma cewa, "to wannan motar ta waye kenan idan ke ba Hajiya bace?" "Wai mota ai..." ya katse Hajiya da daka mata tsawa, "keeh!! Ba abin da nake son ji ba kenan".
Ya faɗi yana duban mutumin gefen sa ya ce, "je ka amso min duk abu na moruwa a wurin su" yana faɗi mutumin ya je gurin su Hajiya tare da bayyanar da ruɓaɓɓiyar adda wacce take kewaye da tsatsa, "ku firfito da duk wani kayan ado da yake wurin ku, da jakar ku da wayoyin ku, maza maza" ya faɗi musu cikin ƙatuwar murya, "bakin Malamin nan guba ce wallahi" Hajiya ta faɗi cikin ranta, jiki na ɓari ta fara circiro kayan ƙyale-ƙyalen da ta sa masu tsada, haka itama Ladingo, suna ji suna gani suka miƙawa wannan ɓarawon komai.
Hajiya ji take kamar gaba ɗaya kadarar ta guda ta miƙa musu, wasu hawayen baƙin ciki da da na sanin zuwa wannan ƙauye take tayi, "na rantse da na sani da sarƙunan roba na sa" ta faɗi cikin zuciya tana kuma matso ƙwallah. Sa yaran san nan ya kuma yi suka ƙwamushe masa Malam aka kawo masa gaban sa, roƙe-roƙe Malam ya hau yi don ya san halin su, shi wallahi da yasan haka ai da su Hajiyan na zuwa ya kora su, domin yasan ɓarayin nan baza su masa ta daɗi ba, ɗauka za suyi dama can haka yake mu'amala da Hajiyoyi".
Su Hajiya kuwa jikin su sai aikin sa yake tayi na mazarin tsoro, Hajiiya ji take tamkar ta shaƙe wuyar Ladingo saboda tsabar haushi, domin duk ita ta jawo mata wannan iftila'in. Kasancewar ita mace ce mai jiki sosai, yanzu ɗan wannan tsugunnon da take, jin ƙafafuwan take suna mata zafi, a ɗan mintuna da tayi a haka.
Bayan mintuna kaɗan.
Ɓarayi ne tsaye a waje, Hajiya da Ladingo da driver a gaba, boss ɗin ɓarayin ya ce, "mun gama abun da ya kawo mu, abun da na ke son kuyi yanzu shine, kusa gudu daga nan har sai mun daina hango ku!" Fiddo Ido Hajiya tayi, jin aikin da ɓarayin nan ke son sa su, hakan yasa ta ce, "gwara da su Ladingo ne ma, amma ranka ya daɗe ɓarawo da girma na, da jikin nan nawa, amma ace nayi irin gudu haka? A dai duba lamarin" "ohoo to bari in nu na miki yadda zakiyi gudun, kai Zarto miƙa min wuƙar nan".
"A ah wallahi ai ba sai mun kai wannan matakin ba, yanzunnan zanyi, zaku irgamin lamba ne ko ko intai haka?" Ganin amsar wuƙar da yayi ne yasa Hajiya da kuma su Ladingo suka palpala da gudu, ƙafa me nace ban baka ba, suka bar Malam da shi da ɓarayi, yayin da Malam ɗin kam Allah kaɗai yasa iya tsoron da ya tsinci kansa ciki, domin shi ya san ɓarayin nan ba su da imani, haka suka addabe ƙauyen, amma da dare suka fi aiwatar da abunsu, amma da yake yau sun ga lafiyayyen mota shine suka zo.
Su Hajiya guda suke sosai, kar kaso kaga yadda Hajiya ke gudu, saboda ƙafar ta sanye da takalmi mai ɗan tudu, yadda kasan agwagwa mai koyon tete, suna gudu tana kiran su Ladingo, "wai baza ku jira ni ba? Wato in mutu ko oho a wurin ku ko? Harda kai da kake bawa na?" tana faɗi tana sauke numfashi, amma babu mai kula ta kowa dai gudun sa yake, musamman ma driver da yake namiji. Bayan ɗan lokacin da suka share suna wannan gudun suka iso gurin da akwai mutane ɗai ɗaya, hakan yasa su tsayawa, suna sauke numfarfashi, da 'yan tazara Hajiya ta ƙaraso bayan ta cire takalmin ta da taga yana yi mata cikas.
Ƙafafuwan nan burum-burum da ƙura, sauke ƙatuwar huci Hajiya tayi, domin jin jikinta take yana yi mata wani irin ciwo tun ba'aje ko ina ba, da ƙyar ta samu ta zauna akan wani rabin block ɗin ƙasa da ke wurin, sai dai tana gama sadaukar da jikin ta kan sa kawai ya rushe tayi ƙasa, dama block ɗin daɗaɗɗene, "sannu ƙawata, amma yau munga iftila'i!" cewar Ladingo. Cikin haushin abubuwan da ya faru Hajiya ta fara yiwa Ladingo magana.
"Dalla yi min shiru! duk abin da ya same mu ba ke ki ka ja mana ba? Ni har na ma fara shakkar bakin ki, an ya babu tsinuwa a wannan bakin na ki? duk shawarar da kike bani ba bu na alkhairi a ciki, daga wannan sai wancan, wallahi nayi dana sanin karɓar shawarar ki da nayi, kuma bani ƙa rawa" "haba ke kuwa Hajiya! Ya isheni wallahi! ako da yaushe sai kina bani laifi idan shawara batayi aiki ba, wato yau harda tsinuwa ki ke cewa a kwai a baki na? Bayan ke ce babbar laifin! wancan na bokan da aka samu matsala, ƙila ma aikin ne baki bi ƙa'ida ba, wannan kuma ni da kai na na ce miki kar muje da motarki, don nasan ƙauyen sai a hankali, amma ki ka ce afurr an buga bindiga a mota zamu, amma yanzu kuma ki ɗaura min laifin komai a kai na?".
Driver kam kallon su kawai yake da mamakin magan-ganunsu, yadda suke cece-kuce mai makon su godewa Allah da ɓarayin basu lahanta su ba, wato dama gurin boka suka zo? Ga shi sun tsunduma shi cikin matsala, harda fasa masa goshi akayi, sannan ga asarar wayarsa da yayi, wanda yasan sai yatara albashinsa na watanni ida zai sake sabo. Hajiya ce ta ƙara cewa, "to in ba laifin ki ba na waye? Ga shi kin sa ni asara! kin san wayar da suka amshe min nawa take kuwa, harda sarƙunan gol ɗina" ta faɗi tana matsar ƙwallan takaici, da kuma zafin abubuwanta da ta rasa, ga ƙafafu sunyi suntum-suntum.
Wani mota 'yar ƙurƙura ne yazo wucewa a wurin, hakan yasa driver kallon su Hajiya yana faɗin, "Hajiya ga wata mota nan ko in tare shi? ƙila mu samu ya kaimu ko cikin gari ne, naga yamma ya fara yi" duban inda motar take Hajiya tayi yadda motar ke tafiya kamar ana turata saboda rashin saurin ta, gashi sai wani ƙara take, ta juyo wurin driver da masifa ta ce, "wani irin asara ne zai sa ni in hau wannan motar mai kama da gon-gon?" "Kaga je ka gwada mana sa'arka, ƙila ya kaimu, inyaso mu mutai mu bar Hajiyar", cewar Ladingo tana kauda fiska.
Wucewa driver yayi gurin mai motar, Hajiya kuwa ta haɗe girar sama da na ƙasa saboda haushin da Ladingon ta ƙara bata, duk ba ita ce silar kasancewarsu haka ba? "Me kike nufi ke Ladi? Don bazan ma ƙara ƙarasa sunan na ki ba" Juyowa Ladingo tayi tana duban Hajiya da mamakin abun da ta faɗi, Hajiya kuwa ta kuma cewa, "ai bara kiji ni ɗin nan Zainabu na daɗe da sanin cewa kishi da ni ki keyi, idan ba haka ba, taya bayan amshe min gwalagwalai da kuma mota da 'yan silalla amma kamar murna kike da hakan? Wannan ai baƙin ciki da kuma na hali ne".
"Ah lallai Zainab! Ina ce nima an amshe min nawa kadaran? wato duk halaccin da nayi miki baki gani ba? Koda yaushe gurin warware miki matsalar ki nake, da kin shiga damuwa ki min waya, wato shine yanzu ki ke da bakin cewa ina miki baƙin ciki? To akan me zan ma mai maƙon tsiya baƙin ciki?" Ladingo ta faɗi, gaskiya ne faɗin Hajiyar, sai dai yau batayi farinciki ba, don tunani take ina ma ace abubuwan da ɓarayin nan suka kwashe na Hajiya ita zata mallake su, ai da ta rage zafi da su.
"Ashe kin min halacci?! kuma ni ce mai maƙon tsiya? sai ki faɗa min ina kike kai abincin da kike ci a gida na? Wanda ki ke haɗawa da guzuri in zaki koma gida, kuma indai wannan mugun shawarar da kike min ne halacci to ki riƙe abinki, domin ni banga ranarsa ba, daga yau ban ƙara karɓar sa"
Suna cikin kace nace driver ya dawo, Ladingo ce ta dube shi tana cewa, "ya amince?" "Eh ya amince, amma fa ya ce dubu goma sha biyar za a ba shi, idan ba haka ba to bazai je ba" "cab ɗi! Dubu goma sha biyar a wannan lokacin? Kuma cikin gon-gon ɗin nan? A lallai wannan ya cika ɓarawo", cewar Hajiya cike da masifa, Ladingo ta dubi Hajiya ta ce, "to kinga maƙon ko? Yanzu ko million mai motar nan ya ce baza ki iya biya mu tafi ba?".
"Keh Ladi ki kiyayeni, toh kimin tijara gaban driver ya raina ni, kinga kin huta ai ko?" "To ni ɗazun ba tijarar kikai min à gaban sa ba?" Dakatar da su driver yayi da faɗin, "Hajiya to yanzu ince ya tafi kenan? Ga shi can yana jira, kuma idan muka rasa wannan motar da ƙyar mu samu wata, ƙarshe sai dai muyi kwanan hanya" "Eh to kuma ka faɗi gaskiya, to muje kawai" Hajiya ta faɗi hakan tana kuma komar da kallonta ga Ladingo ta ce, "kowa ya biya kuɗin sa, babu wanda zan biya wa" "kan kin ma in kinso kar ki biya!" Ladingo ta bata amsa cikin Haushi.
Ƙwafa Hajiya tayi tana ƙoƙarin tashi, da ƙyar ta samu damar tashi, sai dai ƙafafuwan n'a a tsame ta kuma jin su fiye da na ɗazu, da ƙyar ta isa gun motar, sai dai wani tashin hankali hawan motar, "wayyo ni duniya me nayi miki yau? Wannan masifa da me yayi kama? Yanzu ya zan yi in hau wannan motar, ga cinyoyi duk ciwo suke min ga ƙafafuwa suntum kamar an kwaɓa fulawa" Hajiya ta faɗi a zuciya kamar ta kwarma ihu.
"Malama ki hau mu sa ta mana! Don alfarma ce na muku fa, domin ina dan inda zani amma na amince zan kai ku" cewar mai motar, cikin ƙarin takaici Hajiya ta kallesa, "yanzu kai baka ji kunya ba? Ka tsuga uban kuɗi akan wannan kwarɓaɓɓiyar akori kuran ta ka, amma kace wai alfarma kayi mana? Wato don ka ganin duk ƙura ta mamaye ni shine kake min tsawa" Ta faɗi cike da haushi, don ita ta tsani abun da za a ce na fidda kuɗi ne.
Da ƙyar da siɗin goshi Hajiya tayi nasarar hawa motar, bayan wahalar da tasha harda ƙara tsinewa shawarar Ladingo, nan suka kama hanyar fita daga ƙauye, duk da abu ya haɗe musu hamsin da biyar, ga ƙarar motar da yake kashe musu dodon kunne, sannan ga jikin su da yake girgiza saboda tsabar gargada, sannan ga iskar ƙurar da suke shaƙa na hanya, domin dama ɗazu da yake lafiyayyen mota ne sai ya rage musu wani abun, musamman ma Hajiya yadda jikinta ko wani kafa ke bada amshi, cinyoyinta kamar ana soya mata su, domin tsintuwar da take yiwa shawarar Ladingo a halin yanzu yana ƙoƙarin cika buhu. Ladingo kuwa sai ƙara jin haushinta take, itama tayi dana sanin ba wa Hajiya shawarar, don yanzu ji take kamar baza ta ƙara yiwa Hajiya magana akan matsalarta ba.
AMNA.
Yauma bayan lokacin da ya kamata ta tafi gida yayi, don haka ta wuce wannan gurin motsa jikin, kamar dai jiya canza kaya tayi izuwa na excise, nan ta fara yin abunta, wayarta ne t'a fara ƙara, barin abun da take tayi tana zuwa ɗaukar wayar da gaggawa, numbern MR ta gani, domin jiya bayan ta gama waya da Raheena ta maida sum ɗin ƙaramar wayar izuwa wayarta, don ko zai iya kiranta idan ba tanan, domin jiya bayan ta dawo ta tadda missed call ɗin sa, don ƙila yana amfani da