Showing 48001 words to 51000 words out of 129098 words

Chapter 17 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

34

bazan bar hakan ya sake faruwa ba" tana faɗi tana kauda kanta daga garesa, shiru sukayi jin yadda ta ɗauki zafi, "Wali me haka yake fita ta hancin ka? Kai kamar jinine fa" cewar Zarah bayan taga jinin da ya fara fitowa daga hancin Wali.

Da sauri Amna ta juyo da kallon ta kan Wali dan ganin jinin da Zarah ta ambata, daidai lokacin da shima yayi saurin sa hannunsa dan taɓo abu mai kama da ruwa da yaji saukar sa a ƙasar hancinsa, saurin miƙewa yayi cikin firgici sauran ma haka dan suma tashi sukayi banda Amna da dama a miƙe take, matsowa kusa da shi tayi tana kallonshi cikin tsoron Allah dai yasa ba abun da ta gani a waya bane ke shirin faruwa.

Hayaniya suka faraji a cikin makarantar lokacin wasu mata biyu suka shigo ɗaukar jakan su, binsu da kallo su Amna suke ganin yanayin su "hei he What is happening outside?" Ta tsaida su da tambayar bayan sun ɗau jakukkunan su suna nufan ƙofar fita, "Wallahi mutane ne keta faɗuwa a waje, kamar abunda ya faru a wasu garuruwan jiya, ni dai tsoro nake ji dan haka gida zamu".

Ɗayar na gama faɗin haka suka fice harda gudu cikin ru ɗu, zaro ido su Amna su kayi suna kallon junan su a razane, da sauri gabaɗayan su suka fita dan tabbatar da zancen 'yan matan nan, aikuwa suna fita suka ga makaranta a ruɗe, mutane wasu sun faɗi ƙasa wasu kuma sai ihu suke, ga yadda jinin yake fita kamar yadda ya faru a wasu garin.

Hatta malamai a ruɗe suke don kuwa har 'yan cikin su sun faɗi, Amna ce me dauriya harda addu'a takeyi a bakin ta, amma Zarah da Nabila kam jiki sai kyarma yake saboda tsoro, dan ɗauka sukayi suma hakan zai faru dasu, shi kuwa Wali bakinsa ne ya fara fitar da jini daga ƙasar madasar haƙoransa, riƙe kansa yayi sakamakon yadda yake juya masa. Saurin riƙosa Amna tayi lokacin da yake ƙoƙarin faɗi. Ƙasa da shi tayi cikin tashin hankali, suma sauran durƙusawa sukayi suna ambaton sunan sa cike da far-gaba da kuma tashin hankali.

Mutane ne suka kusa fa ɗawa kansu sabinda yadda duka makarantar suke a matuƙar tsorace, sai gudu suke, dan wasu rasa hanyar fita m'a sukayi saboda tsabar tsoro, "Mubarak!" Ta furta haɗi da zaro ido dan tunda suka rabu gurin shiga aji bata ganshi ba, dan tasan angama musu papern farko tun ɗazu, Zarah tace "bari inje induba ko yana class ɗin su" "no ku kukula da Wali Let me go look for him" tayi maganar tana tashi ta nufi ɓangaren class ɗin su Mubarak ɗin su kuma sai ambaton sunan Wali suke akan ya tashi dan Allah, kiransa suke yi suna hawaye.

Bata sameshi a aji ba, hakan yasa ta zagayawa tana ƙwala mai kira amma shiru, saboda rikicewar da makarantar tayi bata samu mai mata sharhin koya ga inda Mubarakyake ba, sake shiga matsanancin damuwa tayi dan idon ta har ya fara rinewa, tun tana nema akan ko yana can, a a ƙila ta can yake har ta fara fita daga hayyacin ta.

Tana cikin tafiya tana waige-waige aka bangaje ta har glashin ta ya faɗi ƙasa, kuma aka ta ka, bata tsaya bi ta kansa ba ta dawo inda tabar su Zarah, tarar dasu tayi sai kuka sukeyi, durƙusawa tayi ƙasa tana kallon su cikin rashin fahimtar dalilin kukan na su tace "banga Mubarak ba, ko kun ganshi? Me yasa ku kuka?".

Tayi musu mabanbantar tambayoyin lokaci ɗaya, tana maida hankalin ta gun Wali, "bamu ganshi ba, Amma dubi Wali gaba ɗaya ya fita daga hayyacinsa, jinin yaƙi tsayawa" Zarah tana ƙarashe maganar suka sa kuka ita da Nabila, kan Amna ta yunƙura gurin yin magana taji muryar Wali n'a cewa "ku.. tafi gida.. karku ra ɓu... ni dama mutuwa... mutuwa zanyi" yayi maganar da ƙyar saboda yadda yake jin ƙoƙalwarsa take masa yanayi ji yake tamkar ta ko ina aciki farfashewa yake.

Maganar shi ta ƙara sa su Nabila fashewa da kuka "No no no no babu komai babu abinda zai sameka, ku kuma kudaina kuka, muje mukai shi hospital" cewar Amna tana miƙewa, ɗaukar sa tayi cak à hannun ta sukayi waje, sai dai a wajen ma hakan take domin shima mutane a hargitse suke, sai surutu ta ko ina, ko napep ɗin da zai ɗauke su basu samu ba dan babu mai tsayawa.

Ganin hakan yasa ta ijje Wali ƙasa yayinda zuciyar sa ke bubbugawa dim dim, dan da badon babu asibitin kusa ba da a hannun zata kaishi, tsayawa tayi gaban wata baƙar mota mai tsada, hakan yasa matuƙin yayi saurin ta ka birki dan saura ƙiris yabi ta kanta, dukda ya tsaya amma bai fito ba kuma bai sauke gilashin motar ba, bere tayi tinanin zai mata masifar abinda tayi.

Zuwa tayi ta tsaya gefen gilashin motar, duk da bata da tabbacin nan ne mazaunin direba da zata sami mutumin zaune ko ba nan bane, dan babu lokacin yin tinanin hakan, sanya hannunta tayi tana ƙonƙosa gilas ɗin, aikuwa tayi sa'a nan ɗinne ke zaune, a hankali ya sauke gilashin kamar baisan abinda ke faruwa waje ba, sanyin AC motar ne ta bugeta dukda kuwa a waje take, saidai hakan bai mata wani tasiri ba sanadiyyar halin da take ciki na tashin hankali.

Fiskar sa da facemask ko idon sa bata kallo sosai saboda facingcap ɗin da yasanya, kuma bai juyo gareta ba bare ta samu nasarar ganin ko ƙwayar idon sa, "baiwar Allah lafiya?" Yayimata tambayar ba tare da ya ga inda ta tsaya ba, ba tareda ta damu da rashin kallonta da baiyiba tace.

"Aboki nane ba lafiya kuma yayi tsanani dan Allah kataimaka ka kaimu asibiti" tana ƙare maganar ta juya ɗauko Wali ba treda ta jira amsarsa ba, ko tinanin zai iya tafiyar sa ba. Saida tabar jikin motar sannan ya bita da kallo, matuƙar mamakine ya cika sa lokacin da yaga ta cicciɓo ƙaton saurayi a hannun ta, ba tareda nuna da ƙyar tayi riƙon ba.

#Hmm ba magana kudai mu haɗu a next part dan jin yadda zata ka ya.

______________________________________________________________________________________________

Part 5️⃣1️⃣▶️5️⃣2️⃣

Sai da tabar jikin motar sannan ya bita da kallo, matuƙar mamakine ya cika sa lokacin da yaga ta cicciɓo ƙaton saurayi a hannun ta, ba tare da nuna da ƙyar tayi riƙon ba, kamar wacche ta riƙo jariri, "cab wannan mata maza ko me?" Ya jefawa kansa tambayar, yana buɗe bayan motan yadda ko sunyi ƙoƙarin buɗewa baza su jisa à rufe ba.

Tana isowa Zarah tasa hannu tana buɗe marfin baya dan asa Wali ciki, gaba ɗayan su suka shiga ba tareda hankalin kowa ya konta daga abinda ke faruwa ba, saidai ma tsoron halin da abokin su ke ciki, yiwa motar key yayi ba tareda ce musu ƙala ba.

Suna isa suka tadda asibiti cike da mutane sosai abu kamar masifa? "Wai hakan na nufin kusan duka al'ummar Gombe suna ta'amali da miyagun ƙwayoyi? Kuma na ƙungiyar POSPA? Dan ina da yaƙinin wannan ƙwayar da Wali yace sabuwar fita da walakin akansa, to amma ya akayi hakan ya faru?" Abinda ta faɗi a konyarta kenan.

Basu samu likitan da zai duba su ba saboda yadda mutane sukai musu yawa, barin Wali sukayi gaba ɗaya suna zagayawa dan neman likitan da zai dubashi amma basu samu ba, hannu ɗaya Amna ta sanya a goshin ta cikin matsanancin damuwa da tinanin abinyi, dan so take idan ansamu doctorn da zai dubashi tabar asibitin taje ta duba na ta ahalin, domin gaba ɗaya hankalinta yana garesu, saboda yadda zuciyar ta ke tayi mata wasu zantuka akan tayi sauri taje kar wani abun yasame su.

Suna tsaye cikin rashin abunyi Nabila ta hango wanda ya kawo su a mota gun Wali yana duba shi, "Amna duba can kamar wanda ya kawo mu asibiti yana duba Wali, dama doctor ne?" ta faɗi tana share hawayen da keta zubo mata, itama Zarah share hawayen na ta tayi dan tabbatar da abinda Nabila tace, Amna kuwa ko ɗigon hawaye babu a idon ta saidai launin ja da ya kewaye farin, amma bai shafi ƙwayar idon ba.

Juyo da akalan idon ta tayi zuwa ga inda Walin yake, ba tare da ta musu magana ba ta fara tafiya zuwa wurin, su kuma suka ta ke mata baya, sosai yake duba Wali yana bashi kulawa, ba tare da sun isa gab wurin ba suka dakata, suna ganin yadda yake ƙoƙarin sa a kan abokin su, ciro waya Zarah tayi dan ta kira 'yan uwan ta.

"Ina da buƙatar ruwa" mutumin ya faɗi yana waigawa ko zai ga ruwa, ganin hakan ne yasa Amna saurin cewa "bari inkawo" tana faɗi ta juya nemo ruwa, bayan 'yan mintina ta dawo da ledan ruwa ƙolli ɗaya tana cewa "da ƙyar na samo wannan Allah yasa ya'isa" "is ok dama kaɗan nake buƙata" ya faɗi yana miƙa mata hannu alamar ta miƙo masa, har lokacin kuwa fiskar sa sanye da mask.

ɗago ruwan tayi dan ɗaura masa bisa hannun, hakanne ya bata damar ganin ƙwayar idon sa, kamar yadda shima sai yanzun yaga na ta, "wow eyes ɗin ta so amazing" yayi furucin daga zuciyar sa, saurin sakin ruwan tayi ya faɗi ƙasa tare da sakin ɗan ƙara, sakamakon shocking ɗin daya ziyarci hannun ta lokacin da take miƙawa mutumin ruwan, wanda hakan ya farune sanadiyyar hannun su daya ɗan haɗu kan ta kaiga sakin masa ledar.

Riƙe hannun ta tayi da ɗayar hannun tana murzawa tana kallonsa, shima haka ana shi ɓangaren ya ji shocking ɗin hakan yasa su kallon kallo a junan su, ƙawayen ta da suka matso kusa da ita tun bayan da sukaji ƙarar da ta sakine suka haɗa baki gurin faɗin, "sannu" koda basu san abinda yasata ƙarar ba. Ta saukar da kai ta ɗauki ruwan dan sake miƙa masa.

Sai kuma hakan ya sake faruwa karo na biyu wanda yasa har hankalin wasu dawowa kansu duk da a ricike suke kuwa, a yanzu kallon junan su suke da matuƙar mamaki, ganin abinda ya faru ne yasa Nabila ansan ruwan da kanta ta miƙa masa, ba tare da ya fita daga mamakin faruwar hakan ba ya amsa haɗi da mayar da hankalin sa kan majinyacin.

Su Nabila tsaye a tsorace cirko-cirko suna ganin yadda abokinsu ke jin jiki, numfashinsa tamkar zai tafi dan har kauda kansu suke suna sharɓar hawaye, hayaniya ne ke cigaba da tashi cikin asibitin, daga majinyata, doctorcin dakuma wa'enda ba cutar ta samesu ba kowa da ka ganshi kasan yanacikin tashin hankalin da bazai kotantu ba. Ana haka wayar dake cikin aljihun Amna yayi ƙara, sa hannunta tayi ciki tana zaro shi.

Numbern Mubarak ta gani kan screen ɗin wayar, ita tama manta ma dawani tinanin kira da ba tun ɗazu ta kirashi ba, saurin komawa gefe tayi tareda ɗagawa tana toshe ɗayar kunnen ta domin ta jishi da kyau, don gefen data koma har yafi surutun mutane, magana take amma taji shiru, dubawa tayi ashe ya tsinke ma, "credit ɗin shi ne ya ƙare kome?" Sai kuma ta sake trying, nan ma aka sake katsewa, "ha'a me haka? Why he's interrupting my call?" Tayi tambayar wa kanta.

Bata sadudaba takuma sake kira karo na uku, sai dai wannan karon a kashe taji wayar, fiskar ta alamar tambaya da tinanin Allah dai yasa ba wata matsalar bace, domin a yanzu jin zuciyar ta take a wani matsayi daban.

"Zanje gida duk abinda yake faruwa ku sanar dani duk da nasan kuma neman ku ake yanz..." Amna ta faɗi haka bayan ta dawo wurin su Nabila tana duban Wali cike da tausayawa, sai dai kan ta ƙarisa Zarah ta katseta da cewa "ba damuwa, mun sanar da su dan yayana ma yana kan hanya, ɗazu na tura musu massage dukan su sabida banda kati, ita kuma Nabila yau batazo da wayan ta".

"Aini banma yi tinanin kiran kowa bama, to yanzu dai ni bari na tafi dan Allah ku kula dashi, memakon hawayen da kuke ta zubarwa tun ɗazu kuyi masa addu'a Allah ya bashi lafiya mana, hakan zai fi ai" insha Allah suka amsa mata dashi ita kuma ta fice ba tareda tayiwa wanda ya kawo su kuma yake kula musu da aboki godiya ba, dan ta tafi ne da yaƙinin zata dawo.

Da ta fita bata samu abun hawa ba, da sauri da gudu-gudu harta isa gida bayan dogon tafiya da tasha, domin da nisa tsakanin asibitin da kuma gida, amma juriya irinna ta bai nuna alamar gajiya tattare da ita ba, gurin ƙarfe biyu ta isa gida, dan ko sallahr azahar basu samu nutsuwar yinsa ba.

A wangale tatarda ƙofar gidan "ƙofa a buɗe?" Ta jefawa kanta tambaya, batayi wata-wata ba ta antaya cikin gidan, sai dai me? Tarar da gidan tayi a hargitse kamar anyi yaƙin 1918 a cikin sa, da gudu ta faɗa ɗakin Mamma amma wayam ba ta ciki, ta shige na Ummee ma haka a'ah takuma zuwa na Mubarak nanma wayam, sai firfito da ido takeyi tana bin ko ina na gidan da kallo.

Kamar zararriya ta fara zagaye gidan tana duba su itane toilet, kitchen, kai hardasu walldrop, sai kiran sunan kowanne a cikin su take da ƙarfi, amma shiru kake ji kamar anhaɗiyi radio, da dukkanin alama dai su Ummee sunyi ɓatan dabo a cikin gidan su.

Zama tayi a kan kujerar falon Ummee, sai a lokacin ta fara fitar da numfashin tashin hankali, zunbur ta miƙe tana nufan ƙofar gida, bata tsaya a ko ina ba sai agidan maƙoftan su da suka fi shaƙuwa tana tambayar su ko su Mamma sun shigo gidansu, amma fa sukace, a ah amma ɗazu sunji ɗan hayaniya a gidan koda suka leƙa basu tadda kowa ba sai ƙofa a buɗe, dan su kansu sun shiga damuwa.

Bayan mintuna kaɗan Amna ce ke shiga cikin gidan su jikin ta kamar ba laka takejin sa, rasa à wani mataki take tayi yayinda zuciyar ta ke yi mata wani'irin suya, ta tattambayi maƙoftan su amma babu wanda yasan abinda ya faru, sai wani yaro mai kimanin shekara bakwai ne ya sanar da ita yaga sanda aka sa su cikin farar mota aka wuce dasu.

Tsayawa tayi à tsakar gidan tanabin ko ina da kallo kamar yaune farkon shiganta ciki, sakin jikin ta tayi tana durƙusar da guiwowin ta ƙasa, rasa abinda yake mata daɗi kota-kota tayi, zafi takeji ne koko sanyi? Itama bata sani ba, rusinar da kanta ƙasa tayi tana hawaye, gwara tayi kukan ma ƙila ta samu sauƙin azabar da takeji a cikin ranta, kuka ta farayi, tun tana mara sauti har tafara mai ƙara, babu wanda yazo rarrashinta cikin maƙoftan na su kowa a tsorace dan wasu har garƙame ƙofofinsu sukayi, dama ga abinda ya faru a gari, wasu kuma suma iftila'in yafa ɗa musu suma

Tashi tayi jiki asanyaye dan gabatar da sallahr da batasamu nutsuwar yi ba gashi har la'asar yayi, alwala taje taji ta dawo cikin ɗakin Ummee dan gabatar da sallah, bayan ta idar sai a lokacin ta fara tinanin shin suwaye sukayi garkuwa da iyayen ta? Domin yanayin yadda ta sami gidan ya tabbatar mata da cewa fa, ba a hankali aka tafi dasu ba, to meyasa? Akan wani dalili? Shin kasheta suke son yi ne? Da zasu kama mata ahali su barta ita ɗaya? Meyasa ma tun farko bata dawo gida ba, da duk hakan baifaru ba, dan da saita kusa kashe wa'enda sukayi hakan.

Tana zaune a wurin tana karanta wasiƙan jaki, tunda ta sake alwalar magriba bata gusa ba har tayi isha'i, lokaci ya wuce ƙarfe tara na dare, gajiya da ƙarar da wayanta yake tun ɗazu tayi, hakan yasa ta ɗagoshi zatai wulli dashi bata sani ba hannun ta yadanna accept, "hello Amna" jin maganar yasa ta fasa abinda tayi niyya tana sawa a kunnen ta dan a tinaninta Ummee ce, "hello hello Ummee" "ba Ummee bace nice Zarah" Zarah ta faɗi tana fashewa da matsanan cin kuka.

Miƙewa da sauri Amna tayi zuciyar ta na tsananta bugu tace "Zarah me yasa kike kuka? Meyasame ki?" Da ƙyar ta tsaya tana sheshsheƙar kuka ta furta "Amna Wali yaaa" ta tsaida ƙarisa maganar saboda kukan da ya ƙara taho mata, "what? What? Kamar fa so kike ki gayamin Wali ya rasu fa, no bahaka bane tell me the truth" tafaɗi tana ƙolalo ido kamar Zarah na gabanta "yes Amna Wali he's death".

"Innalillahi wa inna ilaihi raju'un, innalillahi wa inna ilaihi raju'un, innalillahi wa inna ilaihi raju'un" ta ambata cikin tashin hankali, juye-juye ta farayi kamar wacche ta manta wani abun, "Wali ya mutu, kuma bashi kaɗai ya mutu ba, nasan suna dayawa, me haka me hakaaaa" ta kai ƙarshen maganar da ƙarfi tana sinnewa ƙasa, idonta ne ya koma tamkar garwashin tukubar mai tsire, domin gaba ɗaya damuwar da ke zuciyar ta ne ya dawo kansu.

Haka ta kwana wannan ranar ba tareda ta rintsa ba, ko bacci da yake ɓarawo fa yau bai sace taba, dan babu wannan damar, tinani ne birjik a cikin konyarta, amma da ta kamo wannan sai wancan ya wargaje ta rasa a mizanin da zata ɗaura tambayoyin da zuciyoyin ta ke yi mata, haka har gari ya waye.

karkaso kaga Amna awannan tiƙin domin yadda ta dawo tamkar abin tsoro, ƙasan fatan idonta yayi baƙi shi kansa fiskar na ta fatar ta koma ja, musamman hanci da kunnuwan ta.

Gari kuwa abu yaɗan lafa, saidai anyi asarar rayuka da dama, masu kwana a gaba kuma suna asibiti.

BAYAN SALLAHR ASUBA,

Babu wanda ya leƙota daga cikin maƙofta dan ganin ya ta tashi, dan sunsan tabbas ita ƙolli ɗaya ta kwana cikin gidan,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login