Showing 93001 words to 96000 words out of 129098 words

Chapter 32 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

50

ta ce, 'Ammu hoton, 'yar ki, sak hotona fa, lokacin da nake ƙarama" ta faɗi tana sauke Numfashin tsantsar ruɗewa.

Itama Ammu ƙara shiga mamakin tayi, "Taya hakan zaiyu? Kamanin mu lokacin ƙuruciya da kuma girma duk iri ɗaya, maganar mu ma ɗaya, signing ɗin mu ma ɗaya, kamar almara? Kai! ban taɓa jin haka ba, Ammu ko ke kin taɓa ji ko ganin ko sauraron haka?" Tayi maganar tana ƙure Ammu da ido" sai kuma ta koma kan gadon ta kuma kwantawa kamar na ɗazu, ta kuma shiga cikin zurfin tunani.

Ruki. Tunda Amna ta bar inda suke zazzaɓin tsoro da azaba suka rufe ta, saboda ba ƙaramin zafi take ji a gaba ɗaya jikin ta ba, ba ƙaramin buguwa tayi a wannan matattakalan ba, tabbas cewar aljanun ne don da basu tausaya mata kamar yadda suka ce ba, da babu shakka yanzu a kar-karye take. Hajiya kuwa dake cikin tashin hankalin ganin ɗiyar ta haka fiska kamar zatayi kuka ta ce, "kin gani ko? Kin gani ko? Sai da nayi ta miki hannun ka mai sanda amma kika dubure, yanzu wa takasance wa?" ta faɗi tana ƙollah.

Ɗaga ta tayi tana faɗin, "dubi yadda ta maida miki fiska kamar jajjagen tumatiri, kai ya wannan aljani baiyi b..." bata ƙarasa cika wa kalmar haƙƙin sa ba Ruki ta rufe mata baki tana ci gaba da sakin kukan ta sannan tace, "Hajiya karki zage shi kada ya dawo" ta faɗi tana ƙoƙarin miƙewa, "Hakane kuwa wallahi na sha'afa ne" cewar Hajiya cikin tsoro, haka suka wuce Ruki na ɗingishi, zuciyarta cike da dana sanin abin da ta aikata, to meyasa ma bata yarda da maganar da akayi mata a baya ba?.

Amna. Tabbas wannan shine labari mai kama da almara da taɓa ji a rayuwar ta, wanda ya girgiza mata tunani, wannan wani irin kama ne haka? Koda tana jin ana cewa mutum yana da kaman sa guda bakwai a duniya amma ba'irin haka ba, kama ba tare da haɗa jini ba?

Dare.

Marwan da Hajiya da Dady ne zaune cikin ɗakin Dadyn, "Alhaji har yanzu banji ka ce komai ba, kuma ya kamata a ce anfara Shirye-shiryen auren Marwan, amma tun da ka dawo nake jira inji daga bakin ka amma hakan bai kasance ba, banda ma haka tun da kayi tambayar auren nan banji wata magana ta shiri da ta fito daga bakin ka ba, har yanzu saura sati biyu" cewar Hajiya, ammafa har yanzu muryar ta sai a hankali, sai da Alhaji ya ni sa sannan ya ce, "dama mata aka sani da shiryawa, ni wani shiri zanyi? Allah ya kaimu lokacin".

Ya faɗi haɗi da juya kan sa gefen Marwa dake latsa waya, ya ce, "ana magana amma kai hankalin ka kan waya" "Dady kun riga da kun tsara komai, ni ma ina nan ina tsara nawa shirin, ai akwai chilling" murmushi kawai sukayi, Hajiya ta kuma cewa, "duk da mu mata muke da bidiri amma fa yaron nan shine babban ɗan mu, kuma wannan auren shine wanda zamu fara aurar wa, ka ga kuwa ya kata ayi shiri na musamman, ni nariga da na tsara abubuwan da zamuyi, kuma muna buƙatar kuɗaɗe sosai don aiwatar da hakan, saboda biki ne za'ayi na manya cikin manya, domin yarinyar itama iyayen ta ba da ganan ba" murmushi kawai Dady yayi.

WASHE GARI.

Shiryawa Amna tayi cikin shigar doguwan riga, a da riga da wando ne favourite ɗin ta, amma anan dole dogon riga zai maye gurbi, tunda babu yadda za'ayi ta sa riga da wamdon, har ta fara jin daɗin sa saboda sabon da ta farayi da shi, sallama tayi wa Ammu sannan ta fita riƙe da haɗaɗɗiyar jakar ta a hannu, ta fito sak 'yar masu hannu da shuni, sai shining take yi. Tana isa falo ta ci karo da Dady shima ya fito, gaishe sa tayi shi kuma ya ɗora da cewa, "yata akwai aikin da zan sa ki" "toh Dady ina jinka".

"Akwai baƙon da zanyi, Marwan da Saleem suna wani uzuri, ita kuma Auta wai bata da lafiya, shine nake son ke kije ki tarbi baƙon, ƙarfe biyu jirgin su zai sauka, sannan na samar miki driver da zai dinga kaiki office da duk wata uzuri da zai taso miki" da to ta amsa masa suka fice waje.

Nuna mata drivern yayi da kuma bata numbern wanda zata tarba ɗin, sannan driver ya buɗe mata mota haɗaɗɗiyar motan kalar shuɗi ta shiga mazunin baya ya rufe kana daga baya ya ja su.

COMPANY.

Suna isa companyn kowa ya ke ta bata girma, harda masu yi mata rakiya cikin mutane da kuma security, samun wuri tayi ta zauna kan kujerar office ɗin bayan ta kaiga shiga, mutanen da suka rufa mata baya ne suka gabatar mata da kan su, kowa da aikin sa a gare ta, domin sune zasu kasan ce mafi kusa da ita akan sauran a duk lokacin da take da buƙata.

Sanar da su tayi da sukawo mata files masu muhimmaci da kuma bayanai da zasu sa tasan inda zata fara. Amsa mata sukayi cikin girmamawa, sannan suka wuce.

Kallo ta fara bin office ɗin da shi, haɗi da kwantar da kanta a jikin kujerar, nitsawa tunani tayi lokacin da Mubarak yake sanar mata da burin sa da kuma fatan sa, "remain one year mu gama school, nifa na ƙosa lokacin yayi, sannan bayan mungama na samu aiki a lafiyayyen company ina zaune a ƙayataccen office ƙafa ɗaya kan ɗaya habawa ai babu wani shege wallahi".

Murmushi tayi bayan ta tuna maganar ta sa, da ace shine ya tsinci kansa a wannan matsayin da bata san farin cikin da zata gani a kan fuskar sa ba. Murmushi ta saki me cike da kewan sa, wanda take ji lokaci da dama, tayi kewan faɗar su.

Babu daɗewa wa'yan nan mutanen suka dawo ɗauke da files, amsa tayi tana kuma tambayar su, domin ya zama wajibi a gareta ta mayar da hankali kamar yadda aka umurce ta, duk da bata taɓa sanin aiki game da aikin company ba amma bai sa taji cewa baza ta iya ba.

Yaudai bata ɗau wani aiki da yakamata ta fara a companyn ba, sai nazari da kuma duba files da tayi, don ta kamo bakin zaren. Haka har lokacin sallah yayi, gabatar da sallan tayi a cikin ɗakin hutu, duk da cewa akwai masallatai manya da yake a cikin kamfanin, na mata da kuma na maza.

Tunawa da abun da Dady yasa ta ne tayi, hakan yasa ta ta miƙe haɗi da duba lokaci a agogon dake hannun ta, ganin ƙarfe biyu ya kusa ne yasa ta ɗaukar wayarta ta sa shi a acikin jakan ta, fitowa tayi tana zuwa gurin réceptionist.

Cikin girmamawa suka gaisheda Amna da faɗin, "welcome out Madam C.E.O" amsa musu Amna tayi da thank you, sannan ta kuma cewa, "zan fita yanzu, idan ankawo min wasu files ɗin ku adana min zuwa lokacin da zan dawo" amsa mata sukayi ita kuma ta wuce.

Shin kuna ganin Amna ta fara aiki a sa'a?

Zata ci nasara don a miƙa mata iyayen ta?.

Waye zata je tarba duk da abaya munji waye shi? Ya zata kasance?

Ruki dai ta karɓi rabon ta😂

Sannan gashi ana maganar auren Marwan, ashe dai ya kusa angon cewa bamu da labari.

Mukasan ce a part na gaba..

___________________________________________________________________________________________________________

8️⃣9️⃣

▶️

9️⃣0️⃣

Da isan su filin jirgi.

Fitowa daga motar tayi bayan driver ya buɗe mata ƙofa cikin girmamawa, har wani irin abu taji ya zilla daga zuciyar ta, wai ita ce a mota kuma ba ita take tuƙin ba harda driver, hmm amma baza ta ɗauki wannan amatsayin jin daɗi ba, domin ba a hurumin ta take ba, bazata sakan-kance akan abinda ba tada haƙƙi a kansa ba.

Zuciyarta ce ke tunanin wannan sabon baƙo da Dady ya ce tazo tarba, koya yake ne ma? Babba ne ko saurayi? Domin da badon ya ce mata baƙo ba da baza ta san mace ko namiji ba domin bai sanar mata da sunan sa ba. Ciro wayar ta tayi ta fara duba numbern da Dady ya bata, sai dai bata gansa ba, da alama dai tayi kuskuren saving numbern, iska mai sanyi ta furzar daga bakinta, tana mai tunanin hanyar da zata bi, ba tada numbern Dady bare ta kira shi ya turo mata wani, tun da ɗazu kawai bata yayi ta kwafa.

Mutane cike a filin jirgin kowa na hada-hadar gaban sa, wasu tafiya wasu dawowa, zagaya idanun ta take tayi tana kallon mutane, to taya zata gane mutum ɗaya a cikin ɗunbin mutane haka, wanda bata san suffan sa ba?

Tana a haka taji dirar mutum a gaban ta, kamar mai koyon tsalle, ɗaga idon ta tayi tana duban wannan sha-sha-shan, washe mata bakin sa yayi kamar gonar auduga, gashi bakin na sa da faɗi ai sai ya zama kamar zai haɗiye ta.

Aliyu ya ce, "Beauty ya kike? Ashe na kasance mai sa'a matuƙa, da ya kasance na same ki anan, me kikazo yi?" Murmushin haushi ta sakar masa ba tare da ya kula ba, "eh me yakawo ki nan? Duk da nasan harda kasancewar sa'a agare ni" ya kuma yi mata tambayan ganin bata basa amsa ba, kauda kai tayi gefe kamar dole ta furta, "akwai baƙon da zan tarba ne" "da kyau amma wannan baƙon ya kamata na saka masa, domin silar sa na sake kuma haɗuwa dake, shin kin san yadda soyayyar ki ta kasance a zuciyata bayan mun rabu jiya kuwa?" Cewar Aliyu yana ƙara washe gonar audugar sa.

Surutu yake ta zubawa ba tare da ya san haushi yake bata ba, gashi ita kuma dole tayi haƙuri, saboda Dady ya ce mata shi ɗin ɗan abokin sa ne, to don haka kuwa ai dole ta kasance mai nuna masa sakin fiska a matsayin Safna.

"Soyayyar ki ta kasance kamar kogin ƙorama ce dake wucewa a ƙarƙashin zuciya ta, Safiyya kin sace min zuciya, kin chake ta da kibiyar son ki fiye da tunani, yanzu ki sanar dani shin nayi miki? Kina so na? Amma zan so in samu kyakykyawar amsa daga gare ki" cikin neman barin inda yake ta ce, "muyi maganar wani lokaci, yanzu ya kamata na maida hankali na akan abinda nazo yi nan".

Ta faɗi tana ƙoƙarin tafiya, sai dai saurin shan gaban ta Aliyun yayi yana ƙara cewa, "a ah ki sanar min kafin ki tafi, abin da bai gaza kalmomi goma ba?" Juya idon ta tayi ta sauke, alamar oh fitina sannan ta ce, 'bari inje" kallonsa take cikin mamakin ƙarfin halin sa, haɗuwar su jiya wanda ko takamammen minti goma basuyi ba, amma yau kuma ya haƙiƙance wai dole ta ce tana son sa?.

"Me ma sunan ka?" Ta faɗi tana kallon sa don ta kawo ƙarshen zancen na sa, ya ce, "Oh sorry ko ban sanar dake sunana ba? Sunana Aliyu ɗa ga Alhaji Sabo Nasarawa, mahaifina mai kuɗi ne sosai, kowa yasan da shi kamar na ki iyayen, kinga kuwa wannan shine haɗi mai tsananin kyau, ayi aure na manya" saida ta saki tsaki cikin zuciyar ta sannan ta ce, "Look Aliyu.." kan ta kaiga ƙarisa furucin ya katseta, "abun da nake son ki sanar dani kawai ina son ka, don Allah ina sauraron ki".

Wata ajiyar zuciya ta sauke mai cike da tunanin hanyar da zata bi ta rabu da shi, babu damar yi masa rashin mutunci, ƙila ya ɗau labari ya kaiwa Dady, ita kuma yanzu bata son wata matsala da zai sata ƙara yiwa su Dady ƙarya, bayan wanda tayi musu na cewa tana da aljanu, amma to wace hanya zata bi don warware wannan? Gashi lokacin ƙarfe biyu yayi, ya kamata zuwa yanzu ta haɗu da wanda zata tarba.

Ci gaba da matsa mata Aliyu yayi, duk da kasancewar ta mai surutu, amma shi wannan surutun na sa ɓata mata rai yake matuƙa, domin har ta fara tunanin canza mai launin fiskar ta yanzu. Idon ta ne ya faɗa kan wani saurayi, kyakykyawa, fari tamkar yadda take fara, dogo ne ƙirar jikin sa na cikakken namiji, riga da wando ne ya saka irin na maza 'yan ƙwalisa, yayin da ƙwanjin sa suka ɗan fito daga jikin rigar sa, ya kasance tamkar wani ɗan balarabe.

Ƙure sa da ido tayi abin da bata taɓa yiwa wani ɗa na miji ba, domin kallo ne cike da burgewar da yayi mata, tabbas wannan bawan Allahn ba ƙaramin haɗuwa yayi ba.

Aliyu kuwa ganin kamar hankalin ta ba a kansa yake ba ne yasa ya furta, "beauty... kyakykyawa.." sai da ya na na ta hakan sau uku sannan ta farga da hakan, juyowa tayi tana kallon sa shi kuma ya ce, "ina sauraron ki" ya faɗi yana ci gaba da jiran ta furta masa abin da zuciyar sa ke so.

Maida kallon ta gun mutumin da ke tahowa tayi, yayin da shi kuma ya kusa isowa inda suke, ƙara na na ta maganar Aliyu yayi hakan yasa wani tunanin mafita yazo gare ta, idon ta kan mutumin, "shine mafita a yanzu" ta faɗi cikin zuciyar ta haɗi da saurin zuwa gurin sa, ba tare da wani tsoro ko fargaba ba, shi kuwa Aliyu ya bita da ido ganin saurin wucewa da tayi, to ko dai guduwar maganar sa zatayi ne?.

Shi kuwa saurayin ganin budurwa ta tsaya a gaban sa, yasa shi tsayawa yana kallon ta da mamakin tsayawar da tayi gaban sa kuma idon ta kansa, "please ka tsaya min" ta faɗi tare da marai-raice fuska, ba tare da ta jira amsar shi ba, ko kuma fahimtar tsayawar da take nufi yaji ta fara magana bayan wani saurayi ya biyo bayan ta.

"Yauwa Aliyu wannan shine amsar tambayar ka" cikin mamaki Aliyu da ya biyo ta bayan yaga tsayawar ta gurin mutumin don dama sun kusa gab ya ce, "wannan shine amsar me? Wani amsar?" Murmushi tayi irin na musamman ɗin nan, sannan takai idon ta kan mutumin da yake binta da ido kawai ta ce, "shine dalilin da yasa ban sanar da kai ina son ka ba, saboda shine masoyi na kuma wanda zan aura, don haka kayi haƙuri".

Ido kaɗan mutumin ya buɗe ganin wannan mahaukaciyar, to idan ba mahaikaciya ba taya daga ganin mutum zatayi irin wannan ƙaryar? Shi kuma Aliyu wani baƙin ciki ne ya turnuƙe masa zuciya, haɗe fiska yayi yana kallon wanda ta ce saurayin ta kuma wanda zata aura, maida kallon sa gun Amna yayi ya fara magana cikin rashin jin daɗin abinda ya faru, "amma bai kamata kimin haka ba Safiyya! Kina nufin in zare wannan kibiyar da kika sokeni a zuciya kenan? Haƙiƙa kin raunana min zuciya".

"Duk yadda kake so kayi da zuciyar, amma kar ka yiwa kibiyar cirewar garaje, gudun abin da ka iya je ya dawo, domin zaifi kyau idan ka samu wata ta shiga da salama ba da rauni ba, koh masoyi na?" Ta ƙarashe maganar tana kai idon ta kan mutumin dake gefen na ta, yana yi mata kallon wani irin maganar banza kikeyi?.

A zuciye Aliyu ya wuce yana jin haushi, wannan ai baƙar magana ta gaya masa, shi da yake murna yayi mata? Amma shine zata cewa wani tana son sa kuma a gaban sa? "Wayyo Safiyya haƙiƙa zuciya ta zatayi jinya" ya furta a fili, don harga Allah shi fa baiji daɗin wannan abun da ya waka na ba, shi dama ya titsiye ta ne don ta furta kalmar so a garesa ko da bataso ba, ta yadda zai samu hujjar kafa tutar sa a zuciyar ta, ta hanyar samun dama izuwa gidan su, idan kuwa hakan ya faru ai ya warke, saboda ita ɗin billionaire ce yanzu, sai gashi ta nuna masa wani haɗaɗɗe a matsayin wanda zata aura, kaii amma fa yazo gurin jirgin nan da rashin sa'a.

"Wow.. wow wannan guy ɗin ya haɗu" maganar wata budurwa da tazo wucewa kenan ta furta da ganin wannan saurayin da tayi, maganar ya faɗa kunnen Amna, hakan yasa ta dawo da kallon ta gare sa, idon su ya faɗa kan na juna, kallon mintuna uku sukayiwa junan su ka na ta saukar da na ta idon, cikin ƙasaitacciyar murya saurayin ya ce, "wannan abun da ya kamata ayi ƙarya a kai ne?" Cikin jin kunya da abin da tayi ta ce, "na sani, amma bani da wani zaɓi ne, kayi haƙuri" ta faɗi haɗi da wucewa dan itama bata so tayi hakan ba, gashi yadda yake wani binta da kallon raini.

Binta yayi da kallo wace irin yarinya ce wannan? Tsaki kaɗan ya saki na ɓata masa lokacin da tayi, ya wuce yana duba wayar sa.

Bayan Amna ta bar gurin wannan saurayi, ta fara duddubawa ko zata ga wani wanda zai gane ta ya ce shine wanda aka aiko sa gurin ta, amma wannan wani irin tunani ne?. Ta ɓata lokaci sosai a wurin a ƙarshe dai ta yanke shawarar komawa gida kawai. Driver na ganin ta doso wurin ya fito ya buɗe mata ƙofa, yana faɗin, "Allah ya ja zamanin Hajiya.." "a ah kar ka kirani Hajiya banje Makka ba, ka kirani Amn..." sai kuma ta tuna ashe dai ba wannan sunar bane take amfani da shi, kar tayi suɓul da baka.

"Ka kirani Safna" "hajiya ai ban isa ba, bazan iya kiran ki babu girmamawa ba" "toh naji, ka kirani madam C.E.O kamar yadda ake kira na yanzu, amma kar ka kirani Hajiya ka jira zuwa na Makkah tukun" ta faɗi cikin dakewa ba raini, hakan yasa driver ƙara jin tayi masa kwarjini, domin ba ta bashi alamar wasa ba".

Jan mota yayi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login