Showing 78001 words to 81000 words out of 129098 words

Chapter 27 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

43

ta dawo daga baya kuma taƙi hakan fa?".

Cikin rashin fahimta Hajiya ta kuma cewa, "ban gane ba" Ladingo tayi murmushi tana faɗin, "ina nufin ki tursa sa wa yarinyar ƙin aikin kawai, wato ta cewa Alhaji ba ta buƙata da kan ta, idan ta faɗi hakan ina bazai tirsa sa mata ba?" Sai da Hajiya ya ni sa ka na ta ce, "ba shakka wannan shawara ce mai kyau, ƙorai idan ta ƙi bana tinanin zai tursa sa ta, amma taya zata tsoratan?".

"Wani irin tambaya ne haka ƙawata, ina ce yarinyar nan tana matuƙar tsoron ki? Dan haka abu ne mai sauƙi ai," Hajiya ta amshe da faɗin, "ke ni wallahi na rasa gane kan yarinyar nan tun da ta dawo gidan nan, jiya fa na buɗe baki zanyi mata magana kenan, ta ce min, wai yanzu zata tafi babu buƙatar in wahalar da baki na, na daɗe ina tunanin wannan furucin na ta, Safnan da dana sani koda zaki sanya mata wuta a harshe baza tayi motsi ba".

Hajiya na gama maganar Ladingo ta tsaya nazari, sai kuma ta matsa kunnen Hajiya tana raɗa mata yadda zatayi.

DARE.

Kamar yadda Dady ya sanar Amna tazo ta zauna akan dining, bayan ta riga da ta ciyar da Ammu, Saleem kuwa har yanzu ya ƙule a ɗaki yaƙi sakin jiki bare ya fito waje, koda aka kira shi cin abinci ya ce ba zai ci ba, Hajiya da Ruki sai hararan Amna sukeyi ita kuma ko ajikin ta, Dady na barin wurin Hajiya ta ɗau jus ɗin zoɓon dake cikin jug tayiwa Amna wanka da shi, cikin ɗagun murya ta ɗora da faɗin,.

"ki saurare ni da kunnen basira, jibi ne Alhaji yace zaki fara zuwa kamfani ko? To ki jini da kyau, ki sanar da shi baza kiyiba ba kya buƙata, idan ba haka ba kuma, kina fita daga gidan nan to fa kiyi bankwana da jatumar ki, domin kuwa sai dai ki dawo ki tadda anyi jana'izar ta, ko gawan ta baza ki gani ba" Hajiya tana kammala gargaɗin ta wuce.

Amna da ta miƙe jikin ta na famar rawar hasala ta bi Hajiya da wani irin kallo, sai kuma ta koma da idon ta kan Ruki da ke mata dariyar mugunta, domin shi Marwan ana zuba mata zoɓo ya tashi ya bar wurin, ba don komai ba kuma sai dan ya tsira, koda mutanen ɓoyen zasu gani to su tabbatar baya cikin wannan sabga.

Ɗayar jug ɗin da ke ɗauke da zoɓon ne ta ɗauka ta antayawa Ruki itama a jiki, a fisace Ruki ta ɗago zata mare ta amma ta ga ashe wucewa ma tayi, kallon jikinta ta farayi ganin kalar ya ɓata mata jiki, da sauri ta bi Amna da kulan jar miya, dan ta rama abinda tayi mata, ta kuma ƙara zuba mata miyar dake cikin kulan.

Sai dai tayi mamaki da taga Safna na hayewa sama, "me zai kaita sama?" Tayi tambayar wa kanta, tana tafiya don ganin abinda zai kai Safnan, kuma gashi tafiya take ba tare da tsoro ba.

Amna ɗakin Hajiya ta nufa gadan-gadan, Hajiya ba ta daɗe da shiga ba Amna ta rufa mata baya, tana buɗe walldrop ɗin ta kawai ta ga dulum ankashe wutar ɗakin, waigawa ta fara yi gashi wayar ta ba a hannun ta yake ba, kafin ta fara lalube kawai taji an cafkar mata wuya, take aka manna ta da bango, da ƙyar ta samu damar magana cikin murya a shaƙe ta ce, "wa waye, ne? Sake, min wuyaa na, kashshe ni za'a, yi ne? Taimakoo, taimakoo" faɗan hakan da tayi ne yasa Ruki da ke neman inda Amnan ta shige ta ji muryar mahaifiyar ta, hakan yasa ta ijje kulan da ta riƙo.

Amna kuwa ƙara matse wuyar tayi dan hana ta samun wurin yin wata maganar, "Hajiya kina inaa? waye ya shaƙe miki wuya?" Cewar Ruki cikin tashin hankali, gashi gurin duhu ne bare ta ga komai, kuma tana tsoron shiga itama a dawo kan ta, hanyar ɗakin Dadyn su ta nufa da gudu. Jikin ta na famar kyarma.

Fa ɗawa ɗakin tayi tare da kiran sunan sa, saurin sauke wayar da yake yi daga kunnen sa yayi kamar mara gaskiya, juyowa yayi yana kallon ta, tabbas sallama abu ne mai kyau, da Safna ce ta shigo ɗakin nan ya san da sai ta yi sallama kuma ta nemi izini, amma da yake Wannan ce ga shi ta shigo kamar wacche aka koro, bata damu da ako wani hali zata tadda shi ba, abinda ya faɗi cikin ransa.

Kan ya tambaye ta ta fara faɗin, "Dad Hajiya naji tana neman taimako, kuma ɗakin na ta cikin duhu, akwai abinda yake faruwa" ta faɗi tana sakin ihu a firgice, fitowa Dadyn yayi don zuwa ɗakin ta, lokacin Marwan ya haye sama dan zuwa ɗakin sa, shima Saleem ɓurun-tun da yaji yasa ya fito a tsorace, ganin Dady da Ruki da sukayi suna nufan ɗakin Hajiya ne yasa su suma yin sashin, domin da ganin su ba ƙalau ba.

Amna da ɓacin rai ya hanata tunanin komai ta kuma matse wuyan Hajiya kamar zata karta, ɗaga ta ta fara yi tana raba ƙafafuwan ta da tayis ɗin ƙasan, Hajiya kuwa abu yayi abu, ta sadaƙar da cewa yau sa inta yayi, ɗaga ta sama sosai Amna ta ƙara yi, tana jin kamar ta buga ta a ƙasa, wani lokacin idan ranta ya ɓaci sosai rasa hankalin ta takayi, ba ƙaramin ɓata mata rai Hajiya tayi ba, bayan wanka da zoɓo da tayi mata har tana ikirarin zata kashe mata Ammu, zata kashe mata wacche a yanzu take ɗaukar ra kamar mahaifiyar ta, to tunda zata iya aikata kisa, bari ta fara yi mata nata tukunna.

Hasken da ya gauraye ɗakin ne ya sata juyowa ƙofar ɗakin inda makunnin yake, Dady ne ta gani a wurin, hannun sa kan madannin bai cire ba, bayan sa kuma su Marwan, gaba ɗayan su sun ƙwalalo ido waje suna kallon abinda yake wakana, Safna riƙe da wuyar Hajiya, kuma ba riƙo na wasa ba, kallon da ta lura suna yi mata ne yasa ta fahimtar akwai abinda yake faruwa, ahankali ta juya da idon ta dan ganin abinda hannun ta ya riƙe, ganin shaƙar da tayiwa Hajiya tayi, ga idon Hajiyar kamar zasu fito waje saboda bala'i

Saké wuyar ta tayi Hajiya ta faɗi ƙasa riis, ko numfashi sai ta yi i da gaske take yin sa, ga idanuwan ta babu abinda take gani sai duhu, duhu asalin duhu, nufowa da gudu su kayi inda Hajiya take kwance rai a hannun Allah, girgiza ta suka farayi, suna ambatan sunan ta, ganin kamar rai na niyyar yin halin sa, da ace sunyi jinkirin zuwa da ƙila gawa zasu tarar.

"Na shiga uku, ya akayi raina yayi ɓacin da bana so? Ba fa yamin haka sai in abu yafi ƙarfi sosai, kisa? Da fa kashe ta zanyi" Amna ta faɗi cikin ran ta bayan hankalin ta ya soma komawa jikin ta, kuma cewa cikin ran ta tayi, "na rusa komai, yanzu wani dabara zanyi don kuɓutar da kaina? Ya Allah ka taimake ni, idan har komai ya rushe a yau to fa zan iya rasa ahalina" ta faɗi tana rintse idon ta, don ita kan ta bata so abinda ya faru ya faru ba.

Wani tunani ne yazo mata hakan yasa ta faɗi ƙasa alamun suma, dai dai lokacin da Dady ya ɗago da idon tuhuma ya ɗaura mata, sai dai ganin itama ta faɗi yasa shi tunanin wani abu, numfashin Hajiya ya fara dawowa, hakan yasa shi komawa inda Amna take ya fara kiran ta da sunan Safna.

BAYAN WASU AWANNI.

Amna ce ke Ijje ruwan da ta sha, tana bin kowanne da kallo, kamar yadda suma kowannen su ita ya zubawa na mujiya, Hajiya riƙe da maƙogoron ta da akayi mata tritment a asibiti, aka kewaye mata wuyan da auduga, hakan yasa sai kaga kamar ɗaga kan nata take, sai cigaba da sauke ajiyar zuciya take yi, itama tana bin Amna da kallo, da tsana fiye da na kullum da kullum.

"Yata me haka?" Cewar Dady, Hajiya ce ta fara magana cikin muryar ta da yake baya fita sosai saboda ɗaurin da akayi mata a wuya ta ce, "Alhaji akan me, sai ka tsaya, kana tambayar ta? Bayan komai a bayyane yake, kashe ni take son yi, abun da ya faru aidon ka".

"Ban fahimci abinda kuke faɗa ba, Dady ni ce nake son kashe Hajiya?" Amna ta faɗi harda marai-raice fuska ita nan wai ba ta da labariin abunda ya faru, tsananin mamaki ne ya cika su jin furucin da tayi, "ba shakk..." Hajiya bata kai ga matakin ƙarasawa ba ta kame wuyan ta, saboda raɗaɗin da taji a ciki, sakamakon fara maganar da tayi da karfi, hakan yasa ta fasa maganar da tayi niyya tayi shiru.

Tambaya Dady ya kuma yi mata da cewa, "my daughter kina nufin ki ce min baki san abin da kika aikata ba?" "Eh Dady realy I don't know" cewar Amna tana kuma maida fiskar ta alamar rashin sani, Marwan da Saleem kam kowa ya sawa bakin sa kwaɗo, saboda a tunanin su aljanun nan ne suka shiga jikin Safna, idan ba haka ba, taya zata iya ɗaga Hajiya duk ƙibar da Hajiya take da shin nan? Sannan kuma gashi ta ce ba ta da masaniya akan hakan?.

Tsaki Ruki ta ja tana ganin Safna rena musu wayo kawai take yi duk da tsoron yanayin da ta kalli Hajiya a hannun ta bai gushe daga zuciyar ta ba ta ce, "kina nufin shaƙar da kika yiwa Hajiya na kawo wuƙa baki sani ba?" Saurin miƙewa daga zaune kan tayis tayi cikin mamaki ta haɗe fiska kamar da gaske ta ce.

"Ruki, ni da kaina na shaƙe Hajiya da kuma hannu na?" Ta tambayi Ruki, sai ta kuma cewa, "kenan har yanzu suna nan basu tafi ba?" Ta faɗi tana haɗe fiska alamar damuwa, cikin rashin fahimta gaba ɗayan su suka kuma kallon ta, Dady ne ya kuma tambayan ta, "me kike nufi 'yata?" Sai da ta koma ta zauna amma a saman gado sannan ta fara cewa, "labarin mai tsawoo ne sosai, amma ya kamata insanar da ku komai, saboda kar ku ɗora min abin da ba a sanina na yisa ba".

Maida hankalin su gare ta su ka ƙara yi, suna jiran abin da zata ce, ɗaukar ruwan zafin da aka kawo mata da ya fara sanyi tayi tana kallon Amna. Zama mai kyau Amna ta gyara ganin tunanin ta zaiyi nasara.

#Mu haɗu a kashi na gaba don jin ƙaryar da Amna zata shafa musu.

Hajiya ta leƙa lahira kaɗan 😂

Saurin ɓacin ran da Amna ke dashi, ku nada wani tunani akan sa?

____________________________________________________________________________________________

Part 7️⃣9️⃣▶️8️⃣0️⃣

Zama mai kyau Amna ta gyara ganin tunanin ta zaiyi nasara, sannan ta ja numfashi mai ƙara, saboda idan ta fara zayyano musu wannan ƙirƙirarren labarin to fa sai sun amince zata barsu, "ke muke sauraro" faɗin Dady sauran ma suna jiran lafazin da zai fito daga bakin ta.

"Wato Dady, wani ƙaa surgumin jinnu ne ya shige kaina" "what!?" Cewar Dady da ƙarfi domin ya ga kamar Safna na son kawo zancen da kunne bazai ɗauka ba, sauran kuwa zaro ido su kayi kamar zai fito waje, kowa da labarin ƙanzon kuregen da yake sa ƙa wa cikin ransa.

Cikin tabbatar masa da abinda ta faɗa ta kuma cewa, "eh Dady! Wannan zancen ba makawa haka take, kuma hakan ya faru ne sanadiyyar barin gidan nan da nayi zuwa Nijar" "Nijer kuma? Yaushe hakan ta faru?" Dady yayi maganar kafin Amna ta kamo wani zancen.

Sai da ta juya da kallon ta gun Hajiya, tare da sakin murmushin gefen baki na mugunta, a ranta ta ke faɗin, "da ganin yadda ta mayar da idon ta gefe alamar mara gaskiya hakan na nuna baisan da zuwan Safna Nijar ba" Juyowa da kallonta ta kuma yi gun Alhaji tare da canza fiska ta kuma cewa, "Dady ina ce kaine ka bada umarnin turani ƙasar don ziyara? Haka Hajiya ta sanar da ni, ko Hajiya?" Ta kai ƙarshen batun tana kallon Hajiya.

Hajiya kam da zafin ciwon wuya da kuma tsoron fallasar da Amna ta fara yi mata ya haɗe mata biyu, ta yunƙura zatai magana, idon ta ya gauraye cikin na Alhaji da yake binta da kallon da gaske ne? tunda Safna ta ce tasan hakan, "ni na bada umarnin hakan?" Dady ya tambayi Hajiya kan tayi magana.

Rasa abinda zata faɗa masa tayi, domin bata tanadi zuwan lokacin ba, "Dady bari ingama baku labarin kafin kaje tuhuma wa Hajiya" cewar Amna don so take ta gama sharara musu ƙaryar da take son yi, in yaso daga baya sai ya koma wa Hajiya tambayar, sauke rushe-shiyar ajiyar zuciya Hajiya tayi, Dady kuwa ya ce, "ok cigaba".

"Kamar yadda nace hakan ya faru ne sanadiyyar barin gidan nan da nayi don zuwa Nijar, sai dai na sauka a garin ba tare da na san inda zan nufa ba, haka nayi ta yawo babu wanda ya taimake ni, na rasa abinda zan sa a bakin salati, bare gurin kwana, a ƙarshe sai a jikin wata bishiyar da bansan ta me cece ba na yada zango, wanda sai daga baya na gane ashe gidan Aljanu ne, to fa nan ne wani mugun aljani ya shige jiki na, wai na toshe masa ƙofar shigar iska a hancin sa, tun daga lokacin yake sauya min halayya, musamman idan aka min abun ɓacin rai, saboda akwai wani mutumi da ya tsokane ni a wannan garin, kun san me sakamakon da nayi masa?".

Marwan da Saleem da jikin su ke famar girgiza saboda tsoro, da kuma Ruki da take zaro ido sukayi saurin cewa, "a ah!!" Cike da tsoro wato dai so suke suji me ta yiwa mutumin da ya tsokane ta, Hajiya ma zancen ya fara shiigan ta, Alhaji kam bai nuna hakan ba, ci gaba da magana Amna tayi ganin sun bata gaba ɗaya nutsuwar su.

"Ɗage shi sama nayi kamar na ɗaga sanda, sai da na wulwula na nuna wa sama shi ka na nabuga shi da ƙasa" ta faɗi tana yi musu alama da hannu wai yadda tayi wa mutumin, ta cigaba da cewa, "mutumin nan da Allah ya so shi da rahama, haƙar-ƙarin sa na hagu ne kawai ya kare-raye, amma in banda nan komai na sa ƙalau yake" "eehh!!?" Suka haɗa baki gurin furtawa harda ƙara fiddo da ido da kuma doro da kawuna, alamar sun matuƙar girgiza da lamarin, amma banda Dady, domin shi bai nuna wata alama da zai nuna yayi mamaki ko kuma tsoro da furucin ba, to bamu sani ba ko ya bar haka a ran sa. Hajiya riƙe da audugar dake wuyan ta, har tana tunanin ashe dai ita babbar arziƙin ta auna, da ba'a karta ba, duk da tana jin itama kamar ƙashin wuyan ta ba'a daidai yake ba.

Amsa ta basu da fiska da kuma baki, "ehh haka batun yake, ai yanzu abun yayi sauƙi ma, duk da har yanzu idan aka ɓata min rai ina hakan amma na rage sosai, shine fa nayi tunanin hakan ya daina faruwa ashe ba haka bane" ta faɗi tana juyawa wurin Hajiya ta ce, "Hajiya ki godewa Allah da ya kawo su Dady a lokaci, da ban san iya yadda abun zai tsaya ba".

Wani nyawu mai ɗaci hajiya ta haɗiye tana godewa Allah, "kenan ranar su ne ajikin ki? Lokacin da na haɗu da ke a waje?" Marwan ya faɗi yana kallon ta kallon tsoro, ta amsa masa da, "ina ga! Hakan zai iya kasan cewa, domin hakan ya sha faruwa" Marwan ya kuma cewa, "kuma sune suka sa ni tsallen kwaɗo ranar?" Saleem ma cikin halin tsoron ya ce, "kenan ni ma su suka saka min wannan marukan a fiska? Har fiska ta ta canza kamanni? Dubi har yanzu a kumbure yake" ya faɗi yana taɓa fiskar sa da yake kamar gudan zuma ne sukayi bidiri a kai.

Tsaki Marwan ya sake yana bin Saleem da kallo ya ce, "kai kana maganar wani mari, ni fa bayan sun sa na mari fiska ta da ƙarfi wanda bansan adadin sa ba, suka kuma sa ni tsallen kwaɗo har na ke jin ƙafa ta kamar ba tawa ba, kwanan nan duk fama nake da shi, amma kai ɗan marukan da kasha kake wani kuru-ruta abun" Cike da haushi Saleem ya kuma ce wa, "eh mana kai naka ka sani ai, da ace marin da kayiwa kanka su sukayi maka da ka gane kuren ka" "dalla wuce nan kai dai ragon banza ne, koda ke dama ai nine babba, shiyasa na fi ka dauriya" cewar Marwan har da wani gyara kolar riga.

"Wa yaga babban banza" yana rufe murfin bakin sa, Marwan ya sake masa mari a fiskar sa da yake kamar balan-balan, wani irin ƙara ya sake jin azabar da yayi akan fiskar sa da yake ji kamar gyambo, shima niyyar ramawa yayi lokacin Dady ya daka musu tsawa, hakan yasa su dakatawa, kowa na huci. Dariya Amna ta fara yi babu ƙaƙƙautawa harda rufe ido, ganin yadda suke faɗa akan waya fi jin zafi a cikin su, amma ita ta san kowa a cikin su yaji jiki.

Ruki kam tuni ta hau layi jikin ta ya fara kyarma kamar mai far-faɗiya, sakamakon batu-tuwan da taji yayyin ta na yi, sannan kuma ga gaskiyar nan gaban ta wato Safna, sai yanzu ɗagun da tayiwa Hajiya ya dawo idon ta, raba ta da ƙasa ta yi fa, to idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login