Showing 84001 words to 87000 words out of 129098 words
Chapter 29 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
ba tayi laifi ba, "yanzu ne zaki fara abin da ya kawo ki gidan, mayar da hankalin ki sosai za kiyi a Mai Daraja cotton company".
"Kenan dama mining ɗin M.D kenan? Kuma kamfanin auduga ne?" Amsa ya bata da cewa, "da me kika ɗauki mining ɗin sa? Companyn auduga ne, shine babba daga cikin sauran, kuma shi ne mafi riba akan sauran, sai dai baya samun kula da ya dace, dan haka idan kika je ki tabbatar kin mayar da hankali a kowani ɓangare, kafin ki tambayi familyn ki suna lafiya, idan kika tafiyar da komai daidai zaki gan su". Yana kai ƙarshe ya katse wayar.
"Dama aikin sa kenan" ta furta, sai kuma tayi saurin sallamar Ammu da cewa inta fita zata samu 'yar aikin da za ta kula da ita kafin ta dawo, Ammu tayi mamakin maganar ta, wani 'yar aiki hajiya zata bari ta zo kusa da ita?, ta faɗi cikin ran ta ba tare da ta san wainar da Amna ta gama toya wa ba, da sauri ta fita tsakar gidan don ta san ba ƙaramin ɗaukar lokaci tayi ba.
Duk da ta fita ne ba tare da tabbacin a ina Dady yake ba, amma sai ta gan shi yana ƙoƙarin zuwa wata haɗaɗɗiyar mota blue colour, da sauri ta nufi inda yake, "I'm so sorry Dady" ta faɗi bayan ta isa, juyowa da murmushi yayi ya furta, "baki makara ba 'yata" Itama murmushi tayi ta ɗora da faɗin, "Dady dama inason in sa masu aiki kula da Ammu kafin na dawo" "ok bismillah" ya bata amsa da lama da hannu.
Nufan gurin ɗakunan su tayi tana tinanin wa zata sa wannan aiki? Sai Jummala ta faɗo mata rai, domin matar tana da kirki, hakan yasa da taje wurin ta fara kiran sunan ta, fitowa Jummala tayi domin yanzu ta daina mamakin kiran ta da Safna take yi mata, "na'am Safna'u" "yauwa dan Allah so nake na baki aikin kula da Ammu, ba yau kaɗai ba, gobe zan fara zuwa aiki, dan haka zaki rinƙa zuwa ki kula da ita kafin na dawo".
Cikin ɗan tsoro Jummala ta ce, "amma Safna'u Hajiya baza ta barni ba" "Wace Hajiya kike magana? Kinga, abinda na faɗa miki za kiyi, idan Hajiya ko ɗaya daga cikin su ya hanaki kula da Ammu to ki sanar da ni" Tana gama faɗi ta juya, sauke numfashin da ta riƙe tayi, dole tayi abinda Safna ta ce mata, tun da bata san me ta taka ba ta faɗa mata haka, don Safnan yanzu ba ta son raini ko kaɗan.
Shiga motar Dady tayi ya ja su, wani tunani ne ya faɗo mata rai, hakan yasa ta gyara zama ta juyo ta dube shi ta ce, "Dady ina son roƙan wata alfarma" "ina jinki 'yata faɗi duk abinda kike so" "dama ina da buƙatar ƙarin kayan sawa, sannan ba nida waya, ina ganin kamar ya kamata na samu wayar riƙewa zai min amfani" ta faɗi domin ya kamata ta samo ko da dogayen riguna ne na zuwa office, saboda baza ta iya da riga da skirt da kuma da zani ba, inba haka ba wata rana fa ɗi zata yi in tana tafiya da su.
"Wannan ba abun damuwa bane 'yata, nima ya kamata ace nayi tunanin haka tun tuni, saboda na daɗe ban baki kuɗi ba, bayan mun kammala abinda ya kai mu, sai in haɗa ki da driver ya kaiki shopping da kuma gurin sayen waya" "thank you Dady" "don't worry that's my responsibility".
#Muje dai zuwa😊
____________________________________________________________________________________________
Part 8️⃣1️⃣▶️8️⃣2️⃣
Miƙewa tayi saboda ƙoshin da tayi, "ya kika miƙe 'yata?" Dady yayi tambayar ganin ta miƙe, amsa ta bashi da cewa, "ƙoshi nayi ne Dady" "ok to kije ki shirya idan na kammala sai muje ko?" Da toh ta amsa mishi sannan ta wuce.
Sai da Hajiya ta leƙa don tabbatar da wucewar Amna sannan ta dawo da kallon ta kan Alhaji ta ce, "Alhaji kana ganin barin yarinyar nan taje kamfanin nan a haka ba laifi?" Ta kai ƙarshen maganar tare da ɗora hannun ta ga audugan da ke wuyar ta.
Gyara zaman sa yayi cikin rashin fahimta ya kalle ta ya ce, "me abun laifin? Idan akan abin da ya faru jiya kike magana babu buƙata, tunda ta riga da ta faɗi sharaɗin" "eh ta faɗa, amma su 'yan aikin ai basu sani ba, ka ga kada hakan ya dawo ana kace nace" ta faɗi domin so take tayi yadda zata sa ya janye batun, suma su Saleem hakan take a wurin su, burin su suji maganar ta rushe, amma basu sani ba wannan maganan ba bu abinda zai hana shi faruwa, idan ba mutuwa Safna tayi ba.
"Kada hakan ya dame ki" ya faɗi yana gyara zaman babbar rigar sa ya kuma cewa, "akwai wani maganar da nake so inyi da ku, Hajiya idan baki manta ba kwanaki na yi miki maganar wani shahararren mai kuɗi da keda zama ƙasar London ko?" Maida hankalin ta da kyau tayi kan sa tana cewa, "ba shakka munyi batun da kai, idan ban manta ba ma sunan sa Abu Shuraim koh?" "Ƙorai kuwa Abu Shuraim, to ɗan na sa Shuraim ɗin zai zo Nigeria kuma garin nan zo, wato Kaduna, dan gabatar da wani aikin sa, bayan ƙoƙarin da nayi na ci nasarar amincewar sa yaron anan gidan zai sauka".
"Allah Alhaji? Kana nufin ɗan hamshaƙin nan a gidan nan zai sauka? Wannan ai abun farin ciki ne" cewar Hajiya cikin jin daɗi, su kuwa sauran kallon su kawai suke tun da basu san da batun ba, Alhaji ya kuma cewa, "haka ne, kin san na sanar da ke buri na shine na shiga jikin sa sosai, saboda idan har na samu muka haɗa hannu da shi gurin kasuwan ci to ba ƙaramin riba zamu samu ba, kin ga kuwa wannan babban dama ne".
Ba tare da washe bakin da take ya gushe ba ta ce, "sosai ma kam, tunda har ya amince da ɗan na sa ya zauna a gidan mu ai kamar wata alama ce ta nuna zai iya hakan nan gaba" juyawa gurin sauran yayi yana faɗin, "abun da nake so daku ku kuma, yaron nan idan yazo ku girmama shi, koda ace kun girme sa, tunda ni ban taɓa ganin sa ba, bare nasan shekarun sa, don haka ku bashi girma, saboda wannan dama ce a gare ni da kuma ku baki ɗaya, kunga idan na rasa wannan damar tofa mun tafka babban asar".
Gaba ɗaya yaran haɗe fiska su kayi da jin maganar mahaifin su, Saleem ya ce, "Dady ya kake magana kamar kai ɗin talaka ne? Ko da ace ka rasa wannan damar taya zai zama abun damuwa? Kar ka manta kana da dukiya mara adadi fah" tsaki Dady ya ja yana kallon Saleem cike da takaici ya ce, "rufe mana baki sha-sha-sha kawai, kai maganar ka ina da kuɗi-kuɗi, ba ce maka nayi ka daina irin maganar nan ba? to bari kaji, ka ga wannan mutumin da nake magana a kai? Da za'a tara mutane masu kuɗi iri na, guda huɗu, to baza su fisa kuɗi ba".
Zaro ido gaba ɗayan su sukayi, gaskiya wannan mutumin ba na wasa bane, "cab ɗi! Wannan kam to ai ko ni sai inwa ɗan na sa biyayya! kace haka suke da ma ƙudan kuɗi?" Cewar Hajiya jin batun zun-zurutun kuɗi, amsa Alhaji ya bata da cewa, "fiye da yadda kike tunani, kuma wannan yaron shine kaɗai jinin sa".
Marwan da ke son magana ya dakata saboda yaji maganar da girma, duk da shima yana ganin taya za'a kawo mutum gidan su ya girmama shi? Miƙewa Alhaji yayi yana kallon Ruki ya ce, "auta na kiramin 'yar-uwar ki, idan ta gama shiryawa mu tafi" "Dady ni ba 'yar-uwa ta ba ce" ta faɗi harda turo baki, "ke, kin manta abin da ya faru jiya ko?" Cewar Saleem, Marwan ma ya ce, "rabu da ita, saboda babu abin da sukayi mata shiyasa take faɗin hakan".
"Dady bari na kira maka ita" Saleem ya faɗi hakan yana wucewa kiran Amna. Barin wurin Dady yayi Marwan ma haka, taɓe fuska Ruki tayi tana maida idon ta kan Hajiya ta fara cewa, "Hajiya wani irin dabara kika samo mana akan shegiyar yarinyar nan? Saboda bai kamata mu barta haka b..." kan ta ƙarisa Hajiya ta miƙe riƙe da wuya, cikin ɓacin rai ta fara magana.
"Zaki rufamin baki ko kuma na hamɓare miki shi? Gaskiyar Marwan da ace ta lasa miki wani abu da baza kiyi zancen ba, kin san yadda naji lokacin da ta shaƙe min wuya ne? Ba sai yadda naji kawai na sanar muku ba? Ana cewa in mutum ya suma taurari uku zai gani, ni kuwa biyar reras n'a gani à cikin maganuwan nan nawa" ta faɗi tana nunawa Ruki idanun ta tana ci gaba da cewa, "sai da naji kamar ƙafa ta ɗaya à duniya ɗaya a lahira, to wallahi idan na kuma jin wannan banzar maganar to sai na maida miki fiska kamar na Saleem da yake yanzu a saɓe" tana ƙarasa maganar ta wuce ta bar Ruki tsaye ƙerere kamar ta haɗiyi taɓarya.
Sauke numfashi tayi tana tunani, duk yadda Hajiya ke tsanar Safna amma yau tsoron ta take yi?. Hajiya da shigar ɗakin ta kenan kiran ƙawar ta ya shigo waya, ɗagawa tayi ba tare da ta faɗi ƙala ba, "hello ko ba kyaji na ne ƙawata?" cikin muryar ta da ke haryanzu bai washe ba cikin haushi ta ce, "niko nake jin ki har da sauraro m'a" Ladingo ta amshe da faɗin, "au ho, koda na ji, saboda yanzu nayi kiran waya amma network ɗin dai dai yake. Dama cewa nayi in kira inji yadda kika ƙare da matsalar ki".
"So kike kiga yadda na ƙare da matsalar tawa?" Cewar Hajiya har ta fara hasala, Ladingo kuwa duk da ta ji muryar aminiyar ta ba a daidai yake ba amma ta amsa da cewa, "eh" "to ki kirani bidiyo ki gani" ba tare da tunanin komai ba Ladingo ta katse tana shiga WhatsApp, kiran numbern Hajiya ta vidéo call tayi.
Hajiya kuwa ɗagawa tayi tana yin gaba da hannun ta, saboda ta ba Ladingo damar kallon rawanin da akaiwa wuyan ta, "subhanallahi! Hajiya me nake gani haka?" "Me za ki gani in ban da abin da kikayi min, Allah ya wadaran wannan shawar da kika bani!!" cewar Hajiya cike da haushi, domin da bata bi shawarar ba da wani labarin ake ba wannan ba.
Fuska a damuwa Ladingo ta ce, "me kike cewa ne Zainab? Na san ba ma haka dake" "Taya baza muyi haka da ken ba? Ina ce ke kika ban shawara akan in tsoratar da Safna? To kin ga sakamakon da hakan ya min, ashe tura ta Nijer ɗin da nayi ta gamu da iskokai, ina matsalar Marwan da Saleem da na fara sanar dake? To ashe dai aljanun ne suka aikata, bayan na yi mata kalaman da kika ƙisa min, ina isa ɗaki yarinyar nan ta ritsani, in taƙaice miki shaƙe min wuya tayi, ta kuma ɗaga ni sama, wallahi har sai da naji kamar leƙawa lahira nayi na dawo, saboda àzaban da naji a wannan shaƙa, da sai dai ki riski mummunar labari".
"Haka akayi?" Faɗin Ladingo, cikin tunzura Hajiya ta ce, "tambaya kike?" "A ah wai naga maganar ce abin dubawa" tsaki Hajiya tayi tana sauke wayar daga kunnen ta.
AMNA. Bayan ta isa ɗaki ɗazu ta sanarwa Ammu maganar Alhaji duk da babu abinda Ammun zata ce, shiga toilet tayi, tayi wanka, bayan tafito ta tsaya gaban walldrop ɗin da ta buɗe, tana kallon kayan da ke ciki ta rasa wanda zata sa, sa hannun ta ciki tayi tana duddubawa har ta janyo wata haɗaɗɗiyar dogon riga atamfa, pink, white and light purple colours, kalar sa ba ƙaramin burge ta yayi ba, juyawa gurin Ammu tayi tana nuna mata rigar haɗi da fadin, "Ammu wannan zai min kyau?".
Murmushi Ammu tayi, hakan yasa ta fahimtar ta ce eh, sanyawa tayi ta kuma gyara kayan basajar ta sannan ta ce, "Ammu ina kayan kolliyar Safna ne? Tun da nazo ban gan su ba" ƙoƙarin ɗaga hannun ta ɗaya tayi tana yi mata nuni da wani wuri, zuwa wurin tayi ta buɗe ta dauka, duk da fauda da jan baki da gazar baƙi ne kawai a wurin, zama gaban mirro tayi tana shafawa, da faɗin, "ita Safna ko kwalliya ba tayi da alama" cikin ran ta.
Tana à haka Saleem ya turo ɗakin ya shigo, hakan ya ɓata mata rai rashin sallamar da baiyi ba, juyawa tayi tana kallon sa, hakan yasa shi sauke kai ƙasa ya furta, "Dady na kiran ki" "ina zuwa!" Juyawa yayi zai wuce sai kuma yaji maganar ta, "idan zaka sake zuwa ka rinƙa sallama, ka kuma nemi izini, saboda ba ɗakin ka bane" yadda tayi masa maganar ya ɓata masa rai amma ya danne ya fice waje.
"Kamar ba musulmai ba, na lura dukkan su haka suke yi ko gaishe da Ammu baiyi ba, kamar bai san da zaman ta a ɗakin ba" ta faɗi tana sakin tsaki, Ammu da ke can gefe ta saki murmushi jin maganar da Amna tayi, ɗaukar gele da kuma takalmi tayi ta sa bayan ta kammala kolliyar, tayi kyau matuƙa gaya, fiskar ta ya ƙara fitar da haske baza ka tantance ba idan aka haɗa ta da balarabiya, kafin ta fita ƙaramar wayar ta tayi ƙara, zuwa da sauri tayi ta ɗauka da sallama, wannan karon bai riga ta magana ba, sai da ta gaishe sa ya amsa a dake ka na ya ce.
"Sannu da aiki" shiru tayi Tana tunanin dalilin da yasa ya faɗi hakan, "à tunanin ki bansan abun da ki keyi a gidan bane? To ki sani na san duk abin da kike aikatawa" sai da ta ɗan fiddo da manyan idon ta jin maganar sa, kenan ya san duk abinda nake yi? Tayaya? Hakan na nufin ina laifi kenan? Duk take faɗi a ran ta, n'a ta tsinkayi maganar sa yana ci gaba da cewa, "kar ki damu domin ba ƙaramin ƙoƙari kika yi ba, saboda haka na jinjina miki, dama abin da nake buƙata kenan" sauke dadɗa-ɗan numfashi tayi, jin ba tayi laifi ba, "yanzu ne zaki fara abin da ya kawo ki gidan, mayar da hankalin ki sosai za kiyi a Mai Daraja cotton company".
"Kenan dama mining ɗin M.D kenan? Kuma kamfanin auduga ne?" Amsa ya bata da cewa, "da me kika ɗauki mining ɗin sa? Companyn auduga ne, shine babba daga cikin sauran, kuma shi ne mafi riba akan sauran, sai dai baya samun kula da ya dace, dan haka idan kika je ki tabbatar kin mayar da hankali a kowani ɓangare, kafin ki tambayi familyn ki suna lafiya, idan kika tafiyar da komai daidai zaki gan su". Yana kai ƙarshe ya katse wayar.
"Dama aikin sa kenan" ta furta, sai kuma tayi saurin sallamar Ammu da cewa inta fita zata samu 'yar aikin da za ta kula da ita kafin ta dawo, Ammu tayi mamakin maganar ta, wani 'yar aiki hajiya zata bari ta zo kusa da ita?, ta faɗi cikin ran ta ba tare da ta san wainar da Amna ta gama toya wa ba, da sauri ta fita tsakar gidan don ta san ba ƙaramin ɗaukar lokaci tayi ba.
Duk da ta fita ne ba tare da tabbacin a ina Dady yake ba, amma sai ta gan shi yana ƙoƙarin zuwa wata haɗaɗɗiyar mota blue colour, da sauri ta nufi inda yake, "I'm so sorry Dady" ta faɗi bayan ta isa, juyowa da murmushi yayi ya furta, "baki makara ba 'yata" Itama murmushi tayi ta ɗora da faɗin, "Dady dama inason in sa masu aiki kula da Ammu kafin na dawo" "ok bismillah" ya bata amsa da lama da hannu.
Nufan gurin ɗakunan su tayi tana tinanin wa zata sa wannan aiki? Sai Jummala ta faɗo mata rai, domin matar tana da kirki, hakan yasa da taje wurin ta fara kiran sunan ta, fitowa Jummala tayi domin yanzu ta daina mamakin kiran ta da Safna take yi mata, "na'am Safna'u" "yauwa dan Allah so nake na baki aikin kula da Ammu, ba yau kaɗai ba, gobe zan fara zuwa aiki, dan haka zaki rinƙa zuwa ki kula da ita kafin na dawo".
Cikin ɗan tsoro Jummala ta ce, "amma Safna'u Hajiya baza ta barni ba" "Wace Hajiya kike magana? Kinga, abinda na faɗa miki za kiyi, idan Hajiya ko ɗaya daga cikin su ya hanaki kula da Ammu to ki sanar da ni" Tana gama faɗi ta juya, sauke numfashin da ta riƙe tayi, dole tayi abinda Safna ta ce mata, tun da bata san me ta taka ba ta faɗa mata haka, don Safnan yanzu ba ta son raini ko kaɗan.
Shiga motar Dady tayi ya ja su, wani tunani ne ya faɗo mata rai, hakan yasa ta gyara zama ta juyo ta dube shi ta ce, "Dady ina son roƙan wata alfarma" "ina jinki 'yata faɗi duk abinda kike so" "dama ina da buƙatar ƙarin kayan sawa, sannan ba nida waya, ina ganin kamar ya kamata na samu wayar riƙewa zai min amfani" ta faɗi domin ya kamata ta samo ko da dogayen riguna ne na zuwa office, saboda baza ta iya da riga da skirt da kuma