Showing 60001 words to 63000 words out of 129098 words

Chapter 21 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

32

ta bita dashi yasa ta cewa a zuciyar ta, "wannan matar fa ko alama ba ta yiwa mutum, koda yake na ma manta ashe cewa akayi tana da ciwo kamar paralise" tana faɗi ta ɗau spoon ta fara bawa Ammu a baki, a hankali har ta gama, Ammu taji daɗin abincin, rabonda taci ta ƙoshi har ta manta, saboda ko wacche take bata abinci lolacin da Safna ba tanan, a tsorace take ba ta, kaɗan kawai take ci, saboda matar tsoro take kar akamata, shiyasa da ta zo take hanzari ta gama ta tafi.

Kama hannunta tayi tana faɗin "har hannu na ya gaji" kallonta Ammu tayi da mamakin abinda tace, ita kuwa miƙewa tayi ko ruwa bata ba Ammu ba.

BAYAN KWANA HUƊU.

DA SAFE.

Amna ɗaukar ɗawainiya da Ammu take a matsayin ta kura a gareta, sannan gefe ɗaya kuma ga fitinan Hajiya da Ruki, domin har yanzu Marwan bai nuna mata halin sa ba tukunna, saboda basu cika haɗuwa ba, yauma bayan Ruki ta gaggaya mata magana ta nufo ɗakin Ammu a zuciye, tana shiga ta tarar da Ammu gefen gado, batayi wata-wata ba ta nufa inda Ammu take, tana isa ta fara magana cike da haushin da ta ɗibo.

"Madam nifa na gaji wallahi, wai su su Hajiyan nan kam basu da aiki sai ta kurawa 'yarki ne? To nifa bazan lamunta ba haka kawai" ta faɗi harda fitar da numfashin ɓacin rai, "nifa bazan iya tsayawa dogon lokaci ana wulaƙanta ni ba" ta kuma faɗi tana kai idon ta kan na Ammu, "kodai ma kawai zantuka n'a nakeyi bata fahimce ni ba? To naga ita ba ta magana sosai, dan haka zan sanar da ita gaskiyar komai kawai, ta daina ɗauka na 'yarta, dan kar n'a kasa yi mata wani abun taji babu daɗi" tayi maganar cikin ran ta.

A fili kuma tana kallon Ammu ta fara cewa, "Madam! Nifa ba 'yarki bace Safna, ni sunana Amna, kuma ya kamata tun farko kin gane, ni bansan me yasa suka ce na dawo zama gidannan a maimakon 'yarki ba? Na zo gidan nan ba tareda nasan dalilin meyasa akace nazo ba, amma ni bazan iya zaunawa ana min wasu abun ba, wai kin san me suke kirana kuwa? Cemin fa suke mayya, kukuma shegiya, sunaye dai marasa daɗi, to ni bazan yarda ba, idan 'yarki mayya ce niba mayya bace...".

Tsayarda maganganun da take tayi sakamakon hannun da Ammu ta ɗaura mata akan fiska, tana girgiza mata kai a hankali, alamar me yasa kike faɗin haka? Ganin yadda Ammu ke girgiza mata kai da ƙyar ne yasa ta fahimtar matar nan fa bata yarda da zancen da ta faɗa ba, hakan yasata cewa, "baki yarda ba? To da gaske nake bari in tabbatar miki" ta faɗi tana sanya hannunta dan cire alamar dake gefen bakin ta da tasa, yayin da idon Ammu ke kan ta cike da mamaki.

"Kin gani ko?" Amna ta furta bayan ta cire tabon, sake cewa tayi. "Bari in ƙara tabbatar miki" ta faɗi tana ƙoƙarin cire eye color, a hankali tayi nasarar cire na ido ɗaya, tana faɗin "kullum ina cirewa da dare amma ba kya lura" duk da yanayin jikin ta amma bai hana dara-daran idanuwan ta buɗewa kaɗan ba alamar shock, duk da cewa zuciyar ta nayi mata wasu zantuka tun abaya amma bata taɓa tinanin haka ba, take jikinta ya hau rawa sosai ko ta ina, da ace tana tsaye da babu abinda zai hana jikin ta saki ta fa ɗi, hatta zuciyar ta wani irin bugu take da sauri da sauri.

Yanayin ta ya matuƙar tsananta, da sauri Amna ta miƙe tsaye tana zaro ido ganin halin da matar ta shiga sakamakon faɗa mata gaskiya da tayi, saurin riƙe ta tayi cikin tashin hankali ta fara ambatan "Madaam! Madam! Madaaam!" Ta faɗi tana jijjiga Ammu da idonta ke bara barazanar rufewa, "Madam ki tashi dan Allah ki ga farceni" ta faɗi har muryar ta na rawa, har zata fita nemo ɗauki sai kuma ta fa sa, saboda tunawa da tayi da ta cire eye color.

Da sauri ta nufi kofin jug ɗin da ke ƙasa, wanda take sanya ruwa ta ijje, ta dau ƙaramin kofin sa tana tsiya ya ruwa a ciki, tallabo kan Ammu tayi tana kai kofin bakin ta, sai da ya ɗau minti huɗu kafin Ammu ta fahimci abinda yarinyar ke ƙoƙarin sa ta tasha, hakan yasa ta ɗan sha ruwan kaɗan, tana sha Amna ta sauke kofin haɗi da bubbuga bayan Ammu a hankali, cikin ikon Allah hankalin Ammu ya fara dawowa jikin ta.

Jinginar da ita Amna tayi jikin kan gadon, sauke numfashi mai zafi kawai Ammu take, hawaye sai zarya yake akan kuncinta, innalillahi wa inna ilaihi raju'un take ta na na ta wa cikin ranta, zama kusa da ita Amna tayi tana faɗin, "I'm so sorry! Da nasan zaki shiga wannan halin da bazan sanar da ke ba" da ƙyar Ammu ta kamo hannun Amna, saida ta kai idonta kan riƙon da matar tayi mata a hannu sannan ta maida kanta ga Ammu tana cewa, "nima bansan inda 'yarki take ba" ta faɗi ba tareda ta san abunda Ammun ta tambaye ta ba kenan.

"Haɗe idanun ta tayi wasu ƙollan na ƙara fitowa, zuciyar ta na yi mata ƙuna, da tayi tinanin 'yarta ce ta dawo, tayi zaton ko wasu ɗabi'u ne ta koyo a inda taje ashe ba haka bane. "Ina 'yata take? Ina aka kaimin ke Safna ta? Wacece wannan da aka kawomin a matsayin ki? Ya akayi kuka kasance masu kama da juna haka? Ya Allah kai ne kaɗai kasan duk abinda ke faruwa a kaina da kuma 'yata, ya Allah ka kawo mana mafita, ka kare min Safna ta a duk inda take" maganar da take tayi acikin zuciyar ta, haɗi da buɗe idanuwanta wasu hawayen na koranyowa.

Amna kuwa hankalin ta yaƙi kwantawa sam, musamman da taga Ammu na kuka, sai tayi da nasanin maganar da tayi, suna a haka sai ga Ruki ta faɗo cikin ɗakin, da sauri Amna ta rufe idonta da hannu ɗaya, tayi zumbur ta miƙe, ƙa re musu kallo ta fara yi ganin a yanayin da suke, ga mahaifiyar ta kamar tana kuka ita kuma ta wani miƙewa zunbur kamar mai laifi sannan ga rufe ido ɗaya da tayi.

Matsowa kusa dasu Rukin tayi tana cigaba da binsu da kallon baku kaiba sannan ta ce, "me ke faruwa a nan? Ke kuma wani irin iskanci ne yasa ki rufe ido?" Danne haushin dake niyyar zo mata tayi ta ba ta amsa, "am ƙwaro! Ƙwaro ne ya fa ɗa min cikin idon" tana faɗi idonta ya faɗa kan eye color ɗin da ta cire kan gado, sai da ta zaro idon da bata rufe ba sannan ta faki idon Rukin tayi wuff ta ɗauke shi, jan tsaki Ruki tayi ta ƙara cewa, "aikin banza! Ba cewa nayi kizo kimin wanki ba? Ko har yanzu abunda kika koyo a yawan gantalin na ki bai bar kan ki ba?".

Shigewa bayan gida kawai Amna tayi, domin tasan idan har ta tsaya sauraron Ruki babu abinda zai hana ta nakaɗa mata duka, "Iyyehh! Wato ma shigewa toilet kikayi kika ƙyaleni, lallaii! To wallahi zakiga abinda zanyi miki tsinanna kawai" tana faɗi ta bar ɗakin, saida Amna taji alamar barin ɗakin da tayi ka na ta fito, da sauri ta rufe ƙofar ɗakin, tana sauke ajiyar zuciya ta furta, "sai na yi maganin yarinyar nan zata shiga tai-tayin ta" ta faɗi tana jan ƙofa, zuwa drawer tayi ta buɗe ta ɗauki jakan da abubuwan suke a ciki dan ta maida alamar a fiskar ta.

Tana gamawa ta fice ba tareda ta ko kalli inda Ammu take ba, bare taga ta daina kukan ne ko kuwa, Ammu kuwa babu abinda take fa ce sauke ajiyar zuciyoyi a jere, Amna ko tana fita ta samu wani wuri a harabar gidan ta tsaya bayan ta naɗe hannayen ta biyu, ranta har yanzu a ɓace tana tinanin ta yadda zatayi maganin su Hajiya, amma agefe guda kuma tana tuna maganar mutumin nan ɗan kidnapping.

RAHEENA.

Yauma shiryawa tayi dan tazo gidan su Safna ta ga ko ta dawo, sai dai yau driver ne ya kawo ta har ƙofar gidan, bayan an buɗe mata ƙo fa ta gaida Baba Hambali, tun kan ta tambaye shi dawowar Safna ya sanar da ita, farin ciki sosai ta shiga jin aminiyar ta ta dawo, "tana ciki yanzu haka?" Tayi masa tambayar cike da ƙaguwa, yana tabbatar mata tawuce tana dosar ƙofar falo, har jikin ta na rawa saboda farin ciki.

Kamar ance mata ta juya ta hango ƙawarta, a hankali ta nufa wurin, Amna na tsaye kawai taji an rungumeta ta baya, ture Raheena haɗi da ɗaga hannu zata wankawa wanda yayi mata haka, domin da ma a hasale take, zaro ido Raheena tayi ganin abinda ke shirin faruwa, dakatar da marin tayi ganin wacche bata sani ba, da kallon mamaki Raheena ta bita ganin abinda tayi kamar ba Safna ba?.

"Safna! Lafiyar ki kuwa?" Cewar Raheena yayinda ita kuwa Amna ke tinanin, "wacece wannan kuma? Ba'a nunamin ita ba gashi kuma ta kira sunan Safna?" Kallon-kallo suke a tsakanin su, Amna na yiwa Raheena kallon rashin sani, ita kuma Raheena na wa Safna kallon mamaki kamar bata gane ta ba.

"Safna nice fa Raheena wai ko baki gane niba ne?" Cewar Raheena, "wataƙil fa wannan ƙawar Safna ce, idan kuwa hakane dole ki mayar da ita ƙawarki Amna" Amna ta faɗi a zuciyar ta, ta ke ta hau ya ƙen dariya tana faɗin, "aahhh Raheena yakike ya kwana da yawa?" Raheena tace "lafiya lau amma me ke damunki ne? Yi fa kikayi kamar baki sanni ba, har mari n'a fa kikayi niyya" "haba haba ke kuwa ƙawata, kawai so nayi naga react ɗinki fa, kuma na gani" ta faɗi tana cigaba da murmushi.

Murmushi itama Raheena tayi tana faɗin, "yau kuma ke ce da zolaya haka?" Gefe Amna tayi da idon ta zuciyar ta kuma cewa, "oh ita Safna ba ta zolaya kenan?" a fili kuwa tace, "zolayar n'a da kyau ai, koba komai zamuyi nishaɗi" "hakane amma fa kin tsorata ni, yaushe ma kika dawo ne? Kin dawo ko ki neme ni, Baba Hambali bai sanar dake sintirin da na rinƙa yi a gidan nan ba? Amma shine kika manta dani bayan kin dawo ko? nayi fushi".

Jan hannun ta Amna tayi zuwa wani dogon kujerar da ke can gefe suka zauna ta ce, "haba ke kuwa kar kiyi fushi kina raina, kawai dai Allah bai nufa zuwana bane, amma ba gashi kinzo ba?" Sai da Raheena ta murmusa sannan ta ce, "wai kece kike zuba zance haka?" "Wayyo ni Amna wai ita Safna ko magana ba tayi ne?".

Raheena ce ta katse mata maganar zuciyar da take da cewa, "ya jikin Ammu?" Kallon Raheena tayi ta ce, "wace Ammu?" Cikin mamaki Raheena ta ce, "Wace Ammu kuma? Ammu mahaifiyar mu mana" a zuci ta kuma cewa, "ohoo ashe sunan da Safna ke kiran Madam shine Ammu" a fili ta saki dariya kamar ɗazu ta kuma cewa, "yau dai so nake nayita ganin react ɗinki, amma kinga yadda fiskar ki ta koma kuwa?" Dariya itama Raheena tayi ta ce, "besty na kin sani farin ciki wallahi, naji daɗi da naga kina magana haka, abinda tintini nake so, nayi farinciki da dawowarki, yau dai Momy zata gane kan 'yarta".

"Nima naji daɗin ganin ki ƙawata" "ƙawar ki kuma? Malama ki kirani da besty kamar da, nafi jin daɗin haka" faɗin Raheena, Amna ta ce, "indai wannan ne baki da matsala" Raheena tace, "to muje inga Ammu, tun kwanaki na zo amma Ruki ta hanani shiga, harda min maganganu marasa daɗi, ni kuwa naji haushin haka muka kaure da faɗa, saida na fasawa shegiya baki".

"Kin min daidai!" Cewar Amna harda murmushi jin Raheena ta fasawa Ruki baki, har tana jin in ama itace Raheenar ai da ta faffasa mata fiska ba baki kaɗai ba.

#Shin ko Amna zata ɗauki Ammu matsayin mahaifiyar ta?

Zata zama ƙawar Raheena à madadin Safna?

______________________________________________________________________________________________

Part 6️⃣3️⃣▶️6️⃣4️⃣

"Kin min daidai!" Cewar Amna har da murmushi jin Raheena ta fasawa Ruki baki, hartana jin ina ma itace Raheenar ai da ta faffasa mata fiska ba baki kaɗai ba.

Ruki. Tunda ta bar ɗakin Ammu ta nufi kitchen tana ƙofa, "zaki san ni kika ƙyale wato gani banza ko? Meyakamata in mata ne?" Ta faɗi tana cizan yatsa, sai kuma ta cire yatsar daga bakinta ta furta, "yauwaa!" Tana faɗi ta ɗibi ruwa cikin ƙaramin bucket ta sanya cikin freezer.

Zama tayi a wurin saida ta tabbatar da ruwan yayi sanyi sosai sannan ta ciro shi ta nufi ɗakin su, sai dai bata samu Amna a ciki ba hakan yasa ta fita waje nan ta hango ta ita da Raheena, "dai dai kenan! hatta ƙawar ta ta sai ta samu rabon ta yau, shegiya dama itama haushin ta nake ji, aida nasan zata zo da na sanya ruwan da yawa" ta faɗi tana doso inda suke.

Saida ta kusa zuwa dap su ƙafar daman ta ya zame, hannun ta yayi sama da bucket ɗin tayi ƙasa lapp, tun kan ta saki ihun azaban fa ɗin da tayi ruwan ya juye kanta shaa, wani irin sanga-memen nishi ta ja saboda tsaban sanyin da ruwan yake dashi, bata san lokacin da ta sake shaƙaƙƙiyar ƙa ra ba.

Jin hakan yasa su Amna waigawa dan ganin abinda ya faru, ganin ta sukayi ƙasa ga jikin ta a jiƙe shakof da ruwa sai sauke wani irin numfashi take tana ƙame jikin ta, sai da suka miƙe sannan suka fara dariya a tare, dariya suke sosai wanda ya ƙara harzuƙa Ruki, ta gina ramin mugunta amma ita ta afka, da ƙyar ta iya miƙewa tana ɗingishi ta bar wurin ko bucket ɗin bata ɗauka ba, ga faɗuwa da kuma ruwan sanyin da ya jiƙa ta, sannan ga dariyar da Amna da Raheena suke mata duk ya haɗe mata haushi ya cika ta.

Barin dariyar da take tayi tana kallon Amna ganin yadda rake dariya tsakanin ta da Allah, wanda ita a wurinta Safna bata taɓa makamancin hakan ba, kallon Amna take sosai.

Ba ƙaramin daɗin abunda ya faru da Ruki Amna tayi ba, jin Raheena ta taɓa tane yasa ta tsagaita dariyar tana kallon ta, "kee besty! Nifa wallahi na rasa gane miki yau ɗin nan" tsaida dariyar duka Amna tayi jin abinda Raheena tace, kar dai fa tana yin abubuwa da yawa wanda Safna ba tayi, "me yasa kika haka?" Cewar Amna tana kallon Raheena, Raheena ta ce, "dariyar da naga kinyi ya ban mamaki sosai ban taɓa gani kinyi hakan ba".

Kan Amna ta bata amsa wayar Raheena yayi ƙara, saida Amna ta ɗan zaro ido kaɗan ganin waya mai tsadar da Raheena ke riƙe da shi, ji tayi Raheena ta ce, "eh Momy Safna ta dawo ganinan tare da ita ma, dama ina son kiran ki ince miki sai anjima zan dawo kamar bayan azahar, yauwa Momy thank you, to shikenan zan faɗa mata" ta juyo ta kalli Amna dake kallonta ta ce, "Momy na miki barka da dawowa kuma tana gaishe ki".

Murmushi kawai tayi tana faɗi a ranta, "da dukkan alama wannan ƙawar Safna ce ƙud da ƙud, ƙila zata san abubuwa da dama dangane da Safna, kuma abinda nakeson sani kenan, to amma taya zata ban labarin bayan ita a tinanin ta Safnan ce ni?". "Besty muje wurin Ammu in gaishe ta" Cewar Raheena bayan ta katse wayar ta miƙe.

Bayan sun isa ɗakin Raheena ta nufi inda Ammu take kan gado, domin yadda Amna ta barta bata gusa a wurin ba, da sauri ta je kusa da Ammu ɗauke da murmushi a kan fiskar ta, durƙusawa ƙasa tayi tana yiwa Ammu gaisuwan girmamawa, amma taga yau sam Ammu ba tayi mata wani alama dake nuna ta amsa gaisuwan ba, kuma ga idon ta da ya sauya kala, "besty What's wrong with Ammu?" Ta faɗi tana juyawa kallon Amna.

Matsowa kusa Amna tayi tana kallon Ammu dan ga no sanadin tambayar da Raheena tayi, "ƙila tun maganar ɗazu ne hankalin ta bai gama kontawa ba" ta faɗi a zuciyar ta, a fili ta ce, "Lafiyan ta ƙalau fa, kawai dai jikin na ta ne sai a hankali" kauda kallon da takewa Amna tayi ta maida su kan Ammu ta furta, "Ammu Allah ya baki lafiya" da ameen Amna ta amsa tana ƙara faɗin, "Raheena ina son muyi wani game dake" ta faɗi domin so take tabi hanyar da zataji labarin Safna koda kaɗan ne kuwa.

Sai da Raheena ta miƙe daga tsugunnen da take tana murmushi ta ce, "faɗamin wani irin game ne?" Amna ta ce, "Let's go outside before" garden ɗin da Safna ke zama suka je wanda baida flowers dan a tinanin Amna nan zaifi yi musu daɗin labarin, samun wuri sukayi suka zauna. Kallon dogon ƙarfen dake wurin Raheena tayi tana cewa, "wannan shine ƙarfen da ya taɓa jan ki?".

"Kedai muje kai tsaye akan game ɗin da zamuyi" Amna ta faɗa dan kawar da zance kar Raheena ta ƙure ta tun yanzu, "to muje ina jinki" cewar Raheena, sai da ta gyara zama ka na ta fara magana, "yauwa wasan da zamuyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login