Showing 99001 words to 102000 words out of 129098 words
Chapter 34 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
rai? wai sai da Dady ya roƙe shi akan ya taimaka min! To akan me? Ni wallahi da ma ya barni nayi abu na a haka, wai Shuraim ne zai taimaka min akan aikin company, wani abun ɓacin ran ma wai alfarma Dady ya nema, wannan ai sai ya raina ni, dama gashi da wani girman kai!"
Ta faɗi cikin masifa, Ammu kam jin ta take kawai, ba tare da ta fahimceta ba, saboda da sauri take yin maganar, haka ɗazu ma ta zauna tana yi mata magana kuma ta fahimta, harda ɓacin rai yake sa ta sauri a magana wani lokaci".
Shuraim kuwa murmushi ya saki bayan tafiyar ta ya koma kan kujera.
DARE.
Dady ne zaune da Hajiya suna tattaunawa, "Hajiya kamar yadda nace miki, inason ki san yadda zakiyi ki shawo hankalin Auta na, ta faɗa soyayya da wannan yaron da kuma sa shima yaso ta" Cewar Dady cikin nunawa Hajiya manufar sa akan wannan haɗin da yake so, murmushi ta sakar masa ta ce, "indai wannan ne kar ka damu Alhaji, saboda ita da kanta ɗazu take sanar dani cewa ya burgeta, to kaga kuwa ai abun yazo da sauƙi, tun da ka sanar da ni tagomashin da zamu samu akan mahaifin yaron nan nake kwana da tunani, don haka kabar min komai a hannu na" "toh shikenan, inajiran jin sakamako mai kyau".
WASHE GARI.
Zaune suke suna breakfast, Amna ko kamar ɗure ake mata haka take cin abincin, saboda yadda Shuraim ke binta da murmushin gefen baki, hakan kuwa ba ƙaramin ɓata mata rai yake ba, hakan ne ma yasa take wani cin abin ci kamar dole, ai kuwa yayi sa'ar Dady na kusa da ya sani. Shi kuwa cin abincin sa yake kawai cikin natsuwa, Ruki kuma sai kallon sa take, su Saleem da Marwan kam suma haushin suke ji, ba don komai ba sai don maganar Dady akan su ba Shuraim respect.
Ko dake bai kamata Marwan yayi fushi ba ma, tun da auren sa ya kusa, zai rabu dasu kaɗan, ko da bamu san à ina zai zauna ba.
Dady ya ce, "my son idan ka kammala kuma ka shirya sai in haɗa ka da drivern da zai rinƙa kai ka, "ina ga ba wata matsala bace idan na tafi da Safnah" ya faɗi kansa ba gun Amna ba, don da ya ga wani irin kallon takaici da tayi masa, amma babu wanda ya lura da hakan, shi kuwa Dady farin ciki ne yayi masa yawa, sannan ya ce, "to shikenan yadda kake so". Miƙewa Amna tayi alamar ta ƙoshi, ta bar wurin.
Shirin zuwa aiki taje tayi, da sauri ta fito saboda so take kar ta haɗu da kowa, bare Dady ya kuma cewa tare zasu je company da wannan Shuraim ɗin. Sai dai tayi rashin sa'a domin kuwa daidai fitowar Dady da Shuraim ɗin ta fito falon, fiskewa tayi wai don tayi kamar bata gan su, "'yata ya kike sauri haka?" Cewar Dady, tsayawa tayi ba tare da ta juya inda suke ba. "Oh shit!!" Ta faɗi cikin ranta.
Ya kuke tunanin takun-saƙan da ya fara kasancewa tsakanin Amna da Shuraim?
Kuna ganin Amna zata amince da tafiya tare da Shuraim zuwa company ?
Ya zata kasance a company tsakanin Shuraim da Amna?
Muradin Alhaji na Shuraim ya faɗa soyayya da Ruki zai yu? Hakan zai faru?
'Yan uwan arziƙi, Aisha G Umar taku {Mrs Umar} 👸🏽za ta bayyanar muku da komai,
__________________________________________________
_________________________________________________________
Part 9️⃣3️⃣▶️9️⃣4️⃣
"Oh shit!!" Ta faɗi cikin ranta, ƙara magana Dady yayi, "eh 'yata?" Juyowa tayi ta sakar masa murmushin ya ƙe tana cewa, "ai Dady wai so nake na isa gurin motar da wuri" "ok ai ga Shuraim ɗin ma ya shirya, sai ku tafi kunji?" Cewar Dady ya kuma juya da duban sa ga Shuraim ya ce, "na gode sosai Shuraim ɗana, Allah ya taimake ka ya biya maka buƙatun ka" "ba bu buƙatar kayi min godiya, saboda nima gurin rage lokaci na samu, ni ba mutum mai son zama a wuri ɗaya bane". Ta fiya Dady yayi ya bar su a tsaye a wurin.
Wucewa tayi tana wani turo baki, shi kuwa bin bayan ta kawai yayi, sai dai yadda take tafiya da sauri yasa shi saurin shima, yana bin bayanta, driver ya buɗe mata ƙofar baya, amma ta nufi mazaunin gaba, da mamaki drivern ya bita da kallo, duk da ba mazaunin tuƙi ta nufa ba, Shuraim ya fiskanci ba ta son su jera ne yasa take son zama a gaba, hakan yasa kan ta ƙarisa ya ce da ita, "Your are more suited to being at the back like a Queen".
Juyo tayi ta ɗan harare shi ta ce, "sai kuma aka yi rashin sa'a ni ba sarauniyar bace ba, ni C.E.O ce!" Murmushi mai ƙara ya saki ya kuma cewa, "C.E.O na ƙauye dai ko?" Ba ta amsa masa ba ta shige motar, juyawa yayi ya kalli driver ya fara yi masa magana cikin isa. "Zauna a baya ni zan ja motar, sai ka rinƙa yi min kwatancen hanyar" kafin driver yayi magana Shuraim ya buɗe mazaunin driver ya zauna, shi kuma drivern ya shige bayan motar, "me haka kuma?" Cewar Amna ganin Shuraim ya zauna mazaunin driver,
"a matsayi na na assistance ɗin C.E.O bai kamata na zauna a baya ba, ko ki nada matsala da hakan ne?" Yayi mata maganar tare da yiwa motar key. Fiskar ta na kan hanya tana faɗin, "Kar ka ɗauki kan ka awani babban matsayi, domin nice shugaba a nan" ya bata amsa da, "wannan kam kar ya saki damuwa Madam C.E.O, ni dai kawai mai taimakon ki ne" Juyowa tayi ta dube shi ta furta, "Allah ya kiyaye! Kuma kar kasa na sauka a motar nan, don zan iya takawa da ƙafa ta" ta faɗi haɗi da haɗe hannayen ta don haushi, "amma da an buga jarida akan C.E.On da tayi tafiya a ƙafa har company" driver ko jin su kawai ya keyi da mamakin abin da yasa suke wannan cacar bakin, duk da dariya m'a suka bashi.
Babu wanda ya ƙara magana har suka isa company, Shuraim yana yin parking Amna ta fito ko juyar da kan ta gurin batayi ba, mutane na ta bata girma cikin gaisuwa, amma ba wanda ta amsawa sai direct office ɗin ta da tayi, wasu na biye da ita amma ganin babu wanda ta kula yasa su barin ta ta sarara kafin suje inda take.
Ijje jakar ta tayi tana sauke numfashi, da tunanin me zataiwa wannan mutum ta rabu da shi ne? Domin kuwa ta san aiki da shi bazai taɓa yuwwa ba. Ɗaya daga cikin réceptionist ne ta shigo cikin office ɗin, da neman izini da shigowar da tayi duk lokaci ɗaya, kallonta Amna tayi ta fara faɗin, "It seems you should first send me a request, and only after i grant permission can you come in, right? Amma me yasa ba kiyi hakan ba?".
Cikin girmamawa da risinar da kai irin wanda ake yiwa shugaba, réceptionist ta ce, "I'm sorry ma'am, I already sent it to you, and i saw you didn't say anything, and the files i brought you are important, akan meeting ɗin da kike da shi gobe" shiru Amna tayi, don ta ji ƙarar shigowar massage à na'urar amma bata kai hankali ba, ce mata tayi ta ijje akan tebur kawai, sannan ta ɗora da cewa, "nan gaba bana buƙatar hakan ya sake faruwa, make sure I give you permission before you enter" amsa mata da zata kiyaye insha Allah tayi sannan ta wuce.
Bayan Réceptionist ta fita, Amna ta fara duba files ɗin, lokacin Shuraim ya shigo da sallama, kallon sa tayi cikin haushin shigowa office ɗin da yayi, files ɗin tasa hannu zata ɗauka kawai ɗaya ya kauce zai faɗi, Shuraim da yake kusa yayi saurin du ƙawa ya ɗauko shi kan ya kaiga taɓa ƙasa, "Relax, take things easy and do everything with calmness, ko da yake ba damuwa you have a helper" ya faɗi da murmushin da Amna take ɗaukar sa rainin wayo yake mata.
Ƙwace files ɗin tayi, ta yadda shi à ƙasa, sannan ta ɗauka ta juyo ta dube shi ta ce, "i don't really need any assistant!" Ta faɗi tare da zama, "tayu ke baki san waye ni ba, shiyasa kike sakaci dani, amma maganganunki sun fara sani nishaɗi mai makon haushi, can you tell me why?" Ɗago idon ta tayi tana kallonsa ta ce, "kai malam can you let me do what brought me here?" Sai da ya zauna a kan kujerar gefen ta ya ce, "absolutely, why not?" Bata kuma tanka masa ba sai duba files ɗin da take ckkin rashin sakewar kasancewar sa a wurin.
Shi kuwa Shuraim shima ɗaukar wasu yayi yana dubawa, "Oh you have a meeting tomorrow!" Faɗin Shuraim ita ko binciken ta kawai take. Haka suka ɗauki awa ɗaya, suna nazarin files ɗin, kirar da ya shigo wayar sa ne yasa shi tashi daga inda take yana faɗin, "Madam C.E.O let me pick up the phone" yayi maganar yana wucewa,
Dogon numfashi Amna ta sauke bayan ta bisa da ido har fitar sa, "Oh Allah wannan zai barni na sakata na wala kuwa?" Ta faɗi a fili haɗi da ƙara maida hankalin ta akan files ɗin da take dubawa. Massage ne ya shigo na'urar da ke gefen ta, taɓawa tayi taji tambaya, "Madam would you like some cofee,tea, or maybe something else to lift your mood while you work?" Murmushi tayi don taji daɗin haka, batayi tunani ba amma yakamata ta samu wani abun taɓawa yayin wannan duba files ɗin,
saboda suna da yawa, ga na jiya bata gama dubawa ba, ga kuma na yau, sannan harda wani taro wai gobe, ba ma wannan ne damuwarta ba, matsalarta shine akan abin da za'a tattauna, ita kuma har yanzu bata ƙarasa kamo bakin zaren ba, bere ta san abu nagaba da zata yi, "sure i need some coffee" ta basu amsa, suka bata amsa da babu jimawa za'a kawo mata.
Bai ɗau minti biyu ba aka shigo mata da coffee ɗin, nan da nan ta take sa, ai kuwa taji daɗin sa, nan ta basu order akan tana buƙatar wani.
Bayan kusan rabin awa da yayi a waje, ya dawo cikin office ɗin, zaro ido yayi ganin kofunan coffee guda bakwai jere, zuwa yayi ya zauna yana bin su da kallo da alama ma ta gama da su, cikin zolaya da dariyar da ta bashi ya ce, "Da alama dai wannan C.E.O ce ta daban, kai kai amma ta iya shan coffee, but ya kamata tasan C.E.O bawai ga suna kaɗai ya ta'allaƙa ba".
Kallon sa tayi da kuma bin kofunan da ido, ba makawa ita ta handame wa'yannan kofi bakwan reeras, dawo da idon ta gareshi tayi tana cewa, "da alama wannan ɗan ƙasar London ɗin ya iya hausa fiye da tinani, sannan kuma ya cika sa idon tsiya" dariya kaɗan yayi ya ce, "hakane zai iya sayar da C.E.O a maganar hausa" hmmm kawai tayi.
Lokacin tashi.
"Gwara ma ka cewa Dady ya neman maka driver, don bazan lamunci zuwa tare da kai ba komawa ma haka" cewar Amna bayan sun tsaya gun mota, amsa mata yayi da, "amma ban saba ganin mutum na gudun mai taimakon sa ba sai a wurin wannan shugabar", "oho dai ni dai na faɗa maka, wannan shine na farko na ƙarshe, akan zuwa da nayi tare da kai, da ma ka fasa wannan tayin da ka amsa" Shuraimya ce, "taya zan katse wannan nishaɗin da nake samu? Ke dai Madam shiga muje".
"Bazan shiga ba, kai ka fara shiga" ta faɗi don idan ya zauna a baya ita kuma sai ta zauna a gaba, driver da ya tada motar tun ɗazu yake jiran su, zuwa gaban motar Shuraim yayi ya shiga, ganin hakan yasa ta sake murmushi ta shige bayan motar, sai dai tun kan ta zauna taji shigowarsa bayan, yana cewa driver ya tada motar, juyowa tayi tana kallon sa cike da takaici ta ce, "bazaka kiyaye ni ba ko? Me na sai ka zauna a kusa dani?" "Godewa Allah za kiyi da har mutum kamana, yana taimakon ki".
"Wannan bai dameni ba ko kai wani irin mutum ne, nasan da kuɗi kake magana ko? Kuma karka sake cewa kana taimako na, nace maka bana buƙata! Ko baka ji bane?" Murmushin cikin rai yayi sannan ya fara dannan wayar sa, Amna kuma ta mayar da kan ta gefen glass, haka har suka isa gida.
Nan ma bata jira driver ba ta fito harda manta fation bag ɗinta. Kallon jakar yayi ya saki murmushin da ke dawuyan fassara, ya fito bayan drivern ya buɗe masa shi.
Da isan Amna ɗaki ta zube a kan gado, duk da aikin ba wai na yawo ko aikin ƙarfi bane amma ya bata wahala, domin ta basira da kuma hikima da fahimta take bin ko wani shafi, duk da Shuraim ɗin ya taimaka mata, ba tare da ta nuna taimakon na ta yayi ba, amma fa ya taimaka mata matuƙa, idan ya fara yi mata bayani akan abu nuna masa take ba ta buƙata, amma a ƙasan zuciyarta ta so hakan, shi kuwa koda bata nuna masa tana so ba, ya kanyi ta bayani akan hakan, hakan kuwa yasa ta fahimci abubuwa da dama.
Ta shi tayi sanadiyyar tarin da taji Ammu na yi, duk da muryar baya fitowa, da hanzari ta tashi cikin ruɗewa ta ce, "Ummee..Ummee sannu" ta faɗi tana miƙawa Ammu ruwa, sauke ajiyar zuciya tayi ganin Ammu ta daina tarin, hakan yayi mata kamar Ummeen ta ce ke wannan tari, saboda Ummee na da cutar asma, idan ya tashi kuwa yakan bata wahala, idan ta fara tari to fa a ruɗe suke kasancewa, shiyasa taji hakan yayi mata kama da Ummee ce ke tarin.
Kallon Ammu take cikin kulawa, yayin da zuciyar Ammu kuma ke tuna so mata da 'yarta Safna, da kuma tsananin kewarta da take kasancewa a ko wace rana, ko wani lokaci, babban abin da yake sa ta damuwa shine, shin a wace duniyar Safna take yanzu? Tana lafiya ne ko wani abun ya same ta? Tana cikin farinciki ko ƙunci? Waye zai bata duk wa'yannan amsoshin?
Hawaye ne ya gangaro daga fararen idanun Ammu, kan sukai ga sauka jikin kumatun ta Amna tayi saurin tare su da gelen ta, "Ammu don Allah kar kiyi kuka, kin san yadda na ɗauke ki kuwa? Na ɗauke ki tamkar mahaifiyar da ta tsugunna ta haifeni, wallahi Ammu a yanzu bayan abun da yake damuna na ahali na, babu abin da yake gaba na kamar ke, da ace komai zai zo yadda nakeso kuma inada dama da na kawo miki 'yarki Safna gaban ki da kaina, don in nuna miki yadda na ɗauke ki a raina, don haka ki daina kuka, kamar yadda muke addu'a a kowace rana, tabbas zamu ci nasara insha Allah, domin wanda muke roƙa yana jin mu, kuma yana ganin mu, ubangijin mu, zai kawo mana mafita kinji?"
Ta faɗi tana rungume Ammu, shafo idon ta tayi ta duba hannun ta taga ruwa, alamar hawaye ya fita daga idon ta, cikin mamaki ta share na ta hawayen, ta bar jikin Ammu tana cigaba da lallaɓa ta, ta kwantar da ita kan gado, sannan ta shiga toilet, cire ayes colour ɗin tayi, tana kallon fiskarta a mirrorn toilet ɗin, ta fito sak Amnar ta, domin harda tabon ta cire, murmushin tuno wani abu tayi sannan ta gama abin da take ta fito.
Canza kaya tayi, ta zauna a gefen gado tana duba jakan da ta zo dashi wanda gaba ɗaya kayan ciki, black eyes colour's ne da kuma baƙin tabon gefen baki dayawa a ciki, wannan ita karan kanta batasan iya kan su ba, daukar wanda zatayi amfani da shi tayi tana shirin komawa toilet don ta saita su a mazaunin su, kawai taji shigowar mutum ɗakin, take zuciyarta ya bada wani ƙararraki a jere dam dim dam dimmm.
Saurin mayar da kayan tayi cikin jakar ta ja zip, sannan ta miƙe tana tunanin rufe idon zatayi ko me? To kuma tabon ma babu, rasa abin da zatayi tayi, ta ke jikin ta ya fara amsa asiri na ya tonu.
To fah! Amna dai ta shiga hannu, to ko ya zata ƙare mata? Waye ya shigo?
Ku biyo ni don jin yadda zata kaya.
___________________________________________________________________________________________________________
Part 9️⃣5️⃣▶️9️⃣6️⃣
SHURAIM.
Bayan ya shigo falo ɗazu, zama yayi akan kujerar haɗi da ijje jakan Amna da ya shigo da shi a gefe, lokacin Ruki itama ta shigo falon cikin shigar matsatsun kaya, dama daga gurin ƙawayen ta take, domin sun kira ta tazo suyi wani ƙaramin shirin party gobe da dare, duk da cewa jikin ta har yanzu bai zama daidai ba, amma taje saboda baza taso wannan chilling ya wuceta ba, wanda kuma za'a tara yaran masu kuɗi kamar yadda suka saba.
Da murmushi ta iso gaban sa ta zauna a gefen sa, tana murmushi mai saututtuka ta ce, "Shuraim barka da hutawa, ashe ka dawo" ɗaga idon sa yayi ya kalle ta ya kuma maida kansa kan abin da yake, ya bata amsa da yes, duk da kallon da ya jefe mata kallo ne na rashin son magana da ita amma bata fahimta ba ta kuma cewa, "bari in kawo maka jus mai sanyi, don ya sanyaya maka zuciya".
Kan ta tashi da niyyar kawo masa, shi ya miƙe ya furta "no it's okay!" Sai kuma ya