Showing 21001 words to 24000 words out of 129098 words
Chapter 8 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
mahaifin Jalo da shi yaron sa yafi raunana acikin su shima yace "duk da cewa muma an raunana mana namu 'ya'yan amma mungane su ke da laifi, amma dan Allah intambaye ku mana? dan Allah 'yar nan ta ku Mutum ce kuwa?".
Juyowa Amna tayi inda yake, tace "bawan Allah me kake nufi?" "Meyasa za kayi mana irin tambayar nan? Yanzu a gaban ka mutum ce ke zaune ko aljan?" Mamma ta katse Amna da faɗan haka, dan tasan Aminatun na ta, Mahaifin Jalo ya ƙara cewa, "gani nayi yadda tayi ma yaran mu luguden nama, kamar ba mutum yayi musu ba, wallahi kai ka ce wata shirgegiyar mota ce tabi ta kansu, numfashi ma da ƙyar ke fita, ai dole nayi tambayar".
"Koma dai Me Ɗan-iskan ɗan ka ya jawa na mu 'ya'yan, duk abinda ɗana yake shi ke sashi" cewar Uban Usy, cikin ɓacin rai Mahaifin Jalo yace "haba Malam taya zaka ce Ɗana ne sila kuma harda ɓatacciyar kalma a kan sa?" ai nan mahaifiyar Salman ta amshe "yaro na duk yafi naku yaran jin jiki, kuma duk 'ya'yan ku suka jamai, kunganni nan kullum sai nayi wa Salmanu faɗa akan ya daina biyewa sheɗanun 'ya'yan ku amma baya ji, gashi ambar ni da jinya".
Ai nan iyayen su Jalo suka hau cacan baki wannan yace wannan, wannan yace wancan, "kai ya'isa" kofur Ali ya daka musu tsawa, dakatawa sukayi kowa ransa ɓace, "Kaka shugaban mu ne yace mu kawo su, su baku haƙuri, saboda yaran su da kansu suka faɗi gaskiya da bakin su, duk da abinda 'yar ku tayi itama ba daidai bane ɗaukar Doka a hannu, itama muna gargaɗin ta da ta kiyaye ɗaukar Doka a hannu nan gaba, shine abunda ya kawo mu, dan haka zamu tafi, tunda komai ya kammala".
Godiya su Mamma sukayi musu, sannan suka ba iyayen yaran haƙuri, sukai sallama suka wuce, Kofur Habu ne ya juyo ya kalli Amna yace, "gaskiya Amna soja ne ya dace dake, wannan ƙarfi haka" ya faɗi yana murmushi, binsa da kallo kawai tayi ta wuce ɗaki ta barsu Mamma.
Mubarak ne yace "Ummee kin ga abinda nace miki ɗazu ko? Ai nasan da ƙyar su Jalo su yarda aiwa Amna wani abu, saboda sunji jiki wallahi" dariya Mamma tayi tace "kai Aminatu na da ƙarfi take sai kace wanda ta fito daga tsatson ILYA ɗan mai ƙarfi?" Cewar Mamma, "hmm" kawai Ummee tayi ta fara naɗe, shimfiɗun. Dariya Mubarak yayi Yace "Mamma tsoron Police ɗin ya tafi ne? ɗazu fa maganar ki Har rawa take yi" "kadai ji da jikin ka rago kawai" Mamma ta bashi amsa, suka sa dariya.
#Hmm ashe dai Yazeed na kaiwa Ammu ziyara a ɓoye, ko me yasa baya son Safna ta gan shi? Kuma Me yasa Mamma ƙin sanar da Safna hakan duk da tana iya yi mata magana ta ido?.
Ga dai yadda ta kasance ba'a kai ƙarar Amna police ba, sai ma haƙuri da aka basu, kuma kuna goyon bayan Amna?.
______________________________________________________________________________________________
Part 2️⃣3️⃣▶️2️⃣4️⃣
RAHEENA.
Fitowa daga ɗaki tayi, sanye ta ke da doguwar Riga Abaya maroon colour, ta ra taye ƙaramar jakan ta white a ka faɗa, takalmi ma white, ga sarƙa mai tsada a wuyar ta da ɗan kunnen sa, sai agogo a hannun ta, kolliya kaɗan tayi, amma tayi kyau sosai, itama Raheena gurin kyau ba'a bar ta a baya ba, shirin zuwa auren wata 'yar ajin su tayi, zaune a Babba kuma kyakkyawan falon su Mahaifiyar ta take kan Kujera, daga ido tayi ta kalli 'yar ta ta ce, "kinyi shirin fitar kenan?".
"Eh Momy" "ok kinkira Ƙawar ta ki Safna ne?" "a ah, Momy ita fa har yanzu ba riƙe waya take ba, daman nima Napep zan hau sai in biya ta" "yau ma a Napen zaki biya ta kamar kullum? To wai meyasa baza ki bar hawa napep ɗin nan bane? Kamar babu Mota a gidan, ina ce kwanaki sai da Dadyn ki yace driver ya din ga kai ki, inya so sai ki na biya Safnan.
"Haka ne Momy amma in baki manta ba, nace miki Safna ce taƙi hakan, ta ce wai tafi jin daɗin zuwa makaranta a napep, har téléphone nace zan bata kwanaki da nake da guda biyu, amma taƙi, kin san ta da kafiya Momy, Safna ƙawar kirki ce Momy, baza ka san haka ba sai ka zauna tare da ita, ina ƙaunar ta, shiya sa bana son abinda zai shiga tsakani na da ita, shiyasa nake son yin rayuwa kamar yadda take nata, duk da kasan cewar ta 'yar Alhaji Mai Daraja amma ta zama ƙasƙas-tacciya a gidan, Momy ke kika bani labarin mahaifin ta, da gaskiyar shi da Amanar shi, da kuma kyauta-tawa jama'a".
Ƙaramar ajiyar zuciya Momy ta sauke sannan tace "Haka ne 'Yata Allah yaba mahaifiyar ta lafiya, don babu damar zuwa ai dana rinƙa zuwa duba ta" murmushi Raheena tayi "Hmm Momy nima kai na bancika son zuwa gidan ba, saboda yaran wannan Hajiyar basu da mutunci, da ita kanta Hajiyar, kwanaki da naje kusan faɗa na kusa yi da wannan Rukin, har naso jawa Safna, shiyasa ko naje yanzu a waje zan tsaya" .
"Hmm Allah dai ya kyuta amma dai ki kiyaye, karki ja mata wani abun" "insha Allah Momy, to bari in wuce sabida in dawo da wuri kamar yadda kika ce" da addu'a Momy ta bita sannan ta fice, taran napep tayi zuwa first GRA unguwan su Safna, sauka tayi dan Napep baya shiga sai mota.
Ta ku tayi har zuwa ƙofar gidan duk da ba yau bane farkon zuwan ta gidan, amma ta tsaya ƙa rewa gaban gidan kallo, duk da cewa itama iyayen ta masu kuɗi ne, amma in aka danganta da dukiyar iyayen Safna to su ba komai bane fa ce talakawa, saboda daga ganin ƙofar gidan ma ba magana.
Barin kallon tayi ta nufi ƙofar ta fara ƙon-ƙosawa, ba'a daɗe ba Baba Hambali ya buɗe, gaishe sa tayi ya amsa, "tana ciki ki shiga mana" ya faɗa mata bayan ta tambaye shi Safna, badon ta so ba ta shiga.
A hanyar shiga falon ta haɗu da Saleem, ko kallon inda yake batayi ba bare tayi masa magana, shi kuwa bayan ta yabi da ido, yana faɗin "beautiful" a hankali.
Addu'a take a ranta, Allah yasa karta ƙara haɗuwa da wani, Allah ya karɓi addu'an ta, dan kuwa har ta nufi hanyar ɗakin da tasan suke ba tayi karo da kowa ba, sallama tayi kamar me jira Safna ta buɗe, rungumar juna sukayi cike da farin ciki kamar ba Friday suka rabu ba.
Janyo ta ciki Safna tayi, zuwa kusa da Ammu dake zaune a kan Kujera, tsugunnawa tayi tana gaishe da Ammu cike da girma-mawa, murmushi Ammu tayi alamar ta'amsa, kawo mata ruwa tayi, sannan tace, "ƙawa ta nifa na manta da zuwa gurin bikin nan, dan yanzu ma da ƙyar inje Ammu ba lafiya" Safna ta faɗi hakan, cikin sassanyar muryar ta.
Cikin nuna damuwa Raheena tace, "Ayyah sorry, ashe Ammu ba lafiya tun yaushe?" "jiya ne, kawai kije ke kinji" "duba Ammu na ɗaga hannu" Cewar Raheena da idon ta ke kan Ammun" saurin zuwa inda take Safna tayi, da'alama Ammu ba Safna umarnin tafiya take, Ganin yadda Safna ke Gir-giza kai, alamar toh.
Da mamaki kawai Raheena ke kallon su ganin wai magana suke a haka, dawowa inda Raheena take tayi tana faɗin "Ammu ta ce inje ba komai" murmusawa Raheena tayi tace, "thank you Ammu" ita ma murmushin tayi mata.
Ganin lokacin sallar La'asar ya yi, yasa su yin sallah harda Ammu, sannan Babu ɓata lokaci Safna tayi wanka, ta sanya doguwar Riga Atamfa, Safna kam dai tana son Atamfa, sa ɗan kunne tayi, ba tare da sa sarƙa ba dan bata cika son sa ba, haɗe Gashin ta da ba a kitse ba tayi, saboda baya ɗaukar kitso sabida tsan-tsin sa, ita ma white shoes tasa da mayafi ma white, sai kuma fation Bag ɗin ta Black, , cream kawai ta shafa sai ta sa man Baki, ---woohoho, Hajiya ta fa ta haɗu ba magana, haka ma wai batayi makeup ba---.
Sai da ta mayar da Ammu gado sannan kafin suka yi mata Sallama suka fita, Ruki suka tadda hakimce a falo, amma basu tanka mata ba suka wuce, ita kuwa da kallon banza ta bi su.
BABA.
Addu'a kawai yayi wa 'ya'yan na sa lokacin da yaji abinda ya faru, sai da ya ƙara yiwa Amna nasiha sannan ya rabu da ita, bayan yayi Sallan La'asar ya shirya cikin blue jince da kuma T-shirt fari, sai blue jacket a kai, yauma Face mask yasa, sai dai duk ƙwarin guiwar da yake dasu yau ya rasa, sabida gaba ɗaya rashin karsashi yake ji a jikin sa, amma duk da haka bai sa re ba.
Inda ta ce zasu haɗu ne yaje dan tace yau ba'a Ƙoƙolwar ka Zan-Zan zasu haɗu ba, saboda wannan karon haɗuwar su ta musamman ne, duk da gefen zuciyar sa ta gargaɗe sa da zuwa, amma sai ɗayar ta basa ƙwarin guiwa, Tsayawa yayi a gefen hanya yana jiran ta kamar yadda tace.
SAFNA.
Suna cikin tafiya Napep ya tsaya, babu yadda suka iya sai suka sauka dan samun wata, sai dai duk wanda suka tsayar in suka sanar masa da unguwar da zasu sai ya wuce, wani mutum ne yace musu, "ai baza ku samu Napep ɗin unguwan anan ba sai kun je can gefen" godiya suka masa Sannan suka fara tafiya inda aka ce musu.
BABA.
Juyawan da zaiyi idon sa ya gane masa wani abu da ya gigita tinanin sa, ta ke zuciyar sa ta fara bugu da sauri da sauri, "Amna! Wannan suffar..." ya faɗi bayan ya hango mai kama da Amnar sa sak kamar an tsaga kara, ba shiri ya nufi inda suke dan tabbatar da abinda idon sa ya gane masa, tsayawa yayi a gaban su yana ƙarewa yarinyar kallo.
tabbas kama da Amnar sa take idon sa ba ƙarya yayi masa ba, sai dai ita ƙwayar idon ta baki ne, sai kuma baƙin tabo da ke gefen bakin ta, shine kawai ya bamban ta ta Da Amna, idan badon wannan ba, da babu abin da zai sa bazai ce Amna bace.
"Sannu lafiya?" Cewar Raheena ganin mutumin baida shirin matsawa, sai da ta faɗa sau biyu sannan hankalin sa ya dawo gare sa, "am ba komi, amma yarinya me sunan ki?" Yayi tambayar idon sa kan Safna, shiru tayi masa yayin da zuciyar ta ke mamakin tambayar.
Shi ma saida ya ƙara yi mata tambayar sannan ta ce, "yallaɓai lafiya kuwa? Meyasa kake son sanin sunana?" Ita ma tayi masa tambayar, Nan ma zaro ido yayi jin irin muryar Amna, sai dai wannan muryar ta da Sanyi "I'm sorry 'yata, so nake naji sunan ki saboda..." kirar Zilla da ta shigo wayar sa ya tsaida mai maganar.
Napep ne yazo wucewa gefen su, Raheena ta tare shi, ta kuma yi sa'a zai kai su, "Safna muje" Cewar Raheena, yana ƙoƙarin ƙara yi musu magana suka shige ciki, mai napep ya ja, jin sunan da ɗayar ta kira ta da yasa shi nanata sunan a bakin sa "Safna, Safna, Safna," ikon Allah, Allah mai halitta.
Mamaki ne yaƙi barin Safna da tinanin, "waye wannan mutumin me yasa ya tambaye ni suna na?".
Daidai ta kan sa daga ruɗanin da ya shiga yayi, sannan ya ɗaga kiran wayar lokacin da ya shigo a karo na Uku, "kana ta ina ne?" Cewar Zilla daga wayar, waiga wa yayi ya hango ta, yace "gani nan zuwa".
Ƙarasawa yayi inda take, yau kuma Riga iya Cibi da wando iya Cinya tasa, saboda ko kai guiwa ma bai yi ba kalar Tumatur sai gashin atach Baƙi, sai takalmi mai tudu, yau dai shigar cikakkun 'Ƴan-duniyar tayi, dan shigar jiya ta fi arziƙi, kauda kallon sa yayi daga kan ta, cike da ƙyama.
Zuwa tayi dan rungumar shi, tana cewa "beautiful i miss you, lallai ka cancanci award sabida yadda ka jawo hankali na cikin ƙanƙanin lokaci" saurin ja da baya yayi yana murmushi, da kallo kawai ta bishi ita ma, tayi murmushi amma na gefen baki.
Lokacin wayar sa ta fara ruri, ciro ta a aljihu yayi, ganin numbern abokin sa Hamza yasa shi ce mata, "excuse me please bari in ɗan daga waya" ok kawai ta furta masa, yin gefe yayi tare da ɗaga waya, sallama yayi masa suka gaisa, sannan Hamza ya fara yi masa bayani.
"Aboki na kamar yadda nace zan taimaka maka gurin binciken wannan 'yar Barikin, to à yanzu haka nasamo maka wani abu, à gaskiya saurin à mincewa da tayi da kai a koi dalilin ta nayin hakan, dan a tarihin Zilla bata taɓa amincewa da mutum a banza, ta wuce duk yadda kake tinani, wannan Gidan 'yan shaye-shayen ba wurin zaman ta bane".
"kana son kace min kenan wannan labarin da naji gurin wa'ennan gayun shiri ne?" Cewar Baba cike da mamaki, amsa ya bashi da "tabbas kuwa..." sai shiru ya biyo baya, hello, Baba yayi ta faɗi amma shiru, yana dubawa yaga ashe ma katsewa yayi.
Tinanin meya kamata yayi ya fara yi a zuciyar sa, wani irin manufa Zilla take dashi a kan sa, katse tinanin yayi da komawa inda take, yasan dabarar da zai mata, ya rabu da ita, yasan me zai shirya nan gaba, ita kuwa da tun tafiyar sa take kallon sa har izuwa dawowar sa, tace "yadai zamu iya tafiya?" Ta faɗi masa ganin canjin yanayin sa.
"No sai wani lokacin a koi abun da yakamata inje yi yanzin" dariya ta ƙyal-ƙyale da shi, tsare ta da ido yayi da mamakin dariyar ta ta, ba tare da ankare wa ba ta fesa masa wani irin abu a fiska da yayi sanadiyyar ɗaukewar numfashin sa na wucen gadi,, riƙe sa tayi daidai zuwan wata baƙar mota, shigar dashi tayi itama ta shiga, suka ja motar.
Hakan bai bada wata alamar tuhuma ba, hakan yasa mutane basu wani ankara da abun da ya faru ba.
#Cab wata sabuwa kenan, dama haka Safna tayi kama da Amna?
Ashe zilla duk shiri take yiwa Baba? To ko dai sa ta akayi ne? Ina zata kaishin?.
______________________________________________________________________________________________
Part 2️⃣5️⃣▶️2️⃣6️⃣
Suna tafiya Zilla n'a duba location, Tafiya mai nisa sukayi dan kuwa har dare yayi musu a hanya, sabida har cikin gari suka bari, tsayawa sukayi à gefen wani Hanyar Daji da yake shiruu, Zilla tana faɗin "yauwa nan ne" babu jimawa Mota white color ta iso wurin, kamar dama sun san da zuwan su Zilla, fitowa sukayi a Motar su Huɗu kayan jikin su ma Farare kai ka ce matattu ne suka dawo, sai dai yadda dare ya fara yi, yasa su Zilla tsorata da shigan mutanen, fiskar su rufe da ƙelle baƙi, A tsorace Zilla suka fito a motar ta su.
ba tare da magana ya gifta a tsakin su ba, Suka miƙa musu Baba da yake kamar Gawa, saboda ƙarfin à bin da ta fesa mai yasa face mask ɗin da yasa bai masa amfani ba, bayan sun Riƙe shi, ɗaya daga cikin su yace, "ina wayar sa?" Baki na rawa Zilla tace, "na man ta.. a ya faɗi" ba tare da sun ƙara yi mata magana ba suka juya zuwa farin Motar su, shiga ciki suka yi suka kutsa zuwa cikin Dajin, yayin da suka bar su Zilla tsaye, jiki sai rawa yake.
Matuƙin da ya ja Zilla ne Nass cike da tsoro yace "ke Zilla yanzu wucewa zamuyi kokuwa tsayawa za muyi mujira kuɗin, to ko binsu za muyi ne?" fiddo Ido waje tayi tace "waa ? ni shegiya inji ɗan Daudu, ai inka ganni à lahira kaini akayi, kai daga ganin mutanen nan ai kasan ba masu imani bane, mu bisu su fille mana kai à ah, muje dai in yaso sai su turo mana kamar yadda sukayi alƙawari".
Shiga motar su kayi suka fara komawa baya inda suka fito, "my Love Nass nifa har yanzu jiki na bai fita daga tsoron da naji ba, sabida ban taɓa ganin mutane haka ba duk shaharan da nayi à a Bariki kuwa" "hmm ai faɗa ma ɓatawa, ke ni fa wannan tuƙin ma da ƙyar nake yinsa, kamar 'yan ƙungiyar asiri? Intambaye ki mana? Da ki ka sa ni à wannan aikin kam à ina kika haɗu da mutanen ne?" Nass yayi mata tambayar.
Saida ta ni sa sannan tace "nima fa bansan su ba" "me...? Baki san su ba?" "Eh ban san su ba, kasan ni da son kuɗi, kirana kawai akayi à waya kwana biyu da suka gabata, bayan na dawo daga yawon sheɗanci na, ranar n'a tadda baka dawo ba, na ji takaicin rashin dawowar da bakayi da wuri ba, bayan ka faɗamin yau tare zamu kwana, ina zaune kawai naji kira ya shigo waya ta, ina dubawa naga baƙuwar number, kasan mu mun saba da irin haka, kawai na ɗaga ba tare da tinanin komi ba, nan fa mutumin ya min alƙawarin 50 millions idan nayi aikin, ai daga jin kuɗi na'amin ce tun kafin nasan aikin, turomin da hoton sa da kuma location ɗin sa yayi, Yace min insan yadda za'ayi inja hankalin sa da maganar Ƙwaya, ai nan fa na fara tinanin yadda zan tsara, aikuwa dabara ta zomin, na nemi 3 guys na biya su su en kuɗeɗe, suka aiwatar min da komi yadda na tsara, nima nayi nawa shirin, zuwa gurin Ƙoƙolwar ka Zan-Zan, bayan nan suka