Showing 114001 words to 117000 words out of 129098 words
Chapter 39 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
lokacin tashi ne yake kiranta, lokacin ita kuma bata koma gidan ba.
Amsawa tayi à kunnenta da sallama kamar kullum, amsawa yayi ya ɗora da faɗin, "Mrs C.E.O ya exercise ɗin? Ki dai yi a hankali kar ki karya ƙashin ki" shiru tayi Tana sauraron muryar sai ya fito kamar muryar mai takura mata, sannan kuma ya akayi yasan tana gurin? Sai kuma ta ƙara jin maganar sa ya ce, "ki koma gida jikin mahaifiyar Safna ya tashi, kuma ki tabbata kin bata kulawa" sai dai yanzu da ya mata maganar sai taji baiyi kama da na Shuraim ɗin ba, wanda ɗazu tayi tunani.
Cikin tsananin damuwa tayi saurin cewa, "Ammu? Jikin ta kuma? Subhanallahi! Yanzunnan zan je" tana faɗi ta sauke wayar ta fara shiri ckkin gaggawa ta fito, driver ya ja motar zuwa gida, bayan azal-zalar da take yi masa akan yayi sauri.
Da sauri ta buɗe murfin motar ta fito, ɗakin Ammu gadan-gadan ta nufa, don da wani zai yi mata magana a wannan lokacin da baza ma ta bi ta kansa ba, domin yadda hankalinta yake a tashe ƙololuwa. Tana shigewa ɗakin Ammu da mamaki ta tarar da Shuraim na ƙoƙarin fitowa da Ammu daga cikin ɗakin, bata tsaya tunanin ya akayi ya shigo ɗakin Ammu ba, saboda yadda Ammun ke fitar da numfashi sama-sama. Bin bayan sa ta fara yi tana kiran sunan Ammu cikin tsananin ruɗu, zuciyarta da tunani
Hajiya dai ansha gwagwarmaya😂
Zata biya kuɗi ko zata ƙara rikicewa da mai mota?Tunda ba mai waya a hannun su.
Sannan ga jikin Ammu ya tashi, me zai faru da ita?
Mu kasance a next part in Allah ya kaimu.
___________________________________________________________________________________________________________
Part 1️⃣0️⃣5️⃣▶️1️⃣0️⃣6️⃣
A motar sa yasanya Ammu, ita ma ta shige da gaggawa, ta ɗaura kan Ammu a kan cinyarta tana ta ambatan sunanta, ba tare da hawaye ya fito daga idonta ba, sai dai sunfara yi kamar yadda suka saba ja.
Asibiti mafi kusa suka nufa, suna shiga likitoci suka karɓi Ammu aka shige da ita ɗakin bada kulawa, sai dai nurse ɗaya ya tsaya yana faɗa musu cewa doctor baya nan amma yana kan hanya nan bada jimawa ba zai iso, "don Allah ku fara duba min ita, ku bata kulawa, wai baku ga yadda numfashinta yakeyi bane? Don Allah kuje ku duba min Ammu na" cewar Amna idonta na shirin kawo ƙwalla yanzu.
Nurs ɗin ne ya bata amsa da cewa, "hakan muke ƙoƙarin yi yanzu, sai dai doctor Salis ne kaɗai wanda zai fi ba ta kulawa yanzu, mu dai 'yan ƙananan gwaje-gwaje zamuyi mata" "kamar ya? Wallahi idan wani abu ya samu Ammu akan rashin dubanta da ba kuyi da wuri ba ko? Duk sai nayi maganin ku, wannan hospital ɗin sai an rushe shi" "calm down Safnah" Shuraim ya faɗi ganin tana cikin damuwa sosai na halin da Ammu ke ciki.
Cikin damuwa da masifa Amna ta kuma cewa, "baka ji abun da suka ce ba? Wai fa sai wani yazo sannan ya kula da Ammu, kuma baya nan, basu san yaushe zai zo ba, kuma laifin ka ne! Me yasa ka kawo mu wannan asibitin? Mu ɗauki Ammu mu kai ta wani wurin daban" tayi maganar ba tare da ta san lokacin da hawaye ya fara zuba daga idonta ba, tausanta Shuraim ya farayi da faɗin, "kwantar da hankalinki Safnah, kiyiwa Ammu addu'a, yanzu idan muka ce zamu sake kaita wani hospital ɗin a halin yanzu, zai iya zama matsala a gareta, kinga tana cikin tsananin ciwo yanzu, ki zauna please". Ya faɗi mata cikin sigar rarrashi.
Kallon nurse ɗin dake tsaye tayi sannan ta.zauna tana kuma faɗin, "amma yanzu haka zamu zauna doctor bai zo ba?" Tana faɗi sai ga nufowar doctor wurin, "yauwa ga ma doctor Salis ɗin nan ya ƙaraso" cewar nurse ɗin, da sauri suka kuma miƙewa suna ƙarasawa inda doctor yake, babban mutum ne shi, Babu ɓata time likita ya shige room ɗin.
Amna kuwa ta kasa zama sai tunani take ya akayi hakan ya faru? Shuraim ma ya shiga cikin damuwa sosai, zuwa wurinsa Amna tayi tana faɗin, "Shuraim tell me, me ya same ta? Ya akayi hakan ya faru da ita?" "I don't really know what happened, amma komai zai zama dai-dai kar ki damu" rufe ido kawai tayi sannan ta kuma buɗewa, da ƙyar ya shawo kanta ta yarda ta zauna a kan kujerar wurin, sannan ya miƙa mata ruwa, amsa tayi tana binsa da kallo, yadda shima ya shiga damuwa saboda abun da ya faru.
Kira ne ya shigo cikin wayar Shuraim,.ya ɗaga tare da sanar da su asibitin da suke, kallon sa Amna tayi tana tambayar sa waye ya kira sa, ya bata amsa da cewa Dady ne.
Doctor Salis. Bayan ya shiga room ɗin don aiwatar da abun da yakamata kan majinyaciyar, sai dai ya bita da kallon mamaki sosai, tabbas bazai taɓa manta wannan fiskar ba, domin kuwa abubuwan da suka faru a wani lokaci. Barin wannan tunanin yayi ya fara aiwatar da abun da yakamata a gareta.
Bayan wasu mintuna ya fito, kan ya ƙaraso inda su Amna suke, su suka tadda shi, "ya take yanzu doctor? Don Allah kace min tana lafiya" Amna ta faɗi cikin tashin hankalin amsar da ka iya fitowa daga bakin sa, magana ya fara yi mata da cewa, "alhamdulillahi, ku godewa Allah domin a yanzu zamu iya cewa ta fara dawowa dai-dai" wani irin ajiyar zuciya mai ƙarfi Amna ta sauke, wanda yayi dai-dai da fitar hawaye cikin eyes ɗin ta, n'a farinciki sosai.
Shima Shuraim murmushin jin daɗi yayi, doctor ya kuma cewa, "amma akwai matsala" "matsala kuma?!" Amna da Shuraim suka haɗa baki gurin furtawa, cikin damuwa sosai, "eh amma ba sosai ba, gurɓataccen jini ya yi yawa a jikinta, yanzu haka shi muke cire mata, sai dai dole sai an kuma sanya mata sabo, don haka ana buƙatar jini nan da 'yan mintuna, don ana so daga an rage wancan gurɓataccen sai a saka mata" "a sa mata nawa!!" Shuraim da Amna suka sake faɗa a tare, kallon junansu suka hauyi ganin sun furta magana iri ɗaya a tare karo na biyu.
Doctor ma kallon su yake da mamaki sai kuma ya ce, "ke ce 'yarta ko? Ya sunan ki?" Yayi maganar yana kallon Amna, "da mamakin tabayar da doctor yayi mata ta dubi Shuraim, sai kuma ta dawo da duban ta kan doctorn ta furta, "Safna" domin yanzu ta fara sabawa da wannan sunan. Murmushi doctorn yayi da wani fasali daban, wanda basu iya fahimtar sa ba, "doctor muje a ɗibi nawa" Shuraim ya faɗi, kallonsa tayi ta ce, "a ah Shuraim babu buƙatar sai ka sa kanka a matsala haka, ka bari a ɗibi nawa".
Murmushin kiran sunan sa da tayi yayi sannan ya ce, "nan ɗin ma ba a buƙatar taimako na? Aikin alkhairin ake guje min?" Ya faɗi yana cewa doctor su je. Murmushin farinciki ta sakar akan kyakykyawar fiskarta, ganin ya matuƙar damuwa da Ammu, zama tayi tana ci gaba da murmushin da kuma bin bayansa da kallo har ya ɓacewa ganinta.
Angwada jinin Shuraim sai dai baiyi match da level ɗin da ake so na Ammu ba, cikin rashin jin daɗi ya fito doctor biye da shi, "shikenan doctor, amma ku gaggauta please, tun da ku da kanku kuka sa lokacin" cewar Shuraim, doctor Salis ya ce, "insha Allah" taran su Amna tayi tana tambayar komai yayi? Cikin damuwa Shuraim ya sanar da ita baiyi ba, ganin yadda ya shiga damuwa yasa ta je kusa da shi ta ce, "me ya sa ka shiga damuwa haka? Bai kamata ka damu ba" "me yasa zaki min wannan tambayar!? Kin san ya take a wuri n..."
Sai kuma ya dakata da maganar da yake ya koma ya zauna, da mamaki ta bisa da ido har ya zauna, tana tunanin maganar da ya fara faɗa bai ƙarisa ba, har zatayi masa magana sai kuma ta fasa sanadiyyar zuwan nurse wurin, kafin nurse tayi magana ta ce da ita, ita aje a gwada na ta jinin. Bin bayanta Shuraim yayi yana faɗin ta bari a nemi jinin kada ta illata kanta, sai dai bayan ya gama wannan furucin ta ce da shi.
"Ita ɗin mahaifiyata ce, haƙƙina ne in kula da ita, koda zuciyata zan bada" sai da taji wani irin yanayi ya gauraye ilahirin jikinta, sakamakon wannan furuci da tayi.
Mamakine ƙarara à fiskar Amna, da jin maganar doctorn bayan angama gwajin, na cewa wai jininta babu maraba da na Ammun, lallai wannan kama ita da safna ya fi ƙarfin yawa.
HAJIYA
Bayan Isha'i aka sauke su a ƙofar gidan Ladingo, bayan roƙon mai motar da suka yi akan ya kawo su, don Hajiya cewa tayi gwara a sauke su à gidan Ladingon, don idan aka kaita unguwar su ai sai ana nuna ta da yatsa, kimarta ya zube a banza. Gurin saukowa daga motar nan ma Hajiya an ci kwakwa, gaba ɗaya ta fi su fita hayyacinta, "ai ni dama tun da naji kince a kawo mu gidana nasan so kike ki min wayau, wato ni inbiya kuɗin motanmu, ya zama nayi biyu babu kenan?" Ladingo ta faɗi cikin haushi, bayan ta miƙawa mai motan kuɗi ya ja ya tafi, don ta san da ƙyar Hajiya ta biya ta kuɗin da ta ba mai motar.
Cike da haushi da kuma wahala itama Hajiya ta ce, "wallahi Ladi kina bani mamaki" "au har yanzun ba ki saita min suna kenan?" "Eh ba ni saitawa, aikin banza! Bayan duk abin da ya sameni yau laifin ki ne, wai kin samu sabon malami, ashe sabon matsoraci kika samar mini, wayasan ma ko ƙila haɗa baki kukayi, don ke ba son cigabana kike ba" Hajiya na faɗi ta dubi driver ta ce, "kai tarar mana adai-daita sahu, don ko shiga gidan na ki ma na fasa".
"Ko ma dai me kice amma wallahi sai kin bani dubu sha biyar ɗina kamar yadda kika ce" "ni in baki dubu sha biyar? Ashe dai bada ke aka hau motar ba" Hajiya ta faɗi tana juyawa tana tafiya da ɗingishi, Ladingo kuwa ta kuma cewa, "eh da ni aka je amma ina ce dalilinki ne?" "Dalilin banza, dalilin wahala" Hajiya ta faɗi tana shiga napep ɗin da driver ya tara musu, tana kallon sa ta ce, "kai kuma saboda ganin isa zaka zauna kusa da ni? Wato abun da ya faru ya cire maka girmana a idonka kenan?".
Da sauri driver ya sauka daga bayan napep ya koma kusa da matuƙin, bayan zaman da sukayi à cikin 'yar ƙur-ƙura amma yanzu wai ba ta son zama kusa da shi, gashi shi inda aka fasa masa kai ma ciwo yake masa.
YAZEED.
Shigowa bedroom ɗin sa yayi hannu ɗaya riƙe da smartphone ɗaya da teacup, zama a gefen bed ɗin yayi ya ijje tea ɗin akan ƙaramin center table ɗin da ke gefe. AC ne ke ta aikin hidima a ɗakin, sai kuma dadɗa-ɗan ƙamshi mai sanyi da yake tashi a ciki, numbern Hajiya yake kuma trying karo na uku, but still baya shiga, numbern Saleem ya nema shi kuma switch off, cikin damuwa ya nemo numbern Marwan, bayan 'yan mintuna Marwan ya amsa.
Tambayar sa Hajiya yayi, "dama nasan ba niyyar kirana kayi ba, kuma i told Hajiya, da ƙyar kazo wedding ɗin nan, dama ba ɗauka n'a kayi à matsayin yayanka ba, don haka zaka iya ƙin zuwa ma ai ba abu ne mai wuya a wurinka ba" Marwan ya faɗi hakan, Yazeed kuwa cewa yayi, "look Marwan, ni fa ba na kiraka don ka faɗamin son ranka ba ne, just tell me where is Hajiya?" "I don't no where she is". "Ok bye" kawai Yazeed ya faɗa sannan ya katse wayar.
Yana fita a wurin call hoton da yake kan home wallpapern sa ya bayyana, hoton Safna ce wani lokaci da ya ɗauketa ba tare da saninta ba, tana sanye da himar maroon colour, kasancewar ta fara yasa fiskarta ya fito sosai a ciki, sannan ga ta ƙunshe da wannan murmushin na ta mai ɗauke da kyakykyawar dimple.
Murmushi ya saki yana kai hannunsa kan fiskar wayar, yana shafo hoton kamar yadda yake ko wace rana tun bayan zuwansa Australia, wani irin kewan son ya ganta ne ya taso mai, hakan yasa shi lumshe ido yana kallon ta a cikin fiskar zuciyar sa, maganganunta a majiyar jin sa, "Allah ya baka sa'a akan abun da kaje nema, ka cigaba da roƙon Allah yaya Yazeed, insha Allah komai zai kasance maka da sauƙi da yardar Allah" maganar da ta ce da shi na ƙarshe kenan kafin yadaina samunta a waya, cikin sanyin muryarta me ratsa masa zuciya.
Buɗe idon sa yayi ya ɗaura akan hoton wayar yana cewa, "ina nan dawowa gareki Safnata, zan sanar dake cikakken abun da nake ji akan ki, wanda nake da tabbacin kema kina ji a kaina, zan kula da ke tamkar sarauniya, love you my Safna" ya faɗi tare da rungumar wayar a ƙirjinsa.
HOSPITAL.
Dady ne zaune shima à ɗayan kujerar fiskarsa ɗauke da damuwa, suna zaune suna jiran fitowar doctor ya faɗa musu sakamako.
Doctorn ne ya fito yana zuwa inda suke da murmushi, sai dai murmushin na sa yatsaya sakamakon fiskar Dady da ya gani, shima Dadyn miƙewa yayi yana ƙarewa doctor Salis kallo, Amna ce ta katse kallon junan da suke na mamaki da faɗin, "ya jikin Ammun yanzu doctor?" Barin kallon fiskar Dady yayi kamar mara gaskiya sannan ya ce, "eh alhamdulillahi, komai daidai yanzu" "alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah!" Su Amna suka furta shima a tare.
Doctor Salis kuwa juyawa yayi da sauri zuwa office ɗin sa jikina har yana ɗan ɓari,. Miƙewa Dady ma yayi yana faɗin "abun farin ciki tun da she's okay now, bari inje in kuma ganin doctorn ko a kwai wani bayani da zai yi min" Shuraim ya ce, "ok to muje tare Alhaji" "no karka damu, ka zauna da 'yata ni kuma inje inji komai" toh Shuraim ya faɗi tare da zama a gefen Amna, "Ammu ta warware alhamdulillah".
Shima murmushi yayi mata ya ce "mun gode Allah" "amma wani matsayi Ammu ke da shi a wurin ka? Me kake son faɗi ɗazu?" "Ba wani abu bane, ita ɗin mahaifiyarki ce shiyasa ta zama tana da matsayi a wurina" "wace alaƙa nake da shi a wurinka da har mahaifiyata ta zama haka a wurinka?" Sai da ya saki murmushi ya ce, "a yanzu ke shugabata ce ko kin manta? Ƙila kuma mu sauya wannan ɓangaren zuwa wani", "shirme, shirme ka ke faɗa" cewar Amna tana tashi daga kujerar don zuwa ɗakin da Ammu ta ke, shima ya tashi.
Doctor Salis. Bayan ya shiga office kasa zaune da tsaye yayi, sai tunani yake ya kamo wancan ya kamo wannan, domin ya shiga tashin hankali da tsoron abun ka iya faruwa, "wani irin babban rashin sa'a ne yake shirin zuwar min yau?" Yayi tambayar wa kansa, sai dai muryar Dady da yaji ne yasa shi dakatawa, "ka faɗawa kanka gaskiya!" Dady ya faɗi tare da ƙarasowa inda yake ya zauna akan kujerar gaban teburin doctor.
"Ko zaka iya zama?" Dady yayi maganar yana kallon doctor Salis, zuwa doctor yayi ya zauna yana kallon Dady cike da tsoro harda haɗiye nyawu, yayinda shima Dadyn kallon sa yake, "me ya dawo da kai!?" Dady yayi masa tambayar??
Hmm Yazeed ya kusa dawowa garin Kaduna, to ko ya zai kasance idan ya tadda sabuwar Safna? Shin Amna zata amince da shi a sufa Safna?
Me nene tsakanin Dady da doctor Salis? Gashi doctor har Ammu ya sani, sannan me manufzr tambayan Dady wa docta?
Mu haɗu à next part don jin yadda zata kasance.
___________________________________________________________________________________________________________
Part 1️⃣0️⃣7️⃣▶️1️⃣0️⃣8️⃣
"Me ya dawo da kai!?" Dady yayi masa tambayar, cikin muryar rashin gaskiya da tsoro doctor Salis ya fara magana, "Alhaji Jamilu, wallahi ban daɗe da dawowa ba, kuma zan iya kiran hakan da tsautsayi, wallahi babu abin ya dawo da ni fa ce wannan aikin na likita ba don komai ba" wani irin murmushi ne ya bayyana a fiskar Dady sannan ya miƙe tare da cewa, "bayan abun da ka aikata tsawon lokaci a baya, amma yanzu ka na da zarrar dawowa inda muke? Lallai kana da ƙarfin hali!".
"Wallahi yadda na faɗa maka ba zancen wasa a ciki, ba na dawo ne don in kuma aikata muku komai ba" cewar Doctor cikin tsananin tsoro yana miƙewa, juya masa baya Dady yayi ya ce, "na riga na yafe maka a baya, amma ina son ka sani! A yanzu ba zan iya yi maka hakan ba, abubuwa da dama sun faru tsawon shekaru, wanda ba sai na maimaita maka ba, ka riga da kasan komai! Amma yanzu zanyi maka abu guda" Ya faɗi yana juyowa gun doctor Salis, inda shi kuma doctor zuciyarsa ya kai ƙololuwar tashi akan abin da Dadyn ke shirin ƙarasa faɗi, hatta bugun zuciyarsa sai da ya tsananta.
Shi kuma Dady fiskarsa cikin tabbatar masa da maganar ya cigaba da cewa, "na baka awanni ashirin da huɗu! Kabar wannan garin gaba ɗaya, bari na har abada! Idan kuwa hakan bai faru ba, to zan kai ka gaban alƙali, daga nan sai a yanke maka hukunci dai dai da abin da ka aikata! Domin abun da kayi ba ƙaramin abu ba ne, kuma na tabbata da biyu ka dawo wannan garin" Dady ya faɗa masa kamar gargaɗi, sannan ya nufi ƙofar fita