Showing 123001 words to 126000 words out of 129098 words
Chapter 42 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
da ni, babu wanda ya taɓa kama hannuna da nufin kulawa cikin 'yan-uwana, haka suka barni kara zube kamar ba bil'adama ba, na taso da maraici sosai, ko almajirai sun fini darajar filin kwana da kuma ci ma mai kyau, babu inda nake kwana fa ce kan titi, wani lokaci kuma a bola".
Tsagaita maganar yayi fiskarsa na sauyawa zuciyarsa na tsananta bugu, yana mai jin kamar yanzu ne komai ya faru da shi, rayuwar da yayi koda ɗan akuya ne ba zai so yayi hakan ba. Amna kuwa labarinsa da ya fara bata ne ya ƙara sa jikin ta yin la'asar, duba da yadda yayi maganar kamar yana jin ciwo a ransa, tausayi ne ya fara shiga zuciyarta, sai dai tayi saurin tsaida zuciyarta da faɗin, "ba halinki bane, don haka ki dakata da jin tausayi da wuri haka, domin zuciyarki a dake ta ke Amnah!".
Shuraim kuwa ci gaba da magana yayi, "na kanyi kwanaki kamar sati ko fin haka ba tare da wani abu mai suna lafiyayyen abinci ya shiga cikina ba, sai dai tsinte-tsinte akan hanya, ko roƙo nayi ban cika samun mai bani ba, a wannan halin na ɗauki shekaru biyu a haka, na lalace kamar wanda ke ɗauke da ciwon ƙanjamau idan yasa damuwa a ransa"
Nanma dakatawa ya sake yi, a yanzu idonsa yayi mugun sauyawa, Amna ma ji tayi tamkar idonta na son tsiyayar da ƙwalla, amma ta kuma dakewa, ta rasa yaushe wannan lalura ya kamata, lalurar saurin hawaye da kuma shiga tausayi. "Ranar lahadi! Shine ranar da Alƙalamin ƙaddarana ya juya izuwa sake shaƙar iskar 'yanci, bayan wanda na samu da ran iyayena. Gurin ƙarfe biyu na ranar, Ina kwance gefen bola, jikina ya ɗau zafi tamkar wutar gas, saboda tsananin ciwon da ke zagayawa a duk wata kafa dake ɗauke da jini, jikina na ta aikin kyarma kamar an jona min lantarki, ina a halin mutuwa ko rayuwa, kuma ba komai bane ya ja min wannan azaba na ciwo fa ce dattin da nake turawa ciki na, ba mutane bare na samu mai halin ƙwarai ya taimaka min, bayan tsawon lokacin da na ɗauka a haka, har ya zamana kwata-kwata ba ma na cikin hayyaci na, nan naji tsayuwar wani mutum a kaina, wanda ƙafaffun idanuwana basu bani damar ganinsa da kyau ba, shin kin san waye wannan mutumin?"
Shuraim ya kai ƙarshen maganar tare da dawo da jajayen idanuwansa kan Amna, yayinda itama idonta yake a kwatan-kwacin halin yin hawaye ko rashinsa, "à ah" ta bashi amsa tare da kasa ila-hirin majiyarta kansa, juyawa yayi kamar mai sake tunano wani abun ya ce, "ina a wannan tsananin ciwo Abubakar Mai-daraja wanda nake kiran shi da Abbana ya bayyana! Ban san me ya kawo shi wannan wurin ba, sai dai na san harda sanadina Allah ya turo shi wannan fili, duk da cewa ba lallai bane mai kuɗi irinsa yazo wannan ƙazamammen wurin saboda ƙazanta, domin warin iskar da ke kaɗawa a wurin kaɗai ya kai yasawa mutum cuta, sai dai da yake shi yana da halin daraja sai gashi yazo don warware matsalar mutane, cikin damuwa da tashin hankali ya ɗauke ni a hannunsa, ba tare da jin ƙyama akan yadda nake ba, asibiti ya nufa da ni cikin gaggawa. N'a ɗau sati biyu à wannan asibitin sannan na samu hankalina ya dawo jiki na, amma ba ƙaramin aiki likitoci su kayi a kaina ba, Abba Mai-daraja da matarsa su ne wa'yan da suka kula da ni tamkar iyayena na haƙiƙa, domin duk wani motsin da zanyi a gaban idonsu nake yinsa, sunƙi bari kowa ya zauna da ni, wani lokaci sai dai in buɗe ido kawai naga ɗaya daga cikinsu a gefena, duk dukiyar da suke da shi, amma baisa sun rabu da ni ba".
Duk dauriyar da Shuraim yayi amma sai da hawaye suka fita daga idon sa, cikin tausayawa ta miƙa masa hankicif ɗinta, ya amsa tare da sharewa, sannan ya ɗago idonsa kanta amma ita batayi hawayen ba, sai dai alama da idon na ta sukayi, "thank you" ya furta mata yana nemo murmushi kan fiskarta, kauda kanta gefe tayi itama ta furta, "ina jinka!" Jinjina irin halinta yayi a zuciya sannan ya cigaba da magana, "cikin ikon Allah da kuma kulawan da suka bani na warware kamar ba ni ba, hasken launin fata ta da ya dusashe sai gashi ya fara dawo, Abba Mai-daraja ya so ya kaini gidansa in cigaba da zama bayan na warke, amma hakan baiyu ba, wanda sai daga baya na gane a she saboda gudun matsala ne yaƙi kaini gidan na sa, wani wuri ne ya samar min, inda ake bani kulawa ta musamman, tun daga wannan ranar na ke kiran shi da Abba, matarshi kuma Ammu, domin su ne suka maye min gurbin iyayena. Haka ya sa ni makaranta na fara karatu a ko wanni fanni, sai dai fa ko kusa ban taɓa zuwa inda suke ba, sai dai lokuta da dama su kanzo duba ni, shi da Ammu,. Bayan Ammu ta samu cikin Safnah, zan iya fuskantar farin cikin da Abba Mai-daraja ya shiga, saboda hatta mu amalarsa da mutane ya sauya, ya sake zama mai yawan fara'a sosai, lokacin ne ya bijiro min da wata magana, Ganin ina da ƙoƙari da maida hankali a karatu ne yasa ya biya min kuɗin karatu zuwa ƙasar London, tare da bani kuɗin da ya zama tamkar kamasho a gareni, shi da Ammu suna yawan kirana akai-akai, nima ina kiransu lokaci bayan lokaci. Wata ranar laraba ya kira ni cike da murna, yake sanar da ni cewa na samu ƙanwa, ba ƙaramin farin ciki nima na shiga ba a wannan lokacin, har nake ce masa idan na gama makaranta na dawo zan zauna tare dasu, saboda in kula da ƙanwata sosai, shima ya tabbatar min da hakan za ayi, washe garin kwana uku gaba na rasa wayata, sanadiyyar faɗuwar da wayata tayi, daga baya nayi ta gwada kiransa à wasu wayoyin amma baya ɗagawa, gashi numbern shi ne kaɗai na ɗauka a kaina, tun ina gwada layinsa n'a shiga har na fara samu a kashe, na shiga damuwa sosai, gashi shima banji ya neme ni ba, shikenan ban sake jin labarinsu ba, cikin tunaninsu shi da Ammu da kuma ƙanwata har na share shekaru har shida a haka, lokacin kuma na kai shekaru goma sha takwas".
Kallon Amna ya sake yi yadda ta natsu tana kallo da sauraronsa kamar jikinta baya motsi, sai da ya ja numfashi mai ɗauke da damuwa da kuma ciwo sannan ya lumshe ido na 'yan sakwanni ka na ya buɗe yana ɗorawa da faɗin, "sai dai! Da dawowana, na tarar da mummunar labari, wanda ya girgizani girgizawa na haƙiƙa, wai Abba Mai-daraja yayi haɗari kuma ya rasu, sannan ga Ammu bata da lafiya, sannan ga shi ita da Safna suna shan wuya a cikin gidan da yake nasu, kuma mallakinsu, Amnah" ya kai ƙarshe da kiran sunan ta, gyara zama tayi tare da amsawa, tana ƙoƙarin share idonta, "shin kina ganin, bayan taimakon da bawan Allahn nan yayi min, in bar iyalinsa a haka? Shine fa wanda yayi sanadiyyar inganci ga rayuwata!"
Ya faɗi tare da yin shiru na wani lokaci, yayin da zuciyarsa ke yi masa wani irin suya, "naji duk abun da ka faɗa, kuma tabbas bai kamata ka rabu da iyalan wanda yayi maka alkhairi ba, amma idan hakane, meyasa baka fitar da su cikin baƙan rayuwar da suke a ciki ba tsawon shekaru?" tayi masa tambayar tana sake gyara zamanta, shima Shuraim sai da ya gyara zama sannan ya bata amsa, "wannan tambaya ce mai kyau Amnah! Ga amsarki, Ammu zaman aure ta keyi a gidan, kin ga kuwa ni amatsayin wa zanje da sunan taimakonsu? Ammun ce kawai ta sanni, ita kuma a yanzu babu yadda za ayi ta sanar da su waye ni, zuwa na zai iya haddasa wata matsalar agaresu, amma abu ɗaya yana sani farin ciki sosai, saboda shi baffanta Jamilun yana kula da su. Ban cika wata da dawowa ba wani abokin Abba Mai-daraja ya tun-tuɓeni, ya sanar da ni wani labari mai kulle kai kuma, na cewa ya gano mutuwar mai daraja akwai alamar tambaya a ciki, wato haɗa haɗarin akayi, na shiga ruɗani sosai bayan ya sanar da ni hakan, kaina ya cika da tambayoyi, kenan fa wai kashe Abba akayi, to meyasa za a kashe mutum mai kirki haka irinsa? Duk da cewa dama irin wannan mutumin zaiyi wuya bai samu maƙiya ba, to amma waye ne wanda ya aikata wannan mummunar aikin? Haka dai abokin nan na sa ya umurceni da nazo na same sa, bayan na je muka tattauna abubuwa da dama da kuma yadda zamu tsara komai cikin sirri, nan muka samu damar tura Jummala akan 'yar aiki amma 'yar leƙen asirinmu, sannan mukayi amfani da Hambali mai gadi duk da cewa dama shi asali aikin gadi yake a gidan".
Cike da tsabar mamaki Amna tayi saurin cewa "kana nufin Jummala da Hambali ba wai masu aiki a gidan kawai bane ma'aikatan ku ne?" "Haka batun yake, duk abun da yake faruwa a wannan gidan ta hanyarsu ne muke sanin komai, domin mun basu yadda zasuyi aikin cikin hikima yadda baza'a gane su ba, duk shirin da Hajiya ke haɗawa ita da ƙawarta mun sani, lokacin da ta fitar da Safna da sunan zuwa Nijer ma duk mun sani, Jummala ce ta tona maganin da Hajiya ta binne a lokacin ta kuma ƙona shi, ranar da Safnah ta fita akan ranar zata tafi Nijer, muna tafe don mu tsaida motar da take ciki mu ɗauketa, sai dai bamu sameta a cikin motar ba, nan muka ji sun sauke ta a daji, kuma mun san dajin nan gurin tsakiyar rukunin ƙungiyar Pospa ne, mun shiga tashin hankali sosai da bazama don nemota, amma aka samu matsala muka rasa ta a wannan ranar, tabbas nayi baƙin ciki matuƙa a wannan ranar domin har ɗauka nayi nine sanadin mituwarta, na kasa taimakon wacche take ƙanwa a gareni" ya faɗi idon sa na sake kaɗawa.
"Jummala ce wacche ke taimakawa Ammu a ɓoye gurin bata abinci a ɓoye" yayi maganar tare da dakatawa, gaba ɗaya maganganun sa ya shige jikin Amna sosai, saboda komai da ya faɗa mata bata ji abun da bata yarda ba, cikin neman ƙarin bayani a wasu fanni ta ce, "amma to yaushe ne ka ganni har kasan ina kama da Safnah? Kuma me nene masaniyarka akan ƙungiyar Pospa ɗin?" Miƙewa daga zaunen yayi, yana taku izuwq gaɓar tekun, yayin da ruwan tekun ke gangarawa gaba yana komawa har yana isowa inda ƙafarsa yake, hannunsa yasa cikin aljihun wandonsa, lokacin Amna ta biyo sa haɗi da tsayawa a bayansa tana jiran amsarta.
"Wani aiki ne ya kawo ni garinku, a hanyarki ta zuwa islamiya na haɗu da ke shekaru uku da suka wuce, na yi mamaki sosai lokacin da nayi tozali da ke, sai da na riƙe numfashi na na tsawon mintuna sannan na daidaita, domin da ba don abunda ya ban banta ki ke da ita ba, da tabbas zance Safna ce tazo garin Gombe, tun daga nan na tsananta bincike a kanku. Ƙungiyar Pospa kuma, ƙungiyace ɓoyayyiya, babu wanda yasan inda suke aiwatar da komai na su, duk wanda yayi yunƙurin yin wani abu a kansu a buɗe kuma suka gano shi to fa ta shi ta ƙare, sannan komai yin sa suke da tsantsar dabara, idan ba wai bincike ta nutsuwa sosai kayi ba, to fa baza ka taɓa cewa shike lalatawa da jefa matasa cikin hatsari ba, duk wanda kaga ya san wasu 'yan abubuwa game da Pospa da kuma hatsarinta, to fa ba ƙaramin bincike cikin hikima yayi ba, tun lokacin da mukayi la'akari da masu yawan shan kayan maye sunyi yawa sosai aikinmu ya kasu gida biyu, fannin gano Zabba-ba daga lokacin da muka ji sunan shi shine shugabansu, mun tura masu yi mana leƙen asiri da dama amma ya kashe su, haka har muka haƙuri da tura rayuka ana kashewa, sai dai abun mamakin shine bai taɓa nitsawa da ya nemi masu aika masa da mutanen ba, amma abun da na lura shine, shi ya ɗauki kansa shahararre ne, shiyasa bazai nemi masu aika masa da 'yan leƙen asirin ba, duk da na kanyi tunani ko yana sane da motsinmu, sabida lura da abun da su kayiwa mahaifinki".
Sai da Amna tayi sama da kai kamar mai gano samaniya sannan ta ce, "to menene asalin dalilin da yasa kuka kawoni zama Safna?" Cire hannunsa da ke ckkin aljihu yayi ya juya yana facing ɗin ta, ya ce, "har ila yau tambayar kuma? To shikenan, akwai abubuwa da dama da ya dace mu ƙarasa akan ingancin rayuwar Ammu da Safnan, sai dai Safna ba ta nan, gudun makomar Ammu gaba ɗaya da kuma cika ƙa'idan da aka bari na wasu shekaru à baya, akwai buƙatar kasancewar Safna bayan ta cika shekaru ashirin da uku, domin fara aiki a MD company wato kamfanin mahaifinta, kuma ke kaɗai ce wacche zata taimake mu akan haka, shiyasa mukayi duk wannan shirin akanki, kuma ina so ki sani Amnah, bamu san shirin mahaifinki akan zuwa wannan garin ba, domin shi karan kansa a ɓoye yayi komai, amma bayan yazo kuma mun gane inda yake, mun bi duk hanyar da zamu bi don dakatar da shi, amma shi ɗin ya kasance mai kafiya sosai, munyi masa alamu masu yawa akan hatsarin wannan ƙungiyar, kuma ya gane amma kuma yana da taurin kai sosai".
Rufe idonta tayi tana jin ina ma tuntuni ta san komai, da tasan hanyar da zata bi ta kare mahaifinta. "Yanzu haka ahalinki suna cikin ƙoshin lafiya da kulawa a ƙarƙashinmu, ko sau ɗaya babu wanda muka gwada cutarwa a cikinsu, kuma mun faɗa musu ƙudurinmu a kan ki ba mummuna ba ce, hakan yasa suma suka bamu goyon baya, amma ina mai tabbatar miki Amnah, idan har a yanzu kika buƙaci ahalinki to baza mu hana ki ba, amma muna roƙonki da ki taimaka mana saboda Allah!"
Buɗe idonta tayi, ta kuma komawa gun kujerar ta zauna, tare da sauke numfarfashi, shima kuma dawowa yayi ya zauna, kan ya ƙarisa zaman ta jefa mai tambaya, "meyasa ko sau ɗaya baka taɓa haɗa ni da su ba?" Zama ya ƙarasa ya na bata amsa da cewa, "Kina ganin idan da nayi hakan zaki kai wannan lokacin a nan? A ah, amma na sanar da ke komai a yanzu, ki bani amsar shawarar da kika yanke wa kanki yanzu, zaki tafi kamar yadda kika ce da fari ne? Ko kuma zaki cigaba da taimaka mana?".
Shuraim ya faɗi yana ƙure ta da ido, don jin amsar da zata bashi, amma zuciyarsa na yi masa razani daga amsar da ka iya fitowa daga bakinta, kallon kallon suke a wannan lokacin, Amna na kallonsa cikin dakewa ba tare da shakkar amsar da zata bashi ba, shi kuma gaba ɗaya jiran fitowar kalmar da zata ce kawai yake, tabbas duk abun da ta yanke ba zaiyi mata dole ba, hannayenta duka biyu ta ɗaura akanta, ta buɗe baki don sanar da shi amsarta kai tsaye.
Toh 'yan-uwan arziƙi, kunji yadda rayuwar Shuraim ya kasance, da kuma haɗuwarsa da Abubakar Mai-daraja, da kuma dalilin da yasa suka dawo da Amna Kaduna, tabbas labarinsa ya ɗan taɓa zuciya, amma halin Mai-daraja ya ƙara bayyana.
Wani babban abu kuma, ashe dai daga wannan faɗawa ruwan Safna ta rasu🥺
Shin ya kuke ganin zai kasance?
Wani amsa Amna zata bada? Shin zata amince? Ko kuwa a ah?.
Mu kasance a next part idan Allah yayi da ranmu, don jin yadda za a kaya,
___________________________________________________________________________________________________________
Part 1️⃣1️⃣3️⃣▶️1️⃣1️⃣4️⃣
"Bayan na ji duk abun da kace! Zan baka amsata kamar haka!" Ta faɗi tana kawar da kai gefe, zuciyar Shuraim ne ya tsananta bugu akan amsar da zata ba shi, dawo da kallonta kansa tayi ta kuma haɗe fiska sosai, ta yun ƙura kamar zata ta shi ta furta, "abun da zan ce maka Shine, na yarda!" Shuraim da yayi saurin miƙewa don a tunaninsa kalmar rashin amincewa zata faɗa, amma sai yaji saɓanin haka. Amna kuwa dama bata kaiga tashin ba, don haka ta gyara zama tana kallonsa.
Numfashi mai ƙarfi ya saki tare da farin ciki, sannan ya koma ya zauna, har da murmushi tare da ɗaga hannun damarshi zuwa kusa da goshinsa yana ɗagawa, sannan ya sauke yana kuma sauke numfashi kamar wanda akayiwa surprise, itama murmushi kaɗan tayi tare da zama tana kallonsa yadda yake kamar yana cikin farin ciki, "meyasa ka nuna ɗan ƙaramin shock haka?" Tayi masa tambayar tana kallon kewayen wurin yadda yamma yayi sosai.
Kallonta yayi murmushi na sake bayyana a fiskarsa ya ce, "na razana ne, da na ɗauka zaki ƙi amincewa" "dama kana so na amince ka barmin zaɓi?" Tayi masa tambayar tare da ɗaga girarta, "To ai ke ɗin ce wata irin juyayya" juya masa ido tayi tana cewa cikin nuna ɗan ɓacin rai "oh yanzu kana da bakin tsokanata koh? To ba ma wannan ba, ina son ka haɗa ni da family na, ina son in gan su, a wannan garin kuka ijje su ko kuwa?" "Kiyi haƙuri muyi hakan wani lokaci amma yanzu kinga yamma ya ƙarato sosai, ya kamata mu kasance a gida" "ok to naji! amma wai ina kakai yawansa sa turancin na ka ne?", ta faɗi tana 'yar murmushi.
Dariya yayi mata yana cewa, "to me zanyi da wani turanci, bayan an san ƙaƙale kawai nake" tashi tayi kawai tana wucewa, shima bayanta yabi yana faɗin, "ya dai madam C.E.O, ya zaki tafi ki ƙyale ni?" Tsayawa tayi tana kallonsa sannan ta ce "auu da kai nazo ne?" "A ah amma dole da