Showing 15001 words to 18000 words out of 129098 words

Chapter 6 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

19

Jalo yace "da daɗewa nake son yin maganin ka kai da 'yar uwar ka mai girman kan nan, amma sai yau zanyi hakan, sabida barin ku da ma nayi ku gama na ku sannan ni na baza mulki na".

Sai da Mubarak ya murmusa sannan ya kalli Jalo yace, "kuma wai da gaske kake? Wani tsau-tsayi ne ya saka son ai kata hakan?" Yana ƙara sa maganar suka rufe shi da duka ko ta ina, Ganin abunda ke faruwa yasa su Nabila saurin yin wajen dan ceton sa.

Duk da cewa yana ka rewa, amma sabida taron dangin da suka yi masa yasa shi sadaukarwa, bugu suke yi masa ta ko ina, su Zubee kuwa tsaya kallo sukayi, yayin da Zubee ta ke jin daɗi ganin Mubarak ake jibga, koba komai ai abun farin ciki ne, tun da kowa yasan inhar aka taɓa Mubarak kamar Amna aka taɓo.

Ta tura wayar ta jaka kenan, wasu 'yan-matan ajin su biyu suka shigo da gudu zuwa gaban ta, sai nishi suke, tsayawa tayi tana kallon su cike da mamakin gudun na su, ɗaya daga ciki ce ta fara magana cikin fitar ni shin gudun da tayi "wanke hannu... ka taɓa... am Ɗan-uwan ki" sai kuma ta tsaya sauke numfashi, Zuciyar Amna ce tayi wani irin bugu, da sauri ta miƙe "me yasame shi?" Ta faɗi da sauri tana ƙure su da Ido, haɗi da sauraron abinda suke son faɗa.

Ɗayar ce ta ƙarisa, "Jalo suka tare shi, suna can suna jibgar sa ta wurin Bs Class" tun kan ta ƙarashe maganar Amna ta wuce harda bangar wacce ta tsaya mata a hanya tayi waje.

Koda zuwan su Nabila wurin, Wali yana magana shima ya samu mari, hannu Zanga ya ɗaga zai mari Zarah yaji an tokare shi sai da yayi ba ya ya fa ɗi a ƙasa Timm,, dakatawa suma sauran su kayi suka saki Mubarak jin faɗuwar Zanga, suna kallon wanda ya masa haka, Amna suka gani sai sauke numfashin Tsantsan haushi take, Wali ne yayi saurin riƙe Mubarak da yaji bugu sosai sun farfasa masa fiska sai fitar da Jini yake.

saurin zuwa inda yake. Amnan tayi, tana kallon sa cike da tausayi, shima kallon yake mata a galabaice, ciro Hanki-cif tayi ta fara goge jinin saman goshin sa, dariya su jalo su kayi, cikin ƙufula ta juyo tana kallon inda suke, "Ashe kina hanya? Ai koda baki zo ba dama muma muna tafe, dan yau sai an ka sa gane ku daukkan ku, ke harma da ƙawayen na ki" jalo ya faɗi hakan.

Zubee kuwa daɗi ne ke ziyar tan zuciyar ta, yau dai za'ayi mata maganin matsalar ta, "hmm da alama wa'ennan basu san wa ce Amna ba? Lokacin da suka zo ba mai shiga harkar ta shiya sa" Cewar Nabila a Zuciya, ta juya ta kalli Zarah, suka giɗa kai alamar Zarah ma kotan-kocin tinanin tayi.



#Hmmm ƙura ta tashi, wazai yayyafa mata ruwa ta konta?. Koya zata kaya tsakanin Zakan yar Baba da su jalo?.

Ko Baba zai fara binciken sa cikin sa'a? Ta ina zai fara?

______________________________________________________________________________________________

Part 1️⃣7️⃣▶️1️⃣8️⃣

Hannun ta ta ɗago tasa saman glass ɗin ta a hankali ta fara ja wo sa, yayin da sauran mutanen da suka taru awurin suke cike da mamakin yau Amna na yunƙurin cire glass ɗin ta, koda yake yau dai zasu ga ƙwayar idon da takerufewa, a hankali ta cire sa yayin da idon ta yake a ƙasa.

"please Amna don't do anything, indai dan ni ne kar kiyi komi, na haƙuri, kin tuna maganar Baba da yayi miki, akan hakan? Kar kiyi abunda zai sa shi rashin jin daɗi" Mubarak ya faɗi yana riƙo hannun ta, yana ƙoƙarin ja wo ta, dan baya da buƙatar tashin hankali, koda yasan ta da taurin kai, ba tare da ta ɗago ba ta fara tina maganar Baba da yayi mata a wani lokaci.

"Amna ki rage zafin zuciya, ki kasan ce mai sawa zuciyar ki salama lokacin da kika tsinci kanki cikin hasala, wannan zafin zuciyar bazai haifar miki da komai ba sai dana sani, yanzu ya ki ke tinani in wani abu ya sami yaron nan, na rasa ina kika sami ƙarfin nan mai kama da na Jinnu, haƙuri akan abin da a ka miki bazai rage ki da komai ba, koda yaushe bani da buri da ya wuce inga mutane na alfahari da 'ya'ya na, amma wannan abu da ki ke yi ba bu abinda yake hadda sa miki face bakin mutane, dan Allah Amnan Baba ki rinƙa amfani da abinda nake faɗa miki a ko da yaushe" Baba ya faɗa mata hakan bayan tayi faɗa da wani ɗan Makarantar su, ya kira ta ita da Mubarak.

sai dai bata amsa masa ba, saboda in dai har zuciyar ta ta ɓaci sosai to bata magana sai ta shawo kan matsalar ta, ta hanyar faɗa da wanda ya tsokano ta, kuma in tayi faɗan takan ɗau lokaci kafin tayi magana, saidai na kusa da ita su bada labari, anso kai maganar zuwa police station, sabida yadda tayi masa rauni a gefen wuya, shaidun da suke tare da ita ne ya hana abun yin tsamari sosai, amma an daɗe kan maganar ya wuce, sai da Baba ya bada kuɗeɗen tritment.

Saurin fisge hannun ta tayi daga riƙe tan da yayi, ba tare da ta ɗago idon na ta ba, "baka da hankali ne? Da rai na wasu suyi maka wannan abun ba tare da sun karɓi fiye da abun da suka ma ba?" Ta faɗi cikin kakkausar murya, dariya su Jalo suka ƙara yi a karo na biyu, tsaida dariyar sa yayi haɗi da yin kan ta dan ya bata ma rin da zai sumar da ita, sai dai nushin da Amna takai masa a ciki ne yasa shi yin ƙasa warwas, har lokacin kuwa kanta ƙasa yake.

"Boss Jalo, Boss Jalo" shine su Zanga ke furtawa, juyowa sukayi inda take, dai dai lokacin da ta ɗago idon ta gare su, zaro ido gaba ɗaya 'yan wurin su kayi, ganin manyan idanun ta, ga ƙwayar idon kuma Ash colour, duk da idon ya fara rinewa izuwa ja, sai ta fito zak Baturiya, kallon ta kowa yake kamar yauce suka fara tozali da ita, daga Mazan har Matan, saɓanin Mubarak da abokan su, sabida sun riga da sanin ta haka, wow wow ko wannen su ke furtawa wasu a Zuciya wasu kuma a fili.

Yin kan sauran tayi ta fara basu nasu rabon, naushi take kai musu ta ko ina, ta hana su samun damar guduwa, yadda take jibgar su ko gajiya ba tayi ba, su kuwa ji suke kamar Rodi take buga musu, duk da haƙurin da Abokan ta suke bata amma kamar ƙara harzuƙa ta suke, haƙuri suka fara bata, ganin ba ta da niyyar barin su. Sai ihu suke, ƙattin banza.

Da ƙyar ta da kata dan riƙo ta da friends ɗin ta suka yi, jikin ta har jini ya taɓa saboda yadda itama ta far-fasa musu jiki, su kuwa su Jalo babu abin da suke sai sauke numfar-fashin wahala, "haaaa waiii wayyooo" suke faɗa sai juyi suke kowa na taɓo kota ina na jikin sa inda ke mai zugi, tare da dana sanin Shiga harkar Aljanar nan, dan batayi kama da mutum ba, siririn cikin su harda fitsari ya tsula a wandon sa.

mutanen wurin a tsorace suke, su iya ni Zubi kam tini ta koma baya dan ganin Amna take kamar ma ba mutum ba, sai wuƙi-wuƙi da ido take, "wai ace Mace ta yiwa shirga-shigan Mazan nan duka cab"

Jan Amna su kayi suna ƙara bata haƙuri, suka wuce, ita kuwa ji take kamar bai kamata ta barsu haka ba, sai numfashi take fitarwa da sauri da sauri, idon ta ya rine zuwa ja, hakan yasa ya bada wani kala daban, sanya mata glass ɗin ta Mubarak yayi. Saurin ɗauko jakansu Zarah tayi sukayi hanyar fita, ko hakan zai ƙara lafa abun.

Kusan gaba ɗaya malaman makarantar ne suka yo wurin ganin cinci-rindon ɗaliban su a wurin sai surutai suke, kutsawa su kayi ciki suna tambayar dalilin dan-dazon na su, sai dai abin da suka gani ne yasa su dakatawa da tambayar, ganin samari Biyar a baje sai juyin a zaba suke, riga dik ya ɓa ci da jini.

"Kai wai Trela ce ta biyo ta Makarantar nan bamu sani ba ko me?" Cewar wata Malama tana ƙara ƙure su da kallo dan tabbatar da hasashen ta.

Sai da suka kai Mubarak chemist, sannan sukayi hanyar gida.

BABA.

Kamar yadda ya shirya yau ya fara ai watar da binciken sa, samun labarin wata sheɗaniya yayi daga bakin wasu 'yan shaye-shaye da ya jisu suna hira, ba tare da sun san yana sauraron su ba suke magana, su Uku, ɗayan yake cewa, "ai ita Zilla da kake gani, duk kan ƙwaya ta sani, babu irin ƙwayar da ba ta sha" dayan ya amshe da faɗin "ni fa har mamaki nake yadda kan ta yake ɗaukar kowani iri" na ukun ne yace, "kai to indai hakane kuwa, ai Zilla irin ta mu ce".

dariya Biyun suka kwashe da shi sannan wanda yafara maganar ɗazu ne yasake cewa, "lallai yau na ƙara tabbatar da kai baƙo ne a harkar Bariki, duk wani da ya san gurin Ƙoƙolwar ka Zan-Zan to yasan Zilla ba ta ƙananun marasa kunya bane, ko daga shigar ta, dirin surar ta batayi kama da ƙananun mata ba, ko rabin abun da take sha kana zaka iya sha ne?" Ɗayan ma yace "faɗa masa dai" Yana gama sauraron su ya yi gaba, yana tinanin inda Ƙoƙolwar ka Zan-Zan yake?.

bayan ya samu information akan wurin Zan-Zan babban wurin 'yan Shaye-Shaye ne, ka ya Black yasa haɗi da sa face mask, shigar ta masa kyau, sai ya dawo kamar ɗan saurayi, ya nufi wurin, Babu abin da yake ta shi sai warin Taba da giya, duk da cewa Babban wuri ne amma basu ƙaya ta wurin ba. Ko lafiyayyun kujeru babu sai Bencuna.

Guri ya samu ya zauna kan ɗaya daga cikin Bencin, tare da mamakin guri irin wannan, a zuciyar sa yana faɗin "fisabilillahi duba wurinnan babu abinda suke sai saɓon Allah, kamar ba su san me ake kira da mutuwa ba? Yadda kowa a cikin su yake Shaye-Shayen sa hankali kwance, maza da mata wa'iyazu billahi, wllh wani lokaci duk ƙoƙarin ka na ka gyara matsalolin tarbiyyar mutane ko, inka yi arba da wani abun sai kaga kamar babu abinda ma kayi, Allah ka kiyashe mu ta ɓewa" yana gama faɗin haka a zuciyar sa, ya fara wuwwula idanuwan sa da tinanin yadda zai ga ne wannan 'yar-duniyar cikin yawan mutanen nan.

"Zilla ɗan zo mana" yaji wani na faɗin hakan, juyawa yayi dan kallon wanda aka kira da wannan suna, aiko idon sa ya faɗa cikin nata, tsare shi tayi da ido.

Zubin ta Siririyar mace ce fara tass, amma farin Mai ne, sanye ta ke da ɗamammiyar Rigar kanti da bata kai mata ƙasa ba, bi ma'ana dai ta ɗan fi guiwa, sai gashin atach brown colour, sannan takalmi ma black, riƙe take da android a hannun ta.

----- amma fa banga wani irin waya bane, ni dai bata min kyau ba, amma a wurin mutanen wurin ba ƙaramin kyau tayi musu ba, dan ta fi duk matan wurin class, ni kuma nace a Bariki ba----

Ganin yadda take yi masa wani irin kallo yasa shi ɗauke idon sa a kanta, "wai wannan abar ce wasu suke ribibi akan ta, abu ko kyan gani babu" ya sake faɗi a zuciya, "kai ka kiyaye ni nayi maka kama da Rose irin ku ne?" Ta ba wanda ya kira ta amsa, har lokacin kuwa idon ta na kan Baba.

Ta kowa ta fara yi cikin salo irin na su, wanda wasu suke kallon na ta daban, zuwa tayi gaban sa tana ƙa re masa kallo, yayin da shi kuma kan sa yake ga wayar sa, "ya haɗu" ta furta a zuciyar ta, saboda da ganin sa ba irin Mazan da suke nan bane.

"Hii guy, what do you want" ta faɗa masa haka tare da zama gefen sa, ya furta "not now" "ok har zuwa yaushe kenan, da alama kai baƙo ne anan ko? faɗamin dik abin da kake so anan zan mallaka maka, saboda ka yi min".

Saida ya ɗago idon sa yakalle ta "yes I'm true, ka yimin" ta faɗi masa, duk da bajin daɗin kasan cewar sa anan yake ba, amma ya zame masa dole shima ya zama ɗan Bariki ko dan aikin da ya ɗauko".

Yace mata "ba wannan karon bane zuwa na nan na farko, ni na san ki amma sai dai wannan ne ganin ki da ni na farko, amma kice nayi miki? daga ganin Sarkin fawa" ta ƙarisa masa, "sai miya tayi zaƙi?, nasan karin maganar ai, ka ga, tun da har ka ce kasan ni, to kasan duk Mazan da suke a nan ko wannen su buri yake nayi masa magana, amma fa kai kaɗai ka burge ni a yau, duk da cewa bangama ganin fiskar ka ba saboda mask ɗin da kasa" ta faɗi tana ƙoƙarin shafo hannun sa.

Saurin miƙewa yayi yana faɗin "amma fa ni ba mai kuɗi bane kamar yadda kike so" dariya kaɗan tayi haɗi da miƙewa tace "ban cika neman kuɗi a wurin mutum ba, musamman irin ka, buƙata ta kawai naji daɗin kasan cewa da kai".

Murmushi yayi yana faɗin "zan wuce akoi abunda zanyi" ya faɗi yana fita waje, biyo sa tayi wajen tana cewa "babu abinda ka buƙata a nan kuma zaka tafi? Sannan baka gayamin sunan ka ba? Kuma baka nuna min kyakykyawar fiskar nan ta ka ba, ko kayi murmushi bana ganewa sabida ba ganin bakin ka nake ba"

'Yar dariya yai mata tare da tsayawa, "ina da tambaya ko? Nima bansan dalilin rashin Jan aji na lokacin da na gan ka ba, ka ga, ni suna na Zulahat amma ana kirana Zilla" kallon ta yayi jin sunan musulmai gare ta, duk da hausan ta raɗau yake amma yayi tinanin girma cikin hausawa ne yasa haka, shigar ta baza ka taɓa cewa shigar musulma bace, koda yake 'yar Duniya ce wace irin shiga ne baza tayi ba".

Faɗamin sunan ka mana haɗaɗɗe?" "Hamid ne suna na" "wow sunan ka me daɗi to mene ne laƙabin ka kaima?" Amsa mata yayi da babu, musayar number suka yi, ya wuce ba tare da taga fiskar sa ba mask ba.

Binsa tayi da kallon da ita kaɗai ta san manufar sa, yayin da shi kuma yaji daɗin samun da ma da wuri daga gare ta, da nufin gobe zai fara bugan cikin ta, ta yu ta san ƙwayar



POSPA.

#Lalallai, bakuyi mamakin yadda Zilla ta shigo hannu da kan ta ba, wani irin manufa take da a zuciyar ta?

Shin Baba ya biyo hanyan bincike da kyau kuwa? Bugan cikin ta zaiyu kuwa?

A baya naji Baba shi kansa bason zuwa Kaduna yake ba, ko me dalili?

Ya su Ummee za suji yayin da aka mayar musu da Mubarak da rauni?

Su waye zasu min rakiya zuwa gaishe da su Jalo da jiki?😂

______________________________________________________________________________________________

Part 1️⃣9️⃣

▶️

2️⃣0️⃣

Fannin baiwar Allah SAFNA. .

Ammu ce ta tashi da rashin lafiya duk magun-gunan da take sha Safna ta bata amma jikin sai ƙara zafi da yayi, tinanin yadda zatayi take amma ta rasa, Dady baya nan bere ya kai su Hospital, Hajiya kuwa tasan ko ji tayi Ammu suma take yi ba bu abinda zai sa ta ko kalle ta bere ayi maganar taimako.

Ganin jikin na ƙara zafi sosai yasa ta tashi tayi waje da sauri, turus tayi bayan bangazan Hajiya da tayi, 'ke!" Hajiya ta furta da tsawa da yasa jikin Safna rawa, "dan Allah, dan Allah Hajiya ki gafarce ni, wallahi ban lura bane, Ammu na ce ba lafiya jikin ta ya ɗau zafi sosai" ta ƙarashe faɗi cikin rawar murya.

Wani irin gigi taccen mari Hajiya ta sauke mata da yasa ta yin gefe goshin ta ya bugu da gini, durƙusawa tayi haɗi da saurin sa hannun ta kan goshin na ta, ta rintse ido jin yadda yake mata zugi, tana sauke hannun taga ya ɓaci da jini, ashe fashewa yayi.

Duk da ganin hakan bai sa Hajiya taji tausayin ta ba, sai ma jan tsaki da tayi tana wucewa, hawaye mai tsananin zafi ne ya koranyo daga cikin manyan idonuwan ta, dama fitan da tayi dan zuwa gurin Baba Hambali ne, ko zai bata wayar sa ta kira Dady ta sanar da shi halin da Ammu ke ciki.

Miƙewa tayi zuwa wurin sa, hannun ta da pe da goshin ta, zaune ta sami Baba Hambali kan kujerar zaman sa, ya ka ra Radio a kunnen sa yana sauraron shirin Inda Ran Ka, isa wurin sa tayi duk da tana jin zugi a goshin na ta, "Assalamu alaikum Baba ina wuni" ta gaishe sa, "Lafiya..... subhanallahi Meya same ki haka 'yata?" "Ba wani abu bane Baba, dan Allah ko zan samu waya in kira Dady?".

Tayi masa maganar tana sauke hannun ta a goshin na ta, sai dai jinin bai tsaya ba, sai ma ɓata mata kaya da yayi, "haba 'yata duba fa jinin yaƙi tsayawa ya kama...." Cewar Baba mai gadi cike da damuwa, sai dai katse sa tayi da faɗin "please Baba Hambali dont worry a bout this, kawai waya zaka bani ka ji dan Allah".

Ciro wayar sa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login