Showing 102001 words to 105000 words out of 129098 words
Chapter 35 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
juya ya dube ta ya ƙara faɗin, "take this bag and give it to Safnah" yana faɗi ya juya, "duk da ya burge ni amma akwai jiji da kai, a haka za a kai labari kuwa? To yanzu dai wai in kaiwa Safna jakar ta, ni wallahi ko son ganin ta ba nayi, don gani nake kamar zata kuma turani kan upstairs wallahi". Ta faɗi cikin ran ta haɗi da nufan hanyar ɗakin Ammu.
Amna na tsaye jikin ta na ta bata amsar asiri na ya tonu, kawai taji an rungumeta ta baya. Saurin rufe ido Amna tayi, jin an saketa an kuma dawo gabanta, kwashewa da dariya Raheena tayi harda kama ciki, yayin da Amna kam haryanzu idon ta a manne, "wai, wai, bestyna kin tsorata ne?" Cewar Raheena Tana cigaba da dariya, Amna ta ɗago muryar na Raheena ƙawar Safna ce, hakan yasa taƙi buɗe idon ta ɗan saki murmushin ƙarfin hali ta ce, "Raheena ke ce? Sannu da zuwa...".
"Me na rufe ido to? Se kace wacche ke tsoron ganin abun tsoro?" Cewar Raheena da mamakin rintse idon da Safna tayi, Amna ta lura da Raheena bata kula da babu tabon nan ba, hakan ya sata tunanin gwara tayi mata dabara taje toilet ta canza ba tare da ta kula ba, "jira ni in shiga bayan gida infito kinji?" Ta faɗi wa Raheena tana durƙusawa kaɗan ta ɗauki jakar ta wuce hanyan toilet da dabara, buɗe idon tayi bayan ta bar gaban Raheena.
Da kallo kawai Raheena ta bita, "to ko don yadda na shigo ne ya sata haka? Ƙila ta tsorata sosai" faɗin Raheena a zuciyarta tayi saurin yin gurin Amna ta riƙo ta tana faɗin, "besty nima sopris...." sai dai maganar ta ya tsaya cak sakamakon tozali da idon Amna da tayi. Wani irin gab gab cikin kan ta yayi mata, ta zuro idanu wanda bata gama gane abun da ta gani ba, hannu amna ta ɗaura akai ta sauke alamar abun da nake gudu ya faru.
"Bes...be..ty.. me haka idona ke gani?" Raheena ta faɗi cikin ruɗewa, "eh? Me nake gani?" Ta kuma faɗi, kama hannunta Amna tayi tana ƙoƙarin zaunar da ita kan gado, amma Raheena taƙi amincewa da hakan sai maimaita tambayar take mata, "wannan ba Safna ba ce, wa cece ke? Nayi gaskiya ko? Ba besty na bane" jan ta da ƙarfi tayi ta zaunar da ita tana kallon gefen Ammu da ke kwance idon ta rufe alamar bacci sannan ta dawo da duban ta kan Raheena ta ce, "don Allah Raheena ki dai na maganar nan kin ga Ammu bacci take yi, kar ki tasheta, dama da damuwa tayi barcin".
Tsayawa kawai Raheena tayi tana kallonta cike da ruɗani, ganin Raheena ta riga da ta ga komai, shiyasa kawai ta zauna tana maidasu a fiskarta, gudun kada wani ya kuma gani, idan yaso in ta kammala sai tayiwa mata bayani yadda zata gane. Raheena na kallon Amna har ta gama sanya abubuwan duka, babu abinda ta ke bin Amna da shi sai kallon tsantsar mamaki da rashin fahimta da kuma kullewar kai, "ko za mu iya fita waje? Ba wai cikin gidan nan ba mu ɗan zagaye umguwan nan kaɗan, daga nan sai insanar da ke amsoshin tambayoyin da yake ranki" cewar Amna don gwara suyi magana a wajen zaifi sirri.
"Me kike nufi? Kenan kina son sanar da ni da gaske ke ba bestyna bace kamar yadda nayi tunani tun farko? Tun ranar da na fara ganin ki na shiga tunani, sai dai banbari zuciyata ta gasgata min komai ba" janta Amna ta yi suka fice daga ɗakin, daidai da zuwan Ruki dap ƙofar, "Safna ga bag ɗin k.." kan ta ƙarisa Amna ta karɓa suka fice ita da Raheena, da kallon mamaki Ruki ta bisu, ganin Raheenar cikin wani fasali kamar ba yadda ta saba ganin ta in tana tare da Safna ba.
Sai da suka bar cikin gidan kana Amna ta ce, "wani tunani ne kikayi ranar da kika fara ganina?" Tsayawa Raheena tayi tana dubanta ta ce, "don Allah ki faɗamin amsoshin da kika san nake yi yanzu, wa cece ke? Shin ko ke aljana ce? Saboda a yanzu abun da jikina ke faɗamin kenan" ta faɗi cikin tsoro, tafiya Amna ta farayi tana faɗin, "ni ba aljana ba ce, sai dai ni ɗin kamannin Safna ce, wato dai muna kama da ita, kuma kama ta ban mamaki, wasu dalilai ne yasa ni zama a gidan nan, kuma dalilan da labarin suna da yawa, don Allah ba na son ki tambayi wani abun a yanzu, iyaka amsar da yakamata na baki kenan, amma inda rai da lafiya zaki san komai" Amna ta faɗi bayan ta cigaba da tafiya Raheena ma na binta baya.
Cikin wani mamakin Raheena ta kuma cewa, "kenan kama ce kawai kuke da ke da Safna? Sai iyaka banbancin da na gani? To ina ƙawata take?" ta faɗi cikin tsantsar damuwa, da fa ta Amna tayi tana faɗin, "kada ki damu Raheena, ki sa a ranki tana lafiya, ni bani da masaniya a kan tana ina? Amma ki kasance mai yi mata addu'a, ki cigaba da ɗaukata a matsayin ta, mu kasance ƙawaye kamar ke da ita".
Murmushin da damuwar bai gama tafiya ba Raheena tayi sannan ta dube Amna da ta tsaya tana dubanta ta ce, "ina cikin damuwa sosai, amma ke ya sunanki?" "Sunana Amina amma Amna ake kirana" "ikon Allah kenan mai halitta yadda ya so, amma ita Ammu ta san da hakan?" Cewar Raheena, "eh ta sani tun da daɗewa" Amna ta bata amsa, Raheena ta kuma cewa, "wato duk sauyin da nayi ta gani a matsayin besty na ashe duk ba ita ɗin bace, wato shiyasa kika nemi tarihinta da wayo a waccan ranar?" Murmushi Amna ta saki tana cewa,
Ƙorai da gaske, saboda naga alamar kuna da fahimta sosai tsakaninki da ƙawarki, alamu duk sun nuna amintar da ke tsakaninku, Ammu ba ta iya magana shiyasa na zaɓi ne tambayeki", cigaba da tafiyar sukayi Raheena ta ce, "Allah sarki, Allah yasa bestyna tana muhallin da ya dace" "ameen ya rabbil alamain, mu cigaba da addu'a komai zai warware mana insha Allah!" "Wannan haka ne Amna, na so na tambayeki amma tun da kika roƙi kar nayi miki wata tambaya sai lokaci yayi zanyi hakan, amma idan nace ban shiga damuwa na rashin sanin halin da aminiyata ke ciki ba nayi ƙarya".
Haka dai sukayi ta yin hira Amna na lallaɓan Raheenar da kuma bata labarin abun da tayi wa su Hajiya shiyasa suka shiga hankalinsu a kanta yanzu, dariya sosai Raheena tayi don taji daɗin wannan labarin, haka har suka dawo gida, shiga motar su da driver ke jiran ta kawai Raheena tayi, Amna ta bata sallawun gaishe da Momy, itama insha Allah zata sa rana taje ta gaisheta.
DARE.
Kowa na zaune a dining, Amna ta taho tana tura Ammu a keke ta zo dining da ita, gaba ɗaya suke bin Ammu da kallo, Hajiya da ta samu damar an cire mata audugar wuyarta itama ta bi Amna da kuma Ammu da kallo, hakan na nufin yanzu wa'yannan marasa-galihun nan sun zama masu 'yanci kenan? A gaban idon ta kuma babu yadda ta iya? Bai kamata ta zura ido haka ba, to amma ai batada wata hanya, duk wannan zancen Hajiya tayi a ranta.
Haka sauran ma mamakin sauyawan lokaci suke yi, domin yanzu matsayin Safna na son fin na su a gidan. Shi kuma Shuraim kallon mamakin ganin Ammu yake, koda ya ɗan ga kamannin Ammu kaɗan a fiskar Amna, wanda hakan zai iya tabbatar masa da Cewa 'yarta ce, wani irin murmushi Dady ya saki kamar na dole ya ce, "yata ya kika fito da ita?" Sai da ta zaunar da Ammu kan kujerar dining ɗin wanda Shuraim ma ya taimaka mata gun hakan, itama ta zauna kan kujerar sannan ta ce, "Dady gani nayi ya kamata itama a rinƙa zama da ita kamar kowa, saboda zai sa ta rage jin kaɗaici".
"Hakane wannan tunani ne mai kyau" Dady yayi maganar yana cigaba da cin abincinsa, miƙawa Ammu abinci ta fara yi ba tare da ita tana ci ba, kallon ta Shuraim yake ganin hankalin ta kan Ammu kawai yake burinta ta ciyar da Ammu har ta ƙoshi, ya ce, "Mrs C.E.O kici wa cikin ki, I will give her the food" cewar Shuraim, ta bashi amsa da, "i don't need, i will give her my self!" Juyawa sauran sukayi suna kallon su.
Wani haushi ne ya daki zuciyar Hajiya, saboda ita ba taso ko sannu ya haɗa Safna da Shuraim ba, domin ta ga izina akan Yazeed, duk yadda yake tsawatar mata sai gashi ya faɗa soyayyar ta, shine yanzu wannan ma tana wani shishshigi akan sa, gashi yanzu babban burin ta bai wuce taga yana son Rukinta ba. Tabbas ba tajin za ta cigaba da sawa Safna ido tana abin da take so yanzu a gidan nan, wato ita da 'ya'yan su zama 'yan kallo kenan?
Amna kam sai da ta tabbatar Ammu ta ƙoshi ka na ta fara cin na ta, lokacin kuwa kowa ya tashi ya rage daga ita sai Ammu sai kuma Ruki da Shuraim, don ma Hajiya ce ta hana Rukin tafiya, alama tayi mata na ta ja Shuraim ɗin da magana, "Shuraim ko akwai wani abu da kake so ne? Sai in kawo maka yanzu" cewar Ruki cikin sanyin murya, sai da Amna ta kalleta bisa ga yadda tayi maganar, murmushin ciki tayi, tana cigaba da cin abincin ta.
Shi kuwa Shuraim bai amsa wa Ruki ba, sai ma shirin tashi da yayi, "ko baka da buƙatar komai?" Ruki ta kuma faɗi kan ya ƙarisa miƙewa, ya bata amsa da cewa, "kar ki damu" kallon sa Amna tayi ta ce, "ga mai buƙatar taimakon ka nan, ba ni ba" ta faɗi tana dariya ƙasa-ƙasa, saboda ta ga lokacin da Hajiya tayiwa Ruki alama. Wucewa kawai yayi ba tare da yayi magana ba, juyawa gun Ruki Amna ta kuma yi tana cewa, "'yammata ko dai kin faɗa ne?" Tana faɗi ta miƙe tana dariya ta maida Ammu kan kekenta taja ta suka wuce. Haushi ne ya cika Ruki amma sai haƙuri.
ƘARFE 01:00am.
Zabba-ba ne tsaye sauran muƙarraban na sa gaba ɗayan su suna jere kashi kashi, dukkan su da kaya farare, shi kaɗai ne kayan sa ya ke kasancewa launin da yake so, wa'yan da basu taɓa ganin sa sai yau ba sai saƙa da warwara suke a cikin ransu duk da cewa ba sa iya kallon fiskar sa, sakamakon hasken da ke bayansa, sai dai shi yana iya ganin kowa a cikin su. Ta ke ya fara magana cikin muryarsa ta isa da ta ƙama.
"Kuna aikata kurakurai da yawa, amma nayi shiru na rabu da ku! Ba kuma na ƙyale ku bane don bazan iya aikata muku komai ba! Sai dai don in rabu da ku kuyi gudu zuwa inda zaku tsaya! Don haka yau rana ce da zan tankaɗe, wasu daga cikin ku, zan yi sadaukarwa mai kyau zuwa ga ƙaho mai daraja!" Ta ke jikin kusan dukan su ya fara rawa tamkar ana buga musu ganga.
__abun da yasa Zabba-ba zai aikatawa wasu daga cikin muƙarrabansa hukunci shine. Sune silar sanya shi asarar ƙwayar da ya sarrafa sa watannin da ya wuce, domin shi so yayi a tashi Nigeria sosai da sosai, amma hakan baiyu ba sakamakon salwantar mishi da wasu da dama da sukayi. Wa 'yan da ya kashe guda huɗun can, sune suka sanar da shi gaskiyar abun da ya faru, amma ya aikasu lahira babu imani, sakamakon da hannun su suma a ciki, sauran kuma ya bar su har sai ya gama haɗa wata shaharrariyar chemicals ɗin sa, wanda idan har yayi amfani da ita kuma ya ci nasara, to fa babu abin da bazai samu ta hanyarta ba,, domin a yanzu haka wannam abu yana wurin matsafin sa, saboda zai ƙara yi masa wani gagarumin shiri akai. Wannan chemicals ɗin, idan yayi nasara, to zai mallaki duk abin da yake buri a duniya, babu wata shakka da zaiyi gurin aikata duk abin da yaso, idan kuwa ya samu hakan, to muƙarraban nan na sa basu da amfani a garesa, sai wa'yan da ya so ya bar su su zauna tare da shi__
Wani baƙin hayaƙi ne ya fara fita daga cikin wata kwalba, ta ke ta fara zagaye kowannen a cikin su, da yawa suka faɗi, ya rage ƙalilan, duk da suma suna da yawa, "angama komai Matsafi naa" Zabba-ba ya faɗi cikin sautin amo, maimakon sauran kaga tsoro a fiskar su, amma inaa ko wanne idonsa ya ƙafe.
Lallai! Zabba-ba fa abun nashi na son yin yawa, to ya kuke gani game da shi? Shin zaiyi nasarar wannan sinadarin ko ya ya?.
Amna ta fara fito da Ammu dining, hakan zai ɗore kuwa? Hajiya zata ne mi wata hanyar don ƙuntatawa Amna?
___________________________________________________________________________________________________________
Part 9️⃣7️⃣▶️9️⃣8️⃣
WASHE GARI.
Shiri Amna tayi da wuri wai don kar ta shiga mota ɗaya da Shuraim, tana zuwa ta tadda driver ba ya nan, wani haushi ne ya cikata, to me yasa bata karɓi numbern drivern ba? Tana cikin tsaye sai ga Shuraim ya fito, dariyar sa ne ya ɓoye à cikin sa, domin ya ga lokacin da ta fito da sauri, "haƙiƙa Shugabar MD company she's too selfish, idan ba haka ba, yaushe zata bar assistant ɗinta ko oho?" "Eh naji ɗin, bazan tafi da kai ba yau kam" kwantar da hankalin ki 'yammata, nima babu buƙatar in tafi da ke, because ga driver na can".
Ya ƙarashe maganar yana nuna mata ɗayan gefen, ai kuwa sai ta hangi wani mutum tsaye a gefen wata mota, lokacin drivern ta ya iso, shiga kawai tayi bata tanka masa ba tana murmushi a ranta, shima wucewa yayi gurin na sa motar driver ya buɗe masa ya shiga.
Company.
"Yes ma'am duk abin da kika buƙata an tanadar miki shi, duk lokacin da kike so sai à kawo shi, fannin bed, walldrop.." cewar wani ma'aikaci da Amna ta ba aiki jiya, kan ya ƙarisa ta ce, "tun da komai yana kammale, you don't need to repeat, zaka iya tafiya, zan baka damar kawowa inda nake buƙata idan na tashi" "ok ma'am thank you, na barki lafiya", ya juya ya fice.
Shuraim ne ya shigo cikin office ɗin bayan yayi sallama, amsa sallamar tayi tun kan ya ƙariso inda take ta ce da shi, "yakamata a rinƙa neman izini kafin a shigo, ko haka ake yi a London ɗin?" Ta faɗi haɗi da miƙewa kanta kan wasu takardu dake saman table tana dubawa, ƙarasowa yayi ya zauna kan kujerar gaban tebur ɗin ta, yana sakin murmushi mara ƙara ya ce, "wannan assistant ɗin, he's special! Shine yasa bai da buƙatar hakan" sannan ya ɗora da cewa, "ya maganar meeting ɗin da muke da shi?".
"The meeting belongs to me, not you!" "Ohhh! Calm my C.E.O, dole ne ya zama nima nawa" wucewa Amna tayi don zuwa gabatar da meeting ɗin, tana fita wasu ma'aikata suka take mata baya.
GURIN MEETING.
Shiga ɗakin taron tayi, wanda ya haɗa da manya-manayan masu muƙamai a companyn, tana shiga suka miƙe suna yi mata gaisuwan girma, murmushi kawai tayi musu sannan ta zauna akan kujerar da yake a a tsakiyan dogon tebur ɗin, juyawa gefen ta tayi tana kallon Shuraim da ya zauna a kujerar gefen ta, a ƙasa-ƙasa ta fara yi masa magana, "Mr assistant zan fara da cewa, bana son shishshigi akan duk abun da zanyi a nan kana ji ko?".
"Ok kamar yadda kike so shugabata" ya faɗi cikin zolaya, juya kan ta tayi ta dubi sauran mutanen gaba ɗaya, sannan ta miƙe ta fara magana cikin rashin fargaba, "jiya zuwa yau da fara zuwana companyn nan da sunan fara aiki, i have started the noticing something, na farko wanda shine kan gaba don rusa cigaban MD company, rashin zuwa a kan lokaci, wannan shine a bu na farko da dole mu ƙwarara doka akan haka, sannan na biyu, duk da cewa ban shiga side ɗin sarrafa kaya ba, amma akwai rashin maida hankali akan aiwatar da wannan tsarin, duk da cewa companyn mu ba faɗi yayi ba, amma akwai buƙatar mu ƙara bunƙasa shi" nan dai ta dinga zayyano matsalolin da ta fiskanta kuma ta gani da kuma yadda za'a magance shi".
Tafi Shuraim ya fara yi yana kallon ta yace, "wow!wow C.E.O, wannan maganar ta ki ya burge ni, salo mai kyau" kallon sa tayi zatayi masa magana akan ba ta son yabon sa, kan tayi magana sauran ma suka amshe da tafi, suna gasgata maganar da Shuraim yayi, "nine assistant ɗin madam C.E.O kamar yadda kuka gani, nima akwai wani tsari da nake son kawo taimakon shawara a kai" ya kuma yin maganar yana kai dubansa ga sauran ma'aikatan, "no babu bu..." katseta yayi da cigaba da maganar sa, "strategies should be developed, hakan zai sa duk tsare-tsaren da muka yi su tafi yadda ya dace" shima haka yayi ta zubo dabaru masu amfani, shima yana idawa sauran suka sa tafi, suna faɗin tabbas wannan shawara ce da ya dace.
Haɗe fiska kaɗan Amna tayi don gani tayi kamar so yake ya zama shugaba a wurin, kallonta Shuraim yayi yana matsowa da kan shi kusa da ita ya fara magana shima cikin ƙasa-ƙasa, "ya dai C.E.O? Ko dai haushi kike ji na fiki basira? Da ace gasa a