Showing 81001 words to 84000 words out of 129098 words
Chapter 28 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
ba aljanun ba, wa zai yi hakan?. Hajiya ta rasa ta cewa, domin yanzu ta tabbatar da zancen Safna ɗari bisa ɗari.
Juyowa gaba ɗaya su kayi suna kallon ta, jin dariyar da take yayi yawa kuma taƙi yin shiru, shirun da taji yayi yawa ne yasa ta buɗe idon ta ɗaya, ganin hankalin su akan ta yake yasa ta buɗe ɗayar ma, tana kallon su ba tare da daina dariyar da take yi ba, yadda suke kallon ta yasa ta fara rage dariyar a hankali har ƙarar ya tafi, ya rage saura bakin da yake washe, shima ta kulle sa a hankali, sannan dabarar magana yazo mata, "amm abinda yasa nake dariyar shine, yadda suke ta maganar da ni ban san da shi ba, shine yasa".
Kowa da kalar ajiyar zuciyar da ya sauke, don sun ɗauka ko aljanun ne ke yi, Dady ya dube ta ya ce, "idan maganar da kika faɗa gaskiya ne to baza abar ki haka ba, ya kamata a samo malamai suyi miki ruƙiyya, saboda ki rabu da wannan masifar" zaro ido tayi jin maganar da Dady ya faɗa, yanzu in aka kawo mai ruƙiyya ya tabbatar musu da ƙarya take fa?.
"A ah Dady, Am ina nufin ba sai ankai wannan matakin ba, to dama wannan aljanin ɗan masifa ne, wato baya ƙaunar a tsokane shi, don sunan sa ma Basmasifarr, wato mara son masifa, to idan ya zamana ba a ɓata min rai ba, ko kuwa harara ko dai wani abun na cin fiska, to bazai tashi ba idan har aka kiyaye, saboda ina tsoron a kawo mai ruƙiyya ya nakasa shi, domin shi karan kan sa, Basmafifarr jikan malam ne, to kaga kuwa shima yayi karatun addinin" cewar Amna dan kawar wa Dady wannan tunanin da yake.
"taya kika san, abubuwa akan sa?" Hajiya tayi tambayar cikin shamuƙen muryar ta, "Taya bazan san labarin wanda yake shiga jiki na ba? Bere ma him self ya faɗa min a mafarki" tayi saurin ba Hajiya amsa, "toh shikenan, kun dai ji" cewar Dady yana juyawa kallon kowanne a cikin su, ya cigaba da faɗin, "sai a kiyaye ɓatawa 'yata rai gudun sake faruwar hakan" abinda ko bai faɗi ba kowa a cikin su ya yanke wannan shawarar, hanyar lafiyaa a bita da shekera.
Murmushi Amna tayi haɗi da miƙewa ta ce, "Dady na barku lafiya, Hajiya ki sanar wa Dady komai akan tafiya ta, ƙila ya manta ne" tana faɗi ta wuce, tayi maganar ne don kada Alhaji ya manta da tuhumar da zai mata, domin haka take so. Suma su Ruki kowa a cikin su miƙewa yayi yana fita yin hanyar ɗakin sa, tsoron da suke ji ya ragu, tun da yanzu sun kamo bakin zaren.
Sai da ya bari sun fita kaf sannan ya juyo gun Hajiya da itama ƙoƙarin tashin take, "kafin ki tashi zauna muyi magana before" zama tayi da jin maganar sa, tana neman abunda zata ce masa, "sanar da ni, abinda yarinyar nan take faɗa gaskiya ne?" Nan Hajiya ta fara magana cikin kisi-sina murya kamar zatayi kuka ya hade da ciwon da take ji a wuya ta ce, "to ni me zance? Tun da kai dama ka riga da ka amince da yarinyar, Duk abinda ta faɗa maka gaskiya ne a wurin ka, dan haka me zan faɗa da zaisa ka yarda? Yanzu haka ni kaɗai na san abinda nake ji cikin maƙonloto na"
Ta faɗi harda share ido ita nan ta share hawaye, ta kuma cewa, "ƙila a can wani wurin ta samo aljanun, amma dai babu wani Nijer ɗin da taje, ƙila ma su aljanun ne suka kaita Nijer ɗin koda ma ace ta je kamar yadda ta ce, amma daga ta faɗi sai ka tuhume ni?" Shiru yayi yana kallon Hajiya, duk da yasan tana yi wa Safna abinda bai dace ba amma ya yarda da maganar ta, hakan yasa shi cewa, "na yarda dake, dan haka kidaina share idon ki da hawayen basu kaiga fitowa ba" ya faɗi yana tashi ya fice.
Bin sa da ido tayi har ya fice sannan ta sauke numfashi, tana jin daɗin barin zancen da yayi, "shigiyar yarinya ta so tona min asiri" ta faɗi ƙasa-ƙasa don kada aljanin yaji, tunda ko furuci baya so ayi mata, ita tama rasa ganewa aljanin, to shi kare ta yake ne ko me?.
AMNA. Tana shiga ɗakin ta tarar da Ammu zaune gefen gado, fiskar ta alamar ba a natse take ba, da hanzari ta iso gabanta ta durƙusa tana faɗin, "Ammu me yasa kika tashi? Ko wani abu na damunki ne?" Tayiwa Ammu tambayar a jere cikin damuwa, bata san rashin dawowar da batayi da wuri bane yasa Ammu shiga damuwa, saboda bayan ta sanar da ita cewa Alhaji ya ce tare zasu rinƙa cin abinci a dining tayi mata sallama, amma ganin bata dawo da wuri bane yasa jin tsoron ko akwai abinda akayi mata? Saboda ta san Hajiya da ƙyar ta barta.
Shafa fiskan ta Ammu ta farayi idon ta na kollah, hannun ta tasa da sauri ta share mata hawaye cikin tsananin damuwa na ganin hawayen ta waje ta ce, "Ammu me yasa ki kuka? Wani ne ya shigo?" Tayi maganar ba tare da ta san maganar da Ammu ke yi mata ta ido ba, ganin har yanzu yarinyar ba ta gane maganar da zatayi mata ta ido ne ya sata sakar mata murmushi kawai.
Tunani tayi ƙila Ammu tunanin Safna tayi shine yasa ta damuwa, hakan yasa ta kwantar da kan Ammu kan cinyar ta bayan ta hau gadon, ta fara yi mata maganganu masu daɗi akan Safna zata dawo nan bada daɗewa ba, haka dai har bacci yayi wuff da Ammun.
BAYAN GARI YA WAYE.
Yauma tare su kaci abinci da Amna, wannan lokacin babu wanda yayi mata kallon banza bare magana mara daɗi, ko kallon ta ma tsoron yi su keyi harda Hajiya, Alhaji ne kaɗai ke yin magana da ita. "Gobe ne farkon ranar da zaki fara aiki a company, dan haka ki shirya yau zaki je ki ga ko ina aciki, saboda kisan ta inda zaki fara gobe, kuma ina da buƙatar ki maida hankalin ki matuƙa, kamar yadda na sanki ba kya wasa da karatu, to a wannan fanni ma haka za kiyi, ba daɗewa zakiyi ba iya ka five month ne, shiyasa nake ce miki kada hakan ya dame ki kinji?", murmushi tayi masa da jin haka, ƙila ma kafin lokacin Safna ta dawo matsayin ta, ita kuma ta tafi.
#🤣🤣 Su Hajiya da zuri'ar ta sun musulunta yanzu. Amma fa saura Ruki don bai kamata a barta haka ba ko?
Ya kuke ganin fara aikin Amna zai kasan ce?
Sai da ku 'yan'uwan arziƙi readers 🥰
____________________________________________________________________________________________
Part 8️⃣1️⃣▶️8️⃣2️⃣
Miƙewa tayi saboda ƙoshin da tayi, "ya kika miƙe 'yata?" Dady yayi tambayar ganin ta miƙe, amsa ta bashi da cewa, "ƙoshi nayi ne Dady" "ok to kije ki shirya idan na kammala sai muje ko?" Da toh ta amsa mishi sannan ta wuce.
Sai da Hajiya ta leƙa don tabbatar da wucewar Amna sannan ta dawo da kallon ta kan Alhaji ta ce, "Alhaji kana ganin barin yarinyar nan taje kamfanin nan a haka ba laifi?" Ta kai ƙarshen maganar tare da ɗora hannun ta ga audugan da ke wuyar ta.
Gyara zaman sa yayi cikin rashin fahimta ya kalle ta ya ce, "me abun laifin? Idan akan abin da ya faru jiya kike magana babu buƙata, tunda ta riga da ta faɗi sharaɗin" "eh ta faɗa, amma su 'yan aikin ai basu sani ba, ka ga kada hakan ya dawo ana kace nace" ta faɗi domin so take tayi yadda zata sa ya janye batun, suma su Saleem hakan take a wurin su, burin su suji maganar ta rushe, amma basu sani ba wannan maganan ba bu abinda zai hana shi faruwa, idan ba mutuwa Safna tayi ba.
"Kada hakan ya dame ki" ya faɗi yana gyara zaman babbar rigar sa ya kuma cewa, "akwai wani maganar da nake so inyi da ku, Hajiya idan baki manta ba kwanaki na yi miki maganar wani shahararren mai kuɗi da keda zama ƙasar London ko?" Maida hankalin ta da kyau tayi kan sa tana cewa, "ba shakka munyi batun da kai, idan ban manta ba ma sunan sa Abu Shuraim koh?" "Ƙorai kuwa Abu Shuraim, to ɗan na sa Shuraim ɗin zai zo Nigeria kuma garin nan zo, wato Kaduna, dan gabatar da wani aikin sa, bayan ƙoƙarin da nayi na ci nasarar amincewar sa yaron anan gidan zai sauka".
"Allah Alhaji? Kana nufin ɗan hamshaƙin nan a gidan nan zai sauka? Wannan ai abun farin ciki ne" cewar Hajiya cikin jin daɗi, su kuwa sauran kallon su kawai suke tun da basu san da batun ba, Alhaji ya kuma cewa, "haka ne, kin san na sanar da ke buri na shine na shiga jikin sa sosai, saboda idan har na samu muka haɗa hannu da shi gurin kasuwan ci to ba ƙaramin riba zamu samu ba, kin ga kuwa wannan babban dama ne".
Ba tare da washe bakin da take ya gushe ba ta ce, "sosai ma kam, tunda har ya amince da ɗan na sa ya zauna a gidan mu ai kamar wata alama ce ta nuna zai iya hakan nan gaba" juyawa gurin sauran yayi yana faɗin, "abun da nake so daku ku kuma, yaron nan idan yazo ku girmama shi, koda ace kun girme sa, tunda ni ban taɓa ganin sa ba, bare nasan shekarun sa, don haka ku bashi girma, saboda wannan dama ce a gare ni da kuma ku baki ɗaya, kunga idan na rasa wannan damar tofa mun tafka babban asar".
Gaba ɗaya yaran haɗe fiska su kayi da jin maganar mahaifin su, Saleem ya ce, "Dady ya kake magana kamar kai ɗin talaka ne? Ko da ace ka rasa wannan damar taya zai zama abun damuwa? Kar ka manta kana da dukiya mara adadi fah" tsaki Dady ya ja yana kallon Saleem cike da takaici ya ce, "rufe mana baki sha-sha-sha kawai, kai maganar ka ina da kuɗi-kuɗi, ba ce maka nayi ka daina irin maganar nan ba? to bari kaji, ka ga wannan mutumin da nake magana a kai? Da za'a tara mutane masu kuɗi iri na, guda huɗu, to baza su fisa kuɗi ba".
Zaro ido gaba ɗayan su sukayi, gaskiya wannan mutumin ba na wasa bane, "cab ɗi! Wannan kam to ai ko ni sai inwa ɗan na sa biyayya! kace haka suke da ma ƙudan kuɗi?" Cewar Hajiya jin batun zun-zurutun kuɗi, amsa Alhaji ya bata da cewa, "fiye da yadda kike tunani, kuma wannan yaron shine kaɗai jinin sa".
Marwan da ke son magana ya dakata saboda yaji maganar da girma, duk da shima yana ganin taya za'a kawo mutum gidan su ya girmama shi? Miƙewa Alhaji yayi yana kallon Ruki ya ce, "auta na kiramin 'yar-uwar ki, idan ta gama shiryawa mu tafi" "Dady ni ba 'yar-uwa ta ba ce" ta faɗi harda turo baki, "ke, kin manta abin da ya faru jiya ko?" Cewar Saleem, Marwan ma ya ce, "rabu da ita, saboda babu abin da sukayi mata shiyasa take faɗin hakan".
"Dady bari na kira maka ita" Saleem ya faɗi hakan yana wucewa kiran Amna. Barin wurin Dady yayi Marwan ma haka, taɓe fuska Ruki tayi tana maida idon ta kan Hajiya ta fara cewa, "Hajiya wani irin dabara kika samo mana akan shegiyar yarinyar nan? Saboda bai kamata mu barta haka b..." kan ta ƙarisa Hajiya ta miƙe riƙe da wuya, cikin ɓacin rai ta fara magana.
"Zaki rufamin baki ko kuma na hamɓare miki shi? Gaskiyar Marwan da ace ta lasa miki wani abu da baza kiyi zancen ba, kin san yadda naji lokacin da ta shaƙe min wuya ne? Ba sai yadda naji kawai na sanar muku ba? Ana cewa in mutum ya suma taurari uku zai gani, ni kuwa biyar reras n'a gani à cikin maganuwan nan nawa" ta faɗi tana nunawa Ruki idanun ta tana ci gaba da cewa, "sai da naji kamar ƙafa ta ɗaya à duniya ɗaya a lahira, to wallahi idan na kuma jin wannan banzar maganar to sai na maida miki fiska kamar na Saleem da yake yanzu a saɓe" tana ƙarasa maganar ta wuce ta bar Ruki tsaye ƙerere kamar ta haɗiyi taɓarya.
Sauke numfashi tayi tana tunani, duk yadda Hajiya ke tsanar Safna amma yau tsoron ta take yi?. Hajiya da shigar ɗakin ta kenan kiran ƙawar ta ya shigo waya, ɗagawa tayi ba tare da ta faɗi ƙala ba, "hello ko ba kyaji na ne ƙawata?" cikin muryar ta da ke haryanzu bai washe ba cikin haushi ta ce, "niko nake jin ki har da sauraro m'a" Ladingo ta amshe da faɗin, "au ho, koda na ji, saboda yanzu nayi kiran waya amma network ɗin dai dai yake. Dama cewa nayi in kira inji yadda kika ƙare da matsalar ki".
"So kike kiga yadda na ƙare da matsalar tawa?" Cewar Hajiya har ta fara hasala, Ladingo kuwa duk da ta ji muryar aminiyar ta ba a daidai yake ba amma ta amsa da cewa, "eh" "to ki kirani bidiyo ki gani" ba tare da tunanin komai ba Ladingo ta katse tana shiga WhatsApp, kiran numbern Hajiya ta vidéo call tayi.
Hajiya kuwa ɗagawa tayi tana yin gaba da hannun ta, saboda ta ba Ladingo damar kallon rawanin da akaiwa wuyan ta, "subhanallahi! Hajiya me nake gani haka?" "Me za ki gani in ban da abin da kikayi min, Allah ya wadaran wannan shawar da kika bani!!" cewar Hajiya cike da haushi, domin da bata bi shawarar ba da wani labarin ake ba wannan ba.
Fuska a damuwa Ladingo ta ce, "me kike cewa ne Zainab? Na san ba ma haka dake" "Taya baza muyi haka da ken ba? Ina ce ke kika ban shawara akan in tsoratar da Safna? To kin ga sakamakon da hakan ya min, ashe tura ta Nijer ɗin da nayi ta gamu da iskokai, ina matsalar Marwan da Saleem da na fara sanar dake? To ashe dai aljanun ne suka aikata, bayan na yi mata kalaman da kika ƙisa min, ina isa ɗaki yarinyar nan ta ritsani, in taƙaice miki shaƙe min wuya tayi, ta kuma ɗaga ni sama, wallahi har sai da naji kamar leƙawa lahira nayi na dawo, saboda àzaban da naji a wannan shaƙa, da sai dai ki riski mummunar labari".
"Haka akayi?" Faɗin Ladingo, cikin tunzura Hajiya ta ce, "tambaya kike?" "A ah wai naga maganar ce abin dubawa" tsaki Hajiya tayi tana sauke wayar daga kunnen ta.
AMNA. Bayan ta isa ɗaki ɗazu ta sanarwa Ammu maganar Alhaji duk da babu abinda Ammun zata ce, shiga toilet tayi, tayi wanka, bayan tafito ta tsaya gaban walldrop ɗin da ta buɗe, tana kallon kayan da ke ciki ta rasa wanda zata sa, sa hannun ta ciki tayi tana duddubawa har ta janyo wata haɗaɗɗiyar dogon riga atamfa, pink, white and light purple colours, kalar sa ba ƙaramin burge ta yayi ba, juyawa gurin Ammu tayi tana nuna mata rigar haɗi da fadin, "Ammu wannan zai min kyau?".
Murmushi Ammu tayi, hakan yasa ta fahimtar ta ce eh, sanyawa tayi ta kuma gyara kayan basajar ta sannan ta ce, "Ammu ina kayan kolliyar Safna ne? Tun da nazo ban gan su ba" ƙoƙarin ɗaga hannun ta ɗaya tayi tana yi mata nuni da wani wuri, zuwa wurin tayi ta buɗe ta dauka, duk da fauda da jan baki da gazar baƙi ne kawai a wurin, zama gaban mirro tayi tana shafawa, da faɗin, "ita Safna ko kwalliya ba tayi da alama" cikin ran ta.
Tana à haka Saleem ya turo ɗakin ya shigo, hakan ya ɓata mata rai rashin sallamar da baiyi ba, juyawa tayi tana kallon sa, hakan yasa shi sauke kai ƙasa ya furta, "Dady na kiran ki" "ina zuwa!" Juyawa yayi zai wuce sai kuma yaji maganar ta, "idan zaka sake zuwa ka rinƙa sallama, ka kuma nemi izini, saboda ba ɗakin ka bane" yadda tayi masa maganar ya ɓata masa rai amma ya danne ya fice waje.
"Kamar ba musulmai ba, na lura dukkan su haka suke yi ko gaishe da Ammu baiyi ba, kamar bai san da zaman ta a ɗakin ba" ta faɗi tana sakin tsaki, Ammu da ke can gefe ta saki murmushi jin maganar da Amna tayi, ɗaukar gele da kuma takalmi tayi ta sa bayan ta kammala kolliyar, tayi kyau matuƙa gaya, fiskar ta ya ƙara fitar da haske baza ka tantance ba idan aka haɗa ta da balarabiya, kafin ta fita ƙaramar wayar ta tayi ƙara, zuwa da sauri tayi ta ɗauka da sallama, wannan karon bai riga ta magana ba, sai da ta gaishe sa ya amsa a dake ka na ya ce.
"Sannu da aiki" shiru tayi Tana tunanin dalilin da yasa ya faɗi hakan, "à tunanin ki bansan abun da ki keyi a gidan bane? To ki sani na san duk abin da kike aikatawa" sai da ta ɗan fiddo da manyan idon ta jin maganar sa, kenan ya san duk abinda nake yi? Tayaya? Hakan na nufin ina laifi kenan? Duk take faɗi a ran ta, n'a ta tsinkayi maganar sa yana ci gaba da cewa, "kar ki damu domin ba ƙaramin ƙoƙari kika yi ba, saboda haka na jinjina miki, dama abin da nake buƙata kenan" sauke dadɗa-ɗan numfashi tayi, jin