Showing 120001 words to 123000 words out of 129098 words

Chapter 41 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

24

banganewa jikin na ta ba, domin yanzu ko motsi ba tayi kamar da" ta faɗi cikin damuwa sosai tana kuma share idonta domin gaba ɗaya ranta ya kasa sukuni.

Juyo da kaff haknalinsa yayi kan ta fiskarsa alamar tambaya ya ce, "ba ta motsi kamar baya? Amma tukunna ma menene silar ciwon na ta ne?" "I don't really know Dady, nima kawai dawowa nayi na sameta cikin wani yanayi, sannan abun da ya dameni shine doctor Salis ya ce gurɓataccen jini ne a jikinta, kuma sun cire sun sauya mata da wani, amma to me yasa hakan zai faru?"

Tun kan Amna ta ƙarasa Dady yayi saurin miƙewa, "an sauya mata jini?" Ya furta cikin tsananin damuwa, saboda bai san da hakan ba, ko da ya je asibiti anriga da an ɗibi jinin Amna, kuma basu sanar da shi ba. Cikin mamaki da yadda yayi maganar Amna ta ce, "eh an sauya mata, akwai matsala da hakan ne Dady?" Saurin sakin murmushi yayi ya koma ya zauna sannan ya ce, "no 'yata! Jeki kawai, zan duba lamarin, zan kaita wani babban asibiti don a duba lafiyanta, amma yanzu karki damu, hakan na faruwa dama, idan akayi sauyin jini, bayan auren Marwan zai kaita a sake dubata, domin zamu fi maida hankali akan matsalar, kar ki damu yanzu, babu abin da zai sameta kinji?".

Cikin farin ciki da abun da Dady ya ce ta furta, "to Dady nagode, kana kula da mu sosai" murmushi yayi ya kuma cewa, "na faɗa miki ki daina min godiya 'yata, because that my responsibility" murmushi tayi sannan ta fice ta barshi.

Fiskar Dady ce ta sauya izuwa damuwa sosai, "doctor Salis ya sauya mata jini? Tabbas na san akwai wani mugun abun da ya sanya mata, abun da nake gudu kenan, ashe ya riga da ya aikata hakan, tabbas shine silar shiganta wannan halin, idan har wani abu ya samu maryam bazan taɓa ƙyaleshi ba" ya faɗi yana kuma tunano wani abun.

Amna komawa ɗaki tayi, da murmushi akan fiskarta ta nufi inda Ammu take tana furta, "Ammu da na shiga damuwa ashe hakan na iya faruwa" ta faɗi tana ɗaukarta Ammun ta kaita toilet, ta kunna na'urar ruwan zafi sannan ta yiwa Ammu abin da ya kamata sannan ta fito da ita, gado ta maida ta domin ta ga kamar baza ta iya zama mai kyau ba, kallon Ammu ta cigaba da yi cikin tausayawa sosai, yayinda Ammun kuma ta fara gudanar da sallar a haka, tare da wani tunani a ranta, bayan ta idar da sallah, addu'oi ta fara jerowa cikin ranta, tare da godewa mahaliccinta, domin tana iya tabbatar da wannan sauyin jini ka iya dawowa alkhairi a wurinta, ta mutu ko tayi rai, duk abin da ya faru cikin biyun nana zatayi farinciki da kowanne.

Gurin ƙarfe biyar da arba'in masu aiki biyu suka shigo gyaran ɗakin kamar yadda Amna ta tsara musu, ba tare da ta fita ba suka gyara komai tsaf, har jikin su na ɗari-ɗari kar suyi laifi. Fitansu da 'yan mintuna wasu kuma suka kawo break fast na alfarma, jera komai su kayi a inda tayi musu nuni sannan suka fice, ita kuma ta je don ba Ammu abincin.

Bayan ta kammala ba Ammu itama ta ci sannan ta shirya, da wuri ta fita zuwa in da motar Shuraim yake tsaya, sai dai a kulle ta ji shi, hakan yasa ta jingina jikin motar tana jiranshi, domin ta ƙagu taji komai daga bakinsa, ya sanar da ita amsoshin tambayoyinta, domin babu abin da take tunani a yanzu fa ce shi.

Drivernta ne ya ƙaraso inda take bayan gaisuwa cikin girmamawa ya ce, "madam ba yanzu zamu tafi bane? Ko inkawo motar nan inda kike?" Idonta na kan hanyar falo ta bashi amsa, "a ah, jeka yau a wannan motar zan tafi" "toh kenan a wannan motar zan tuƙa ki?" Kafin ta bashi amsa wayarta ya fara ruri, numbern Shuraim MR ne ya shigo, "ba na gidan, mu haɗu à company!" Kawai ya faɗi mata bayan ta ɗaga wayar.

Cikin mamaki da maganar sa ta matsa daga jinginen da take, to amma ba da motar nan ya fita ba, juyawa tayi gun driver sannan ta ce, "muje toh".

COMPANY.

Sai dai da mamaki Amna bata kalli Shuraim ba tun bayan zuwan ta company, cikin ɗaurawar kai ta ke tambayar Raheena ko yazo, "a ah ni ban ganshi ba gaskiya" cewar Raheena tana matso da bakinta gun kunnen Amna ta ce, "amma ya naganki a damuwa haka? Ko dai mummunan ya fara tafiya da hankalinki ne?" Ture bakinta Amna tayi ta furta. "Malama ya isheki" murmushi Raheena tayi ta kuma cewa, "afwan mai gidata tuba nake" ta faɗi tana ɗan kama kunne, da murmushi Amna ta wuce office.

Haka har aka tashi babu Shuraim babu labarinsa, tun da tazo bata samu maida hankali a aikin ba, domin tunanin da ke ta yawo a cikin ƙwaƙwalwanta, sai a lokacin ta ji ƙarar massage cikin wayar ta, "a maimakon zuwa exercise mu haɗu à wani wurin mama" abun da ya rubuta mata cikin massage ɗin kenan, tare da sanar da ita wani wurin, wani sabon mamaki ne ya ritsata, don haka ta fice da sauri.

GAƁAR TEKU.

Shine wurin da Shuraim ya sanar da ita su haɗu, da Isanta gurin ta tadda shi tsaye idonsa na kan tekun da yake tsaf kamar babu datti a cikinsa, mutane ɗai-ɗaya ne a wurin domin babu waƴanda suke kusa da su, a hankali ta ida gabanshi, ''barka da isowa'' ya furta mata hakan tare da juyawa in da take yana murrmushi, da mamaki ta fara cewa, "Akan wani dalili ka aikata min hakan? Me yasa ka kawo ni gidan su Safna a matsayinta? Me yasa ka ɓoye gaskiyar kai waye a wurina? Kuma kayi wasa da hankali na? Akan me zaka rusa min babban buri na da nake da shi?" Ta jero masa wa'yannan tambayoyin a jere ba tare da ta sauke numfashi ba.

"Burinki shine gano wanda ya kashe mahaifinki haɗi da yi masa sharri ba?" Ya faɗi bayan ya dawo da dubansa gareta, manyan idanunta ne suka ƙara girma saboda tsabar mamakin da ya ziyarci zuciyarta, idonta cikin na sa cikin muryar tsantsar mamaki tafara magana har bakinta da rawa kaɗan ta ce, "how? ya akayi kasan wannan?!!" Murmushi ya yi sannan ya juya zuwa kujerar da ke gefe da su ya zauna, a mamakance ta bisa tana cigaba da kallonsa, "zauna!" Yayi mata maganar a dake.

Babu musu ta zauna domin bakinta ya kasa sake furta wata kalma, "dole na san wannan domin harda silar sa ne na kawo ki gidansu Safnah" ba tare da ta sake yi masa magana ba ya kuma cewa, "na san duk abun da ya faru da mahaifinki, duk da ba abun mamaki bane domin a gidan radio akasa shi, sai dai sanin sa da mukayi ne yasa muma mu kasan sharri akayi masa, domin mun daɗe muna bibiyarku tun bayan da muka san kina da kaman-cece-niya da Safnah, mahaifinki mutumne mai jajircewa akan aikinsa, domin shi ba gamagarin 'yan jarida ba ne, shi kawai kama mugaye ne yasa a gaba".

Tsayawa da maganar yayi yana buɗe goran jus ɗin da yake a wurin tare da tsiyayawa a glass cups, sannan ya tura mata cup ɗaya gabanta shi kuma ya ɗauki na sa sau biyu sannan ya ijje su yana ɗorawa da faɗin, "wannan ƙungiyar da mahaifinki ya jefa kansa a ciki, ƙungiyace mai haɗari, domin muma munsha aikawa da masu yi mana leƙen asiri, amma aka kashe su" "idan har gaskiya ne abun da ka faɗa, me yasa baku ba mahaifina kariya ba lolacin da ya tsunduma rayuwar sa a haɗari?" Amna tayi masa tambayar zuciyarta na yi mata zafi.

Murmushi ya kuma sakarwa sannan ya ce, "karki manta, duk abun da ya faru da mahaifinki dama zai faru da shi, haka Allah ya nufa" miƙewa Amna tayi cikin zafin zuciya ta ce, "dama haka zaka ce ai! Bayan maganar da ka faɗa mun yanzu, zan iya ɗauka kune silar da na rasa mahaifina! Amma duk da haka, kuka sace min ahalina! ka san irin halin da na shiga da abubuwa guda biyun nan suka same ni? A ah koh? Dama baza ka sani ba, saboda son ranku kawai kuka aikata min, don akan kawai wani muradin ku, akanme zaku rabani da 'yan uwana ku kawo ni wannan gidan!?" Tayi maganar da ƙarfi cikin zarra.

"Ki kwantar da hankalinki, ba wai nufin ki da sharri mukeyi ba Amnah, taimakon mu muke son kiyi, tun bayan rashin Safnah muke neman hanyar da zamu bi don mu dawo dake wannan gidan amma bamu samu hanyar ba, saboda ke mace ce jaruma, barazana bazai taɓa sa ki kiyi mana hakan ba, wannan dalili yasa ni da kaina naje garinku Gombe, hakan kuma yayi daidai da yaɗuwar cutar wannan azzalumin Zabba-ba cikin garin, nine wanda kika tsaida lokacin da abokinku yake cikin ciwon wannan annobar ƙwayar".

"Mee?! Kana nufin kaine wanda ya kai mu asibiti a wancan ranar!? Ta faɗa cikin mamaki sosai, "eh tabbas ni ne, domin lokacin da na ɗauka tare da ku ne ya bamu damar ɗauke familynki, ba kuma don mu cutar da su ba, a ah! Sai dai don muyi amfani da hakan gurin kawo ki gidansu Safna, mun dawo da ke gidan ne domin ki magance mana wata matsala, kasancewar kina kama da ita sosai".

Ran ta ne ya ɓaci a kan duk abubuwan da suka faru, "shikenan na ji duk abun da ka faɗa, gaskiya ko ƙarya MR, a ah kokuma ince Shuraim ɗan ƙasar London! Amma bari kaji wani magana!" Shima Shuraim miƙewa yayi yana kallonta, domin yadda tayi masa maganar ya nuna ranta yayi matuƙar ɓaci.

"Na taimaka muku tsawon lokaci ba tare da nasan ni cuta ta kuke ba, don haka daga yau n'a bar wannan aikin, ku bani ahalina in koma da su, mu cigaba da yin rayuwarmu kamar baya, zamana a matsayin Safnah ya ƙare, bazan ƙara yarda da kai ba!" ta faɗi cikin tabbatarwa da dakewa, "a ah Amnah! Don Allah ki bani haɗin kai mu kammala wannan paputukan da muka fara" ya faɗi mata sigar roƙo, "bazan ƙara yin hakan ba, yau ba sai gobe ba, zan bar gidan su Safna da zama kuma zaku ban ahalina in koma da su gida!!!", tayi maganar cikin ƙaraji.

"Amnah ki fahimceni don Allah, idan har kika tafi a wannan lokacin akwai abubuwan da zamuyi asararsu, da kanki kika ce kin ɗauki Ammu a matsayin mahaifiyar ki, to me yasa zaki tafi ki rabu da ita? Bayan kinsan rayuwarta sake komawa kamar yadda yake a baya zaiy...? "Kar kayi tunanin zaka iya karyar min da zuciya da Ammu! Tun kafin ta sanni take rayuwa, don haka rashina babu abun da zai sa ta, tun da har babu abun da ya sameta wata ɗaya ba tare da kulawa ba".

Ta faɗi tana ɗaukar jakarta da ta ijje akan tebur ɗin tana wucewa. Cikin tashin hankalin abun da take son yi musu ya bita yana faɗin, "Amnah kar kiyi mana haka" ya faɗi tare da shan gabanta, kallonsa tayi cikin ƙarin ɓacin rai sosai sannan ta ce, "ka bani wuri in wuce! Dole yau zanbar wannan aikin muguntan, dama ai kuna da basira sosai, tun da har kuka san komai akaina ni da family na, da farko cewa kayi Safna ta ɓata ko? Nasan kun riga da kun samo ta, don haka ku dawo da ita ta cigaba da abunta, dama ai matsayinta ne koh?" Ta faɗi tana bin gefensa ta wuce.

Taku uku ta tsaya cak, kanta ya girgiza, zuciyarta ya dakata, idonta ya dena zagayawa, jikinta yayi mugun sanyi sakamakon firucin da ya fito daga bakin Shuraim.

'Yan uwa kun dai ji abubuwan da ya faru a wannan part ɗin, to muje zuwa.

Mu kasance a next part don jin yadda za a kaya.

___________________________________________________________________________________________________________

Part 1️⃣1️⃣1️⃣▶️1️⃣1️⃣2️⃣

"Ka bani wuri in wuce! Dole yau zanbar wannan aikin muguntan, dama ai kuna da basira sosai, tun da har kuka san komai akaina ni da family na, da farko cewa kayi Safna ta ɓata ko? Nasan kun riga da kun samo ta, don haka ku dawo da ita ta cigaba da abunta, dama ai matsayinta ne koh?" Ta faɗi tana bin gefensa ta wuce.

Taku uku ta tsaya cak, kanta ya girgiza, zuciyarta ya dakata, idonta ya dena zagayawa, jikinta yayi mugun sanyi sakamakon furucin da ya fito daga bakin Shuraim. "Safnah bazata taɓa dawowa ba! Domin, saboda ta muttu!!!" Shine abun da ya faɗi mata da ƙarfi tare da rintse ido. Tsawon minti biyu Amna batayi motsi ba, domin wannan maganar ta sa ba ƙaramin buganta yayi ba, hatta numfashnta sai da ya kulle, iska mai sanyi sosai da ke kaɗawa a wannan filin ne ya bugeta, sannan ta dawo da numfashinta jikinta, a hankali ta juya inda yake tana kallonsa bakinta cikin nauyi ta furta, "Safnah, Safnah, Safna ta mutu!?"

Ƙarasowa gabanta yayi yana sauke wani numfashin rashin jin daɗi, saboda bai so ya faɗa mata wannan maganar ba, sai da ya ni sa na 'yan sakwanni sannan ya ce, "of course Amnah, Safnah ta rasu! Kuma wannan shine babban dalilin da yasa muka dawo da ke gidansu, yadda Ammu da kuma makomarta zai kasance, tabbas idan ta san 'yarta ta rasu zata iya shiga mummunan hali fiyeda tunani, inda zata yi rayuwa ne cikin ƙunci da rashin madafa" sannan kuma akan mutuwar mahaifinki, ko da bamu kawo ki garin nan ba tabbas binciken da zakiyi zai iya kawo ki, tun da komai a nan ya faru, ki bani dama in sake fayyace miki komai da komai please".

Sauke numfashi a karo na babu adadi tayi, gaba ɗaya jikinta ya mace murus da maganganun MR, idan kuwa haka ne, to ya kamata ta tsaya ya kuma fayyace mata komai, maganar mutuwar Safna ya razanata sosai da sosai, kenan Ammu tana can tana dakon jiran 'yarta ashe dai ta riga da ta tafi inda ba a dawowa? Share hawayen da ke son gangaro mata tayi tun kan ya kai ga saukowa.

Ammu ce kwance ba ta motsi, domin har yanzu jikin na ta baya motsawa, hayewa gado tayi ta zauna gaban Ammu, yayin da Ammun ke binta da kallo ka wai, Amna kuma idanuwanta cike da hawaye sosai, a hankali ta fara magana haɗi da ɗaura hannunta gefen fiskar Ammu, "Ammu ki yafe min don Allah, Wallahi ban san cewa Safna ta rasu ba, sai yau, don Allah kiyi haƙuri, babu yadda zanyi ne dole na faɗa miki" zazzaro idanu Ammu tayi, ta ke suka fara canzawa, jikinta ya hau kyarma har gadon ma na girgiza, hannayenta ne tafara ɗagawa tana jujjuya su kamar ana matse kayan wanki, hankalin Amna ne yayi ƙololuwar tashi, zuciyarta ya tsananta bugu sosai, take ta fara jijjiga Ammu tana kiran sunanta, sai dai jikin Ammu ya riga da ya tsaya cakk babu alamar rai a cikinsa.

Ganin cewa kamar hankalin Amna baya tare da shi ta shige duniyar tunani ne yasa ya fara faɗin, "Amnah, are you with me!" Ya ƙarshe da ɗan ƙara haɗi da ƙyafta mata yatsa kan idonta, a razane ta dawo daga tunanin da take tare da kiran sunan Ammu cikin tashin hankali da razana, "Ammuuh!!" Tayi maganar kamar me shirin fita daga hayyaci, "Kina lafiya kuwa?" Yayi mata tambayar cikin shiga damuwa da yadda tayi, kallonsa tayi tare da haɗe nyawun tashin hankalin da tashiga sanadiyyar Ammu da ta gani a cikin tunaninta, "ba komai!" Ta faɗi kawai, shi kuma ya ce, "to don Allah ki koma ki zauna, muyi magana ta fahimta sosai" Shuraim ya kuma faɗin hakan, kamar bazata motsa ba, sai kuma ta wuce ba tare da ta bashi amsa da baki ba, ijje jakarta tayi tare da matse igiyar jakar da ke cikin yatsunta, tana kallon jakar kawai yayin da zuciyarta ke ta yin mata zullumi iri daban-daban.

Shima dawowa yayi ya zauna tare da sauke ajiyar zuciya haɗi da naɗe hannayensa kan ƙirji yayi murmushin jin daɗi sannan ya ce, "naji daɗi da kika fahimce ni" wani irin kallo ta jefa masa yayin da idonta ke wani suffa daban tana cewa, "ban san me yasa na dawo don in saurareka ba, sai dai na san na ji mutuwar Safna har cikin zuciyata, karkayi tunanin zan rabu da kai akan abubuwan da ka min, ko kuma zan cigaba da wannan aiki, kawai dai so nake ka gama yi min zantukan da kake son furzarwa daga bakin ka, daga nan ni kuma inyi wucewata!".

"Na yarda da duk hukuncin da zaki yanke, amma sai bayan na gama sanar da ke komai sannan ki yanke hukuncin" "wanene kai? Me alaƙar ka da Safna?" Tayi masa tambayar tana cigaba da kallonsa, jan numfashi sosai yayi sannan ya sauke ya fara magana kamar haka, "kamar yadda kika sani ne ni sunana Shuraim, MR kuma shine sunan da nake amfani da shi a ɓoye, duk da na samu wannan Haruffanne da ga M na ƙarshen sunan da kuma R na huɗun harafin sunan. Tambayarki akan wanene ni da kuma me tsakani na da Safnah, zan baki amsa kamar yadda kike so",

Ya faɗi haɗi da sauke hannayensa ya kuma cewa, "ni maraya ne, wanda ke nuna banda uwa kuma banda uba, iyaye na sun rasu abun da na sani kenan, lokacin ina da shekaru huɗu suka bar duniya ta hanyar hatsari, sai dai babu wanda ya riƙe ni, babu wanda ya kula

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login