Showing 30001 words to 33000 words out of 129098 words

Chapter 11 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx

18 Sep 2025

19

karo na biyu, aikuwa sai ji tayi an riƙe mata hannu, wa zata gani Safnan ce kuwa.

ƙara sa ɗayan hannun ta tayi aikuwa Safna ta kuma riƙewa da ɗaya hannun, sakin baki sakaka Hajiya tayi tana son fisge hannun ta amma kamar a ƙarfe ya maƙale, ja takeyi amma Safna ko gezau sai ma ƙara ƙure ta da ido da tayi, yayin da ƙwayar idon ta ke shirin sauya kala.

ƙara zaro ido Hajiya tayi, wannan karon harda tsoro ya cika ta, ganin ƙwayar idon Safna na chanzawa izuwa wani launin, Ammu ma kallon mamaki takewa gudan jinin na ta irin sauyawar da tayi cikin ƙanƙanin lokaci.

Dorinar da aka zuba mata a baya ne yasa ta sakin hannun Hajiya tare da rintse ido da ƙarfi, "shegiyar yarinya mayya kawai, Saleem cimin uban ta, naga alama idon ta yayi ƙwari yanzu, nan gaba duka na ma zata yi" Hajiya ta faɗi wa Saleem da shi ne ya zubawa Safna dorina a baya,

lokacin su Marwan suka ƙaraso wurin jin maganar da tayi da ƙarfi, "Hajiya me sheɗaniyar yarinyar nan tayi miki?" Marwan yayi mata tambayar, sai da ta nuna Safna sannan tace "shegiyar yarinyar nan ni take nunawa iya ka ta yau ɗin nan, saboda wuyar ta ya isa yanka, gata ta zama budurwa ba mai iya taɓa ta yanzu".

Amsan bulalan Marwan yayi ya fara zuba mata a jiki, sai a lokacin ta buɗe idon da ta rintse haɗi da durƙusawa ƙasa tana basu haƙuri, dan ita da kanta bata san abinda tayi ba, sai darawa Ruki take tana mai jin annashuwa a ranta, wanda takeji duk san da akayiwa Safna mugunta, saboda itafa ba ƙaramin tsana tawa yarinyar ba, dalili kuwa shine Hajiya tun lokacin da suke ƙanana ta sanya musu tsana mai ƙarfi tsakanin su da Ammu da kuma 'yarta, kai harma da Mai Daraja kafin ya kwanta dama.

Kuka take sosai tana roƙon Marwan yayi haƙuri amma yaƙi, tun tana durƙushe har ta kwanta a ƙasa, miƙawa Saleem yayi shima ya dasa nasa salon muguntan, hawaye keta zarya kumatun Ammu ba ƙaƙƙauta wa, da ƙyar ta sauka daga kan keken ta tana nufan inda ake jibgar mata 'ya, kuka Ammu take sosai amma ko kaɗan bakin ta baya buɗuwa bare sauti ya fito, "bari ni inwuce ciki, ku tabbatar kun lahanta min ita kan kubar ta, sannan ita wannan nakashashshiyar ita ma in ta ƙaraso kusa da ita ku haɗa da ita, me za'ayi da dangin Mayu"? Hajiya ta faɗi tana wucewa.

Dukan ta sukeyi kota ina ba ƙaƙƙautawa, Ruki ma tana mata na ta hanyar to kari da ƙafa, tun tana roƙon su har bakin ta ya mutu, gurin da shekaran jiya ta bugu ne ya fara fitar da jini sakamakon bulalan daya taɓa wurin, duk da cewa 'yan aikin suna kallon abunda ke wakana amma babu wanda yayi jarumtar zuwa wajen, domin kowanne tsoro yake kar yayo abinda zai sa a kore shi, daga nesa suke aika mata da kallon tausayawa.

Ammu tayi nasarar zuwa kusa da Safna, amma babu tausayi babu tsoron Allah Saleem ya zuba wa Ammu bulalan kamar yadda Hajiya ta basu umarni, wani irin azababbiyar azaba ne ya ziyarci Ammu to dama ga yadda jikin na ta yake, cikin tashin hankali Safna ta zaro ido ganin abinda akayiwa mahaifiyar ta, saidai bata da kuzarin miƙewa, domin jiri-jiri ne ma ke ɗiban ta yanzu.

Yana ƙoƙarin zubawa Ammu na biyu, Yazeed yayi kukan kura ya hankaɗa shi gefe, ya amshe bulalan ya fara zuba mishi, har da Ruki, nan suka fara ƙara, shigowan sa kenan yanzu, dan motar sa ma a waje yayi parking ɗin ta, saboda dawowar gaggawa ne yayi dan ɗaukar wani abun sa, sai kuma ya tadda faruwar hakan.

ƙwace bulalan Marwan yayi, Saleem da Ruki suka yi gefe riƙe da inda ke musu zugi, Marwan yace "kai Yazeed miye haka?" juyawa yayi rai ɓace yace "tambaya na kake ko kuwa ni zan tambaye ka? baku da hankali ne zaku rufe ƙaramar yarinya haka da duka? saboda rashin imani harda wacce take matsayin uwa a gare ku?" Ya faɗi har jikin sa na rawa sabida ɓacin rai.

"Sai dai mahaifiyar ka ba dai tamu ba wallahi kuma ma kasan abinda tayi ne?" Mauji ya kaiwa bakin Ruki tana ƙarasar da zancen, "kai Yazeed enough, ya isa haka" "bai isaba, look your self, kaida yakamata ka hanasu amma harda kai a ciki, baka chanchanci zama babba ba sai dai babban Kobo".

"Ni kake gayawa wannan maganar Yazeed?" "Of course kai, akwai abinda za kayi ne?" Cike da ɓacin rai Marwan yayi kan Yazeed dan yin kokuwa da shi, saboda ya kaisa maƙura da maganar da ya faɗa masa, ƙarar motan Dady ne yasa shi fasawa.

Shi kuwa Yazeed kallon sa ya maida inda Safna take kwance ga Ammu kanta tana kuka da alama ma dai suma tayi, da sauri yayi wurin ta yana jijjiga ta, sai dai jikin ta ya saki, cikin tashin hankali ya sunkuce ta ya nufi waje inda motar shi take, Dady da direba ya buɗe masa ƙofar mota ya fito ya bi Yazeed da kallon tuhuma.

Kafin ya kai ga zuwa gate Baba Hambali ya buɗe masa ƙofar gidan, haɗi da fita buɗe masa na mota, baiyi wata-wata ba ya sa ta cikin motar ya ja ta da mugun gudu ya nufi Hospital da ita.

Tambayar abunda ya faru Dady yayi yana kallon ko wan nen su da fiskar sa tanuna rashin gaskiya a ciki, suma dai sun ɗan tsorata kaɗan ganin sumar da Safna tayi, babu wanda ya amsa masa saima wucewa da su kayi, ba wani abun damuwa bane dan basu tanka masa tambayar ba, saboda akan tarbiyyan hakan suka tashi, wanda shima da kansa ya bada gudummawar sa cikin koyar dasu wannan tarbiyyar.

Kawai sa masu aiki shigar da Ammu ciki yayi da kuma kulawa da ita sannan ya shiga ciki, Ammu ta shiga ɗimuwa sosai da tsoron kardai wani abu ya samu gudan jinin ta, addu'a kawai take ta jerowa a zuciyar ta.

Yana shiga harabar babban Hospital ɗin, ya ɗauke ta ya nufi shiga cikin asibitin da Safna a hannu, da sauri likitoci suka karɓe ta, suka shiga da ita ɗakin bada kulawa, "jiramu a waje" cewar Doctorn da turanci, dan ba Bahaushe bane, "a'a badamuwa ayi komai a gaba na" Cewar Yazeed shima da English.

Allura suka fara yi mata wanda zai taimaka mata gurin rage zogi sannan suka yi mata duk abinda ya dace, yadda ake ƙara wanke mata goshin ta da yake ta zubar jini kamar yau abin ya same ta ne yasa shi rintse ido, ita akewa amma shi yake ji a jiki, shi da kansa baisan dalilin hakan ba.

#Hmmm a wani number kuka sa muguntar Hajiya da 'ya'yan ta?

Ya Hajiya zata ji yayin da labari ya iske ta na Yazeed ya kai Safna Hospital? Bayan duk tsoron da takeyi na karya faɗa kogin soyayyar Safna?

Amma fa nidai Yazeed ya biyani😊

kuma Yazeed ya birgeku?.

______________________________________________________________________________________________

Part 3️⃣3️⃣▶️3️⃣4️⃣

A haka har aka gama mata, bai matsa daga wurin ba har lokacin da ta farka 05:55. "How are you feeling now? da sauƙi? ko akoi wani wurin da ke miki ciwo? kina da buƙatar wani abu?" A jere yayi mata tambayar.

da kallon tsoro kawai take binsa ba tare da tace masa uffan ba, sai sauke ajiyar zuciya take, ya fiskanta hakan shiyasa ya ƙara cema ta, "karkiji tsoro kontar da hankalin ki" ya faɗi yana kama hannun ta tare da cigaba da yi mata kallon tausayawa, ganin yadda fiskar ta yake a kunkumbure.

Saurin ƙwace hannu tayi tana faɗin. "ina Ammu wani abun ya same ta?" "Babu abin da yasame ta, tana lafiya kece abin kulawa yanzu" ya faɗi cikin sassanyar murya wanda bata san yana da shi ba, ganin kallon da yake mata yasa ta sauke kanta ƙasa, nufin kunya da kuma fargaba.

"Please Yaya Yazeed inason komawa Gida" "babu inda zakije sai kinyi one week before Doctor zai sallame ki" saurin ɗagowa tayi tana duban sa jin abinda yace, Lokacin doctor ya shigo ya basu 'yar takarda da kuma wasu magun-guna haɗi da yi musu baya ni akan maganin.

Da ƙyar take taka ƙafafuwan ta, sabida gaba ɗaya jikin ya kumbura kamar wacche tasha yis, kota ina sai yi mata tsami yake, lura da hakan yasa shi ɗaukar ta sama cak, ganin yadda ya haɗe fiska ne yasa ta gimtse bakin ta da take shirin magana.

shigar da ita gaban motar yayi shima yakoma gurin zaman diriver yaja su zuwa Gida, ko atishawa bai shiga tsakanin su ba har isowar su gidan, Baba Hambali ne ya buɗe musu ƙofa jin hon ɗin da yayi, ya tsaida motan ya fito.

a ƙoƙarin ta na buɗe ƙofar dan itama ta fito ne ya katse ta da buɗewa, kallo kawai ta bisa da shi kan ta zuro ƙafan ta ƙasa nan ma ya ɗaga ta, jin abun take wani banbaraƙwai duk da so tayi ya barta ta ƙarisa ciki da kanta kodan gudun idon wasu, amma yadda ya haɗe fiskar sa tamau ne yasa ta yin shiru har suka nufi hanyar falon, duk da a tsorace take kuwa.

Hajiya ce zaune a falo ta kasa ta tsare, ta cika ta ba tse, tana jiran dawowar Yazeed ta sauke masa buhun masifa, tun da shi yace baya gane hannun ka mai sanda.

Gaban ta ne ya bada rassss Miƙewa tayi haɗi da fiddo Ido da kuma sakin baki ga la la, ganin shigowar Yazeed ɗauke da Safna a hannu kamar wanda ya riƙo jaririya, "kai Yazeed!" Hajiya ta kira shi da ƙarfi ganin yana shirin wucewa kamar bai san da zaman ta a falon ba.

Dakatawa yayi tare da juyowa inda take, Safna kuwa tsoro ta shiga sosai dama hakan ne babban abinda take gudu, saboda tasan Hajiya ɓaɓɓalla ta za tayi dama ya aka ƙare bare taga hakan ai sai tayi zaton wani abun daban, "I'm coming Hajiya" shine kawai yace mata yana nufan sashin su Safnan.

Hajiya kuwa bushewa tayi da mamaki, me hakan ke nufi? Shin Yazeed ya shiga komar yarinyar nan ne ko kuwa? Nashiga uku!, shine abinda ta faɗi a ranta haɗi da komawa kan Kujera tana faɗin "inaa! Hakan bazai taɓa faruwa ba cab a ah".

Ganin cewa fa Yazeed shigar da ita ɗakin Ammu zai yi, domin kuwa ɗakin ya dosa yasa ta jin wani abu, taya zai shiga da ita ɗaki ɗauke da ita a hannu kuma Ammu ta gani, hakan yasa ta sakin marayan kuka tana faɗin "dan Allah Yaya Yazeed ka sauke ni, zan taka da ƙafana, dan Allah".

Sauke ta yayi ganin kukan da ta saki domin sam baiji daɗin saukar kukan a zuciyar sa ba, a hankali harta shige ɗakin yayin da shi kuma ya juya dan ɗauko magungunan da aka bata.

Gurin Ammu dake kwance kan Gado tayi a tinanin ta ma bacci Ammun ta ke, sai dai bata sani ba cewa Ammu baza ta iya rintsawa ba batare da taga lafiyar ta ba, tana isa kusa da Ammu, a hankali ta sanya hannun ta kan na mahaifiyar ta, ta yi mamaki jin Ammu ta damƙe mata hannu, kenan ba baccin take ba.

Alamar son ta shi tayiwa Safna, hakan yasa ta taimaka mata gurin tasar da ita, ta zaunar da ita, cike da damuwa take bin gaba ɗaya jikin 'yarta da kallo, ganin damuwa a fiskar Ammu yasa Safna cewa, "na ji sauƙi ammin alluran rage zugi, shiyasa yanzu banajin zafi ko kaɗan, dan haka Ammu na karki damu kan ki kinji".

Ammu bata daina kallon ta ba, sai ma wasu sabbin hawaye dake fitowa daga cikin fararen idon ta, domin kuwa duk da cewa jinyar shekara da shekaru ta keyi bai hana haske da kuma kyawun ta ya disashe ba, "Ammu kuka?" Ta furta cikin shiga matsanancin damuwa, domin kuwa abu mafi girma da yafi sata a damuwa shine taga wani abu ya sami mahaifiyar ta.

"Ammu me yasa ki kuka? Kodai jikin ki na miki ciwo ne? Ɗazu Yaya Saleem ya miki duka ko? Kodai shine yasa miki jiki ciwo?" Tayi mata tambayoyin cike da damuwa tana share mata hawaye da hannu, da ido Ammu tace mata, "a ah 'yata ba babu abinda yasame ni, kece kike fama da raɗaɗin wahalar da kika sha sannu kinji?".

Sauke numfashi mai ɗumi Safna tayi sannan tace "Ammu na ba fa wani abunda nake ji yanzu, dan Allah karki zubar da hawayen ki mai tsada a gare ni kinji?".

Tsayawa kawai yayi yana kallon soyayyar Uwa da 'Ya gwanin ban sha'awa, bai san lokacin da murmushi ya kufce masa ba, hatta fararen haƙorar sa sai da suka bayyana, gyaran murya yayi bayan ya gama kallon su sannan ya shigo, Ijje maganin yayi ya fice batare da ce musu komai ba, da ido suka raka shi.

"Ba shakka! yanzu Yazeed ni zan maka magana amma kaƙi kula ni? Ina ganinka ka shigo da ita a hannu ga ka ɗan iska kome? sannan ka ƙara fita kamar bakasan da kafuwa ta afalon nan ba kai ga ka riƙe da ƙanwar ka Ruki ko? Cemin a kayi ma har jikin ka na rawa lokacin da zaka kaita asibiti me kake nufi ne?".

Cewar Hajiya tana ƙure sa da kallon takaici, amsa ya bata da cewa "Hajiya wai kinsan abinda yarannan sukayi wa yarinyar nan kuwa?" "Na sani domin ni na saka su" "what! Hajiya kefa kika sa su kika ce" ya faɗi haɗi da yi mata kallon mamaki, duk da cewa ya san Hajiya ta matuƙar tsanan yarinyar amma yayi mamaki da tsanan ta kai har zata iya lahan ta ta.

"Ka fita ido na in rufe Yazeed wai me yake damunka ne? To ko dai son Mayyar yarinyar nan kake ne?" "Hajiyaa!" Ya dakatar da ita da ƙarfi yana ƙara cewa, "wai duk wannan na meye kawai fa taimakon ta nayi, kuma kinsan har suma tayi? Da ace banzo ba ƙila da sai dai kiji ance 'ya'yan ki sunyi kisa, taya zaki sawa ranki wannan banzar tinanin wanda ko a mafarki bazai taɓa faruwa ba, please Hajiya karki ƙara yimin irin wannan maganar".

Yana ida maganar ya wuce ɗakin sa yana muzurai, shifa ala dole ammasa maganar da ta ɓata ransa, taya za'a yi masa wannan maganar hauka yake ne da zai fa ɗa soyayya da shashashan yarinyar nan? So suke kawai ya zuba ido idan suna musguna mata kenan?.

Hajiya kuwa taji daɗi a ranta ko ba komai dai ya nuna ɓacin rai dan an dangana shi da Safna "what happen? Naji muryar Yazeed yana ɗaga murya haka? Ya dawo da 'yata ne? Ya jikin na ta?" Dady yayiwa Hajiya tambayar bayan ya sauko daga matattakala.

Sai da ta taɓe baki ba tare da ta bari ya gani ba tace "eh ya dawo da ita" "ok to amma menene yasame ta? yaran nan sunƙi faɗa min" "nima dai bana ce ba, saboda a cikin ɗaki nake" ta bashi amsa, fita daga falon kawai yayi riƙe da wayoyi uku a hannayen sa.

AMNA.

mutane da yawa sun zo ta'aziyya, sai dai yadda labari yake ta yawo ne ya ƙara tayar musu da hankali, inda wasu mutane ke cewa wai mahaifin su dama ɗan shaye-shaye ne ashe, amma yake ta taimakawa jama'a kamar mutumin kirki, sai gashi mutuwar sa ta zo ta wulaƙnci.

Haka ake ta yamaɗiɗi da maganar, duk da ana samun wa'enda basu yarda da zancen ba.

AFTER 40 DAYS.

Haka har akayi sadakan arba'in, amma fa ko fita su Amna su kayi, to sai an samu masu gulma, abin ya dame su sosai, duk da cewa suna iya ƙoƙarin su dan ganin basu sa damuwa a ran su ba, gefe ɗaya kuma Amna ta sa kanta cikin nazari dumu-dumu dan sanin ta ina zata fara? Saboda ba ta jin za ta iya cigaba da jure gulmace-gulmacen mutane a kan su.

Ummee ta umurci da su koma makaranta saboda sun san burin mahaifin su bai wuce yaga suna karatu ba, dan haka su da ge duk da bai wuci shekara ɗaya su gama ba, badon sun so ba suka amince koba komai zasu cika ma mahaifin su burin sa na biyu, bayan na addini da suka gama.

Hatta a makaranta zancen ya kai, dama akace zancen duniya baya ɓuya, babu wanda yake tinkarar su da maganar sai dai suji ƙus-ƙus, domin kuwa babu wanda ya manta da karan battan da akayi tsakanin Amna da kuma su Jalo, su kansu Jalon yanzu indai suka haɗu da su Amna to mutuntaka ne ke raba su.

Duk da cewa jikin Amna da Mubarak yayi sanyi amma su Mamma sukan ƙarfa-fa musu guiwa, hakan yasa suka dage da wannan shekarar gama makaranta, yayin da Amna ta yanke hukuncin sai ta gama sannan tasan abunda za tayi dangane da mutuwar Mahaifin ta, saboda zata fi maida hankali a kai.

SAFNA.

Tun ranar da abinnan ya faru ta daina fitowa da Ammu waje, saidai ta buɗe mata window kawai sai ta kai ta kusa dashi ta shaƙi iskan kawai.

Saukowa Yazeed yayi daga upstair hakan yayi dai-dai da fitowar Safna ma, "ina wuni Yaya Yazeed" bai amsa ba sai nufan kujera da yayi dan yazauna, yaƙi amsa mata ne saboda gani yake in yana kula ta kamar maganar Hajiya ce zai kasance, wato yaba Safna damar raina shi kenan?

Sai dai kuma yaji rashin daɗin kula tan da bai yiba, kan ya ƙarasa mazaunin ya juya ya dube ta, tana tsaye kamar an dasa ta, kan ta ƙasa jikin ta sai ɗaukar mazari yake da mamaki ɗauke a fiskar sa yayi mata tambaya, "what's wrong with you?".

Ɗago ido

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login