Showing 57001 words to 60000 words out of 129098 words
Chapter 20 - AMNA DA SAFNA Book Complete Hausa Novels by Aisha G Umar.docx
ƙoƙarin juyawa dan ganin gaskiyar abinda kunnen ta ya jiye mata hakan yasa ta kusan faɗi, ganin matar na ƙoƙarin faɗi ne yasa Amna saurin zuwa kusa da ita, tana riƙeta ta furta, "bi a hankali madam".
Taimaka mata tayi dan kaita har saman gado, yayin da Ammu ke yi mata wani irin kallo tana hawaye sosai, domin kuwa ciwon dake ranta ne ya tashi, lumshe ido tayi tana zayyano kalaman godiya ga Allah akan dawowar 'yarta da ta fidda rai a sake ganinta, Amna bata lura da matar na hawaye ba har saida ya ɗiga mata a hannu sannan tayi saurin ɗaga kanta kan fiskar matan, "Allah sarki! Ta azi 'yarta Safna ce shiyasa take kuka" ta furta a zuciyar ta afili kuwa tafara rarrashin Ammu tana faɗin.
"Madam baikamata ki rinƙa kuka ba, kiyi haƙuri kiyi shiru, idan ba hakaba kanki ne zaifara yimiki ciwo da fari, daganan kuma yakai saƙo zuwaga ilahirin jikin ki, sai kuma ya haddasa miki wata matsalar a ƙoƙwalwarki, daga ƙarshe yazama idonki bazai lamunci ganin haske ba ko da kaɗan ne, kinga wa'ennan sune matsalar kuka dan haka kiyi shiru babu amfanin sa kinji?" Tayi maganar tana ƙurawa matar ido, Ammu kam kallon mamaki kawai take bin 'yarta dashi, hawayen sun tsaya, bakomai ne ya tsayar dasu ba face mamaki, Madam kuma? ya akayi take zaro zance haka? Ita da tasan 'yarta da miskilanci, koda tana hira da ita amma yadda tayi maganar cikin sauri ya bata mamaki.
Cire zunbulin hijabin ta tayi tana katse tinanin Ammu da Faɗin "Madam a ina tsintsiyan ku yake?" Ganin Ammu bata da niyyan magana yasata dafa Ammu tana ƙara nanatawa, "eh Madam cewa nayi ina tsintsiyar sharanku yake? Ɗakin yayi datti dayawa inason sharewa" ta faɗi a tinanin ta ko Ammu ba ta ji sosai ne, sai kuma shiru Ammu bata ba ta amsa ba, "to ko sai na faɗi da ƙarfi ne? Kuma Inmata dalla-dalla ƙila za tafi gane wa" ta faɗi a ranta tana ƙara yin magana.
"Madam tsintsiya, abun da ake ko re datti dashi, ai kinsan maganar da hausawa ke cewa tsintsiya maɗaurin ki ɗaya koh? To wannan tsintsiyar nake nufi, saboda in gyara ɗakin nan" harda alama takewa Ammu da hannu dan ta gane abinda take nufi, amma har lokacin taga matar batayi wani motsi ba, fa ce ƙura mata ido da tayi, "batayi magana bafa, to ko dai bayan ciwon da take dashi tana da kurumta ne? Inba hakaba duk hanyar da zanbi na bi dan fahimtar da ita abinda nakeson faɗa amma kamar bata fahimce ni bama".
Ta ƙara faɗi cikin zuciyar ta tana kallon Ammu dake ci gaba da yi mata kallon mamaki, miƙewa Amnan tayi dan neman tsintsiyar da kanta, ta duba ko ina cikin ɗakin amma bata ga abu makamancin tsintsiya ba, hakan yasa ta barin ɗakin ta fita dan neman sa, tafiya takeyi ba tareda tasan inane kitchen yake ba, dan ƙila tacan tsintsiyar yake, cikin sa'a taga matar da ta taimaka ta kawota ɗaki ɗazu, saurin zuwa wurin Jummala tayi tana murmushin ya ƙe tace "am Jummala me yakawoki ko kina goge-goge ne?"
Saida Jummala ta ƙara yin mamakin kiran sunanta direct da Safna tayi a karo na biyu bayan ɗazu, koda ɗazun tinani tayi akan ƙila gajiyan hanyanne yasa ta mantawa, amma sai gashi yanzu ta kuma kiran sunan ta haka ba tareda tasa Inna ba, abunda bata taɓa kiranta haka ba a matsayin ta na babbar mata.
#Saida ku 'yan'uwan arziƙi 😊 ga dai Amna ta dawo gidan su Safna a matsayin ta, ya kuke ganin zaman Amna zai kasance a ciki? Kuna ganin Amna zata juri cin kashin da Safna take jurewa kuwa? Ko kuwa zata danne zuciyar ta domin taimakon ahalinta?
______________________________________________________________________________________________
Part 5️⃣9️⃣▶️6️⃣0️⃣
Amsa ta ba Amna da cewa "eh Hajiya ce tace inje in goge gurin cin abinci yayi datti, amma ya naga kinfito ba tare da kin huta ba Safna'u?" "Dama tsintsiya nake nema zan share ɗakin ne yayi datti dayawa, ina tsintsiyan shara yake?" A ƙasa-ƙasa Jummala ta ce, "ba dole yayi d'atti ba, ɗaki da tsawon wata ɗaya baiga shara ba" "me kikace?" Amna ta katseta da faɗin haka "wai so nake nace bari na ɗauko miki" ta bata amsa tanayin hanyar kitchen Amna na biye da ita.
Ɓangaren Hajiya kuwa tun kan ta isa ɗakin ta fara neman numbern ƙawarta, tana isa ko zama batayi ba tayi diling numbern, bugu ɗaya Ladingo ta ɗaga kasancewar wayar na hannunta, kuma ta san Hajiya saita ta da mata hankali idan bata ɗaga da wuri ba, tana ɗaga kiran ta fara magana cikin murmushi "Allah sarki ƙawata kina raina wallahi, yanzu nake tinanin ki nace munyi kwana biyu bamu haɗu ba, so nake gobe ma nazo, bai kamata muke daɗewa bamuga juna ba, shiyasa ma nake tinanin 'yarki Ruki ta auri Huzaifa dan mu ƙarfa-fa zumuncin mu".
Cikin takaici Hajiya ta fara magana "ke dan Allah rabani, bani da hankali ne zan aurawa 'yata ɗan shaye-shayen ɗakin nan? Allah ya tsari buƙui wallahi, ke nifa bama labarin da nakira muyi ba kenan" duk da Ladingo taji rashin daɗin furucin Hajiya a kan ɗanta amma ta ce, "ina jinki faɗamin" "hmm Ladingo ina cikin tashin hankali mara misaltuwa, wai kinsan me idona ya gani kuwa?"
"Taya zansan abinda idonki ya gani bayan bana wurin?" Cewar Ladingo harda harara kamar Hajiya na gabanta, "to Safna dai ta dawo, kuma muna tare da ita yanzu haka cikin gidan nan" "what! Zainab me kike cewa ne? Wai haryanzu baki cire yarinyar nan a zuciyar ki ba da har kike tinanin ta? Wai ko baccin rana kikayi ne har kikayi mafarkin ta?" Cewar Ladingo.
Sai da Hajiya ta ja siririn tsaki sannan ta ce, "kaiya Ladingo ina nuna miki kudu kina ce min ga arewa, Safna ce dai a gidan nan ɗazun nan ta dawo, ba wani mafarkin da nayi, hakan na nufin wannan bokan a ramin kwaɗi ya jefa mu, to wallahi kisan yadda za'ayi ya mai domin da kuɗina, dan bazan yarda aci kuɗina ba'amin aiki ba" Saurin miƙewa Ladingo tayi daga zaunen da take tana zaro ido ta ce, "a'a ƙawata yaushe za'ayi haka? Su fa bokayen nan baki san halin su ba, karsuyi mana kurciya mushiga uku, ƙila wannan ma akasi aka samu, kedai ki jira zuwana gobe dan musan abinda zamuyi, amma irin furuci haka baikama ceki ba"
"Toh shikenan sai kinzo goben" cewar Hajiya, sauke ajiyar zuciya Ladingo tayi haɗi da sauke wayar a kunnen ta, tana faɗin "kaji wai a mayar mata da kuɗi ita gata uwar mammaƙo, ɗan four millions ɗin da ta bada take son a mayar mata, abinda ko sadaka zata iya bayarwa, hmm ni yanzu idan tace dole a mayar mata da kuɗin ai nice a ciki, domin kuwa fifty thousand kawai boka yaci, dole naje insameta gobe dan insan yadda zankau da maganar data faran nan, saboda nasan Zainab" tayi maganar tana komawa kujeran da ta tashi.
HAJIYA ma zaunawa tayi a kujerar dake ɗakin tana maida numfashi kamar wacche tayi gudu tana faɗin, "wai wannan yarinyar wace iriyar mayya ce? Duk wahalan da nayi nafitar da ita a gidan nan amma sai da ta dawo? Kwata-kwata bata wani daɗe ba ma, ƙila dawowa tayi dan ta ƙarisa ni shegiya" ta ja tsaki tana ƙara cewa "to bata isa ba wallahi, ƙarin wahala ne ya dawo da ita kuma zata samu wallahi mayya kawai" sai ta ƙara jan tsaki domin kuwa yau ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba.
AMNA.
Bayan ta gama gyara ɗakin ta shiga tayi wanka, amma bayan ta buɗe walldrop ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba ganin kayan da suke ciki kusan duka atamfofi ne, haka nan ta ɗauki doguwar riga ta shan iska ta sanya, bayan tayi sallar magriba ta fita tabar Ammu dake ƙoƙarin tashi shiga toilet yin alwala, ba tare da ta yafa wani abu a jikin ta ba sai hula da ta saka, wanda da Safna ce kuwa da babu abinda zaisa ta fita haka, kai tsaye kitchen ta nufa dan samun abincin da zata ci, domin bataci da rana ba, tana isa kitchen ɗin taga ma'aikatan girkin suna fita da kuloli a hannun su da sauri.
"Too! Wa'annan kuma ina zasu kai abincin toh?" Tayi tambayar da bata da amsar sa, hakan yasa tabi bayan su dan taga ina zasu kai, tsayawa tayi a gefe tana bin su da kallo yadda suke jera kuloli da kuma plates a kan dogon dining mai ɗaukar mutane goma sha biyu, "wow design dining table ɗin ya haɗu sosai, kenan anan zamu ci abincin, ashe gwara da na biyo su, da acan tsohon ɗakin nan zanci nawa ba tareda sanin nan ba" ta faɗi ƙasan harshen ta.
Suna barin wurin taje ta samu wuri ta zauna, ɗaukan plate ɗaya tayi tare da buɗe kulolin dan ganin a bubuwan da aka sa aciki, duk abinda ta buɗe saita furta sunan shi haɗi da faɗin zai yi daɗi daga jin ƙamshin sa, har ta buɗe tuwon shinkafa gefen sa kuma haɗaɗɗen miyar ɗanyar zogale, sunkuyar da kanta ta tayi kaɗan tana shaƙar ƙamshin sa ta ce, "himmmmmmm harna tuna da abincin Ummee na, shi zanci ma" ta faɗi tana gyra zama ta ɗauki serving spoon ta fara ɗiba.
Tana kammala zubawa ta zauna ta fara afawa da bismillah, tana ci tana santi kawai taji anbuga tebur, saurin juyowa tayi inda taji ƙarar da ganin a wani dalili aka aikata haka, ganin Ruki ce ya sata cewa "ashe kece har kin bani tsoro" ta faɗi dan ita fa ba'a bata wani labarin halin mutanen gidan ba, ita dai kawai matsayin kowa aka faɗa mata, da sauri Ruki ta ƙaraso kusa da ita tana faɗin.
"Mayyar nan ke kuma yaushe kika dawo?" "Mayya kuma?" Amna ta faɗi a zuciyar ta a fili kuwa ta ce, "ai yau ɗinnan na dawo ɗazu" "ah da kyau wato ɗazu kika dawo, kuma kika dawo da wani sabon salo ko? Waye ya baki izinin zama anan har zaki naɗe ƙafa ki ci abinci?" "Toh ashe Safna bata zama a dining, amma ba'a sanar dani ba" Amna ta faɗi a zuciyar ta, "tashi daga nan kanna wanka miki mari!" Cewar Ruki cikin tsawa.
Wanda hakan yasa Amna matse hannun ta dake saman dining table ɗin, dai-dai zuwan Hajiya wurin "me nene wai?" Ta furta tana bin Ruki da kallo don idonta bai kai kan Amna ba, "Hajiya duba banzar yarinyar nan zaune kan dining, saboda samun wuri tusar asuba ta dawo da sabon salo, ni banmasan me yadawo da ita ba" sai lokacin Hajiya ta maida kallon ta inda autar ta ke nuna mata da yatsa, sannan gashi har abinci ta fara ci, sai dai kanta na ƙasa.
Amna kuwa haushi ne keta cikata sunkuyar da kanta tayi dan ta danne zuciyar ta daga ɓacin ran da ke tasowa taji muryar Hajiya na faɗin "tashi ki barnan mayya, kuma wallahi karna ƙara ganin ki anan, idan da aljanu kika dawo ma to nafi ƙarfin su" miƙewa kawai Amna tayi ta bar wurin ta nufi ɗakin Ammu tana fitar da numfashi a hankali, a zuciyar ta tana cewa "su mutanen nan basu da aiki sai furta munanan kalmomi ne? Sunyi sa'a wallahi".
Tana shiga ta gabatar da sallar Isha'i, bayan tayi sallama ta tsaya ganin Ammu dake sallar tun ɗazu a zaune, kallon ta take harta idar, batasan lokacin da taje kusa da Ammu ta riƙe ta ba ganin tana ƙoƙarin tashi amma jikinta na karkarwa, taimaka mata tayi har izuwa gefen gado, "bari insamar miki abinci madam" ta faɗi bayan tinanin hakan yazo mata, cikin sa'a ta tarar da tuwon shinkafa cikin wata ƙaramar kula, sai dai miyar da ke tukunyar yayi sanyi hakan yasa ta kunna gas dan ɗuma-mawa.
Bayan ta kammala ta koma ɗakin, jawo ƙaramin drawern dake gefen gado tayi ta ɗaura abincin akai tana faɗin "ga abincin kici ni zanje inɗan sha iska a waje" saida ta ɗauki burin ƙoilarta kafin ta fice, da kallon tambaya Ammu ta bita, tun ɗazu take ta wa Safna magana da ido amma kamar ba ta fahim ta wai meyasa haka ne? A yau kawai ta ga canji sosai akan 'yarta meyasa? Shin ko ta je ta koyo wasu ɗabi'u ne? Sune tambayar kallon da Ammu tabi Amna dashi matsayin 'yarta.
Bayan Amna ta fita tsakar gidan babu abinda take yi sai bin ko ina da kallo, duk da dare ne amma gurin tamkar rana yake, saboda fitillu masu haske da suke a wurin har da masu canza kala, gurin ba ƙaramin kyau yayi mata ba, gefen garden mai kyau ta nufa tana kallon haɗuwar sa tun kan ta ƙarisa, zama tayi tana lumshe idonta tana maijin iska mai daɗi.
Ta ɗau kusan 15 minutes a haka kafin ta buɗe idon tana jujjuya wayar hannunta, "gani nazo gidan amma ko su kirani suji ya na iso saboda mugunta" ta faɗi tana kallon wayar, "na fara jin barci ma gwara inje insamu inyi barci da wuri, inga kuma gobe da me za'a tashi" tayi maganar bayan ta miƙe daga mazaunin.
Da sallama ta shiga ɗakin amma ta tarar Ammu har tayi bacci, ga abincin kuma bata ci ba, cikin mamaki ta ce, "ikon Allah ta ƙoshi da abincin kenan? Kuma kamar ko taɓa shi bata ma yiba" ta faɗi tana zuwa kusa da Ammu tana gyara mata kwanciya, sannan ta ja mata bargo ta lulluɓe ta, zama tayi gefen gadon tana faɗin, "amma dole incire wannan pale-palen idon roban, saboda bazan iya bacci dashi in makan ce a banza ba" tana faɗi ta miƙe ta shige toilet.
Fitanshi bai ba ta wahala ba, sanya shi a ledan shi tayi sannan ta fito, saida ta nemi Alqur'ani ta karanta kaɗan kafin ta kwanta itama, asuba ta garii safiyar alkhairi.
WASHE GARI.
A kunnen Ammu à kayi kiran sallahr farko kamar kullum, kusan minti biyar ta ɗauka kan ta sauka daga kan gadon, haka har tayi nasarar zuwa bayan gida, sai dai tayi mamakin rashin tashin Safna domin kuwa wani lokaci ita take tashin ta ma, ta kuma taimaka mata gurin yin alwalar, amma abinda yasa batayi yunƙurin taɓa ta ba saboda atinanin ta ko gajiyan hanya ne tattare da ita.
Sai lokacin da ake kiran sallar asuba sannan Amna ta tashi, kallon Ammu dake zaune takeyi ganin ta tashi da wuri, bayan tayi alwala ta gabatar da sallah gefen Ammu tana idarwa ta kuma hayewa gado ta ɗaura inda ta tsaya, gurin ƙarfe bakwai ta tashi sakamakon yunwar da ke nuƙurƙusan cikinta, domin jiya ba wani cima mai kyau tayi ba.
A zaune kan kujera taga Ammu, sai da ta zazzagaya da idonta ɗakin ko zata ga abu mai kama da abinci amma wayam, sai da ta sauka a kan gadon, ta shiga toilet ta watsa ruwa ta kuma maida alamomin da suke maida ta tamkar Safna sannan ta fito, sai da ta durƙusa kusa da Ammu ta ce, "Madam kin tashi lafiya? Ɗazu ban gaishe kiba saboda baki idar da sallah da wuri ba, nace ankawo mana break fast ne?", haryanzu kallon ta kawai Ammu take ba tare da ta amsa mata ba.
"Inaga basu kawo ba ko? Bari ni inje inɗauko mana" tana faɗi ta fice tana nufan kitchen, ta tarar da masu dafa abinci tayi suna shishshirya abinci, ƙarasawa gurinsu tayi tana faɗin, "ina abincin mu yake?" "Kamarya abincin ku dama ke mukewa girki ne?" Cewar Hanne ta nayiwa Amna kallon rainin wayo, da sauri Amna ta ƙarisa inda Hanne take ta fincikota cikin ɓacin rai tana faɗin "keh ki kiyayeni wallahi! Ban miki kama da wacce zaki jefawa maganar banza ba" ta faɗi tana ƙara yi mata damƙa da hannu.
Jin zafin da taji a riƙon da Amna tayi mata ne ya sata cewa "hannuna zafi ki sakarmin" gaba ɗaya masu aikin barin abinda suke sukayi suna kallon su, da ganin Safna a irin yanayin da bata taɓa yi ba, ganin duka kallon ta suke har da ita kanta Hannen ga ya mutsa fiska da tayi alamar zafi hannun ke mata, hakan yasa Amna sakin mata hannun da sauri ta juya tana buɗe kulolin dake wurin.
Tana ganin abincin da yayi mata ta ɗauki kula ɗaya da plate da cokali ta wuce ba tare da tace musu komai ba, "kai ta ɗauka fa" cewar Hanne tana ƙoƙarin bin Amna ta karɓo, "ke! Hanne me kikeyi haka?" Faɗin matar da ta ɗan girmesu Asabe, Hanne ta ce "Asabe yanzu me za mucewa Hajiya? Kin santa dai".
#Hmm nifa inaganin da ƙyar Amna ta jure wasu abubuwan fa.
Amma kuna ganin Ammu zata gane ba 'yarta Safna bace kuwa?
______________________________________________________________________________________________
Part 6️⃣1️⃣▶️6️⃣2️⃣
"Nasan Hajiya amma idan muka sanar da ita abinda ya faru anan to mu zata rufe da faɗa, dan haka muyi shiru kawai" cewar Asabe, haka dai suka tashi dan kaiwa su Hajiya break fast.
Tana isa ɗakin ta zubawa Ammu abincin ta a plate, yauma ƙara ja wo ƙaramin drawer tayi ta ɗaurarawa Ammu a kai ita kuma ta zauna akan carpet tana cin na ta, saida ta cinye kafin ta miƙe, zuwa kusa da Ammu tayi ta na ganin yadda take ƙoƙarin ɗaukar cokali amma yaƙi ɗaukuwa hakan yasata zuwa kusa da Ammun, jawo ɗayan drawern tayi ta zauna dap da ita tana faɗin "Madam ba kya iya cin abinci da kanki ne? Ko shiyasa jiya baki ci ba?".
Ganin kamar koda yaushe da ido kawai Ammu